Showing 24001 words to 27000 words out of 268471 words

Chapter 9 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

think he is, da driving din da
yake yi ake biyansa yake takama ko me? Waye shi yana matsayin just driver xai kulle
mota yana jin ana kwankwasawa ya ki budewa, kuma ba wai bai gan ni bane" Nihad tace
"Ai ban ta6a ganin mutum me karfin hali irin yaron nan ba" Aliyu yace "Look Nihad
idan kika shiga school gobe xa mu hadu, i can't stand here any longer, mood dina ya
baci seriously, ba a ta6a ci min fuska irin yau ba" Nihad tayi shiru tana kallonsa
duk jikinta yayi sanyi, don kana ganinsa kasan ransa yayi mugun baci da gaske,
tafiya ya fara yi kawai ya koma gun motarsa ya shiga ya tada yayi zoom off, da ido
khalil ya bi sa har ya hau saman titi, Nihad ta dinga kallon motar tana jin kamar
ta rushe da kuka ko xata ji sauki a ranta, mutumin da tayi wata da watanni bata
gani ba, shine wannan drivern xai 6ata ma rai har ya tafi?? Ta fi minti biyu tsaye
kawai kallon motar take with different thought running her mind ga wani kullutu da
ya tokareta a makogwaro sbda bakin ciki da takaici, a duk abubuwan da yake mata
bata jin akwai wanda ya mata ciwo ya ta6a har karshen xuciyarta irin wannan, she is
trying her best not to cry, don har idonta ya cicciko, kiris ya rage ta fashe da
kuka a wajen, Khalil dake ta kallon duk expression da reaction dinta ya shafa
kansa, sai kuma ya sauke both glasses yace "Naga kamar kin fasa siyayyan, kuma ga
hadari, ni kuma bana tuki cikin ruwa ko in baki makullin in yi tafiyata??" Wani
matsiyacin shegen kallo tayi masa, ta bude back seat ta shige motar ta kulle da
karfi tana kara danne kukan dake cin ta, tada motar yayi, yayi reverse ya dau
hanyar gida, har suka isa gida Nihad danna kukanta take, bayan yayi parking ta bude
motar ta sauka ta tafi gun driver seat ta tsaya tana nunasa da yatsa tana huci tace
"Sai kayi da ka sanin abinda kayi min yau wllh, kuma ni ce sanadin barin ka gidan
nan, banza mahaukaci kawai talaka" Kashe motar yayi ya sauka yana kallonta ya kara
mata kunne gaba yace "Kamar kina magana?" Da wani bakin ciki ya mamayeta bata san
sanda ta cakumo kwalarsa ba duk da uban tsayinsa tsaurin idonta bai sa taga hakan
ba, tana jijjigasa da duk karfinta hade da kunduma masa wani mummunan zagi, mai
gadi dake ganin komai ya karaso da gudu jikinsa na bari yana cewa "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un, Subhanallahi... " Khalil dai kallonta kawai yake baya ko
kiftawa, cikin nutsuwa yace "Cika ni" Ta buga wani uban tsawa tana dungure masa
goshi tace "An ki a cika ka din, kayi uban da xaka yi in ga, kai har ka isa kana
aiki ฦ™arฦ™ashinmu kana matsayin Drivern gidanmu ka dinga kawo min raini? Ni ce ma
zaka raina? Kasan wa ka walakanta daxu?? To wllh ko kaff zuri'arka xa a siyar idan
har Aliyu ya daureka kudin da aka siyesu bai isa yayi bailing dinka ba" Nihal ta
fito cikin gida da kawarta xata mata rakiya ganin abinda ke faruwa ta karaso da
sauri xata ta janye Nihad tace "Nihad what's this u are doing, don't u have
manners? Meye wannan kike yi?" Nihad na huci ta bangajeta a fusace tace "Eh ban da
shi, sai ki ara min naki ke me shi, a kan matsiyacin nan xaki ce min bani da
manner, kin san abinda yayi min ne?" Nihal na kallon Khalil cike da damuwa tace
"Don Allah kayi hakuri" Yana warware rigarsa da Nihad ta cakuikuye yace "Ba
komai... fita xa ki yi ne?" Nihal dai duk jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai,
yace "Ko ba fita xa ki yi ba?" tace "Aa Kawata xan raka bakin titi" ya kalli
kawartata dake tsaye ita ma tana kallon abun mamaki, yace "Ohk to, ta hau sai na
ajiyeta a gida, xan jira ta a waje...." Yana fadin haka ya koma motar ya tada ya
bar wajen, mai gadi ya tafi da sauri ya bude gate, Nihad bata san sanda ta fashe
da kuka ba, da hanzari ta shige cikin gida tana kuka sosai. Bayan ta ci kukanta me
isarta ta dau wayarta ta kira Aliyu, har ya katse bai daga ba, ta kuma kiransa nan
ma no response, hawaye ne ya dinga sauka idonta, bayan kusan awa daya ta mike ta
gyara idonta ta fita, bangaren Mumy ta tafi sai taga kamar tana da bakuwa, hakan ya
sa ta bar wajen ta tafi gun Umma, Umma tace "Lafiya me ya sami idonki Nihad?" Cikin
rawan murya tace "Umma Aliyu ne ya dawo shine muka yi da shi xa mu hadu a wellcare,
bayan mun hadu sai ya sauko daga motarsa yace bari su gaisa da driver ai ko in gaya
maki mutumin nan yayi masa walakanci mafi muni, ya kulle motar ya kuma ki ya sauke
glass, banda Abba da ya ja mana ina Driver xai ma tsaya same place inda nake balle
Aliyu? Yasan waye uban Aliyu a kasar nan, kaskantar da kansa fa yayi ya tafi su
gaisa maimakon shi drivern ya sauko ya taho har inda yake ya gaishesa amma ya masa
wannan mugun walakancin" Umma dai sakin baki tayi tana kallon Nihad, can tayi kasa
da murya tace "Wai har yanzu kuna tare da Aliyun nan ne dama?" Nihad ta gyada mata
kai tana matsar kwalla, Umma tace "Ba kince min kun rabu ba kwanaki?" Nihad tace
"We came back together 1 month ago" Umma tace "Ke dai bakya ji Nihad nace ki fita
harkan yaron nan, ba mutunci ne da familynsu ba kin ki, nace ki rabu da shi in kina
son sama ma kanki mutunci kina son ki tsira da mutuncin ki, ina ke ina Aliyu banda
dai yaudaran kai Nihad? Kika san wasu irin yan mata yake hulda da? 'ya yan shugaban
kasa yake hulda da fa" Nihad taki cewa, Umma tace "Gaskiya kar ki sake kulasa ni
dai na gaya maki, yana son ki ne ko sau daya bai ta6a takowa ya xo gidanku ba? Sai
dai soyayya a titi da makaranta, kema kinsan yaudaran kanki kike don Aliyu ya fi
karfin ki, me ma xai kawosa gidan nan? waye ubanki a inda ubansa yake, inaa ai
nisan ma yayi yawa, balle ma duk yan iska ne yaran masu kudin nan wa enda idonsu ya
yage har kunne, banda lalata yara da bata masu rayuwa babu abinda suke" Nihad still
ta ki cewa komai, Umma tace "Kin min alkawarin xa ki rabu da shi kiyi blocking
dinsa kamar yanda kika yi blocking din Ahmad yanxu?" Nihad ta turo baki tace "Ni
dai ina sonsa Umma, shi ma kuma yana so na ai, da baya so na baxai dinga kirana ba
har yace mu hadu a wani waje, dama ce maki xanyi xan je gidansu Baffa ko da Mumy ta
tambayeni" Daga haka tayi ficewarta daga parlon Umma ta bi ta da ido ko kiftawa
babu, Nihad na sauka downstairs ta fito compound, fuskar nan nata a murtuke ta nufi
gate, mai gadi dai ya kauda kai da sauri don tare suke da Khalil, shi dai ya rasa
kan wannan abinda ke faruwa tsakaninta da Khalil, yana mugun ganin karfin halin
Khalil da baya nuna shakkarta kamar su, har ta fita gate ta dawo tana kallon mai
gadi fuskar nan nata babu rahama tace "Kai in ji dai kuna kula min da tsuntsaye na?
Don idan har wani abu ya samesu wllh kaf gidan nan duk sai kun raina kanku ban cire
kowa ba kuma" Da ladabi yace "Ko daxu sai da naje can da kaina Hajiya" Ficewa tayi
daga gate din bayan ta maka ma khalil da bai ma san tana yi ba harara, Mai gadi ya
kalli khalil yace "Sai fargaba nake kar tace xaka kai ta wani waje" Khalil yayi
murmushi yace "Meye a ciki, sai a kai ta ai..." Da yake babu wani nisa da kafa
Nihad ta bi ta cikin anguwanni har ta isa gidan yayan Abbanta, Hamid na xaune
compound tare da wani abokinsa, kallo daya tayi masu ta kara gaba abunta, Abokin
nasa yace "Wannan ba cousin din nan taka bace, naga ta wuce bata ce maka komai ba,
and kamar kuna good time da ita ai" Hamid yace "Noo, step sisters dinta ne muke
good time, wannan ai yar iska ce" Abokin yace "Shit but sun yi kama sosai, kamar
har ya wuce misali" Hamid yace "Toh wannan da kake gani ji take da girman kai da
rainin wayo, sannan runz girl ce..." Abokin ya wara ido yace "Waow dai dai mu
kenan, ka hadu mu to" Hamid ya masa wani shegen kallo yace "Ai da manyan mata ake
runz ba kwailaye ba, kwailar ma fitsararriya irin wannan" Tuni Nihad ta shige
gidan, direct part din Kakarta ta nufa, tana bude kofar dakin ta shiga, inna tace
"Aa, daga ina haka, Ibrahim din ya shigo ne" Nihad tace "Ni kadai ce" Inna tace "Aa
naga sai ya taso keyarki kike xuwa shi sa abun ya daure min kai, ina ce tare ku ke"
Nihad ta nemi waje ta xauna, Inna tace "Baki da lafiya ne?" Nihad ta fashe da kuka
kamar jira take tace "Inna wani sabon driver Abba ya dauka, yaron ba shi da kunya
ya raina ni inna, ba irin rashin mutuncin da baya min" Inna da ta saki baki tace
"Shi Dreban?" Nihad ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Inna tace "Ko ba
wani gansameme ba yana tafiya gansan gansan?" Nihad tace "Shi" Inna tace "Toh ai
Ibrahim din ya kawo sa har nan ya gaisheni, amma ni na xata ษ—an arxiki ne, don har
kasa ya duka ya gaida ni" Nihad tace "Wllh na munafurci ne...." Nan ta labarta ma
inna abinda ya faru kamar yanda ta gaya ma Umma, Inna tace "Ba lafiya, shi
dreban??"




โœ๐Ÿป
07087865788

๐Ÿ’–๐Ÿ’– *NIHAAD*๐Ÿ’–๐Ÿ’–




โœ๐Ÿป
By _Khaleesat Haiydar_



9.....


Nihad na shesshekan kuka tace "Wllh shi inna, kawai an bar sa yana ta abinda ya ga
dama a gidan kamar gidan ubansa, duk ya gama rena ni, ko gaisuwa bata hadani da
shi" Inna tace "Duk ba wannan ba, yanxu kin kira Aliyun??" Nihad ta daura kanta
gefen gadon inna hawaye na sauka idonta tace "Bayan ya ki dagawa" Inna ta dauko
wayarta ta mika mata tace "Kirasa da nawa" Nihad tace "Ae idan ba shi da numberka
baxa ka iya samunsa ba, ya sa layinsa a Private" Inna tace "Wai ko ba dai Aliyu
ษ—'an wajen janaral Habubakar jikamshi ba?" A hankali Nihad tace "Shi..." Inna tace
"To wannan dreba duk yanda aka yi tsinanne ne, ko don nace masa ya saki jikinsa
yasa ya sake kamar gidan ubansa? to ai ni na xata yaron arxiki ne" Salati inna ta
saki tayi tagumi tace "Yau naga dreban jaraba, ashe duk ni na ja komai da nace ya
saki jikinsa, to a kira min Ibrahim din tun yamma bai yi ba ya sallamesa" Nihad ta
dau wayar inna da sauri ta fara neman number Abba tayi dialing, Inna ta bude baki
ta rike ha6a tace "To shi kuma Aliyun banda abunsa garin yaya xai ce sai yayi ma
dreba magana mutumin da ba ajinsa ba, ai abinda bai sani ba talakawan nan haka suke
da dacin rai kamar mutum ne ya doro masu talaucin, ina shi ina wani basamuden buzun
dreba can? To ko a almajiri dai baxa su yarda su ajiye wannan mutumi a gidansu ba
balle dreba, su da tun daga titin da ya yanka unguwarsu xaka fara ganin dirka
dirkan sojoji har da motocinsu...." Nihad ta turo baki tace "Abba bai daga ba" Inna
tace "Ina xai daga, ya tashi ya kawo wani kato gansameme kamar mutanen farko ya dau
mota ya basa, ni wllh ranan da na fara ganinsa sai da na tsure, sai fa ya daga
mutum ya nanasa da kasa sau biyar bai gaji ba, irinsu ai gadin dogon banki ya
kamata a basu ba wai motar mutane ba" Nihad dai tayi tagumi don abinda ya dameta
daban, ita yanxu ta ya xata fara shawo kan Aliyu, da yaya ma suka dawo soyayyar,
Inna tace "To ko kin san inda ya sauka ki rakani mu je in basa hakuri" Nihad ta
kalleta tace "Ji ki kuma, kawai don ki ja min raini?" Inna tace "Wani raini mutumi
na nema ya kubuce, wa ke ta wani raini Nihad, idan ma baxa ki shiga ba ni ki rakani
ki nuna min hanya in je in samesa" Nihad tace "Aa ke dai kawai duk yanda xa kiyi
kiyi Abba ya kori driver din nan kawai" Inna tace "Yo sai ma kin fada, abu har ya
kai yana korar ma jikokina samari" Hamid ne ya bude kofar dakin ya shiga yana
kallon Nihad yace "Ke don uwarki ni sa'anki ne xaki wuce ni da abokina baki
gaishemu ba" Nihad ta turo baki ta koma gefen Inna, Inna dai bata ce komai ba, Yace
"Mahaukaciya kawai, uban wa xaki dinga daga ma kai?" A fusace Nihad tace "Kina dai
gani babu abinda na masa ya xo ya fara xagina ko inna, ni fa shi yasa bana son xuwa
gidan nan wllh, kowa yaje yaji da mugun halinsa" Cikin xafin nama ya nufeta, Inna
ta mike ta wangale hannu tana tare Nihad tace "Dokeni to, Hamidu nace ka dokeni"
Huci yake yana kallonta, Inna tace "Ai dama ka saba dukan nawa yanxun ma ka duka,
ranan da ka biyo Bilkisu ai ni ka jibga ba ita ba" Nihad ko kallonsa bata yarda ta
sake yi ba, Yayi wani kwafa ya fice daga dakin, Inna ta kulle dakinta tace "Kinsan
korosa aka yi daga can kasar wajen wai wa'adinsa ya kare a can, to kuma sai kayi ta
hucewa kan ya yan mutane" Nihad bata san lkcn da ta kyalkyale da dariya ba, Inna
tace "Allah haka uban yace min, duk a booth din jirgi aka kwaso su aka dawo" Nihad
dai bata ce komai ba, Inna tace "Yanxu ko kin boye number ki baxai daga wayar ba?"
Nihad ta mike tace "Ni dai xan tafi inna dama anjima da daddare kice Hamid din ya
kawoki nan gidanmu ki samu Abba da kanki" Inna tace "Toh shkkn ma, kawai bari inje
in riskesa a gidan ba sai mun yi waya ba, idan ma ya kama ko shi sai ya kira Aliyun
ya basa hakuri" Bude baki Nihad tayi, can ta kyabe bakin tace "Ni dai sai kin zo"
Daga haka ta fita daga dakin, A bakin gate abokin Hamid ya tare ta da ya faki idon
Hamid ya biyota, yana fara magana ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tana
yatsine fuska tace "Ina wasa da kai ne malam?" Daga haka ta ja tsaki tayi ficewarta
daga gate din, ya bi ta da kallo baki bude, dama Hamid ya gaya masa ya ki ji. Nihad
na komawa anguwansu ta yi ido hudu da Khalil dake xaune kan dakali a kofar gida
wayarsa na kare kunnensa, yana ganinta bai sake cewa komai ba a wayar da yake kuma
bai cire wayar a kunnensa ba, har ta isa dai dai inda yake, tayi masa wani harara
ta ja tsaki ta shige cikin gida tayi banging gate din. Abba na tsaye balcony bayan
magrib Khalil ya karaso da ladabi yana kallonsa yace "Gani Alhaji" Abba yace "Yauwa
pharmacy xan aikeka ka siyo min magani yanxu" Khalil yace "Toh, ya sunan maganin?"
Abba na duba wayarsa yace "Yanxu likitana ya turo min ta message bari dai in duba"
Abba na shiga message din har ya fara pronouncing sunan maganin kawai ya fasa kar
khalil yaje ya masa shirme, yace "Bari kawai xan rubuta maka a takarda kaje ka
siyo, idan ka siyo sai...." Abba ya dakata ganin mai gadi na bude gate, sai ga
motar Hamid ya shigo compound din, Abba yace "Je ka xan rubuta sunan maganin a kawo
maka yanxu" Yace "Toh Alhaji" daga haka ya nufi boys quarters, Inna ce ta sauka
daga motar ta nufo balcony, Abba dai na tsaye yana ta tunanin ko lafiya, Tana isowa
ganin yanayinta yace "Lafiya inna?" Tace "Ina fa lafiya, mu je parlor baxan iya
tsayuwa ba" Sai da ta fara shiga parlon Abba ya bi ta, kanta tsaye ta tafi parlonsa
duk yana biye da ita, ta nemi waje ta xauna shi ma ya xauna yace "Ina yini Inna?"
Tace "Ibrahim a ina ka samo wannan gansamemen dreban naka?" Abba yace "Wani abu ya
faru ne?" Tace "Meye baxai faru ba, ya kora ma Nihad saurayi, d'an wajen Janaral
Jikamshi, har yaron ya goge numberta yanxu haka da nake maka magana" Abba yayi
shirui yana kallonta as if confused don ya kasa fahimtar xancen nata, Inna tace "A
kara min Ac, xafi ya isheni" Abba ya dau remote ya kunna Ac din, yace "Ban fahimta
ba Inna" Nan inna ta xauna tayi ma Abba tsari da abinda Nihad ta fada mata da ma
wanda bata fada mata ba duk ta dire ma Abba, Abba yace "Ikon Allah, ke yanxu wa ya
sanar maki wannan?" Inna tace "Har gida ta sameni tana kuka kamar ranta xai fita,
hankalina yayi mugun tashi shine nace da kaina xan taho da daddaren nan, sannan a
kira min dreban in ji uban da ya aikosa wajenmu, ni dama ina ganinsa na sha jinin
jikina ban yarda da shi ba kawai nayi shiru ne, wa yasan adadin binne binnen da
yayi maka a gidan nan yanxu? Huhuhu kana wasa da buzun mutum, Ai irinsu xuwa suke
su tarwatse gida kai har ma su talauce mai gidan su saci abinda xa su sata su gudu
su koma Nijar, to Ibrahim ko motar nan ma ya gudu maka da shi ai ya cuceka, to
yanxu ni dai a kira min shi ko in tafi in samesa da kaina" Abba yace "Aa ba sai kin
samesa ba, ai sallamarsa kawai xanyi ya tafi ba sai anyi wani tashin tashina ba"
Inna tace "Aa ko xagi ne a bari in masa kafin ya tafi ai" Abba yace "Ke dai nace ki
bar komai a hannuna, bari Hamid ya xo ya maida ki gida dare yayi" Tace "Ai
Habubakar ne ya sa ya kawoni banda haka waye ubana Hamid xai kawoni, tun fa da aka
korosa daga kasar wajen yake jin haushin kowa, to ni nasan sanda ya koma can da
xama balle sanda aka korosa, kawai gani nayi ya dawo da manyan jakunkuna, ji yake
kamar duk ya kashe mu yanxu haka" Abba yace "Ke wa yace maki an korosa, don Allah
ki bar fadin wnn magana a xata da gaske ne" Mikewa yayi ya fita daga parlon ya kira
Hamid dake main parlor yace "Zo ka maida Hajiya gida" Yace "Toh Abba" Har mota ya
rakata, bata ce xata shiga wajen matansa ba shi ma bai ce ta shiga ba, don da suka
fito parlor ma yace Nihal ta kirasu su gaisheta ta hana, yana tsaye compound din
har motar ta fita, yana kallon mai gadi dake kulle gate yace "Kai ina Ibrahim?"
Aminu bai kai ga bada amsa ba sai ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login