Showing 66001 words to 69000 words out of 268471 words

Chapter 23 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

Nihad tace "Toh, Umma su Husnah ne ke son xuwa kuma ni ban san
address din nan ba" Umma tace "Gaskiya baxa ki sani ba, kinsan me xai faru?" Nihad
tace "Aa" Umma tace "Kice kawai su taho nan gida sai su biyo Amina tunda ita ta san
gidan" Nihad tace "Toh Umma" daga haka Nihad tayi mata sallama ta katse wayar, ta
kira Husnah ta sanar mata yanda suka yi da Umma, Husnah tace "Hakan ma yafi sauki
wllh, turo min number Aminar" Nihad tace "Toh, amma kar ki kira layin nan na kanwar
Mumy ce" Husnah tace "Toh shkkn, kawai sai mun zo anjiman" Nihad tace "Toh" Daga
haka ta katse wayar, tayi deleting duk calls din da tayi ta goge message da tayi ma
Husnah na number Amina, sannan ta mayar da wayar cikin jakar. Bayan la'asar Aunty
Jamila ta gama girka shinkafa da miyan, A plate ta xubo ma Nihad ta fito parlor
tana kallon khalil tace "Ga can abincin an gama" Yace "Toh sannu da aiki Aunty, Mun
gode" Dakin Nihad ta wuce ta ajiye abincin a kasa, Nihad ta fito daga bandaki daure
da towel, ta xauna gefen gado tana kallon Aunty Jamila tace "Sannu da aiki Aunty"
Aunty Jamila tace "Yauwa sannu, kiyi maza ki ci abincin" Nihad tace "Toh nagode"
nan ko ta rasa ta yanda xata tambayeta yaushe xata tafi don bata son su Husnah su
zo tana gidan nan, ganin bata da niyyar tashi Aunty Jamila tace "Toh tashi ki fiddo
kayan da xa ki sa mana" Nihad ta mike ta bude jakar ta dauko riga da skirt, bayan
ta shafa mai ta sa turare sannan ta sa kayan, Aunty Jamila ta dauko abincin ta mika
mata, amsa tayi ta fara ci, gaba daya taji bakinta babu dadi tura abincin kawai
take, Aunty Jamila ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah,
tana idar da sallah tace "Aunty ke baxa ki ci abincin ba?" Aunty Jamila tace "Aa na
ci abinci kan in fito gida" Nihad bata kuma cewa komai ba, Aunty Jamila tace "Toh
ni xan tafi Nihad" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve don abinda take ta jiran
ji kenan ganin hudu da rabi yayi tasan kilan ma su Husnah na hanya yanxu, Aunty
jamila tace "Ki bude kunnenki ki saurare abubuwan da xan gaya maki da kyau" Nihad
ta sauke idonta a hankali tace "Ina ji Aunty" Aunty Jamila tace "Ki nutsu ki dawo
hankalinki, kinga wancan mutumin dake parlor??" Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci
daya har hawaye ya cika idonta tun bata ji abinda xata ce ba, Aunty Jamila tace
"Toh mijinki ne shi yanzu...." Nihad ta rushe da kuka tace "Don Allah Aunty ki
daina cewa haka, wayyo ni a daina ce min haka gaskiya" Aunty jamila tace "Ba
shakka, to rufeni da duka sai in daina ce maki haka, ke ba taimakonki yayi ba da ya
rufa maki asiri ya aureki?" Kuka kawai Nihad take, Aunty Jamila tace "Toh wllh idan
ba fushin Ubangiji kike son ja ma kanki ba ki bi mijinki kiyi masa biyayya ki zauna
lafiya a duniya, naga kamar baki saduda ba har yanzu baki dau darasi daga abinda ya
sameki ba, ni iyakar abinda xan gaya maki kenan idan kin ji yayi maki amfani idan
kika yi watsi da shi kuwa kuka bai kare maki ba a duniya" Daga haka Aunty Jamila ta
mike ta dau mayafinta ta yafa, ta dau handbag dinta, kuka kawai Nihad take ganin ta
nufi kofa sai kuma ta mike ta bi bayanta cikin rawar murya tace "Toh Aunty karatuna
fa?" Aunty Jamila ta juyo ta kalleta tace "Wannan kuma sai ki tuntubi mijinki ki
ji, mu kam ai bamu da iko da wannan, in ya amince sai ki ci gaba" Nihad na girgiza
kai tace "Aunty don Allah kice masa ran monda xan tafi makaranta ni dai" Aunty
Jamila tace "Ohk ni ce ma xan gaya masa, ashe shkkn iyakar karatunki kenan a duniya
in har ni xan gaya masa" Fita Aunty Jamila tayi daga dakin tayi ma Khalil sallama a
parlor, ya mike yace "Aunty har za ki koma" Tace "Ehh wllh na bar yara a gida" Yace
"Toh bari in ajiye ki" Tace "Aa da kayi zamanka kawai Nagode, ina fita xan samu
adaidaita sahu" Yace "Aa bakomai, xan ajiye ki yanxu" daga haka ya dau makullin
mota ya fita, sai taji dadin yanda ya karramata sosai, kuma ko ba komai xata samu
enough chance tayi masa magana a mota a kan Nihad, Nihad ta bi sa da wani harara,
Aunty Jamila ta kalleta bayan ya fita tace "Wa kike harara Nihad?" Kin cewa komai
Nihad tayi, Aunty jamila tace "To ki sani yau shine ganina na karshe da xaki yi a
gidanki, indai baxa ki kwantar da kai ki zauna lafiya da mijinki ba" Nihad ta fashe
da kuka har da bubbuga kafa tace "Ni Aunty ki daina ce masa mijina don Allah, wayyo
Allahna na shiga uku" Kofa Aunty jamila ta nufa ta fice daga parlon, sai da suka
fita daga gidan Nihad ta koma dakinta tana share idonta, Allah ya kiyaye wannan ya
zama personal driver dinta balle kuma wai miji, suna fita ko minti goma ba ayi ba
taji ana kwankwasa gate, da sauri ta mike ta fice daga dakin ta tafi compound don
ta san su Husnah ne suka iso, tana isa gate din taji muryarsu kuwa, sosai wani
farin ciki ya lullubeta amma kuma lkci daya fara'ar fuskarta ya bace da ta ji ta
kasa bude gate din, kuma kamar ta waje aka kulle, Naf tace "Gate din ya ki buduwa
ne kin bar mu tsaye cikin rana?" Nihad tayi narai narai da ido tace "Wllh kamar ta
waje ya kulle" Husnah ta bude baki haka Zully, Naf tace "Amma dai wannan a yan
iskan ma A ne shi, ta waje ya kulle gate? To a saboda me? Akuyarsa ya ajiye a gidan
yake tsoron kar ta gudu da xai kulle ki cikin gida?" Nihad bata san sanda ta fashe
da kukan takaici ba shkkn da gaske kulleta yayi, Husnah tace "Ke kuma matsalarki
kenan, to meye na wani kuka" Amina dai na tsaye rike da ledan waya a hannu, Naf
tace "Toh wai ina yaje?" Nihad tace "Wai fa Auntyna ya kai gida shine sabida bashi
da hankali ya kulle min gate ta waje kamar gidan ubansa" Husnah tace "Kuma wllh
makulli ya sa, ni ko har na kagu in ga wannan me ido da kwallin" Nihad ta goge
idonta tace "Kawai ku ɗan jira a nan yanxu xa ku ga ya dawo" Haka suka yi ta jira a
bakin gate din, ita kuma ta zauna kan dakalin dakin da aka tanadar don mai gadi a
compound din, tun daga nesa khalil ke kallonsu a bakin gate din, yayi parking ɗan
nesa da gidan, Amina tace "Yauwa gashi can, motar gidanmu ce wannan" Su Naf duk
suka kafe motar da ido ana jiran aga fitowarsa amma bai fito ba, Husnah tace "Ji
gantalalle ya ki saukowa a motar" Zully tace "Shi ne ai nake kallon ikon Allah" Naf
ta kalli Amina tace "Ke tafi ki karbo mana makulli wajensa tunda ba shi da hankali,
uban wa zai bari tsaye cikin rana" Amina ta tafi a gun motar yana ganinta ya sauke
glass din can side din don duk sun gwala ido su ga ya sauke glass din side dinsa ko
xa su samu a little glimpse of him, Amina na ganin haka ta zaga tana kallonsa ta
cikin motar tace "Ka bamu makullin gidan" Yace "Su waye bakin gate din?" Amina tace
"Kawayen Aunty Nihad" Yace "Ohk, ke kika kawo su kenan?" Tace "Ehh Umma ta bani
sako in kawo mata ne shine muka taho tare da su don basu san gidan ba" Ya mika
hannu yace "Toh kawo a ajiye mata sakon, yanxu kasuwa xanje in yanko wani makullin
wancan ya fadi" Amina tayi kasake tana kallonsa, mika hannu yayi ya amshe ledan
hannunta yace "Ko xaki shigo in ajiye ki gida daga nan in wuce kasuwar?" Amina ta
daure fuska tace "Ni ai a motarsu muka zo" Yace "Toh koma motar tasu" Daga haka ya
ja glass ya tada motar yayi reverse ya bar layin.....
*Kiyi subscription ki karanta hankalinki kwance yar uwa*



*Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence via👇🏻
07087865788

22

Husnah suka kalli junansu da sauri ganin Khalil ya juya motar xai bar layin, Amina
ta dawo fuska a daure tace "Wai wani zai je ya yanko wani makullin" Husnah ta rike
kugu tace "Tashin hankali, lallai wannan mutumin dan iska ne, karya fa yake yi
wllh, mu din dai ne baxai bude ma gidan mu shiga ba" Nihad ta taso da sauri ta
tsaya jikin gate din tace "Me ya faru?" Naf dai ta kasa cewa komai tun da ta bi
motar da ido baki bude, Zully tayi wani dariya ta rike ha6a tace "Kan uban can...
Amma gayen nan daga ɗan iska sai shi, but don Allah ku baku ji kun kagu kuna son
ganinsa ba? It's the gut for me" Nihad dake ta zaro ido ta kasa fahimtar abinda
suke cewa tace "Don Allah ku min magana mana, ya dawo ne?" Husnah ta sauke wani
uban ajiyar zuciya ta koma bakin flower ta zauna tana girgiza kafa, Naf da wani
bakin ciki ya isheta tace "Amma idan ban tara yan sara suka da yan da6a sun ma
drivern nan mugun bugu ba ku ce bani bace, don kaza kazansa da uwar me yake takama
xae walakanta mu haka da girman mu, wa ye shi xai dinga feeling kansa haka yana
fama da talauci..." Tuni Nihad ta fara fahimtar abinda ya faru hawaye ya cika
idonta, ita dai ta shiga uku da abinda wannan yaron ke yi mata, Husnah ta kara
sauke wani axababben ajiyar xuciya ta mike tace "Nihad mu xa mu tafi, ashe da
gasken gaske tsinanne ne mutumin nan sai yau na sake tabbatarwa, wato tantirin ɗan
iska ne na bugawa a jarida, har mu zai walakanta ya juya kan mota ya bar mu uwa yan
iska a tsaye bakin gate? Who the hell did he think he is" Nihad ta sakar masu kuka
tace "Ba ina gaya maku ba kun zata exaggerating nake, ai wallahi zai iya yin abinda
ya fi haka, ina Amina?" Amina tace "Ga ni" Nihad tace "Ki kira Umma da wayarki ki
gaya mata abinda dan iskan yayi maku" Amina ta fiddo wayarta a jaka ta hau kiran
Umma, Umma na dagawa ta larabta mata abinda khalil yayi masu a bakin gate, Umma ta
rike ha6a bayan ta gama sauraron Amina tace "Yau ga shegen mutumi, kuna nan har
yanzu bakin gate din kenan a tsaye?" Amina tace "Wallahi" Umma tace "Ina wayar
Nihad din?" Amina tace "Ya karɓe wai xai ajiye mata" Umma ta wani mulmulo zagi ta
lafta mata tace "Uban wa yace ki basa? Wajensa na aiko ki xaki basa waya? To
wallahi duk inda xaki nemosa ki nemosa ki amsar min wayata, kaji min doluwar
yarinya kawai" Amina ta turo baki tace "To wai ba karbewa yayi a hannu na ba, ni me
xan ce masa" Umma ta kara kunduma mata zagi tace "Ubanki ne ya siya min wayar da xa
ki ba wani ɗan iska can? Na dai gaya maki kar ki kuskura ki dawo min gida babu
wannan ledar wayar, shashashar banza kawai doluwa" Daga haka umma ta katse wayar
tana huci, Nihad tace "Ban gane ba, wayar kika basa Amina?" Amina tace "Toh wai ba
amshewa yayi a hannuna ba yace xai ajiye maki" Nihad ta kunduma mata zagi ita ma
tace "Wallahi maza ki bi sa ki amso min wayata, meye hadina da shi da har xai amsar
min waya yace xai ajiye? Munafuki kawai" Amina tace "Ni dai wallahi ku daina min
masifa tunda ba ni na mika masa ba" Husnah tace "Toh wannan takadirin ai ko bata
basa ba xai iya fizgewa a hannunta, don naga kamar ya ta6a dabanci, ni dai wllh bai
walakanta banza yau din nan ba, xai san ya ta6a Clique dinmu..." Naf duk ta fi su
shiga takaici a wajen, she really wants to meet with Khalil ya ga karshen rashin
mutunci da tijara, Zully tace "Ni anya ma ba shi yaje ya samu Abban yace a basa
auren Nihad din ba kawai don ya samu hanyar dinga walakantata?" Nihad na tafe hannu
tace "Ai ko da kansa xai tafi ya samu Abban yace masa yayi hakuri ya fasa auren, i
am going to make life miserable for him, xai san cewar ni ba sa'ar zama waje daya
da shi bace balle uwa uba aure, shi har ya isa ya aureni? Wallahi da wuri wuri zai
koma gun Abba yace ya fasa" Husnah tace "Atoh, duk wannan koke koken da kike yau
kwana da kwanaki babu abinda xai tsinana maki sai ma 6ata lokacin ki da kike ki ji
in gaya maki, yanzu kamata yayi ace kin zauna kin nutsu kin fara nazarin ta yanda
zaki fara musguna ma shege, kar ki kuskura ki raga masa daga cikin tijara da
iskanci da muka iya a Clique dinmu, In his next life ko million daya xa a dinga
basa ya zo gidan masu kudi yayi driving wallahi baxai zo ba, shi din banza shi din
hofi" Sosai hudubar Husnah ke shigar Nihad da taji daga wannan moment din ta daina
kuka, baxata kara asaran hawayenta ba akan Halilu, sai dai ta fara daukan action a
kansa, kuma da ƙafafuwansa xai gudu ya bar mata gidan ya koma kauyensu na har
abada, Husnah tace "Kuma gidan nan ko da uban wa yake yawo sai mun shiga gobe,
balle daga shi sai talauci yake yawon ma, wallahi kamar mun shiga gobe, Allah ya
kai mu goben, kuma ina fatan Allah Ubangiji ya hada mu da shi face to face goben"
Nihad ta sauke ajiyar xuciya saboda sosai ta samu kwarin gwiwa, tace "Amina ki ɗan
ara min wayarki mana zuwa gobe" Amina tace "Toh ni sai in yi amfani da wanne?" A
fusace Nihad tace "In za ki ara min ki ara min malama, banza kawai ba ke kika je
kika mika ma wawan can wanda Umma ta baki ki kawo min ba? Dallah bani wayarki ai ba
cinyewa xan yi ba" Amina tace "Ban ga xan iya ba, ni islamiyya ma xan yi tafiyata
daga nan, duk an bata ma mutum lokaci ansa na makara kawai a banxa, sai da nace ma
Umma ni islamiyya xan tafi amma ta ki" daga haka ta juya fuuu ta bar su wajen a
tsaye, Husnah tace "Ke rabu da wani aran waya, gobe ni da kaina xan kawo maki waya,
screen touch kuwa" Nihad tace "Toh ta yaya, bayan kina ganin abinda yake yi da
gidan kamar na ubansa" Husnah tace "Baki yi trusting dinmu ba kenan?" Naf tayi wani
Murmushi tace "Ai kamar mun shiga gidan nan gobe idan Allah ya kai mu, ki saurare
mu idan mun tashi test" A hankali Nihad tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu" Zully
tace "Toh wai ya sunan wannan tatattcen mutumin ne?" Nihad tace "Halilu naji ana
kiransa" Duk suka kwashe da dariya Husnah tace "Za mu haliro masa gobe kuwa" Daga
haka suka yi mata sallama, tana jin suka shiga motarsu suka bar layin, ta sauke
wani ajiyar xuciya ta juya ta koma cikin gidan. Sai bayan magrib Nihad ta ji
shigowar Khalil gidan, nan da nan taji bacin ranta ya ninku a kan na da, tana jin
sa ya shigo parlor ta mike ta fito parlon, bai ko kalleta ba ya ajiye ledan
hannunsa ya zauna saman kujera ya dau remote yayi powering tv, a fusace ta karaso
cikin parlon ta fixgo ledan da ya ajiye don a tunaninta wayarta ce, da ido ya bi ta
har ta gama bincika ledan ganin fruits ne ta cillar a gefe, tana tafe hannu cike da
tsiwa tace "Ka buda kunnenka da kyau ka saurareni, yau ya zama first and last day
da xaka sake kulleni a gida idan xaka fita don ni ba akuyarka ko tinkiyarka bace,
kuma ka bani wayar da Ummata ta aiko min" Kallon Tv kawai khalil yake, tayi masa
wani tsawa tace "Baka ji na ne ina maka magana?" Still bai kalleta ba balle ta sa
ran xai amsa, a mugun fusace ta tafi ta kashe socket din gun Tv din gaba daya tana
kallonsa tana huci, Khalil ya kalli karamar wayarsa dake ring, dagawa yayi ya kai
kunne yace "Idan na gama abinda nake xan kira ki Hajiya" Huci kawai Nihad take tana
kallonsa, yana katse wayar ya mike ya nufi bedroom, wani bakin ciki ya kara rufeta
ta bi sa da sauri ta shige gabansa tana cewa "Ni ce ma zan dinga maka magana zaka
tashi ka bar wajen, to wallahi baka isa ba...." zata cakumosa kamar yanda ta saba
ganin kallon da yake mata sai ta fasa kai hannun nata kwalarsa, Cikin kakkausar
murya yace "Matsa ki bani waje" Duk da yanda gabanta ke faduwa tace "Baxan matsa
ba, ka bani wayata tunda ba kai ka siya ba...." Irin kallon da taga yake mata yasa
ta fashe da matsanancin kuka ta durkushe wajen don can kasan xuciyarta a tsorace
take da shi, ya bi gefenta ya shige daki abunsa ya kulle kofar. Mikewa tayi tana
kuka tana bubbuga masa kofa tace "Ni wallahi ka bani wayata tunda ba da kudinka aka
siya ba, ina ruwanka da sakon da aka kawo min da xaka sa hannunka ka amsa" Banza
yayi mata, ita kuma bata fasa bubbuga kofar ba, bayan kusan minti biyar taji ya
bude kofar sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri amma kuma bata fasa fadan
abinda take fada ba, taga ya sa ma dakin makulli ya cire sannan yayi hanyar kitchen
ya shiga, bin sa tayi har bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kuka tace "Wallahi
idan na maka Allah ya isa sai ya bi ka har generation dinka, ka bani wayana nace"
Gas ya kunna ya dau karamin tukunya sabo ya dauraye ya sa ruwa a ciki ya daura
saman gas din, bata fasa masa fitsaran da take ba a bakin kofa, ya juya ya ɗan
kalleta, ta wani maka masa harara tace "In kuma siyarwa kaje kayi sai ka gaya min
in cire rai" Shi dai bai ce mata komai ba ya rungume hannunsa yana jiran ruwan ya
tafasa, ta rushe da kuka ta hade kanta da kofa tace "Wayyo Allahna na shiga uku" Ya
daga kai ya ɗan kalleta, juyawa yayi yana kallon ruwansa dake saman gas, ta dago
kai cikin kuka tace "Koma me kayi da wayar ban yafe ba...." Ko rufe baki bata yi ba
taga ya cire hannunsa da sauri daga handle din tukunyar alamar ya kona sa, ya koma
baya yana kallon tukunyar, wani shegen dariya ta saki har da kyakyatawa ta durkusa
a wajen, yanda take dariyar kai kace bata da sauran damuwa a duniya, ya ɗan kalleta
sai kuma ya shafa kansa ya juya yana murmushi ya kalli inda ya tukunyar ta kona sa,
ruwan da bai juye ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login