Showing 147001 words to 150000 words out of 268471 words

Chapter 50 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

plss, wannan bata kai ta sa ki
shiga damuwa ba har ki zubda hawayenki a banza, me xai yi da ita? Da akwai wani abu
tsakaninsu ma ai baxai fara kawota gidan nan ba, kuma saboda mugun abinda tayi shi
yasa ma ba a son ta zauna hostel may be parent dinta suka yi requesting ta zauna a
nan, shi sa ma kika ganta a nan" Nadeeyah ta gyada mata kai kawai, Noor ta ci gaba
yi mata hiran da take mata a nutse..... Har karfe biyar khalil na zaune inda yake a
cikin compound din yana danna waya, so yake ya maida Nadeeyah gida kafin ya je inda
yake son zuwa, wayarsa dake hannunsa ya fara ring, ya dinga kallon number wanda ke
kiransa, ya dai yi picking daga karshe yakai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace
"Dama wani aiki ne ya shigo da ni Abuja yau, so gobe da safe in sha Allah xan koma
kd, shine nake son inji wani wajen ku ke a Abujan?" Khalil ya sauke idonsa yace
"Ohk, maa sha Allah, goben za ka zo kenan?" Farooq yace "No, na gama abinda nake yi
yanzu, goben da sassafe nake son tafiya" at first khalil ya rasa abinda xai ce
masa, Farooq yace "Hello" Khalil yace "Eh ina jin ka, xan tura maka address din
yanzu" Farooq yace "Toh ina jira" Daga haka ya katse wayar, Daga nisa ya dinga
kallon Nadeeyah har ta iso inda yake, ta dauke kai tace "Xan tafi gida" Ganin mood
din ta yace "What happened Nady? Are you okay?" Ta ki ce masa komai, ya mike yana
kallonta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, da damuwa yace "Talk to me plss, me ya
faru?" Cikin rawan murya tace "But you neva told me ba kai kadai ka dawo Abuja ba"
Yace "Shit... Toh menene tsakanina da warce na dawo da? There is nothing Nady kawai
karatu ta zo yi a garin nan, and she have no where to stay shine take zaune gidan
nan, bayan nan babu wani abu kuma trust me" Ta goge Idonta tace "Naji, I want to go
home" yace "Noo, not in this manner pls, but ta maki wani abu ne?" Nadeeyah tace
"Kawai shigowa tayi ta hararemu ta fita babu sallama balle gaisuwa" Khalil yayi
wani sigh yace "But you guys shouldn't have taken it personal, she is a
sociopath...." Nadeeyah ta tabe baki dai bata ce komai ba, khalil ya kalli wayarsa
dake ring da sauri, ganin Farooq ne ya daga yace "Ina tura maka ne" Farooq yace
"Ohk" Daga haka ya katse wayar, Khalil yace "Look Ki koma ciki yanzu, i will be
having a visitor immediately, idan ya tafi sai muje ki sha ice cream sannan in
maida ki gida" Murmushi kawai tayi ta juya ta fara tafiya, yea dama murmushin kawai
yake son yaga ta yi which means komai ya wuce kenan, ya sauke ajiyar zuciya ya
zauna ya shiga sending ma Farooq address.....
*Nihad* is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence of payment via 07087865788


45

Farooq was perplexed bayan yayi parking dai dai inda Khalil yace ya tsaya ya
jirasa, yana kallon sojojin dake opposite dinsa amma nesa da shi, ya dinga bin area
din da kallo with mouth agape, ina ne nan din khalil yace ya zo? And why will he
tell him to come and wait here? He could see 3 of the soldiers advancing toward his
car with haste, and bai san me xai masu ya kawo shi nan ba idan sun karaso, can
nesa ya hango khalil na tahowa ta inda sojojin suka yi creating barriers, sojoji
ukun suka karaso har inda yake suna masa alamar ya sakko fuskarsu a murtuke babu
rahama, Farooq ya kashe motarsa ya sauko with calmness ya gaishesu, Maimakon su
amsa strictly suke tambayarsa where is he from kuma tsayuwar me yayi a nan? Farooq
yayi karfin halin nuna masu khalil dake tahowa yace "I was waiting for him...." Da
sauri khalil ya fito daga wajen barrier din ganin sojojin da suka tsare farooq, ya
daga ma sauran soldiers din dake wajen a zaune hannu ya nufi gun farooq, sojojin
dake gaban farooq na ganinsa suka juya suka koma position dinsu, Khalil na Murmushi
yace "Yi hakuri na bar ka a tsaye, barka da isowa yallabai" farooq dai sai kallonsa
yake still surprise, can dai yace "Ina ne nan din Khalil?" Khalil ya zaga daya side
din motar not wanting to answer him yace "Mu karasa can ciki Yallabai, ba a tsayawa
a nan...." Farooq ya shiga motarsa har sannan mamaki ne shimfide a fuskarsa Khalil
yace "Mu je can gaba" da wani expression Farooq ya masa wani kallo yace "Mu je
ina??" Cause ta wajen barriers din da sojojin ke tsaye yaga Khalil na nuna masa wai
su bi, Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace "Gaba xa mu yi, kuma hanya ce ai"
Farooq yace "Ta gaban sojojin can xa mu bi kake nufi?" Khalil yace "Ba komai, nace
maka hanyar kowa da kowa ne" Bayan few seconds Farooq dai ya tada motar yana
driving din a hankali yaga sojojin sun daga masa karfen da ya rufe layin, ya wuce
ciki still driving careful, Bayan sun shiga Farooq na kallon Khalil yace "Wai ina
ne nan din Khalil?" Khalil na nuna masa gaba yace "Can gaba xa mu karasa, ba nisa
sosai" Farooq dai ya ci gaba da driving din amma carefully cause the security in
there isn't funny, very tight security, gasu fuskarsu babu rahama duk a murtuke,
Farooq dai na driving yana kare ma anguwan kallo, bayan tafiyar few minutes, Khalil
ya nuna masa gate yace "Baƙin gate din can xaka yi horn" Farooq ya juya yana kallon
Khalil, Khalil bai yarda ya kallesa ba ya danna horn din da kansa, Sojojin wajen
suka taso zuwa gun motar, tuni khalil ya sauke glass ganinsa suka koma, aka bude
gate din, sai da Khalil yace "Mu shiga yallabai" sannan Farooq ya ja motar zuwa
cikin compound din, Khalil ya nuna masa inda xai yi parking, kai kana ganin farooq
kasan abun ya gama daure masa kai, he is more than confuse, Khalil ya sauka daga
motar ya zaga yana kallon farooq, farooq ya sauko daga motar shi ma yana kallonsa
amma ya kasa cewa komai, Khalil na dan murmushi yace "Ya kwana da yawa Yallabai?
It's a pleasure meeting with you after a while" A hankali Farooq yace "Now tell me,
why did u chose to hide ur Identity? Why?" Khalil ya sauke idonsa kasa yace "I was
left with no choice Farooq, but the beautiful part of all is that i meant no harm
to your family, something's are better left unsaid, and mind you this is my
father's house not my house, kuma shi namiji ai baya tutiya da gidan ubansa, all
what u are seeing in here is for my dad, and i am not him in anyway" Khalil bai
jira abinda Farooq xai ce ba yayi gripping hannunsa yace "Mu shiga ciki" Daga haka
suka bar wajen, Farooq couldn't stop looking at Khalil, babban tambayar da yaji
yake bukatar amsarta shine me khalil yaje yi gidansu? meye manufarsa na zuwa
gidansu yace zai yi driving? Driving fa?? Shi dai From day one yasan there is
something about Khalil that is hidden, he knows that, and here is what was hidden
today, Suna shiga Main parlor Khalil ya sake hannunsa, Farhana dake parlon ta bi su
da kallo, Daga khalil har Farooq da yake tafiya with calmness babu wanda ya kalli
inda take har suka haura sama, Farooq couldn't hide how amazed he was with all what
he is seeing, and he felt so happy for his Lil sis, har suka iso parlon Mami,
Khalil na kallonsa yace "This is my mum's part, za ku gaisa da ita" Farooq na
murmushi yace "Sure" Suka shiga first parlor sannan second, Nadiya dake zaune ita
kadai tana danna waya ta daga kai jin an bude kofa, Farooq yayi sallama ya shiga
bayan Khalil yayi taking lead, Nadiyah ta kalli Khalil sannan farooq, Khalil yayi
mata murmushi yace "Meet my frnd Farooq" Da fara'a Nadeeyah ta gaida Farooq ya amsa
with calm smile written all over his face sannan ya zauna saman kujera, Tuni Khalil
ya shiga dakin Maminsa, bayan few minutes sai ga shi ya fito tare da Mami, da
fara'a Mami suka gaisa da Farooq dake ta kallonta saboda resemblance dinta da
khalil is very obvious, khalil ya zauna gefen Farooq yana kallon Mami yace "Yayan
Nihad kenan Mami, he is Farooq by name...." Mami tace "Maa sha Allah, you are
welcome son" Khalil na Murmushi yana patting shoulder din Farooq gratefully yace
"They are the most nicest family i have met so far in life, they really made my
stay with dem a memorable one, they made me felt at home all through my stay with
them, and i owe them for that..." Farooq dai kawai yayi murmushi, Mami tace "Allah
sarki Allah Ubangiji ya karfafa zumunci, Allah ya saka da alkhairi.... This is so
beautiful to hear" Farooq wish he could express how happy he is for his Lil sis at
this moment, a ko da yaushe addu'arsa ga Nihad shine Allah ya dauwamar da ita cikin
farin ciki bayan all What she's gone through, yana mata addu'ar Allah yasa aurenta
da Khalil ya zama sillar farin cikinta na har abada, he sees her as a strong young
girl, don yau ace Nihal ce abubuwan nan suka faru da yasan she is definitely going
to break, yasan she can never endure it for long, duk abubuwan da Khalil ke fada
akan karamcin da suka masa a kano Farooq hankalinsa ba nan yake ba, ganin komai
yake kamar a mafarki, tuni Mami ta kira Bilkisu ta kawo masa drinks and small
chops, Mimi ta shigo parlon rike da laptop dinta zata dau charger da ta bari, Mimi
na kallon Farooq tace "Good evening" With smile on his face yace "Evening dear" Ta
dau charger xata fita Khalil na kallonta yace "Can you pls call ur new friend?"
Mimi ta ɗan juya tace "You mean Neehad?" Yace "Yeah" Ta gyada kai tace "Sure" Daga
haka ta juya ta fita daga dakin.... Kwance ta tadda Nihad kan gado, Nihad ta juya
tana kallonta, ganin yanayinta Mimi tace "Are you okay?" Kai kawai Nihad ta gyada
mata ta mike zaune, Mimi tace "But there is tears in ur eyes" Nihad ta girgiza mata
kai trying not to break cike da karfin hali tace "I am fine, kawai ciwon kai
nake...." With concern Mimi tace "Eyya Allah ya sauwake, i will get u drug, ki zo
parlorn Mami ana kiranki" Nihad ta hadiye abinda ya tokare mata cikin karfin hali
tace "Ohk" duk zaton ta Mamin ce ke kiranta, Ta sauka daga saman gadon ta bi bayan
Mimi tana tafiya a hankali suka fita daga dakin.... A hanya suka hadu da Noor,
ganin she is dressed up Mimi tace "Are you going out big sis?" Banza Noor tayi mata
saboda tana tare da Nihad, ta wuce su kamar xata bangaje Nihad din, Nihad dai ta bi
ta da kallo bata ce komai ba, Mimi tayi kasa da murya bayan Noor ta wuce su tace
"Sorry.... she is angry at you may be because u just badged into the parlor when we
came back from school, baki yi masu sallama ba kuma sannan baki yi recognizing
dinsu ba, which isn't right" Nihad ta dinga kallonta tace "Ta yaya zan shiga waje
ban yi sallama ba, sai dai in basu ji ba, ko kuma nice ban yi yanda xa su ji ba,
beside they were discussing ta ya za su ji?" Mimi tace "You just have to raise ur
voice za su ji, and why didn't you recognize them?" Nihad ta ɗan buda ido tace "Do
i have to?" Mimi tace "Yeahh, as far as ke kika shiga kika samesu a wajen, sai kiyi
acknowledge din haka" Nihad ta tabe baki tace "Sai dai in yi ma yayarki amma ita
dayar i have no business with her don ban santa a gidan nan ba, why will i
recognize her?" Mimi tayi letting sigh tace "But fiancee din yayanmu ce" Nihad ta
buda ido sosai tace "Ohh ashe fiancee ce kawai!!" Mimi tace "Yeah, and she is going
to be his wife soon" a takaice Nihad tace "Then i will wait till she becomes his
wife if that's possible, before i can recognize her...." Mimi tace "Now accept that
u are wrong Neehad" Nihad tace "I accept, but by not recognizing only ur sister"
Mimi ta daga kafada tace "Ohk then, and can i ask u one more thing" Ba tare da
Nihad ta kalleta ba tace "Ohk" Mimi tace "I noticed u don't greet my brother, why?"
Nihad ta kalleta da mamaki, can tace "But u advised i should be avoiding him
totally" Noor halted with mouth wide open tana kallon Nihad, bata san sanda ta
fashe da wani dariya ba, she laughed for some seconds kafin tace "But u neva told
me it's you, u said ur friend" Nihad ta ɗan zaro ido tace "Oh, oh... I.... I mean
to say...." Sai kuma ta rasa abinda xata ce lokaci daya taji kunya, Noor na dariya
tace "You are so funny Nihad, ni bance kar ki gaishesa ba, i only said u should be
avoiding him, but not ignore greeting him" Nihad dai ta ki cewa komai, Mimi ta
langwabar da kai tace "Yayana na da kirki sosai fa, you only misperceived him, just
try turning friends with him zaki gane hakan, he is a simple and sweet person....
Give what i said a trial pls" Nihad taki cewa komai ta ci gaba da tafiya Mimi na
biye da ita har suka iso parlon Mami, khalil kadae Nihad ta gani zaune saman
kujera, sai Nadeeyah dake parlon ita ma, bata ma lura da Noor dake tsaye daya side
din ba, ta juya zata kalli Mimi ta tambayeta wa ke kiranta tayi ido hudu da ya
farooq dake tsaye side din kofa ya rungume hannunsa yana kallonta with smile
written all over his face, Kasa kwakkwaran motsi tayi a inda take, don kawai sai
abun yayi mata kamar mafarki take, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, ganin haka
kawai ya nufeta yana murmushi ya rungumeta, he understands
she is shock and neva expect seeing him at that time, Nihad ta kankamesa ta fashe
da kuka, tana son magana amma ta kasa cewa komai, Khalil da Nadeeyah dai kallonsu
kawai suke, haka Noor dake tsaye, lkci daya Mimi dake murmushi ta fahimci yayanta
ne, haka Noor da ta kasa barin inda take a tsaye, ganin kukan da Nihad take farooq
yayi kasa da murya yace "Ain't you happy seeing me Lil sis?" A hankali cikin rawan
murya tace "Don girman Allah kar ka tafi ka barni a nan yaya, wallahi baxan iya
zama a nan ba, take me back home in roki Abba yayi hakuri ya yafe min" Farooq kadai
ke jin abinda take cewa, yayi kasa da murya yace "You are a married woman now
Nihad, you have to stay where ever ur husband is staying" Nihad ta kara rushe masa
da kuka, ya kama hannunta ya tafi da ita suka zauna saman kujera yana kallonta,
kuka kawai take tana share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai khalil kallonta
kawai yake, Farooq yace "Now stop that cry ko inyi tafiyata, and i am serious" Da
sauri ta fara goge idonta tana kallonsa ta hadiye kukan da take ta jinginar da
kanta kan shoulder dinsa.

Umma na kallon Kamila cikin fada tace "Magana nake maki kika kauda kai" Kamila dai
danna wayarta kawai yake, Umma tace "Ke yanzu kina nufin ban isa in gaya maki kiji
ba? Zaman gidan nan yafi maki ki koma dakinki kike nufi? To wai ma uwar me kike
tsinana min a nan da kika zo kika jaɓe min?" A fusace Kamila tace "Umma ni wallahi
baxan koma in zauna da manemin mata ba, baxan iya ba wallahi" Umma ta buda baki
tace "Duk da baki san yana neman mata ba sai yanzu Kamila?" Kamila tace "Nace maki
yanzu ya fara Umma, don wannan abun da nake gaya maki ko wata biyu ba ayi ba da ya
fara... Sannan the worst part of all is that guilty conscience ya sa ya dau zargi
ya daura min, kwata kwata na lura yanzu bai yarda da ni ba, ban isa in motsa ko nan
da can ba, ba dama yaga wayana yayi ring, to a kan me?" Umma tace "Toh duk ba
ruwana da wannan wallahi, tunda har ya kira ki tattara ki koma dakin ki, banda
iskanci shekaranku biyu tare baki san yana neman mata ba sai yanzu? Dariya kike son
a min a gari ko me? Kina zaune da mijinki lafiya ga arziki sai yanda kika yi da shi
amma saboda shaidan na maki ganga a kai shine xaki billo da wannan iskancin? Ko duk
matan duniyan yake bi ma ina ruwanki? Balle wannan sharri ne kawai kika masa"
Kamila ta mike fuuu ta fice daga dakin a fusace, Umma tace "Wallahi baxaki kwanar
min a gidan nan yau ba, maza dau jakarki ki koma dakinki, na gaji da boyeki haka
kuma"

Nihad ta dade bata shiga farin cikin da ta shiga a yau ba, a haraban gidan take
zaune ita da yayanta bayan sun fito parlon Mami, Farooq dai sai kallonta yake ganin
yanda ta kara haske tayi kyau sai dai ta rame sosai, he just can't wait to go back
home and break this amazing news to His stepmom ko xata samu peace of mind, a
hankali tace "Ya farooq yanzu Abba baxai yafe min ba? Wallahi i know nothing about
all what that has happened to me" Farooq ya wara ido trying his best ya kwantar
mata da hankali yace "Xai yafe maki mana Lil sis, amma sai kin zauna lafiya da
mijinki, kin masa biyayya... I am assuring you wannan ne kadai zai sa Abba ya yafe
maki, don ya gaya min haka" Nihad tayi shiru tana kallonsa, yace "Yea, when i
begged him on ur behalf abinda yace min kenan, don haka kiyi kokari ku zauna
lafiya, and accept him as ur husband" Hawaye ya cika idonta tace "But shi ma baya
sona fa Ya farooq, we don't like each other" Farooq ya girgiza kai yace "Da baya
sonki baxai kawoki har nan gidan iyayensa ba, ke dai ce baki son zaman lafiya
Nihad, ko da baya sonki ke ba mace bace, teach him how to love" Hawaye kawai Nihad
take bata ce komai ba, Farooq yace "I know it's hard dear, amma kiyi hakuri, komai
xai daidaita wataran, za kuma kiyi farin cikin Kasancewarsa mijinki" Cikin rawan
murya tace "Bayan sai yayi ta daga min shoulder saboda yaga suna da kudi" Dariya
sosai farooq yayi yace "Ke sanda kika dinga daga masa naki shoulder din a gidanku
fa?" Nihad ta hade rai tace "Aa ni ban daga masa shoulder ba, kuma shine sai yayi
ta tsokanata" Farooq yace "Toh yanzu dai duk ba wannan ba, all i want from u is to
love and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login