Showing 264001 words to 267000 words out of 268471 words
da zata sa, Aunty Maryam ta fita daga
dakin don dauko abu ta dawo, Aunty Jamila na juyawa taga Nihad durkushe gaban
Babynta dake kwance cikin cot dinsa sai kallonsa take babu ko kiftawa, Aunty Jamila
ta rike haɓa don bata da aiki sai kallon jaririn ko a gaban waye kuma, in ko bata
gansa ba irin anje masa wanka to sai ta bi sa, Aunty Jamila tace "Toh wai ko mayar
da yaron nan ciki za kiyi ne?" Da sauri Nihad ta bar wajen tana murmushi, Aunty
Jamila tace "Ikon Allah, Ke ko kunyar surkanki da sababbin ido bakya yi, toh kar in
sake ganin kina makale masa kina masa wannan kallon kamar zaki cinyesa, idan duk
aka watse daga yau zuwa gobe sai ki zauna daga safe har dare kina kallonsa babu me
hanaki, amma yanzu ki rufa mana asiri don Allah" Ita dai Nihad bata ce komai ba ta
sunkuyar da kanta, Aunty Jamila ta ajiye mata kayanta tace "Ta shi ki shirya, ina
Aunty Maryam take ajiye maki socks din naki?" Nihad ta nuna mata sannan ta mike ta
shirya cikin kayan da Aunty Jamila ta dauko mata, Aunty Maryam ta dawo dakin rike
da glass din ruwa da drugs dinta, tana bata ta sha ta fita da glass din, Yau kwana
sha biyar da haihuwan Nihad, a jiya kuma aka yi suna wanda za a iya cewa bikin da
ba ayi a baya bane aka samu privilege din yi yanxu, don kuwa sunan nan ya samu
halartar manya manyan kasar daga garurruka daban daban kai kace biki kawai ake, yan
yemen ma duk sun zo kwansu da kwarkwatansu don taya Mami murnan samun first
grandchild, Hajiya Safeenah dai abu nasu maganin a kwabesu, tayi kokari tayi
bajinta sosai don kaya na gani na fada ta hada ma jaririn bayan sun dawo US, Janar
ya kashe kudi me sunan kudi a sunan nan don a gidansa aka yi sunan, Nihad kuma ta
samu kudi iya kudi don kamar ba a son kudin aka dinga bata, kawayen Mami ne, Abokan
Janar, yan uwa da abokan arziki, kudi dai kam ta samu, shagali sosai aka yi a sunan
nan abinci iri iri da nama kuwa ba a cewa komai sai wanda ya gani, komai irin na
yan gayu aka yi a sunan, har Umma sai da ta zo sunan da autarta Amina ta kuma ga
abinda bata taɓa zato ba don ma dai Aunty Jamila na ta jan ta jiki duk don ta sake
ayi komai da ita kamar yanda dai matan Alhaji Abubakar suka saki jiki ana ta hidima
da su, Nihal tayi aurenta da Ayman wata daya da sati daya da suka wuce baya, wanda
Mumy na daga cikin wa enda suka kai ta har UK where Ayman is based, family dinsa
dake Uk din suka amshi Nihal hannu bibbiyu don duk abinda ɗan uwansu ke so su ma
suna so, Nihad taji takaicin rashin zuwanta bikin er uwartata saboda nauyin da tayi
a lokacin amma Su Mami da Noor da Khalil har Hajiya Safeenah da Nadeeyah duk sun
tafi, gashi har Nihal ta tafi bata san gidan Nihad na Abuja ba, don kwantar mata da
hankali Khalil yace idan ta haihu da wata uku zai kai ta har Uk din gun Nihal.
Kamila ma dai ba a bar ta a baya ba wajen zuwa suna duk da ita ma dai tana ta
shirye shiryen komawa gidan tsohon mijinta zai mayar da ita, Farooq zuwansa hudu
gidan Janar tun da Nihad ta haihu don ya dawo Abuja da aiki, Usman kuma sai ranan
sunan ya zo daga kaduna yaga Baby, ko wannensu was so happy for their lil sis, dubu
dari Usman ya bata ta siya duk abinda take so, Farooq kuma ya siya mata tsadaddun
atamfa har biyar da kayan baby iri iri, duk wanda ya ga Inna ranan sunan nan kuwa
sai yayi tunanin ita ta haifi Janar din gaba daya, Babu kayan fitan sunan da Khalil
yayi ma Nihad don Janar yayi mata yayi kala talatin a gidan kuma duk kayan da ta
saka babu na banza a ciki kaya ne masu sunan kaya, Mami ta siya mata jaka da
takalmi dai dai da kayan fitan sunanta, Aunty Maryam kuma ta siya mata jewelries
masu shegen kyau da tsada, Jaririn ma daga waje aka yi masa order din duk
kayayyakinsa banda wanda Khalil ya siya masa tun ba a haifesa ba, hakan yasa Khalil
ya siya ma Nihad dankareren dankunnen zinari da sarkansa don tana da zobuna da Mami
ke bata sun yi biyar ynxu, yaro ya ci sunan Abban Nihad za kuma a kirasa da Aaryan,
Inna kuka ta dinga yi wiwi jin sunan da aka sa ma yaron.. Tun kafin EDD din Nihad
ya cika dama suka fita US da Mami don sun bi duk process a can suke son ta haihu,
daga baya kuma Khalil ya bi su don kawai azarbabin Mami ya sa ta tafi da ita kafin
lokacin haihuwan, sai da ya dai dai ci saura few days EDD dinta sannan ya dau leave
a wajen aiki ya bi su, sun kusa kwana goma a US kafin Nihad ta haifo santalelen ɗan
nata, after 3 days bayan ta huta kuma suka juyo suka dawo Nigeria. Duk da 2 days
ago aka yi suna amma har yanzu da sauran baƙi a gidan da suka zo daga nesa. Nihad
na ganin Aunty Jamila ta fita, ta mike da sauri ta koma gun Babynta tana kallonsa,
yaron kamar ubansa yayi kaki, komai na Khalil ya dauko har hancin da bakin, the
baby is so cute and fair, with pink lips, ta durkusa kusa da shi tana kallonsa with
smile all over her face wani farin ciki na musamman take ji idan tana kallon yaron
nata, murya can kasa tace "Abbana" Yaron ya bude ido a hankali yana kallonta kamar
ya ji abinda tace, wani dadi taji har ranta har da kyalkyalewa da dariya, ta lumshe
ido ta manna masa kiss a soft cheeks dinsa tace "I love you so much" dai dai
shigowar Aunty Jamila, tsaye tayi bakin kofa tana kallonta baki bude, Nihad ta mike
ta bar wajen da sauri tana kame kame tace "Aunty na ji yana kuka ne shine na
dubasa" Aunty Jamila dai bata ce mata komai ba ta karasa cikin dakin, Nihad ta zaro
ido ganin warce ke bayan Aunty Jamila, da sauri ta tafi ta rungumeta cike da farin
cikin ganinta, Mami dake tsaye gefen Mumy tayi murmushi tana kallonsu, Mumy tace
"Menene haka Nihad? Ke baxa kiyi hankali ba har yanzu" Nihad was more than happy
seeing her mother don har ta cire ran zuwanta da ta ga har an yi suna bata zo ba,
Mumy ta dau jaririn bayan ta zauna tayi masa addu'a ta saka masa albarka sannan ta
maida shi cikin cot dinsa, Nihad dake ta kallonta tace "Wallahi nayi missing dinki
Mumy" Ita dai Mumy murmushi kawai tayi bata ce mata komai ba, Mumy bata wani dade a
gidan ba ta bi Hajiya Safeenah zuwa gidanta wai can zata kwana zuwa gobe kuma ta
koma kano, babu yanda Mami bata yi da ita a kan ta zauna gidan ba amma taki, kana
ganin reaction din Mumy kasan eh lallai jinin fulani ce... Daren ranan Mami na
guess room tare da Aunty Jamila da Aunty Maryam wanda ita ta kirasu zuwa dakin
saboda baƙin dake bangarenta kuma tana son masu magana ne, Mami tace "Jamila kin
tuna lokacin rasuwan mahaifin Nihad Janar yaje tare da wani amininsa a lokacin? Duk
da dai abokan nasa da suka je suna da yawa amma wannan idan dai ba mantawa kika yi
ba suna tare always..." Aunty Jamila tayi shiru sai kuma tace "Kamar na so in
ganesa, he is a bit fair nd tall ko?" Mami tace "Yauwa kin ganesa kuwa, to tun dai
sanda Hajiya Maryam ta fita takaba ya nuna interest dinsa na aurenta, shi ma dai
matarsa ta rasu yau shekara bakwai kenan, yaransa uku a duniya biyu maza sai mace
daya, Babban ɗan sa is 30 yanzu, me bi masa kuma is 28, kuma duk basa kasar yanzu
haka a waje suke aikinsu dukkansu, autarsa ce dai me suna Maryam she is just 17
years now kuma tana wajen matar kanin baban nata, to tun dai da ya nuna interest
dinsa bayan fitar ta takaba Janar ya sa na kira Hajiya Maryam a lokacin nayi mata
magana amma sai ta nuna ita kam ba wani auren zata yi ba tana son ta kula da
yaranta maza biyu babu aure a gabanta, sannan step children dinta ma duk a gabanta
suke ita ke rike da su, This man is also a Lieutenant General sunansa Ahmad, kuma
na tabbatar da yana da wani flaws that can't be tolerated Janar will neva take him
serious balle har ya sa nayi ma Maryam magana, to ban san ko ta maki maganar ba
this happened almost 3 months ago, kuma har yau Janar Ahmad bai hakura ba, ni kuma
gaskiya naki basa numberta don idan na basa ban san yanda zata dau hakan ba, to
zuwan da tayi gaida janar dazu ai suna tare da Janar Ahmad din a parlonsa, shine
Janar ya kirani ya sa in sake mata magana, na kuma yi mata kafin ta tafi gidan
Safeenah, but still abinda ta gaya min a baya shi ta sake maimaita min yanxu ma,
sai ban ji dadi ba da naga tana hawaye, i know it's not easy but dole life have to
go on, she have to move on, balle ma naga ita er uwar Nihad din ma ai tayi aure
bata ma kasar yanzu, ina ce ita kadai ce step daughter dinta da take rike da" Aunty
Jamila ta sauke ajiyar zuciya tace "In sha Allahu zan mata magana Aunty, ina ga can
gidan Hajiya Safeenar ma zan je in kwana duk za mu hadu mu yi mata magana" Mami
tace "Toh don Allah kiyi iya kokarinki, Janar Ahmad zai rike mata yaranta maza, he
said this tun farkon maganarsa da Janar, kuma kin ga shi ma a nan Abuja yake" Aunty
Jamila tace "In sha Allahu we will talk to her Aunty" Kamar yanda Aunty Jamila tace
gidan Hajiya Safeenah ta tafi ta kwana don yi ma yayar tata magana don tasan idan
Hajiya Safeenah ma tasa baki kilan su rinjaye ra'ayinta. Har kusan karfe biyun dare
Hajiya Safeenah bata hakura ba sai da ta cusa ma Mumy ra'ayinsu na son ta amince da
auren Janar Ahmad. Washegari duk aka gama watsewa a gidan Janar kowa ya koma
various destination dinsa, Duk yanda Mumy ta so tafiya ranan Hajiya Safeenah bata
barta ta tafi ba har sai da Janar Ahmad ya zo ya sameta a gidan. Rayuwa kenan, babu
yanda Mumy ta iya haka ta hakura da auren bayan shi kansa Janar Jikamshi ya zaunar
da ita yayi mata magana ta nutsuwa da fahimta, Inna ma ta saka baki, babu yanda
Mumy ta iya haka tayi accepting auren, a cikin sati biyu kacal aka daura mata aure
da Janar Ahmad, amma bata yarda ta tare ba sai da ta ga Kamila ta koma gidan
mijinta, Alhaji Abubakar duk shi yayi mata wasu sabbin kayan dakin don daga ita har
Umma suka siyar da tsofaffin kayanta, bayan kwana biyar da komawar Kamila gidan
mijinta, Mumy ta hada komai nata a kano ta bayar don Janar Ahmad yace mata babu
abinda babu a gidansa, a Private jet aka tafi da su Abuja ta tare da yaranta maza
biyu a Mansion din Janar Ahmad, daughter dinsa Maryam me sunan Mumy ta dawo wajen
Mumyn da zama,
dalilin rufe gidan Abba kenan aka sallami su Aminu, Isiya, Saminu da dreba, duk
aka rabu ana kuka, Aminu had nothing to loose don da taimakon Khalil ya gina
dankareren gidansa a kauyensu ke kya ce ba me gadi bane don gidan duk ya fi na yan
kauyen, sannan Khalil ya basa jarin miliyan daya ya fara kasuwancinsa a cikin garin
kano. During period din nan kuma aka sa ma Noor rana da babban ɗan Janar Ahmad dake
Turkey don dama shi ne saurayinta, as at that time Nadeeyah dake masters dinta tana
tare da wani Young Brigadier general wanda sun fi shekara biyu da sanin juna but
bata basa lokacinta ba sai yanzu and he and his family are fully prepared su je
gaida dangin Mahaifinta a Yemen, idan ba message din Khalil ta gani a WhatsApp ba
ita har mancewa take da shi a Abuja, gashi dai zumunci suke yi sosai da Nihad don a
lokacin da ta haihu kullum sai taje gidan har aka yi suna amma Khalil kam mantawa
take da shi wllh.... Sai da Nihad tayi 50 days a gidan Mami, bayan Mami ta tabbatar
tayi mata duk gyaran da ya kamata tayi mata Hajiya Safeenah da frnd din Mami suka
maida ta dakinta tare da Mimi that will be of help to her zuwa wani ɗan lokaci
saboda jego, da yammacin ranan suka bar gidan, Mimi made sure ta gyara ko ina na
gidan ta sa turaren wuta. Karfe biyar da rabi Khalil ya dawo aiki, he was so happy
to see his wife and son don bai san ranan za su dawo ba, Mami dai ta amshi spare
key din gidan nasa kusan kwana shidda da suka wuce a baya, kullum sai ya dawo aiki
yake zuwa can gidansu ganin family din nasa, kuma sai kusan karfe goma yake komawa
gidansa yau kam yana dawowa ya gansu a gidan and he was very happy, sai dai kuma
Farooq da ya gani a gidan nasa made him believe what he was thinking before, kusan
duk dare idan yaje can gidansu sai ya ga Farooq a gidan sai yanzu ya sake tabbatar
da cewa wajen Mimi yake zuwa ba Nihad ba amma sai ya fake da kamar gun er uwarsa
yake zuwa, ita kuwa Nihad tuni ta gano zuwan me Farooq yake kullum, sai bayan
magrib Farooq ya bar gidan, Mimi ta kai ma Yayan nata shayi a parlonsa kamar yanda
ya bukata, da sallama ta shiga parlon, Nihad dake zaune kusa da Khalil dake rike da
Aryaan ta amsa mata sallaman, bayan ta ajiye shayin Khalil na kallonta yace
"Wajenki farooq ke zuwa ko?" Ta wani zaro ido ta dafe kirji tace "Ni??" Dariya
kawai Nihad tayi tana kallon Mimi da ta daburce, Khalil ya jefa mata wani kallo
yace "Tafi ki bani waje with ur hypocrisy" Ta sunkuyar da kai kamar munafuka ta
juya tana murmushi ta nufi kofa. Daren ranan Khalil ya nuna ma Nihad yanda yayi
kewanta sosai, ita ma kuma tayi kewan mijin nata, she truly missed him soo much.
Washegari da ya kasance asabar Khalil baya fita aiki, wajen karfe goma na safe ya
fita shopping da Nihad leaving Mimi and little Aryaan at home, Nihad ta dau duk
wani abu da tasan za su bukata a gida, bayan ya biya kudi aka kai masu mota, tana
kokarin shiga mota taji ana kiranta, waigawa tayi taga wata mata ta nufota da sauri
fuskarta rufe da Face mask, matar na karasowa kusa da ita ta sauke Facemask din, ko
kusa Nihad bata gane ta ba, Matar tace "Nihad ni ce fa" Sai a sannan Nihad ta dau
muryarta ta zaro ido da mugun mamaki tace "Zully???" Shi dai khalil har ya bude
driver seat ya shiga yana kallonsu, Zully ta cire face mask din gaba daya tace "Ni
ce Nihad" Da mamaki Nihad tace "Me ya sameki haka? Where u sick??" Zully ta fara
kikkifta ido sai kuma ta fashe da kuka a hankali tace "Ehh wallahi na kwana biyu
bani da lafiya amma na fara samun sauki yanzu tunda gashi har ina fitowa" Nihad na
kallonta daga sama har kasa tace "Me kike yi a nan?" Zully ta sunkuyar da kanta
tayi shiru, daga sama har kasa Nihad ke ta kallonta don she look so tattered and
unkept, sae bugawa ma take, ga wani ramewa da tayi ta koma bakakirin maimakon fara
da Nihad ta santa a baya, dama can ita iyayenta talakawa ne sosai don uwarta ma a
kauye take ubanta kuma ya rasu, Naf ce dai er masu kudi a cikin su ukun, lokaci
daya jikin Nihad yayi sanyi, a hankali tace "Husnah fah?" Zully ta kara fashewa da
sabon kuka tana girgiza kai tace "Ai Allah ya mata rasuwa ko sati biyu ba ayi ba,
tayi fama da cancer ga kuma HIV daga karshe kuma rai yayi halinsa" Nihad ta dafe
kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Husnah ta rasu??" Zully ta gyada
kai cikin sanyin murya tace "A gidansu ta rasu a garin kaduna don babu kudin zuwa
asibiti, kafin ta rasu ta damu tana son ganinki, kuma an je har gidan ku nemanki
amma aka tarar babu kowa a gidan an ma kulle da kwado" Hawaye na sauka idon Nihad
tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Zully ta kara fashewa da kuka sosai tace
"Don Allah ki yafe mana Nihad duk abinda ya sameki mu ne muka ja maki wallahi daga
karshe kuma sai gashi ya zame maki alkhairi, wannan video din naki Husnah ce tayi
sa amma ba da nufin ta yada shi a social media ba, lokacin da Aliyu zai turo
iyayensa gidanku Umma ta kira Husnah duk ta zuzzugata wai haka za mu sa ido ɗan
Janar guda ya zo ya aureki muna gani alhalin mu har yanzu ba mu yi aure ba duk kuma
mun girme ki, sai Husnah take ce mata ai ko me za mu ce maki baza ki ji ba don son
Aliyu ya rufe maki ido akansa har rashin mutunci kike mana a kansa, Umma tace to mu
bi maki ta karkashin kasa mana, da so tayi ma mu bi ta zuwa gidan Malamai amma ko
wacce xata kawo ɗan abinda za a ba ma malam don tace bata da kudi ita a lokacin,
shine Husnah ta tuna wannan video dinki dake wayanta wanda tayi maki sanda kika
koma hostel da zama, ranan mun je zaria mun sauka wani hotel za ayi Birthday din
wata kawar Naf, gaba dayanmu sai muka sa maki kwaya a drink dinki kin fita kiyi
waya da Abbanki, mu ma duk mun saka a namu tunda mun saba sha, wllh wllh ba don
video dinki ya tafi viral aka yi ba Nihad, mun yi sa kawai saboda nishadi, we did
it da wayar Husnah just for fun saboda yanda kika dinga reacting very drunk after
taking the juice, Da Umma ta kawo mana batun zaki yi aure ki bar mu and we are
doing nothing about it kuma ta nemi mu kawo kudi ta kai mu gidan malami sai Husnah
ta tuno da video din da tayi maki, wallahi Umma ce cause din sakin wannan video din
a social media, da mun bi ta Naf ma baza a saki Video din ba don she was against
that amma saboda son zuciya ni da Husnah sai da muka bi bloggers muka tura masu
video din duk don Aliyu yace ya fasa aurenki, don girman Allah ki yafe min Nihad,
ita dai Husnah ta rasu, ni ma dai