Showing 198001 words to 201000 words out of 268471 words

Chapter 67 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ce daya, amma gun dangin ubanta ta
taso" Inna ta rike haɓa, Mumy ta leko parlon tace "Hajiya karaso kiyi alwala" Aunty
Maryam na kallon Inna tace "Bari in yi alwala" daga haka ta ajiye mayafinta ta
shiga bedroom din Mumy, inna tace "Ashe tsinanniya ce take neman kawo min raini"

Umma bata yi awa biyu a asibitin ba aka sallameta suka nufo gida don tun kan ma su
isa asibitin ta farfado, dressing din mata ciwon da taji a goshi kawai aka yi sae
hannunta da ta samu dislocation shi ma aka gyara sannan magunguna da aka bata to
relieve the pain, Har cikin compound motar da aka kai ta asibiti da shi ya shiga
yayi parking bayan sun dawo gida, sojan dake tuka motar ya sauka ya bude ma Umma
kofa, Umma ta sauko daga motar a hankali da katon bandage a goshinta ga hannunta da
take lallabawa kar ta fama, ta dinga bin gidan da kallo kamar bata taɓa ganin gidan
ba, yanda take yi da idanuwa zaka ce tayi wata da watanni a kwance ba lafiya sai
yanzu aka fara samo kanta, Farooq ya sauka motar don a tare yake da ita a back seat
din, Khalil ya bude front seat shi ma ya sauko yana rike da drugs din nata dake
cikin leda, Farooq na rike da hannun Umma mara ciwon suka nufi entrance din cikin
gidan Khalil na biye da su, Mami da Aunty Maryam ne kawai a gidan, Inna ta shiga
gari sanar da yan uwa da abokai abun arxikin da ya samesu, Aunty Hassana kuwa tana
ganin Janar ya bar gidan ita ma ta shiga garin kano ko zata fara nemo solution
dinta a nan, Janar bai bar gidan ba sai da ya dire ma Abba miliyan daya, wanda yace
ya ba inna 300k sauran kuma ya raba ma duk yan gidan.... Tun bayan da aka kai Umma
asibiti Mumy ke bedroom dinta tare da Aunty Maryam da Aunty Jamila, Mami ce kadai
ta ki shiga dakin duk yanda Mumy tayi da ita kuwa, har abinci ma bata ci ba balle
small chops din banda bottle water kawai da ta dauka shi ma ba sha tayi ba kawai a
gefenta ta ajiye, Aunty Maryam ko ta ci abincinta ta koshi, ta kara da snacking,
yanda take hira da Mumy kamar ta taɓa saninta, Aunty Maryam bata boye ma Mumy duk
abubuwan da suka faru can Abujan ba kan yanda Khalil ya rufa cewar Nihad matarsa ce
for almost 2 months din da suka yi a can, ita dai Mumy ta ma rasa abun cewa, Aunty
Maryam ta kawo maganar Video din Nihad dake cin ta a rai kenan su Umma suka shigo
gidan daga asibiti, hakan yasa Mumy ta mike tace ma Aunty Maryam bari taje duba
jikinta, Mumy ta bi Umma har bedroom dinta tare da Farooq, Umma ta lallaba ta
kwanta saman gadon kar ta fama hannunta, Farooq ya ajiye ledan maganin da Khalil ya
basa a bedside drawer, Kamila kuwa na kwance can end din gadon, Mumy ta kalleta
tace "Sannu Kamila, na shigo dazu kina bacci" Kamila dai ba bakin magana, Mumy na
kallon Umma tace "A kawo maki abinci ne?" Umma ta girgiza kai da sauri amma ta kasa
cewa komai, Mumy tace "Toh Allah ya sauwake" Daga haka ta juya ta fita daga parlon,
tana komawa ɓangarenta ta kalli Mami dake parlonta tace "Hajiya ko dai kina son a
maki wani abun ne na ci?" Mami tace "No it's okay, mara lafiyar ta dawo mu dubata?
Don za mu koma Abuja yanzu" Mumy tace "Ehh yanzu suka shigo" Mami tace "Toh Maryam
ta fito mu je mu dubata mu kama hanya" Mumy ta shiga dakinta tayi ma Aunty Maryam
magana, Aunty Maryam ta fito, Mami tace "Janar yace akwai jirgin sojoji da zai koma
Abuja yau and it can contain us all" Aunty Maryam tace "Yaushe jirgin zai tashi?"
Mami tace "Soon" Tana fadin haka ta mike tana kallon Mumy tace "Ina bangaren mara
lafiyan?" Mumy ta kai su har bangaren Umma, Umma ta dinga bin su da ido tun da suka
shigo, ko sannun da suke mata ta kasa amsawa, Mami tace "Allah ya sauwake ya sa
kaffara ne Hajiya" Cikin rawan murya Umma tace "Ameen" Aunty Maryam dai sai
kallonta take ta tuna abubuwan da Nihad ta gaya mata a kanta, can ta taɓe baki ta
juya ta fita daga dakin. Mami bata koma bangaren Mumy ba ta zauna main parlor tana
jiran Convoy da suka tafi da Janar su dawo daukansu, babu dadewa kuma suka iso,
Mumy tayi masu packaging sauran small chops din, Aunty Maryam tayi ta mata godiya,
Mami na kallon Aunty Maryam tace "Ki kira Hassana" Aunty Maryam ta ciro wayarta ta
kira Hassana, tana dagawa Aunty Maryam tace "Za mu tafi airport yanzu Hajiya" Aunty
Hassana tace "Gaskiya nayi nisa, ku tafi kawai ko flight din dare idan na samu sai
in biyo" Aunty Maryam bata ce mata komai ba ta katse wayarta. Nihad ta fito daga
dakin Nihal da take ciki tun dazu bayan Mumy taje ta taso ta tayi masu sallama,
Aunty Maryam na kallon Nihad da murmushi fuskarta tace "Zaku taho tare da Khalil
din Daughter...." Nihad dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Sai da taga za
su fita tayi ma Mami sallama, Mami ta amsa sannan ta fita daga parlon, Mumy ta
rakasu har gate, sai da suka bar layin sannan ta dawo ciki, zaune taga Aminu kan
benchi kamar mara lafiya duk yayi sanyi, tana kallonsa tace "Lafiya Aminu?" Aminu
yayi kasa da murya yace "Ina ta tuna ko wani abu ya taɓa hadani da Halilu ne,
kinsan zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa, ni dai a sanina baxan tuna ga abinda nayi
masa ba gaskiya, sai dai ko cikin rashin sani, amma lafiya na zauna da shi wllh, ni
dai dama in ta tsoron inda yake samun kudi kullum sai mun ci tsiren kusan dubu
biyar a nan da daddare, ga lemon kwali me tsada, wani lokacin ma ni yake aika in
siyo mana shi kuma ya tsare gate din, har ta kai ta kawo na daina cin abinci da
daddare saboda yanda muke cika cikinmu da nama, cakulate da manyan biskit kuwa har
yanzu ina da ledojinsu da na tara a dakina, muna zaune lafiya wallahi da shi har ya
bar gidan nan, haka kawai sai in ga ya mun kyautar dubu biyu dubu uku, ni duk
tunanina kudin albashin tukinsa yake ci, ashe ga zance ga magana, dama su isiya ne
suka masa azababben walakanci zuwansa gidan nan, Allah kadai kuma yasan yanda zai
yi da su yanzu" Mumy dake ta kallonsa tayi murmushi kawai ta bar sa wajen ta koma
ciki, Aunty jamila na zaune tare da Nihad a parlon Mumy, Mumy ta shigo ta zauna
tana kallon Nihad, Aunty jamila tace "Sai nake ga kamar uwarsa bata yi farin ciki
da auren nasu ba Aunty" Mumy ta ɗan yi murmushi kawai amma bata ce komai ba, Ita
dai Nihad wasa take ta yi da yatsunta, a hankali Mumy tace "I noticed that too, na
ga alamar hakan..." Aunty jamila ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Nihad tace
"Wani irin zama kika yi a gidansu can Abuja Nihad?" Nihad ta daga kai tace "Ita
dama haka take, she doesn't talk much, and... She isn't friendly, but she is nice"
Aunty jamila tace "Amma bata nuna maki komai ba sanda kike gidan?" Nihad ta girgiza
kai tace "Aa" Aunty jamila tace "Toh Allah ya kyauta" Mumy ta rasa me yasa she
isn't happy about how everything turns out, ko don saboda reaction din Mami ne she
can't tell. Babu yanda Mumy bata yi da Nihad ta shiga duba Umma ba amma kememe
taki, Aunty jamila tace "Aa kar ki takurata Aunty Maryam, ke dai ba kinje kin
dubata ba" Dab da magrib Khalil ya iso gidan, yana bude gate Aminu ya mike da
sauri, ya ɗan duka cike da ladabi yace "Barka da isowa ranka shi dade..." Khalil ya
fara kalle kallen abinda zai dauka ya jefe shi da shi....

Ana idar da sallan magrib Farooq ya tafi kai Kamila asibiti, Umma dama tun dazu
take jiran su tafi asibitin, suna tafiya kuwa ta mike da sauri ta shige bandakinta
ta tura kofar, Hajiya Turai ta shiga kira a wayarta, Turai na dagawa cikin kuka
Umma tace "Dazu muna magana Maryam ta shigo shi sa na katse Turai" Tsabar tashin
hankali zaman dirshan tayi a bandakin ta sa wayar a handsfree ta ajiye a kasa tana
kuka wiwi ta rike kanta tana cewa "Turai na shiga uku, turai na shiga uku na
lalace, wallahi tunda nake ban taɓa girgiza irin ta yau ba Turai, ban taɓa shiga
tashin hankali irin na yau ba, Shi fa Janar jikamshin da kansa ya shigo har gidan
nan namu yau da matansa, convoy kuwa tun daga farkon layin nan har karshensa, ga
sojoji yanda kika san za ayi yaki, Turai dama kin taɓa ce min anya ba basaja Khalil
din nan yake ba saboda jikinsa bai yi kama da wanda ya san wani abu wai shi wahala
ba, ni ko na dage maki cewar har kauyensu Yallabai yaje kawai farin fatar tasa ce
yasa kike ganin haka, Turai ashe duk karya mutumin nan yake, turai ɗan babban mutum
ne, turai ɗan jikamshi guda ne" Sai ta kara fashewa da kuka kamar warce aka yi ma
mutuwa, Turai da ita kanta tayi mugun girgiza da wannan labarin aminiyar tata tace
"Jikamshi? Janar jikamshi fa kika ce, ni wallahi duk kin rikitani, wannan saurayin
nata Aliyu ba shine ɗan jikamshin ba? Ko ya abun yake?" Cikin kuka Umma tace "Ince
maki yau ga mu ga Janar jikamshi da bakinsa kuma yace Khalil din ɗansa ne ki wani
kawo zancen Aliyu, ai tunda kika ga haka karya Aliyun ya sharara ma mutane kenan,
irin yan iskan makaryatan yaran nan ne masu amfani da sunan manya su yaudari yan
mata, kuma Allah ya isa tsakanina da shi don da ba don wannan karyan da yayi mata
ba a ina har za a ga wani video dinta na yawo balle har uban ya mata aure? Wllh duk
Aliyun nan ne ya ja min wannan bala'i, ya cuceni, ya cuceni, da ba don shi ba ai
kawai gantalinta zata ci gaba da yi da bin hotels babu wanda ya sani, ni dai mafita
zaki nemar min kawata, wallahi zuciyata zai iya fashewa in har Nihad ta ci gaba da
auren Khalil, Shine fa ainahin ɗan Janar din nake gaya maki, uwarsa kuwa da kyar
idan ba balarabiya bace, jikinsu duk gwala-gwalai Turai...." Ta fashe da wani
matsanancin kuka tana girgiza kai tace "Kuma fa wallahi da Nihal yaron suke shiri a
gidan, har zama suke yi gu daya su yi fira, amma nasan yanda nayi na sa ta fita
harkansa, har waya fa suke yi na hanata ta karfi da yaji, da na sani me zai sa in
shiga tsakaninsu Turai? Me zai kai ni?? Ai wallahi da sai inda karfina ya kare
wajen tabbatar da cewa ya aureta, amma duk tunanina mara galihu ne shi din" Turai
tace "Tashin hankali.... Yanzu sun koma Abuja da Nihad din kenan?" Umma na
shessheka tace "Ina na sani, tun dazu ni dai ban ji duriyarsu ba kinga ai sun koma
kenan, ita kanta Nihad din har yanzu zancen nan da nake maki bata shigo ta dubani
ba, Yallabai da ya shigo dazu kafin magariba yake gaya min miliyan daya Jikamshin
ya bada a raba ma yan gidan" Turai ta zaro ido tace "Toh baki ga ta kuka ba gaskiya
Sumayya, kuka ba naki bane yanzu, amma dai su ba su da labarin videon da yayi
leaking a gari ne kwanaki?" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Kai bana jin sun sani
gaskiya, wa zai so ɗan sa ya auri irin wannan yarinyar? Ai da sun gani da tun a
Abujan za su sa ya saketa" Turai tace "Toh kawai kudi zaki bada a ba popular
bloggers kamar biyar haka su sake dawo da labarin da zafi zafinsa, nan da nan zaki
ga ya karade duniya" A hankali Umma tace "Ko??" Turai tace "Kwarai kuwa" Umma na
share hawayenta tace "Kamar nawa zan turo yanzu?" Turai tace "Ko dubu dari uku ce a
kacalcala masu, kyau a samu bloggers kamar shidda lafiyayyu" A hankali Umma tace
"Turai zoben fa saura kwaya daya yanzu, duk mun siyar an kai ma malamai" Turai tace
"Amma ai kuma bukata na biyuwa idan ba yanzu da aka samu cikas ba, yanzun ma rufe
ido zaki yi ki siyar kawai a biya bukata da shi, Allahn da ya baki shi zai sake
baki" Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh shikenan Turai, Nagode sosai Allah ya
bar zumuncinmu, in sha Allah gobe xan aiko Amina da shi, ni kinga bazan iya fitowa
goshi a fashe, ga hannu nayi targade" Turai tace "Ba damuwa goben ma zan shigo ba
sai kin aiko Amina ba" Umma tace "Toh nagode sai kin zo" Daga haka Umma ta katse
wayar, nan taji hankalinta yayi mugun kwanciya, ai da Nihad ta zama surkar jikamshi
gwara ko tsirara ne tayi yawo a duniya, sai tasan yanda tayi ta rabata da Khalil
wallahi, mikewa tayi ta nufi kofa ta jawo zata fita taga Abba tsaye bakin kofar
bandakin, Sake wayar hannunta tayi cikin daburcewa tace "Yall.. yallabai yaushe ka
shigo?? Bayan gida na shiga inyi...." Abba dai kallonta kawai yake, can ya juya ya
bar bakin kofar bandakin, walking slowly ya fita daga dakin gaba daya, jikin Umma
ya dau rawa ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, da kyar
ta karasa fitowa daga bandakin taga ledan fruits da ya kawo mata ajiye a kasa....




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788




*CONGRATULATIONS*🥳🥳
*For taking this smart move to growing your business....*

I am zainab Suleiman you can save my contact ummu shaheed or kabzee 08033242995




* I will be giving you the opportunity to connect to Over 80 direct suppliers and
major dealers of various products in Nigeria, where you will be getting goods at
factory prices without Importation and reselling as an wholesaler to make great
profit.*🤑🤑🔥🔥

*This is for everyone that wants to start getting products at good purchase
price/factory prices and become a major wholesalers that other business owners can
buy in bulk from*🔥🔥

*This suppliers contact bundle has solved 70% of the problem of startups, small
business owners, distributors, dropshippers etc...which is the inability of getting
goods at good affordable prices to resell...*


*But the *GOODÑEWS is I will allow Only 20 people access this contact bundle at
a discount rate of N5000 ONLY*

*Ps: this offer is available for just 24 hrs.* ‼️
‼️

*After that price goes back to the usual price of N7,000* ✅✅


60
Nihad ta gama shirin kwanciya a bedroom din Mumy wajen karfe tara da rabi, Aunty
jamila da bata yi tafiyar tata ranan ba sai bin ta take da kallo tana ganin ikon
Allah, sai da ta bari ta kwanta sannan tace "Ke kam ashe har yanzu baki da saiti
ban sani ba Nihad" Nihad ta juya ta kalleta, Aunty jamila tace "Mijinki na gidan
nan tun dazu amma common kije ki ga ko ya ci abinci ma baki je, ko yana da bukatar
wani abu ke duk ba damuwarki bane, babu ruwanki sai harkan gabanki kike, to kuwa
idan kina nuna i don't care attitude din nan naki akan miji kya samu warce kina ji
kina gani zata kwace maki miji" Nihad ta mike zaune tana kallon Aunty jamila, a duk
maganar da ta mata na karshen ne ya tsaya mata a rai, Aunty jamila tace "Shi namiji
in gaya maki riritasa ake, wasu na can a waje suna harinsa ke kuma kina nan kina
shashanci, tun daxu da ya shigo gidan nan sai kije ki samesa ki ji ko yana da
bukatar wani abu tunda nasan Mumy dole zata basa abinci...." Dai dai nan Mumy ta
bude kofar dakin ta shigo, tana kallon Nihad tace "Ke baza kije kiji ko yana da
bukatar wani abun ba?" Aunty Jamila tace "Maganar da nake mata kenan yanzu Aunty"
Nihad ta sauka daga saman gadon a hankali ta dau hijab dinta ta sa, har ta nufi
kofa sai kuma tace "Toh ai ni ban san inda yake ba fa" Mumy tace "Yana dakin
Farooq" Bude kofar tayi ta fita, Aunty Jamila ta rike haɓa tace "Aa gaskiya tana
bukatar counselling akan auren ma gaba daya, don ban ga alamar tasan komai ba" Mumy
tace "Toh idan ba ke ba wa zai mata Jamila" Aunty Jamila tace "Allah ya kai mu
gobe" Mumy tace "Ke baza ki ci abincin ba?" Aunty Jamila tace "Aa na sha shayi...
Uhmm Aunty bamu samu mun yi magana ba har yanzu" Mumy na kallonta tace "Magana akan
me fa?" Aunty Jamila ta rike haɓa tace "Me suma daga ji da ganin abun arxiki, ke
kiji hassada kiri kiri, zuciya ta kasa adana hakan har sai da ya fito fili cikin
bainar jama'a, duk me hangen nesa a parlon nan yasan shock din al'amarin ne ya
sumar da ita ba wani abu ba, and shock in the sense that she wasn't expecting
things to turn out that way, wallahi she never expect that kamar yanda mu ma bamu
yi expecting ba kawai a bazata abun ya zo mana, wato Sumayya ta gina ramin mugunta
without considering zata iya dawowa ta afka ciki ko wani nata ya afka, yau ai ga
Kamilar da take takama tana auren mai kudi a gida ba wai farin ciki nake da hakan
ba don babu wanda zai yi farin ciki da mutuwar auren wani, amma ishara ta fara gani
tun a nan duniya, sai ga Nihad da ta so lalata ma rayuwa tana auren wanda ko a
mafarki bamu taɓa kawo hakan a kai ba, na sha gaya maki da akwai wani boyayyen
lamari game da Khalil din nan, tun ran da na fara ganinsa a gidan nan..." Mumy dai
ta sauke ajiyar zuciya ta ma rasa abinda zata ce ma er uwartata. Nihad na tafiya a
hankali ta nufi dakin Ya farooq, ta tsaya bakin kofar tayi sallama hade da
Knocking, bude kofar dakin aka yi taga Khalil tsaye, ta shiga cikin dakin tana
kallonsa tace "You need anything?" Ya kafeta da ido, sai kuma ya kulle kofar dakin
ya jawota, ta zaro ido tace "What are you doing??" murya can kasa yace "I need
nothing, but you...." Ta wani turo baki tace "Ni ka sakeni kar Ya Farooq ya shigo,
dama su Mumy ne suka ce in zo in tambayeka ko kana da bukatar wani abu shi yasa na
zo...." Kallon lips dinta kawai yake tana magana kuma ya ki sakinta, ganin haka
tace "Ni don Allah ka sakeni, meye haka...." Bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login