Showing 105001 words to 108000 words out of 268471 words

Chapter 36 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

tare da yasan ya fada ba yace "Sorry" daga haka ya
kulle idonsa, ta mike zaune tana kallonsa sosai jikinsa yayi zafi, bubbuga gado ta
shiga yi da sauri tana cewa "Husnah, Husnah ki tashi" Amma jin shiru ta daga kai
taga wayam babu Husnah a dakin, mikewa tayi da sauri ta fita parlor nan ma ta
dudduba bata ga Husnah ba, kamar xata yi kuka tace "Toh ina ta tafi?" Sai kuma ta
marairaice tace "Toh ni ya zan yi yanzu?" Juyowa tayi da sauri ta dawo dakin ta
durkusa gabansa tana kallonsa, sai kuma tace "Toh Abba xan kira da wayarka?" Ya
bude jajayen idonsa da sauri yace "Aa" Tashi tayi ta kara fita parlor dai dai nan
taji kamar ana bude kofar kitchen, tsorata tayi tayi hanyar daki da sauri tana
lekan kofar kitchen din, sai ga Husnah baki ya kumbura suntummm lebbenta ya koma
kamar na rakumi, ga fuskarta yayi jajir kamar nama, jini kuma ya kwanta a idonta
daya, dayan idon kuwa ya manne, kayan baccinta ne a jikinta, Nihad ta dafe kirji a
tsorace tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Husnah what happened" Husnah na
dingishi da kyar tace "Aljanun dare" Nihad ta jingina da bango a mugun tsorace tana
zaro ido tace "Aljanun dare kuma?" Husnah ta gyada kai da kyar tace "Akwaisu a
gidan nan wllh, Dauko min jakata da hijabi na" Nihad da hankalinta yayi mugun tashi
tace "Ganinsu kika yi?" Husnah na sauke numfashi tace "Nace ki dauko min jakata da
hijabi" Nihad taki motsawa daga inda take saboda tsoro, Husnah tayi zaman dirshan a
kasa ta rasa inda xata sa ranta ta ji dadi, gaba daya shatin belt din jikinta yayi
jajir gasu rudu rudu, Nihad dake ta kallonta a mugun tsorace tace "Husnah kalli
jikinki fa" A fusace Husnah tace "Ki dauko min jakata da hijabi nace" Nihad ta juya
ta koma daki da sauri bata ga Khalil kwance inda ta bar sa ba, cikin second biyar
ta fixgo hijabi, jaka da wayar Husnah ta fito da gudu daga dakin, Husnah na ganinta
ta mike ko ina na jikinta na rawa ta amshe jakarta da hijab da waya, bayan ta saka
hijab din ta nufi kofa da sauri, Nihad ta fashe da kuka tace "Tafiya za kiyi ki
barni Husnah?" Ko tsayawa Husnah bata yi ba balle ta juyo ta saurari Nihad tuni ta
bude kofar parlon ta fice da sauri ta saka takalminta luckily taga lock kawai aka
sa ma gate din babu key ta bude ta fice daga gidan. Nihad ta koma dakin Khalil da
gudu ta kulle kofar, kan darduma ta gansa sallan ma ya kasa tashi tsaye, ta durkusa
nan kusa da gado tana kallonsa kana ganin idonta kasan ta tsorata sosai, har ya
idar taga ya fada kan darduman ya kwanta ya kulle ido, ita dai tana ta zaune
maganar Husnah na mata yawo a kai, can ta mike a hankali ta nufi bandakinsa, a bude
ta bar kofar, bayan ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito da sauri... Tana idar da
sallah ta juya tana kallonsa, tashi tayi ta koma inda yake ta duka hucin zafi take
ji a jikinsa, ta dinga kallonsa, a hankali ya bude idanuwansa jin ta a gefensa, ta
6ata fuska tace "Toh kuma kace kar in kira Abba" Wayarsa da ta hango gefen gado ta
kai hannu ta dauka, yayi karfin halin kwace wayar a hannunta ya lumshe ido, tagumi
tayi tana kallonsa, a hankali tace "Toh ni ya zan yi?" Tana ta zaune gefensa har
gari ya waye gaba daya, tun da ya amshe wayarsa a hannunta bai sake bude idonsa ba,
duk da baccin da take ji amma bata yi ba tana gefensa a zaune, lkci daya taga ya
yunkura ya mike zaune, ta zaro ido ta koma baya tace "Amai zaka yi" Ya sunkuyar da
kansa bayan few minutes ya koma ya kwanta ya kulle ido, a hankali ta kai hannu
forehead dinsa taji har sannan da xafi, ya bude ido yana kallonta, tace "Toh safiya
yayi yanzu ka bani wayar in kira Abbana" murya can kasa taji yace "Dauko takarda da
biro" Tace "Takarda da biro kuma??" Jin bai ce komai ba ta mike har ta nufi kofa
sai ga ta ta dawo da gudu ta tsugunna kusa da shi kamar xata yi kuka tace "Wallahi
Husnah tace min akwai Aljanun dare a gidan nan, duk sun mata duka bakinta ya canxa
yayi wani iri"




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, kiyi subscription ki karanta
cikin salama er uwa!!!!

Ur evidence via👇🏻
✍🏻
07087865788




Assalamu alaikum manyan mata!!

For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of
jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰

Message via👇🏻
https://wa.me/c/2349090591769

To view our catalogue🥰


33
Nihad tayi shiru tana kallonsa jin bai ce komai ba, bayan few seconds cike da
karfin hali yace "Baxa ki dauko min ba?" Ta marairaice tace "To wai ba nace maka
tsoro nake ji ba, ni baxan iya fita ni kadai ba wallahi, bayan Husnah tace min
aljanun dare na gidan nan" Da kyar ya mike zaune ya nuna mata jakarsa murya can
kasa yace "Bani shi" Mikewa tayi ta tafi ta dauko jakar ta ajiye masa tana
kallonsa, ya jingina da gado, kana ganinsa kasan ba shi da strength, bayan few
seconds a hankali ya bude side din jakar ya ciro jotter da biro ya ciri jotter daya
ya daura kan main jotter din ya fara rubutu da biron, iya layi hudu yayi rubutun
sai kuma ya rubuta digit hudu sannan ya ajiye biron ya kwanta breathing slowly, ta
dau takardan tana ta kallon rubutun sai kuma ta kallesa tace "Wa ya koya ma rubutu
haka?" Ya nuna mata makullin mota yace "Ki je pharmacy ki basu, akwai Atm card dina
a nan, ga pin na rubuta, current account" Sake baki tayi ta kallesa ta sake kallon
takardan hannunta, can tace "lallai, kai ne xaka wani rubuta ma kanka magani, a ina
ka san magani da har zaka rubuta ma kanka? Ko mutuwa kake so kayi?" fizge takardan
hannunta yayi a fusace yace "Bar shi ma" Ta wani hararesa ta kwace takardan tace
"Toh a ina aka ce ka siya maganin nan ka sha tunda kai dai ba likita bane" Kamar
baxai bata amsa ba don shi kadai yasan me yake ji a jikinsa, sai kuma yayi karfin
halin cewa "Likita ya turo min jiya da daddare" Tace "Wannan da ya zo ya dubani
ranan?" Mika mata hannu yayi yace "Idan baxa ki je ba bani takardan" Tabe baki tayi
ta mike ta tafi inda makullin motar yake ta dauka tare da makullin gida da Atm card
dinsa, sai kuma ta kallesa tace "Savings account?" Ba tare da ya buda idonsa da ya
kulle ba yace "Current" Tsayawa tayi tana kallonsa, sai kuma tace "Kasan meye
current account kuwa?" ya bude ido a hankali yace "Bani, ba sai kinje ba kuma" Ta
turo baki tace "To ai ni dai ba ruwana idan naje aka sa current aka rufe maka
account dinka" Daga haka ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta dawo ta marairaice
tace "Ni fa tsoro nake ji" Lumshe ido kawai yayi, tayi shiru tana kallonsa, can ta
bude kofar a hankali ta fita kafin kiftawar ido sai ga ta a compound tana maida
numfashi, gun motar ta nufa ta bude ta shiga ta kunna tana warming, sauka tayi ta
tafi gate amma ta kasa turawa har xata koma ta gaya masa sai kuma a hankali tace
"Toh ai shi ma ba iyawa xai yi ba tunda ba shi da lafiya" bude gate din tayi ta
fita kofar gida, ganin wani mutumi tace "Don Allah ka tayani bude gate din nan xan
fita da mota" yana shigowa zai bude mata ta tafi ta shiga motar, bayan ya bude ta
fita da motar waje, tana ganin ya kulle gate din ya fito tayi masa godiya sannan ta
sauka ta kulle gidan da makulli ta hau motar xuwa pharmacy, bayan magunguna har da
allurai taga an hada mata, ta basu Atm card dinsa da har xata ce masu Savings don
bata yarda da current da yace mata ba, sai dai kuma tace "Current" Suka cire
kudinsu suka mayar mata da atm card din ta amsa ta dinga jujjuyawa tana kallonsa,
daga karshe ta amshi ledan maganin ta fito ta tafi zuwa inda tayi parking. Nihad na
isa gida sai da ta kara neman wanda ya bude mata gate ta shiga da mota sannan ya
kulle, godiya tayi masa ta nufi kofar shiga ciki ta bude ta tsaya tana bin ko ina
na parlon da kallo, to ta ina Aljanun dare xa su shigo gidan bayan ko ina a kulle?
sai kuma tayi karfin halin shiga tana tafiya a hankali ta karasa dakinsa ta bude ta
shiga, kwance ta samesa yanda ta barsa ta ajiye ledan maganin hannunta ta durkusa
tana kallonsa tace "Ga maganin na siyo" Ya bude ido a hankali yana kallonta, ajiye
makulli da Atm card din hannunta tayi ta fita daga dakin zuwa kitchen, ba a dau
lkci ba ta dawo dakin rike da cup din shayi ta ajiye masa tace "Gashi" Tashi yayi
ya zauna ya bude ledan maganin da ta kawo ya fiddo su gaba daya, ta dau cup din
shayin ta mika masa tace "Gashi" Ya kalli cup din ya kalleta sai kuma ya amsa,
komawa gefe tayi ta zauna, lkci lkci take satan kallonsa kamar yanda shima yake
satan kallonta, da sun hada ido kuma sai kowa ya dauke kai, har ya kusa shanye
shayin sannan ya ajiye cup din taga ya fara hada allura, tana ta kallon ikon Allah,
taga ya sauke trousers dinsa, zaro ido tayi ta kauda kai da sauri ta rufe fuskarta
da tafin hannunta, bayan few seconds ta juyo a hankali, empy syringe ta gani, ta
mike da sauri tace "Me yasa zaka ma kanka allura?" Bai ko kalleta ba ya bude
maganin ya sha da sauran shayin da ya rage sannan ya koma ya kwanta ya lumshe ido
ta dinga kallonsa da mamaki, har bayan kusan minti goma bata ga ya bude idon ba sai
ma taga kamar bacci yake, juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta zauna,
ko minti sha biyar bata yi a parlon ba taji ana kwankwasa gate, ta tashi da sauri
ta koma daki, bacci taga yana yi heavily, ta dau makullin gidan ta fita zuwa gate
ta bude, Amina ta gani a tsaye sanye da uniform din islamiyya don ranan lahadi ce,
Amina na mika mata waya tace "Ina kwana, wai gashi Umma xata maki magana" Nihad ta
amshi wayar sai ga kiran Umma dagawa tayi ta kai kunne daga daya bangaren Umma tace
"Kin isa gidan Amina?" A hankali Nihad tace "Umma ina kwana?" Umma tace "Ya haka
Nihad, tun jiya ina ta jiranki shiru, Nayi ta kiran Husnah kuma bata daga wayar, ko
ta bar gidan ne?" Nihad tace "Ehh ta tafi Umma" Umma tace "Amma ba sai da nace maki
kar ki bari ta bar gidan ba sai mun gama magana da ke?" Nihad tace "Nima tashi nayi
naga bata gidan" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, kin tambayesan kuwa?" Nihad tace
"Ehh Umma, yace min sunan Mamarsa Nihad" Umma tace "Amma dai ke shashasha ce
wawuya, sai kika yi shiru kika kyalesa da yace maki haka?" Nihad tace "Wallahi haka
yace min" Tsaki Umma tayi tace "Baki da wayo ko kadan wallahi, kuma banga alamar za
kiyi wayon nan ba, ai shkkn sai kiyi ta zama da dreban, ni sai anjima, haba sai
kace ba mace ba ki rasa yanda xa ki bi da shi har ya gaya maki sunan iyayensa, ni
gata nake maki, gatan da uwarki ko mutuwa xaki yi baxata ta6a maki ba" Cikin sanyin
murya Nihad tace "Toh xan kara tambayarsa Umma kiyi hakuri" Umma tace "Ni sai
anjima da Allah" daga haka ta katse wayar cike da bacin rai, Amina ta karba tace
"Kin gama?" Nihad bata ce mata komai ba, Amina tace "Sai anjima" Daga haka ta shiga
adaidaita da xai kai ta islamiyya don kudin drop Umma ta bata, a hankali Nihad ta
juya ta koma cikin gidan. Umma ce zaune gaban wani Rantamemen mutumi ita da Hajiya
Turai, Umma na girgiza kai tace "Wallahi Malam ba a samo sunan iyayen nasa ba,
kasan yarinyar shashasha ce ga ta kuma er fari, ba wayo" Mutumin dake kallonsu da
jajayen tulla tullan idonsa yace "To ai tun farko nace maki xa a iya aiki da sunan
nasa kadai kuma aiki zai ci kamar yankan wuka, kawai ku dai in ji dumuss" Umma ta
gyara zama tace "Toh madallah malam, kuma ai kai ma kasan kudi ba matsala bace"
Yana muxurai yace "Ya kika ce sunan nasa?" Umma tace "Ibrahim" Girgiza kafa ya
dinga yi, bayan kusan minti daya ya kalleta da gefen ido yana murmushi yace "Yana
nan wani me kyau, dogo sangameme sannan shi ba baki ba, yana kuma da faffadan
kirji" Umma tace "Haka yake wallahi malam, duk yanda ka fada wllh haka ne" ya
kyalkyale da wani dariya Yace "Toh ai jefaffe ne tun asali, Jifa kuwa ba na wasa ba
aka yi masa, ga shi nan naga jifa iri iri a kansa, a jefe yake..." Su Umma dai suka
yi shiru suna kallonsa, ya langwabar da kai kamar me nazari sae kuma ya gyada kai
yace "Gashi nan an nuna min, ashe ma ruwa biyu ne, ko ta ɓangaren uwa ko na uba"
Umma tace "Ba shakka, hakan take malam, ai buzu ne, uwarsa wai er Nijar ce" Yayi
wani dariya yana jijjiga kai, Umma tace "Toh amma daga ina aka masa asirin Malam?"
Mutumin yayi wani shu'umin murmushi yace "Ɗan wani kauye ne kika ce?" Umma ta
girgiza kai tace "Aa, shi dai maigidana ne yasan sunan kauyen nasu tunda har can
yaje aka daura auren amma ni ban sani ba gaskiya" Yace "Toh daga kauyen nasu aka
jefesa, wato ana masa bakin ciki da ɗan abun da yake samu" Yana gyada kai yace "Shi
din me kwazon nema ne tun da ya taso, yana kuma da farin jini, dalilin da yasa ake
jifansa kenan.... Sihiri me karfi aka yi masa gashi nan na gani" Umma tace "Ikon
Allah, kuma gashi an ga ya fito birni nema dole kuma ya dinga samu sosai" Mutumin
yace "Kwarai kuwa, sannan kamar yanda nace maki Allah yayi sa da farin jini da
cikar kamala, duk wanda ya ra6a sai ya so shi so na gaske, zai kuma iya damka masa
amanar dukiyarsa sbda yarda" Umma ta wani hade rai tace "Toh ni sai6 yanzu so nake
ayi masa yanda sisin me gidana baxai sake shiga hannunsa ba don Ubansa, kasa masa
mugun tsanarsa wanda xai ji baya son ganinsa baya son mu'amala da shi har abada"
Hajiya Turai dake kallonta tace "Idan aka yi haka ke kuma ai sai ya iya cewa sai ya
sakar masa er sa" Shiru Umma tayi tana nazari, can wayar Umma ya fara ring ta bude
jaka da sauri ta fiddo ganin me kiranta tace "Minti biyu Malam" Daga haka ta mike
ta fita can tsakar gida ta daga wayar ta kai kunne tace "Malam barkanmu da safiya"
Ta kara da cewa "Eh ba a dai samo sunan ba amma nan da awa daya za mu karaso in sha
Allah, don Allah ka jira mu Malam kaga dai daga waje me nisa za mu zo" Hajiya Turai
na kallon Mutumin dake gabanta tace "Kana ji malam? so muke shi Alhajin ya fita
tsabgar daga shi dreban har yar tasa, sannan maganan gini da yace zai ma yar a
Zaria a rushe zancen kwata kwata, malam gaba daya a sa yaji bai son su gaba daya,
bai kuma son ganinsu, ita yar dama kawai ya sallama ma duniya ita, sannan abu na
karshe ka saka ma shi dreban jin son zai koma inda ya fito wato kauyensu, ka sa
zaman birnin ya gagaresa, idan ya so su koma can inda ya fito su ci gaba da zama
shi da ita yarinyar" Umma ta shigo ta zauna, Hajiya Turai ta kalleta tace "Duk na
gama gaya masa abinda zai yi" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shikenan"
Dariya mutumin yayi sosai yace "Kudi... Aikinku aiki ne babba, kuma aiki dole sai
da kudi, kinga kafin mu daura aiki a kansa dole za mu warware kadan daga abubuwan
da aka masa sannan aikin mu
xai samu shiga, ba a hada aiki da aiki ai, sai wancan aikin nasu ya lalata min
nawa, wato ya ki barin nawa yayi wani tasiri, ko kuma nawa ya rage tasirin nasu,
haka abun yake, yanzu dai nine xan rage tasirin na kansa sannan in dora nawa" Umma
tace "Tohh mu dai koma yaya za ayi kawai mu ga mun ci nasara malam, sannan ya dai
ci ace an saba yanzu Malam, abu dai shekara da shekaru ana tare ana harka, wannan
karan a dubemu karba tsula mana kudi" Hajiya Turai tace "Ai kuwa dai malam, ayi
mana sassauci gaskiya" Yana ta6e baki na wasu yan sakwanni sai kuma yace "Kawai ki
dire dubu dari da hamsin idan aikinki ya ci ki cika dubu hamsin" Umma ta bude
jakarta ta ciro zoben gwal ta ajiye masa tace "Gashi nan wannan dubu dari da
tamanin ce, ka rike ka fara min aiki" Ya amsa yace "An gama" tace "Toh malam zuwa
nan da yaushe za a fara aikin sannan za a fara ganin tasirin aikin?" Yace "Yanzu
zan afka jeji in fara aikinku babu bata lokaci, gaba daya a yau xan yi duk abinda
xan yi, zuwa gobe kuma aiki zai fara ci kamar yankan wuka" Umma na Murmushi tace
"Toh mun gode Malam, Allah ya saka maka da alkhairi, aikin ka ai mun san ba wasa,
mu yanzu za mu tafi sai na kira ka" Daga haka suka masa sallama suka kama hanyar
wani kauyen daban. Nihad na ta zaune parlor har kusan sha biyu, can ta mike ta nufi
dakin da yake kwance, a hankali ta murda kofar dakin tana kallonsa saman gado ta
gansa yana bacci, ta rufo dakin sannan ta shiga dayan dakin tayi wanka ta dauro
alwala ta shirya ta fito, sai da ta fara zagayawa ta kwaso kayan da Husnah ta wanke
mata ta kai su daki ta linke daga nan ta dawo parlor ta shiga kitchen, kallon
kitchen din kawai take, akwai kayan miya da komai a gidan kawai nama ne babu tunda
babu fridge, ta fito ta tafi dakinsa, ta bude kofar trying to make no sound, gun
Atm card dinsa ta tafi ta dauka da makullin mota da na gida sannan ta fito, cikin
mintin da bai wuce talatin ba ta fita taje ta siyo frozen chicken guda biyu da few
spices sannan ta dawo gida, ta sake daura alwala tayi sallah bayan ta idar ta koma
kitchen din, sai kusan karfe biyu ta fito daga kitchen bayan ta gama duk abinda
take, gaba daya ta gaji likis uwa wace tayi girkin mutane goma, ta fada kan kujera,
har ta mance rabon da tayi girki don ko da wasa Umma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login