Showing 153001 words to 156000 words out of 268471 words
za a rike min abubuwana akan laifin da
ban aikata ba? Akan something i knew nothing about, why???" Aunty Hassana ta bude
baki tace "Akan laifin da baka aikata ba? Ehh lallai ka cika mara kunya kuma
fitsararre, Sannan da ka mike a zabure haka dukan uban naka za kayi ko yaya?" A
fusace yace "Kee ni ban sa bakinki ba Hajiya, babu ruwanki da issue dina da
mahaifina, stay in ur lane and stay out of family issues da bai shafe ki ba" Aunty
Hassana ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da gefen gyalenta tana girgiza kai, sake
baki Abba yayi yana kallon Khalil, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon fuuu,
Mami dai ta ma rasa abun cewa, wato khalil baxai ta6a canzawa ba kenan, Abba ya hau
kai komo a parlon fuskarsa a murtuke, cike da karfin hali Mami na kallon Aunty
Hassana tace "Kiyi hakuri Hassana zan je in...." Wani tsawa ta daka ma Mami tace
"Bana bukata, duk ba ke ke sa shi yake raina mu ba, kiri kiri yaron nan ya daina
gaishe da ni da Amina a gidan nan, yaron da a haife na haifesa, yanzu kuma rashin
kunyar tasa da fitsara har ya kai kan ubansa, kayi laifi amma kafi kowa bakin
magana, miliyan dari takwas wasa ne yanzu? An daga maka kafa albarkacin tausasa
yaya da muke tayi ka dawo gida amma kace mune makiyanka? Yanzu da nawa ɗan nan zai
yarda da abinda khalil yayi min yanzu? Ba tashin hankali xa ayi ba kenan??" Abba
yace "Ki bar zancen nan, i know how to handle it, ke Fatima yarinyar da kika kawo
gidan nan without my knowledge wacece? Kuma daga ina take??" Mami ta kallesa da
mamaki, sai kuma tace "Sauran yaran da ake kawowa gidan nan su karaci zamansu su
wuce ka ta6a tambayar daga inda suke ko wa ya kawosu Yallabai? Yaran da har kudin
makaranta kai ke biya masu sai wannan da ko biyar dinka babu a makarantar da aka
biya mata?" Hassana ta mike a fusace tace "Kar ki kuskura kice zaki masa magana
yanda kika ga dama a gabana Fatima, ke kiyi ɗan ki yayi, to baku isa ba, kuma
wallahi baxan dauka ba don kiji in gaya maki" Mami ta daga kai tana kallonta, can
ta kalli Abba tace "To er ɗan uwana ne, kuma karatu ya kawota gidan...." Mami na
fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Aunty Hassana tace "Toh wa yaki zamanta a
gidan nan dama? Abinda Allah kadai yasan ladan ciyar da ɗan mutum, ai mu bamu ki
tayi ta zama har abada ba ma, kawai damuwar mu kamar yanda na gaya maka Yaya,
kwanaki can wani videon yarinya tsirara na ta yawo a kafofin sada zumunta, to ita
ce yarinyar" Abba na kallonta da kyau yace "Ke kin tabbata Hassana?" Aunty Hassana
tace "Zan maka karya ne yaya? Wallahi ita ce yara duk sun shaida mu ma kuma mun
shaida, babu amfanin nuna video din ne yanzu da sai in nuna maka, sannan tun da
yarinyar ta zo gidan nan bata gaida mu, sai dai mu wuce ta wuce saboda ta isa" Abba
ya dinga zaga parlon yana nazari bai dai ce komai ba, ran Aunty Hassana yayi fari
tass don duk hanyar da zata kuntata ma Mami nemansa take ido rufe.....
Mumy ce ta shigo bangaren Umma ta sameta a parlor tare da Kamila, Mumy tace "Dama
kina gidan nan Kamila?" Da sauri Umma ta amshe tace "Daxu ta zo, yanzu ma mijin
take jira wai" Mumy tace "Ohk, dama tambayarki zanyi kinji daga Nihal kuwa? Tun
jiya bana samunta a waya wallahi" Da damuwa Umma tace "Yanzu ma abinda muke
jajantawa kenan, har na gaji da kiran wayartata wallahi, na kira farooq yace min
yana Abuja amma gobe zai shiga kaduna sai ya karasa Zaria yaga ko lafiya" Mumy tace
"Toh duk yanda aka yi sace mata wayar aka yi" Kamila tace "Nima abinda nace kenan,
amma Umma duk ta daga hankalinta, babu tantama an dauke wayar ne" Umma tace "Sai ta
rasa wayar da xata kira mu da shi a kawayenta tace an dauke mata waya?" Mumy tace
"In sha Allahu lafiya lau take" Umma tace "Toh Allah ya sa" Juyawa Mumy tayi ta
fita daga parlon, Kamila tace "Ke abu indai ya shafi Nihal duk ki daga hankalinki
ki daga na wasu, ni gashi na kawo maki damuwata ko bin ta kaina baki yi ba sai
korata kike in bar gidan nan tun jiya" ko kulata Umma bata yi ba ta mike ta fita
daga parlon.
Littafin Nihaad na kudi ne, ki biya ki karanta cikin salama, idan ba haka ba akwai
dari biyar tsakaninmu.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
47
Washegari wajen karfe tara na safe kiran Farooq ya shigo wayar khalil dake bacci,
bude ido yayi a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, ganin Farooq ne ya
daga ya kai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Pls kwanakin baya kace min kuna
gaisawa da Nihal, when last ku ka yi magana da ita on phone?" Khalil ya ɗan yi
shiru, sai kuma yace "Not too long mun yi magana da ita, ta turo min waec result,
birth certificate, i mean all those stuffs saboda makarantar da nake nema ma er
uwarta...." Farooq yace "When was that pls?" Khalil yace "It was just last week,
Though bana iya reaching dinta a line dina so i used my other line shine na kirata
muka yi magana, hope all is well?" Farooq yace "For 2 days yanzu ba a samunta a
waya, i just arrived zaria but bani da contact din any of her Coursemate as i am
talking to you now...." Khalil ya mike zaune yace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un, or did she lost the phone?" Farooq yace "Ko ma haka ne ai ya kamata tayi
using ko wayar Coursemate dinta ta kira ta sanar, her problem is that she neva get
close or mingle with frnds" Khalil yace "Haka ne.... I am hoping she is fine in sha
Allah" Farooq yace "Shikenan, sae mun yi magana, thank you" Khalil yace "In sha
Allah... Nima xan yi ta trying line dinta" daga haka suka yi sallama, khalil yayi
amfani da daya wayarsa yayi dialing numberta don bata yi unblocking dinsa ba har
sannan daga main line dinsa, shima yaji wayar a kashe, he felt a bit tensed, then
what happened to her? Tambayar da yayi ma kansa kenan, after trying her line for
like 3 times ya ajiye wayar a hankali ya sauka daga saman gadon ya shiga bandaki.
Har kusan karfe sha biyu Khalil na trying line din Nihal also, he is just restless,
and he prays she is okay... Yana zaune parlon Mami wajen karfe uku Mami ta fito
daga dakinta ganinsa tace "Dama kana nan har yanzu?" yace "Eh" Mami tace "Wai har
sun kai kudin, ai kunyi magana da ita ko?" Khalil ya daga kai da sauri yace "Ohh
really, ni nama manta..." Mami tayi masa wani kallo da mamaki tace "Ka manta? I
don't understand ka manta" Yace "Wallahi i am disorganized ne gaba daya yau Mami"
Mami tace "Me ya faru?" Da har zai gaya ma Mami what is happening sai kuma ya fasa
cause bai san ta sigar da zata dau lamarin ba, bai san daga wani perspective zata
yi viewing issue din ba, kar tayi tunanin gidan ba tarbiya or something like that,
Mami tace "Kayi shiru" Ya sauke ajiyar zuciya yace "I am having a terrible headache
tun dazu" Da damuwa Mami tace "Subhanallah, toh Allah ya sauwake, ka sha magani?"
Yace "Yanzu xan je in sha" Tace "Do so immediately pls, ko da abinda kake so a
girka maka?" Yace "No, i am okay" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita
other parlor din, dai dai nan Mimi da Nihad suka bude kofar parlon dawowarsu kenan
daga makaranta, Hijab ne har kasa jikin Nihad with Nikab, she looks so cute in
them, Mimi tace "Yayanmu ina yini" yace "Lafiya lau" Nihad ta sunkuyar da kai ba
tare da ta kallesa ba slowly tace "Ina yini" ya ɗan kalleta yace "Lafiya lau" Daga
haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, suka karasa can parlon, Mimi ta zauna saman
kujera looking very tired ta gaida Mami, Nihad ma ta gaisheta, Mami tace "Sannunku
da zuwa" Mimi tace "Mami Noor bata dawo ba har yanzu?" Mami tace "Tana gidansu
Nadeeyah, kinsan yau aka kai kudin" Mimi ta zaro ido tace "Seriously? Yaushe aka sa
auren?" Mami tace "4 weeks in sha Allah" Mimi tace "Awwnn maa sha Allah, Allah
Ubangiji ya nuna mana lafiya, nasan it won't exceed that... I am so happy for the
love birds" Mami dai ta juya zuwa dakinta ta dalilin wayarta dake ring, Nihad dake
ta kallon Mimi ta mike daga saman Carpet da ta zauna, ta dawo gefenta ta cire Nikab
din fuskarta tana kallonta tace "Who is getting married?" Mimi ta wara ido tace "I
thought i told u yesterday, Yayanmu is getting hitched, yau aka kai kudin aurensa
with sister Nadeeyah...." Tana murmushi ta kare maganar, Kallonta Nihad take babu
ko kiftawa, Mimi tace "U remember me telling you?" Nihad ta sauke idonta tace
"Sure" Tashi tayi tace "Xan je inyi wanka" Mimi ma ta mike tace "I too, i need warm
shower" Tuni Nihad ta rigata ficewa daga parlon ta nufi dakin da take, ta fi minti
2 tsaye bakin kofar dakin bayan ta shiga ciki, can ta karasa inside of the room ta
zauna gefen gado a hankali.... Khalil na komawa dakinsa yaga miss calls din
Nadeeyah har hudu a babban wayarsa, ya zaune gefen gadon ya jingina bayansa da
pillow yayi dialing numberta, yana fara ringing ta daga, a hankali yace "How are
you Nadeeyah?" Kamar xata yi kuka tace "Why ain't you picking ur calls, ina ta
kiranka no response" Yace "Bana kusa ne" Tace "Ta yaya zaka ce min baka kusa, i
called almost 2 hours ago" yayi kasa da murya yace "Kina da son korafi da yawa
Nadeeyah, why?" shiru tayi, yace "Kinsan baxan ƙi daga kiranki just like that ba
ai, so why not believe bana kusa and have rest of mind" Nan ma bata ce komai ba,
yace "Hello, nasan kina ji na" a hankali tace "Shikenan, Allah ya baka hakuri, only
called to say Hi, na ji ka shiru all through" yace "Ina parlon Mami tun daxu, i am
sorry i missed your call, it wasn't intentional....." Ta gyada masa kai kawai bata
ce komai ba, yayi murmushi sanin da kyar if she is not in tears already, yace
"Karfe biyar xan zo in sha Allah, ki min wannan drink din da pancake me dadi da
kika min the other day, immediately after Magrib kuma we will be going out for
shopping" A hankali tace "Ohk" Calmly yace "I love you" Tana goge hawayen idonta
tace "Love you too" Yayi murmushi kawai ya katse wayar. Khalil ya sake trying wayar
Nihal for the countless time but a kashe, as at 2pm dazu ya kira farooq yaji if
there is any positive news, farooq yace har yanzu ba labari, ya ma je har
department dinsu wajen malaman, and an dubo few of her Coursemates sunce ai tun
jiya bata yi attending lectures ba, wannan batu ya sa hankalin Khalil ya tashi.
Biyar saura minti sha biyar Khalil ya shirya zai je wajen Nadeeyah kamar yanda yayi
mata alkawari, yana fita ya nufi bangaren Mami xai je yayi mata sallama, a hanya ya
hadu da Mimi tace "Yauwa yayanmu pls kana da paracetamol a dakinka?" Yace "Check my
room, who is taking paracetamol?" Tace "Neehad ce tace min kanta na ciwo, so i want
to give her to take" Yace "Where is she?" Tace "tana daki" Bai kuma ce mata komai
ba ya karasa parlon Mami ya zauna, after like 15 minutes Mimi ta dawo parlon ya
daga kai yana kallonta, tace "I have given her ta sha, yayanmu fita zaka yi kayi
dropping dina gidansu frnd dita Aziza pls? Today is her birthday...." Yace "Aa, ki
je driver ya kai ki" Tace "Ohk, tot u were going out" Ta figi jakarta don dama ta
shirya tace "Bye" Yace "Wait kin gaya ma Mami?" Tace "Yeah i told her kafin su fita
da Mom, i will be back in sha Allah after Magrib" Yace "Ohk, stay safe" murmushi
tayi masa ta gyada kai sannan ta fita da sauri daga parlon, wayarsa dake hannunsa
ya fara ring ya duba ganin farooq ne ya daga da sauri, farooq yace "I just reached
her minutes ago, the stupid girl wai ta raka wata roommate dinta garinsu bata da
lafiya a nan Zaria, i still don't get dalilin da yasa bayan ta rakata bata dawo a
ranan ba, wai kuma babu wuta and bata je da power bank ba...." Khalil ya sauke
ajiyar zuciya yace "Toh Alhamdulillah, but you have to take it easy pls, kasan ba
halinta bane, baxata zauna haka kawai babu dalili a can ba" Farooq yace "That's so
stupid of her, tasan mutane nawa ta daga ma hankali a can gida, har yanzu maganar
da nake maka bamu sanar ma Abba ba, we don't even have the courage to do so, and
God being so kind dama basu waya da shi kamar yanda yake da Nihad, sai in tana
bukatar abu suke waya da shi" Khalil yace "Take it easy pls, it's well in sha
Allah" Farooq yayi masa sallama ya katse wayar, sauke ajiyar zuciya Khalil yayi don
sai yanzu yaji hankalinsa ya kwanta, Nihal have a special place in his heart cause
she's one of the kindest soul he have ever met, ita ma baxai taɓa mance kindness
dinta toward him ba, dialing numberta yayi ya fara ring, bayan some seconds ta
daga, a hankali tace "Hello" Khalil yace "Me yasa kika yi abinda kika yi Nihal?" Ta
fashe da kuka kamar jira take bata dai ce komai ba, yace "Are you okay?" Ta gyada
masa kai kamar yana ganinta amma ta kasa cewa komai, yace "Nihal" tayi karfin halin
cewa "Na'am" Yace "Don't try that again pls, idan ma zaki je wani waje ki sanar
before doing so, ur parents trusted you so well shi yasa har suka bari kika yi nesa
da su kike karatu, ita er uwarki me gathering bad friends ai kinga they didn't
allow her move an inch from kano" Nihal dai kuka kawai take bata ce komai ba, a
hankali yace "Kin ji abinda nace maki?" cikin rawan murya tace "In sha Allah" yace
"Take care of ur self pls" a hankali tace "Ka gaishe min da Nihad" Yace "I will in
sha Allah" Daga haka ya katse wayar ya mike ya fita daga parlon Mami, dakin da
Nihad take ya nufa ya bude kofar dakin gently, kwance ya sameta ta rufe har kanta
da duvet, ya karasa bakin gadon ya janye duvet din a hankali yana kallonta, she is
just wearing a short gown, ta bude ido da sauri, suna hada ido ta hade rai ta juya,
yace "Ni kika ma wannan kallon?" Ta fashe da kuka ta sake juyowa tace "Ni ba da kai
nake ba" Yace "Tashi zaune" Ba musu ta mike zaune, zai cire duvet din daga jikinta
ta rike da sauri tace "Ni ban sa kaya ba" ya daure fuska yace "Sake" A hankali ta
sake ya cire ya mayar gefe, ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace "What's wrong
with you?" Taki ce masa komai, sai kuma hawaye ya hau zuba idonta, Kallonta kawai
yake ba ko kiftawa, ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, bai san sanda ya
zauna gefenta ba ya dagota da mamaki yace "Are you okay?" Kuka kawai take ta ki
cewa komai, ta sauke kafanta daga saman gadon zata sauka ya jawota ta fado jikinsa,
sai ta kara sautin kukanta, ya rungumeta yana kallonta amma bai sake ce mata komai
ba, ta gaji don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya tana shaƙar kamshinsa,
for almost 10 minutes suna nan a haka,
jin ta sakar masa jikinta gaba daya tana sauke numfashi a hankali ya sunkuya yana
kallon fuskarta, bacci yaga tana yi, ya dinga kallon lips dinta for almost a
minute, sai kuma ya dago a hankali ya jinginar da kansa jikin gadon ya lumshe
idonsa.... Da sauri khalil ya bude ido ta dalilin wayarsa da ke ring, he realized
he just slept off also, shi da baya baccin rana balle na yamma, ya kalli Nihad dake
kirjinsa tana ta bacci kamar warce ta samu lafiyayyen katifa, ya ciro wayarsa da
sauri jin ana sake kiransa, yaga Nadeeyah ce, kallon agogon wayar yayi yaga har
shidda da minti arba'in just few minutes to magrib, he was shocked and surprise at
the same time, ya sake kallon Nihad sai bai daga wayar ba har ya katse, still
Nadeeyah ta sake kira, Nihad ta bude idonta da sauri, dagowa tayi tana kallonsa, ya
wani hade rai, ta fara kalle kalle kamar munafuka, sai kuma ta matsa daga kusa da
shi, mikewa yayi yana rike da wayarsa ya fita daga dakin, sae a sannan ya daga
kiran Nadeeyah, a hankali tace "But you said 5pm" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace
"I am sorry Nadeeyah, i slept off without knowing i did...." Tace "Which means bani
da muhimmanci ko?" Ya ɗan hade rai yace "kin fara da korafinki again" a hankali
tace "Shikenan, sae anjima" Daga haka ta katse wayar, dakinsa kawai ya wuce ya
shiga bandaki.... Wajen karfe tara Khalil na zaune parlon Mami tare da Mimi da
Noor, Mimi na basu labari, Nihad ta bude kofar parlon a hankali, duk suka daga kai
suna kallonta, can ciki ciki tayi sallama that isn't audible, gaisuwan ma can ciki
tayi Noor dai sai kallonta take, Nihad ta nufi Mimi ta duka gabanta tana kallonta
murya can kasa tace "Pls kina da Android charger? I can't find mine" Mimi tace "Ohk
let me check" Tashi tayi Nihad ma ta mike ta bi bayanta Khalil ya bi su da kallo
har suka fita daga parlon, Ganin Nihad zata koma dakin da ta fito, Mimi tace "Mu je
sai in baki na Bilkisu" Nihad ta bi ta har zuwa bedroom din Bilkisu, Mimi na kallon
Bilkisu tace "Pls xaki ɗan mata lending charger dinki" Bilkisu tace "Ohk toh" daga
haka ta tashi ta dauko chargern ta ta mika ma Nihad, Nihad ta amsa tace "Thank you"
Bilkisu ta mata murmushi tace "My pleasure" Daga haka suka fito daga dakin, Nihad
ta wuce dakin da take, Mimi kuma ta koma parlon Mami, tana kallon yayanta da Noor
tace "Yauwa as i was saying" Nan ta ci gaba da basu labarin da take kafin ta fita,
ganin yanda Khalil ya lumshe ido Mimi tace "Yayanmu you are not listening bacci
kake" ya bude ido a hankali yace "I am sleepy" Mimi tace "Labari fa nake baka" Yayi
kasa da murya yace "Bacci" Noor ta kallesa tace "When did u start sleeping early?"
Mikewa yayi yace "Idan Mami ta shigo ku ce na tafi in kwanta