Showing 189001 words to 192000 words out of 268471 words

Chapter 64 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

strict yace "Tashi ki hau kujera" Da sauri ta mike ta zauna
saman kujeran ba tare da ta shirya hakan ba.... Khalil da ya fito part dinsa yana
ganin Aunty Hassana ta daya staircase din tana saukowa ya rage pace dinsa, tun
bayan da ya fito daga bangaren Abba ya shiga dakinsa bai fito ba sai yanzu, sallan
magrib ma a dakin yayi, kuma har zuwa sannan banda shayi da Mimi ta kai masa babu
abinda ya ci, Daga sama har kasa Aunty Hassana ke kallonsa, shi ko ya ki kallon
direction dinta, can kawai ta nufi bangaren Janar ganin can din shi ma za shi,
Khalil ya tsaya ya bi ta da wani kallo yaji kamar ya juya ya koma dakinsa, bude
kofar Main parlor din aka yi, sai ga Aunty Maryam ta shigo da karamin trolly dinta,
Khalil ya zaro ido yana kallonta ko kiftawa babu, Aunty Maryam ta sauke ajiyar
zuciya ganinsa don duk tunanin ko Janar yayi masa wani abun ne da taji Mami na ta
kuka a waya, ta nufosa da sauri tace "Ina Mami??" khalil ya kasa ce mata komai don
ba karamin girgiza yayi da ganinta ba, ta karaso tana kallonsa kafin tace komai ya
wara ido, cike da karfin hali yana murmushi yace "Aunty saukan yaushe? Ko dai dama
kina kasar ne" Aunty Maryam ta galla masa harara tace "Ehh ina kasar, Mami idan
bata daga ma mutum hankali ba bata jin dadi ai, ga dai ni Allah ya kawo ni lafiya,
tana ina?? Shi kuma ya ga daman fitowa da kai daga guardroom din kenan...." Khalil
dai sai zufa yake yana kirkiran murmushin yake ya kasa ce mata komai, duk maganar
da take yi ma shi ba fahimta yake ba, Aunty Maryam tace "Ji wai ina maka magana
kana min Murmushi kamar sha sha sha, tambayarka nake ina Mami??" Ya hadiye wani abu
da ya tokaresa da kyar yace "Upstairs..." Dai dai nan Noor ta fito daga bangaren
Abba, ta zaro ido ganin Aunty Maryam ta taho da gudu ta rungumeta tace "Aunty daga
ina kike haka?" tace "Wallahi daga Uk, tun bayan da muka yi wannan wayar dake
hankalina ya kasa kwanciya kawai nayi ma Abbansu Zeenah magana ya kuma bar ni na
taho, me yasa
Mami take haka don Allah, yanzu ba ga Khalil din ba, duk ta bi ta daga min
hankali, haka kawai taje cutarta ya tashi a banza, komai baxata bi sa a sannu ba"
Noor ta amshi jakarta tana Murmushi tace "Mu tafi sama Aunty, sannu da hanya" sai
kuma ta kalli Khalil da sauri tace "Lahh Abba is waiting for you tun dazu fa
yayanmu..." Bai ce komai ba ya nufi parlon yana tafiya a hankali, Aunty Maryam ta
bi sa da kallo sannan ta kalli Noor tace "Tun yaushe ya sa aka sake sa?" Noor tace
"Tun da safe, da Abban ya dawo ya sa a fiddo shi, kinsan ba shi da lafiya so he is
under medication now" Aunty Maryam ta girgiza kai a ranta tana Allah wadai da mugun
halin janar, sai kace ba ɗan da ya haifa ba, Sama ta nufa Noor na biye da ita a
baya rike da karamin akwatin ta, dai dai kofar shiga parlon Mami suka hadu da
Mamin, Aunty Maryam taji gabanta ya fadi ganin idanuwan Mami and how weak she
looks, hankali tashe tace "Subhanallahi Mami, lafiya?? Me ya sameki haka?" Mami ta
kasa cewa komai ganin er uwartata kawai ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai,
Aunty Maryam ta rungumeta hankalinta a mugun tashe tace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un, Yaya me ya faru? Don Allah ki min magana What's happening?" Cike da karfin
hali Mami tace "Janar ya kira yana jirana a parlonsa, mu tafi can din...." Iyakar
tashi hankalin Aunty Maryam ya tashi a lokacin, ita kanta Noor jikinta yayi sanyi
sosai ta koma gefe ta dinga kallon Mami, Aunty Maryam ta kama hannun Mami ranta a
dagule tace "Mu je parlon" yau ta dau alwashin sai ta ma Janar wankin babban bargo
in har dalilinsa Mami ta shiga wannan damuwar take kuka haka, dama tara sa kawai
take, tana rike da Mami zuciyarta na bugawa tace "Mu je parlon nasa" Mami dai na
biye da ita kawai. Tun da Khalil ya shigo parlon yayi ma Aunty Hassana kallo daya
ya nemi kujera ya zauna, Aunty Hassana bata fasa maganar da take ma Janar ba tace
"Shine fa ta kirani wai bata sani ba ko ta maka wani laifin ne, kasan halin
kauyawan nan da rashin wayewa yanzu yanzu sai su juya wannan lamarin, barin suna
ganin ba uwa daya uba daya bane, to wani tsiyar suka taɓa kullala mana har Allah ya
kawo mu iyanzu? ni nasan duk a kullace suke da kai tun da muka tare nan gidan
shekara kusan shidda kenan babu wanda ya san inda muke iyaka idan zaka masu aike ka
bani in tura masu, toh su ai ba haka suka so ba, sun fi so su yi ta maka zarya wasu
in sun zo ma sai su shekara basu tafi ba ga ka shugaban kasa, Ya dikko ma ta kirani
jiya...." Janar ya dakatar da ita yace "Kee Hassana, maganar da ta kawo ki kenan??"
tayi shiru, yace "Toh bana son zancen, kowa ya dade bai yi tunanin dake ransa ba,
clear??" Sai kuma ya dauke kansa ya kalli Khalil da idonsa ke kan Nihad, ita kuwa
taki barin su hada ido ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Aunty Hassana ta
gyara zama tana kare ma Nihad kallo tana mamakin ita kuma uban me take yau a parlon
Janar, ita dama ba zancen da take ma Janar bane ya kawota, aa dalilinta na shigowa
daban amma sai ta fake da wannan zancen, dai dai nan Mami da Aunty Maryam suka
shigo parlon, Tsabar tashin hankali Khalil ji yayi dama kasa ta bude masa kawai ya
shige, ya kasa hada ido da su biyun, Aunty Maryam tayi mugun mamakin ganin Nihad
zaune parlon, can ta kalli Khalil sannan ta sake kallon Nihad din cike da mamaki,
to me ke faruwa, ba Mami tace mata ta koma gidansu ba, yaushe kuma ta dawo nan,
sannan me take yi a parlon Janar, Aunty Maryam ta kalli Janar dake kallonsu lokaci
daya ta ɗan hade rai, babu yabo babu fallasa tace "Barka da dare Janar" Yace
"Barka" Tana rike da hannun Mami suka tafi 2 seater suka zauna, Aunty Hassana sai
kallon ikon Allah take, yaushe ita kuma wannan galallawar ta dawo kasar, Can dai
tace "Sannu Maryam, yaushe a gari" a takaice Aunty Maryam tace "Daxu na sauka, ya
yaran?" Aunty Hassana tace "Lafiya lau, sannu da zuwa" Daga haka duk suka yi shiru
a parlon, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take, she don't know if she should be
happy or not, duk da damuwan da ya cika xuciyar Aunty Maryam haka ta mata murmushi,
Nihad ta mayar mata da murmushin amma na karfin hali, cikin sanyin murya tace
"Sannu da zuwa Aunty" Aunty Maryam tace "Sannu Nihad" Janar ya nisa, sai kuma yana
kallon Nihad ya nuna mata Khalil yace "Wanene wancan?" Khalil yaji gabansa ya wani
fadi, he wish rana irin ta yau baxai taɓa zuwa ba, amma dole ne ya zo, ya jinginar
da kansa jikin kujeran da yake zaune zuciyarsa na bugawa, gashi dai duk da wannan
tashin hankalin nasa yana jin takaici yanda za ayi magana a gaban Aunty Hassana,
Ita kuwa Aunty Hassana sai gwaggwale ido take a parlon tana son jin dai me ke
faruwa, Nihad ta kalli Khalil ta sunkuyar da kanta a hankali, ita ma har sannan
gabanta faduwa yake sosai, a ɗan tsawace Janar yace "Ke magana nake maki, or are
you deaf?" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta daga kai tana kallon Khalil,
duk a tsorace take, da zaka kalli yanda kirjinta ke heaving sai ka tausaya mata,
Janar ya kula da she is afraid kuma a rude take, Sai yayi calming voice dinsa yace
"Fatima ko??" Nihad ta kallesa da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta,
ya nuna mata gefensa calmly yace "Dawo nan" A hankali ta tashi ta dai daita
tafiyarta ta nufesa walking slowly, ta durkusa inda ya nuna mata, ya nuna mata
saman kujeran yace "No, nan zaki zauna" Kasa kallonsa tayi ta mike a hankali ta
zauna gefensa gabanta na faduwa kamar zai fito, Aunty Hassana dai sai kallon ikon
Allah take, yau ga sabon salo, Mami dai kanta na kasa, Aunty Maryam kuwa sai kallon
Janar take kamar ta shakesa ta huta.... Speaking Calmly Janar yace "Kinsan wancan
mutumin dake zaune Fatima?" Nihad ta kara kallon Khalil ta gyada kai, Janar yace
"To wanene?" Tana tsoron tayi shiru Janar ya mata ihu, sannan kuma ita bata gane
kan tambayar Janar ba, she is just confuse, kamar ya gane she is confuse yace "I
mean, meye tsakaninku Fatima?" Ta sake Kallon Khalil with her heart beating so
fast, shi dai idonsa na kan Ac dake tsaye parlon baya ko kiftawa, a hankali tace
"Ya zauna gidanmu" Janar na gyada kai yace "Good... What took him there?" Cikin
sanyin murya tace "He was our driver...." Ba Janar ba har Aunty Hassana da su Mami
sai da suka kalli Khalil da sauri, shi dai idonsa na kan Ac, Janar look a bit
confused ya dinga kallonsa, can yace "Kamar yaya fatima?" Ta sunkuyar da kanta tace
"Driving dinmu yake yi, Abbana na biyansa kudi" Janar yayi shiru for almost 30
seconds, can ya daga kai ya kalli Khalil, wanda shi ma Khalil din kallonsa yake
this time around, su Aunty Maryam kuwa sai kallon Khalil din suke da mamaki, Janar
ya dauke kansa ya sake kallon Nihad yace "For how long?" Nihad na jan fingers dinta
a Hankali tace "For almost a year" Janar ya sake yin shiru, sai kuma yace "A gidan
naku yake zama kuma?" Nihad ta gyada kai tana wasa da yatsunta tace "A chalet din
gidanmu yake tare da sauran masu aiki a gidanmu" Lokaci daya hawaye ya kawo idon
Aunty Maryam, Khalil ya rike kansa..... Janar dai yayi shiru kamar iyakar
tambayoyin da zai ma Nihad kenan, bayan wani ɗan lokaci ya sake kallonta yace "Did
u have an idea of nawa Abban naki ke basa?" Nihad ta kalli Khalil, a hankali ta
girgiza kai tace "Nima ban sani ba" Janar yace "Sai kuma me ya faru da har ya taho
dake garin nan?" Hawaye ya cika idon Nihad a hankali cikin sanyin murya tace
"Abbana ya min aure da shi" Sai kuma ta rufe fuskarta jikin kujera tana kuka a
hankali, Aunty Maryam tayi mutuwar zaune a inda take saboda yanda ta girgiza da
abinda Nihad tace, ta dinga kallon both Nihad and Khalil a tare, with her mouth
agape, Aunty Hassana bata san sanda ta mike tsaye tana kallonsu ba ita ma, Mami dai
sai hawaye take ta kasa dago kanta, Janar ya dafa shoulder din Nihad yace "Wani
anguwan ku ke a Kano?" Ta dago kanta hawaye caɓa caɓa a fuskarta cikin rawan murya
tace "Nasarawa GRA" Janar yace "Ya sunan Abbanki?" A hankali Nihad tace "Alhaji
Ibrahim Sadeeq" Janar yayi shiru yana gyada kai, can ya mike ya shiga bedroom dinsa
sai ga shi ya dawo rike da Makulli a hannunsa, ya ajiye ma Khalil Makullin yace
"Dauketa ku tafi can gidan naka, ku shirya gobe xa mu tafi kanon gaba daya" Khalil
ya dinga kallon Abban nasa, Janar ya ɗan masa tsawa yace "Baka ji me nace bane"
Khalil ya mike yana kallon Mami da ke ta hawaye, Ita kuwa Aunty Maryam tsabar shock
ta kasa fa rufe baki, Janar ya kalli Nihad yace "Ta shi ku tafi Fatima, Allah ya
tashe mu lafiya" A hankali Nihad ta mike har sannan hawaye na makale idonta, Khalil
ya kalli Mami da kanta ke kasa, Sai kuma ya kalli Abbansa, Wani kallo Janar yayi
masa, ya nufi kofa Nihad ta bi bayansa har suka fita daga parlon, Aunty Hassana
dake ta wurga ido, tana rawan baki tace "Yaya, ban gane ya tafi da ita gidansa ba,
kai ka yarda....." Janar ya dakatar da ita yace "Fita ki ban waje Hassana"


*Kiyi kokarin sauke nauyin 500 akan ki Aunty and Mama*


Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Via 07087865788



https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting
fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any
of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil
perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114


57

Tun da Nihad ta hango Aliyu tsaye bakin kofar Main parlor bayan sun fito bangaren
Janar ta rikice ga shi ba abun tace zata juya ba ko zata canza direction, in ma
tayi hakan ina zata? Ga khalil sai tafiyarsa yake duk da ya gansa, lokaci daya ta
fara bobboye fuskarta da hijab dinta tana sisinne kai kamar munafuka, gaba daya ta
daburce ta rikice, shi ko khalil tunda yayi ma Aliyu kallo daya ya dauke kansa
walking Majestically, Aliyu ya dinga kallon Nihad don reaction dinta ne ma ya fara
jan hankalinsa gareta, at first he didn't even care to notice who she was, amma
yanda yaga take yi ya sa ya dinga kallonta, Khalil ya kai hannu ya bude kofar
parlon, Aliyu ya cire wayar kunnensa a hankali ya mayar aljihunsa yana kallon Nihad
keenly kamar wanda ya gano abu, her eyes, her scent, the way she walks, Nihad dai
taki yarda ta kallesa kuma bata fasa rufe fuskarta da hijab ba ga wani faduwa da
gabanta ke ta yi, sai harde kafa take tsabar rudewa, tana isa dai dai kofar bata
san sanda ta daga idanuwanta suka hada ido da shi ba, ta sauke idonta da sauri tana
kokarin fita yayi hanzarin fizgota ya janye Hijab din da ta rufe fuskarta da shi,
ya wani zaro ido yana komawa baya yace "Nihad????" Ko rufe baki bai yi ba yaji an
wani tura sa yayi baya kamar zai fadi, Khalil na masa wani kallo cikin husky voice
yace "Do not ever try that again...." banda zare ido babu abinda Aliyu yake with
confusion yana bin Nihad da kallo, ita dai Nihad tuni ta fita compound a rikice har
tana neman faduwa, Aliyu ya cakumo Khalil yana masa wani kallo yace "How dare you??
A ina ka santa kake warning dina?" Wani wawan naushi Khalil ya kai masa, Aliyu yayi
saurin kaucewa yana zare ido, Aunty Hassana da ta fito daga bangaren Janar rai a
dagule ta zaro ido tana kallonsu ganin abinda ke faruwa tace "Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, Meye haka???" da gudu ta nufesu ta shiga tsakaninsu ganin ana
kokarin kai naushi, Khalil na ganin haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama,
Aunty Hassana na kallon Aliyu idanuwanta kamar za su fito tace "Ina ruwanka da ɗan
wiwin nan zaka tsaya kana ɓata lokaci a kansa har ku ke neman ba hammata iska? Ina
kai ina shi? Responsible somebody like you, kai da zaka fita Germany ma gobe meye
na biye mara aikin yi wanda ake tsoron daurasa kan harkokin arziki?" Aliyu na zare
ido cikin wani yanayi yace "Mum, mum budurwata ce na gani a gidan nan, ita ce
wallahi, Nihad ce, what is she doing here?" Aunty Hassana tayi galala tana kallonsa
tace "Budurwarka kuma? A ina budurwar taka?" Aliyu na nuna mata waje yace "He just
left with her now, wa ya kawota gidan nan? Wajen wa ta zo?? Mum Nihad ce fa" Aunty
Hassana dai ta saki baki tana kallonsa, can tace "Wai yarinyar nan da ya fita tare
da yanzun nan kake magana?" Da sauri Aliyu yace "Ita Mum, ita nake nufi, wajen wa
ta zo a gidan nan??" Aunty Hassana tace "A'a, anya kanka daya kuwa Aliyu, yanzu fa
yarinyar ke cewa ya zauna a gidansu a kano...." Aliyu da kansa ya gama daurewa ya
dinga kallon Aunty Hassana babu ko kiftawa, a hankali yace "Gidansu kuma? Me yaje
yi gidansu?" Aunty Hassana tace "Wai driving, yanzun nan da bakinta take gaya ma
Janar wallahi....." Still Aliyu yayi yana kallon mum din tasa baki bude, Aunty
Hassana tace "Kaga ka fitar da ni a duhu Aliyu, kai a ina kasan yarinyar?" Yayi
karfin halin cewa "A kano na santa, budurwata ce kuma ita nake son zan aura,
wallahi budurwata ce" Aunty Hassana ta rike haɓa a hankali tace "Budurwarka? Wai fa
matarsa ce an daura masu aure, da bakinta yanzu take gaya ma Janar wai ubanta ya
daura mata aure da shi" Aliyu ya dinga kallonta babu ko kiftawa, a hankali yace
"Shi ya aureta dama??" Aunty Hassana tace "Wallahi haka nan ta ce" A hankali Aliyu
ya juya mata baya with different thought running his mind all at the same time,
Driver? Khalil ne sabon drivern gidan nasu da take gaya masa dama? girgiza kai yayi
da sauri not wanting to believe that, sai kuma ya tuna encounter dinsa da so called
sabon drivern a ranan da yaje ya sameta a Mall, Aliyu ya dinga jin zuciyarsa na
bugawa, wait!! is this really happening??? Aunty Hassana dake ta kallon ɗan nata
tace "Naji kayi shiru, ko dai kawai kaga kama ne Aliyu, amma me zai kawo budurwarka
gidan nan ana zaune lafiya, kamar dai a wasan kwaikwayo...." Lokaci daya Aliyu ya
juyo yana kallonta da karfi yace "Budurwata ce Mum, duk duniya kuma babu macen da
nake so sama da ita, ita fa nake ce maki zan aura kwanaki, ita ce fa, dalilin da na
zo nace maki na fasa auren a lokacin Video dinta with just Underwear aka yi leaking
a internet...." Aunty Hassana ta buda baki hangangan, murya kasa kasa tace "Ita ce
dama da gaske a videon??" Aliyu bai ce mata komai ba, Aunty Hassana ta gyada kai a
hankali tace "Ai ko Janar bai sani ba sun boye masa... Na gaya maka yarinyar fa
cewa tayi Khalil din ya zauna gidansu a matsayin dreba na shekara daya, ashe duk
tsawon lokacin da baya gidan yana can gidansu, sannan ta dawo tace ubanta ya aura
mata shi, da yake asirinsu ya fara ci Janar ko kallon banza bai yi ma Khalil din a
parlon ba, ita kuwa uwar sai kukan munafurci take, yanzu kana nufin ka taɓa soyayya
da yarinyar???" Aliyu na kallon Mum dinsa yayi wani murmushi, calmly yace "Idan
kuwa da gaske shi aka aura ma Nihad, to ina me tabbatar maki in dai ina numfashi
wallahi baxai yi rayuwa da ita a matsayin matarsa ba, yanda naki jininsa baxan taba
bari yayi rayuwa tare da warce nayi soyayya da ba, ko da kuwa ba aurenta xan yi ba,
he is Mad...." Yana kai wa nan yayi hanyar dakinsa kamar zai tashi sama, Aunty
Hassana dai ta bi sa da kallo, can ta gyada kai a hankali kamar me nazari, sai kuma
ta bi bayansa da sauri. Tun barinsu gidan Khalil ke driving yana kallon Nihad da ta
kauda kanta taki kallon inda yake gaba daya, wani mugun haushinsa take ji har
ranta, a tsorace tayi wani kara bayan ya kauce ma wani motar da ya kusa colliding
ma a gabansa, duk da haka kuma sai da ya gurji motar, ta juya da sauri tana
kallonsa tana zaro ido, bude motar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login