Showing 255001 words to 258000 words out of 268471 words

Chapter 86 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ta karshe da
za ki shigo unguwar nan idan ba haka ba wallahi baza ki ji da dadi hannun sojojina
ba" Ta marairaice tace "Toh yaya nagode, Allah ya kara girma" Daga haka ta mike ta
dau Handbag dinta ta nufi kofa, Umaru ya bi ta da kallo baki bude har ta fita,
Janar yace "Na tura maka 100k ka kara mai a motarka" Yayi shiru da farko, sai kuma
yace "Toh, toh, to ba damuwa" Janar yace "Zan shiga ciki, ina expecting wasu baƙin"
Mikewa Umaru yayi ya nufi kofa, kana ganin reaction dinsa kasan ya raina 100k din,
har ya fice daga parlon babu sai anjima, Janar ya koma part dinsa, Aunty Hassana na
barin gidan ta kira wata kawarta da ta hadata da wani sabon malami dake cikin garin
Abuja, bayan sun gaisa tace "Sabira na samo kudi yanzun nan, nawa kika ce yace za a
bashi last price?" Sabira tace "Ke Allah fa ya sa ya samu lokacinmu, Kinsan yan
siyasa kawai yake ma aiki amma zan je har gidansa in lallabasa yayi mana aikin"
Aunty Hassana tace "Yanzu dai nawa za a bashi nake tambayarki?" Tace "Wallahi
miliyan biyu ma Allah ya sa ya kallemu, shi fa aikinsa kamar yankar wuka yake,
karamin kudi da yake amsa idan yayi aiki baya yin kasa da miliyan biyu" Aunty
Hassana tace "Toh zan tura maki yanzu, Don Allah ko ma me zai yi yayi kawai aga
cewar ba er sa bace a result din nan" Sabira tayi wani dariya tace "Sha kuruminki
Hassana, kawai dai ki hado min da miliyan daya da na ara maki kika kai ma wannan
munafukin malamin da har yau bakya samunsa a waya" Aunty Hassana ta ɗan yi shiru,
yanzu fa idan ta tura 3m kudin saura 2m kenan fa, a ranta tace to meye in dai
bukata zata biya, ana gamawa da case din Hanan, sauran miliyan biyun zata ba
malamin yayi mata aiki akan Janar, sanda zai ce ta dawo ba sani zai yi ba. Tun da
Khalil ya shigo corridor din part din Mami ya ji wani kamshin turaren wuta me
birkita hankali na tashi amma ya rasa ta wani direction ne, it's just past 9 now,
yayi ta bin ko ina da kallo, can ya nufi guess room dake part din don kamar ta nan
kamshin ke fitowa ya baza corridor din, bude kofar dakin yayi yana kallon ciki,
tana zaune gaban mirror tana shafa kwallacham, ga garwashin turaren wutan a kasa,
ta zaro ido tana kallonsa har ya tura kofar ya karaso cikin dakin ya nufota yana
kallon gashin kanta da yayi bakikirin sai sheki yake, tayi narai narai da ido tace
"Wallahi yanzun nan Mami ta fita kuma yanzu zata dawo, plssss ka fita kar ta shigo"
Ya jingina da bayanta yana jin wani fitinannen kamshi na tashi a jikinta hade da na
turaren wuta, ga wani laushi na musamman da yaji jikinta ya kara kamar ainahin
auduga, kasa magana yayi da farko, can dai ya dake murya can kasa yace "Ina kika
shiga duk yau ban ganki ba Baby? I have search everywhere ban ganki ba" yana fadin
haka taji chilled lips dinsa a wuyanta, ta marairaice tace "Na shiga uku, don Allah
ka bari pls, wllh Mami is coming back now" Ko rufe baki bata yi ba Mami ta bude
kofar dakin, da sauri ya saketa ya koma baya, kallo daya Mami tayi masa ta nufi gun
garwashin wutan rike da wani kwalban turaren wuta, Nihad dai ta kasa daga kanta ta
ci gaba da shafa kwallacham da take yi, Ya kasa kallon Mami shi ma don juya mata
baya ma yayi, can dai ya shafa kansa ya nufi kofa kamar munafuki har ya fita daga
dakin ya jawo kofar, Mami ta gama sa mata turaren wutan wanda na tsugunno ne, ta sa
mata stool din sannan ta gaya mata yanda zata yi, Mami na tsaye for almost 7
minutes kafin tace "Dau kayan baccin naki mu je ki kwanta" da a nan dakin zata
kwanta amma jin abinda Mami tace mata ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta bi
bayan Mami zuwa ɓangarenta ta kwanta a bedroom dinta, ita kanta wani daban take jin
ta, tun da suka fita daxu da safe suka tafi wani tsadadden saloon wanda ya fi inda
Mimi ta fara kai ta farkon zuwanta gidan, bayan an gama mata gyaran gashi aka kai
ta wajen gyaran jiki duk a katon building din saloon din, ita kanta bayan an gama
gyaran jikin sai da jikinta ya bata sha'awa, luwai din kenan don sai wani glowing
take ko ina yayi sumul a jikinta, washegari da safe ma zata sake komawa saloon din
don ci gaba da gyaran jikin, tun da suka dawo kuwa Mami ta bata abubuwa sun fi a
kirga ta sha, shi yasa ko abincin dare ma bata iya ta ci da yawa ba, a haka har
bacci ya dauketa, da mafarkai iri iri na mijinta. wajen karfe sha daya sai da
khalil ya sake komawa dakin amma ya ga wayam, he felt like dying... Washegari da
safe ya shigo bangaren Mami, jiya da damuwa ya kwanta don ko baccin kirki bai iya
yayi ba, he just can't endure it any longer shi dai kawai a basa matarsa su bar
gidan nan, Bayan ya gaida Mami yayi shiru ya ma rasa me zai ce mata, Wayar Mami ya
fara ring ganin Janar ke kiranta ta mike ta fita daga parlon zuwa ɓangarensa, a
hankali ya mike ya nufi Bedroom dinta don tun da ya shigo kamshin Nihad na jiya
kawai yake ji a parlon, babu kowa dakin kawai ya juya ya fice daga bangaren rai
bace, don kafin ya shigo sai da ya fara shiga guess room nan ma babu kowa ciki, har
dakin Mimi ya shiga yaga ba kowa, kawai ya nufi dakin Noor ko amsa gaisuwarta bai
yi ba yace "Ina su Mimi?" Tace "Mami ta sa driver ya fita da su not too long" Kasa
cewa komai yayi, can ya juya fuu ya bar bakin kofar ya koma dakinsa, makullin mota
kawai ya dauka ya bar gidan ko zae samu relieve din walakancin nan da ake masa....
Mami na zaune parlon janar bayan ya sanar mata dalilin da yasa ya kirata har ya
bata takardan ta duba, cike da murna tace "Alhamdulillah, what a good news, Naji
dadin wannan lamarin wallahi, dama kai ne kawai ka sa kokwanto a zuciyarka tun
farko, amma ni har ga Allah naji a raina ba haka bane, to maa sha Allah tunda yanzu
zaka kauda zargi a ranka" Janar ya nisa yace "Abokina da ke kaduna will be coming
back together with her tomorrow don akwai jirgin sojoji da zai taho nan Abuja" Mami
tace "Toh Allah ya kai mu" Bata jima a parlon ba don ta bar wayarta a parlonta kuma
za a kawo mata turarrukan wuta da tayi order jiya da daddare, har ranta tayi farin
cikin kasancewar Hanan er Janar she is so happy with this good news. Sai kusan
azahar su Nihad suka dawo tare da Mimi glowing din yau har ya fi na jiya, gyara ne
na gaske aka mata wanda da zaka ji kudin da aka kashe zaka rike baki, bayan sun yi
wanka sun ci abinci Mami tace "Kin kira mum dinki yau?" Nihad tace "Ehh mun yi
magana da ita" Mami tace "Good, ki hada duk kayanki dake nan, zuwa da yamma za ku
koma can gidanku..." Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mimi ce ta hada mata
kayan nata duk a akwati biyu, bayan la'asar Mami ta sa ta taje tayi wanka ta shirya
cikin riga da skirt na atamfa da mayafinsa, sannan ta bata sauran magungunan nata
da suka rage ta sakata ta shanyesu tas, Ganin normal dankunne ne a kunnenta ta bata
na gold ta saka, Suna daki Khalil ya shigo parlon ta dalilin kiransa da Mami tayi
almost 2 hours ago, Mami ta fito ta gansa zaune, ya gaisheta can ciki ciki, Mami na
lura da yanda ya wani tamke fuska ta ci gaba da harkokin gabanta a parlon, can dai
yace "Gani Mami" Mami ta kirawo Nihad, Nihad ta fito parlon ta duka jikin kujera
tace "Gani" Mami tace "Fito da kayan naki ku wuce" Khalil ya daga kai ya kalli Mami
da sauri yana son sake tabbatar da abinda tace, Nihad dai bata ce komai ba kuma
bata dago kanta ba, Mami tace "Ko kuma bari in kira Mimi ta kai maki kayan mota" Ta
dau wayarta kan kujera tayi dialing number Mimi ta ce ta zo ita da Bilkisu su fitar
da kayan Nihad zuwa mota, Mikewa Nihad tayi a hankali ta koma dakin, Khalil ya ɗan
kalli Mami sai kuma ya mike ya nufi kofar dakin yana kallon Nihad yace "Ina kayan?"
Ta kallesa da sauri, shi yayi abun amma ita ta tayasa jin kunyan, tayi narai narai
da ido tana kallonsa kamar zata yi kuka, ko a jikinsa ya karaso ya dau duk akwatin
biyun ya fita, Mimi da Bilkisu na shigowa turarrukan wutan da Mami tayi order ma
Nihad suka dinga fitarwa zuwa motarsa, turarrukan wuta ne masu shegen tsada, da na
tsugunno, kwallacham, Humra, miski, infact duk wani abun kamshi dai da mace zata
bukata, Nihad dai na jikin kujera kanta a kasa, Mami tace "Toh Allah Ubangiji ya
baku zaman lafiya Nihad, ki kula da tsaftar jikinki da na gidanki... sannan kuma
kiyi hakuri ki zauna lafiya da mijinki kin ji?" Cikin sanyin murya Nihad tace
"Nagode Mami, Allah ya kara girma" Mami tayi mata murmushi tace "Ameen" Khalil ya
shigo parlon ya shafa kai yana kallon Mami yace "Za mu tafi Mami" Taɓe baki Mami
tayi tace "Allah ya tsare" Daga haka ta nufi dakinta tana kallon Nihad tace "Toh
tashi ku je, Allah ya kiyaye hanya" Nihad da har hawaye ya cika idonta ta mike a
hankali tace "Nagode Mami" Yana gaba tana biye da shi suka fito babban compound din
gidan, Mimi na tsaye har suka bar compound din tana daga masu hannu, sai bayan da
suka bar anguwan ya kalli Nihad dake share kwallar da yaki tsaya mata, ya gyada kai
yace "Na gasken zaki yi anjima, wannan ai ba kuka kike ba" Ta ɗan kallesa cike da
shagwaba tace "Toh ina ruwanka da kukana" Er dariya yayi yace "Kin ga kuwa Anjima
ai da ruwana da kukanki tunda ni zan sa ki"



*Toh a dai yi kokari a sauke hakki, idan baki sauke a nan ba to ban san kuma inda
zaki je ki sauke ba, cause my book is not free*



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788

78

Har suka kusa gida Nihad bata ce masa komai ba don tayi nisa duniyar tunanin da ta
tafi, da ta tuna Khalil is getting married soon sai taji gabanta ya fadi sosai,
amma idan ta duba yanda ta tsallake many challenges a rayuwarta sai taga wannan din
ma she will scale through it, Allah zai tsallakar da ita, amma fa in ta tuna wannan
challenge din is for ever sai taji duk jikinta yayi sanyi, may be Allah bai rubuta
zata ji dadi tayi farin ciki a rayuwarta ba, daga wannan sai wannan, ba a wata daya
sai taga sabon jarabawa, but Alhamdulillah for everything, ya ɗan kalleta yace
"Baby we need to get some foodstuffs" Ta juya ta kallesa a hankali tace "Ohk" wani
shopping mall ya tsaya suka shiga ciki a tare, siyayya suka yi sosai na kayan
abinci da kayan shayi, sae varieties of drinks, duk dai wani abu da yasan za a
bukata a gida sai da ya siya, ta zabi spices iri iri na girki, bayan yayi payment
aka kai masu kayan gaba daya bayan booth din motarsa, ana kiran sallan magrib suka
bar haraban mall din, still kafin su karasa gida sai da ya tsaya wani eatry ya siya
masu abinci da drink. karfe goma saura Nihad ta fito daga wanka kenan ya shigo
dakin da turarrukan wuta da Mami ta yi mata, ya ajiye mata su a kasa yana kallonta
yace "Kin kunna heatern bandakin ne" Ta gyada masa kai tace "Na kunna" Ya nuna mata
turarrukan wutan yace "To su wa ennan ya ake yi da su?" Murmushi tayi tace "Ci ake"
Ya zaro ido yana kallonta, tace "Zaka ce baka san turaren wuta ba?" Ya shafa kansa
yace "Can u pls make me a cup of tea after dressing up ki kawo min daki?" Tace
"Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin, sai da ta gama shafe shafenta, kafin kace me
kamshi ya cika dakinta, ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta dau Hijab har kasa
ta sa ta fito daga dakin, a tunaninta zata gansa downstairs zaune parlor amma bata
gansa ba, ta wuce kitchen kawai ta daura masa ruwan shayin, bayan ta gama ta wuce
sama da shayin, tana tsaye jikin kofarsa tayi knocking a hankali tare da sallama
sannan ta bude kofar, tsaye ta gansa a dakin with short alamar he just took his
bath too, banda kamshi me dadi babu abinda dakin yake ga sanyin Ac da har yayi yawa
a dakin, bata karasa ciki ba murya can kasa tace "Ga shayin na gama" without
looking at her yace "You can come in" Ta turo masa baki tace "Ni ban gama abinda
nake yi ba fa" Ya buda ido sosai yana kallonta yace "Idan kin ajiye ba sai ki wuce
ki ci gaba da abinda kike yi ba, i am not stopping you Love" Shiru tayi na few
seconds sai kuma ta karasa ciki a hankali ta tafi har bedside drawer ta ajiye cup
din shayin, sai kuma ta saci kallonsa taga kallonta yake, zata nufi kofa yayi
saurin jawota ya matseta jikinsa yace "Ni kika ce ma cin turaren wuta ake yi ko?"
Ta marairaice masa tana shigewa jikinsa tace "Toh kai baka san wasa ba, ni fa da
wasa na gaya maka haka" Ya cire mata Hijab din jikinta murya can kasa yace "Noo,
ban san sa ba, you have to tell me how i will start eating it when it's not
you...." Kawai gani tayi ya kashe switch din dakin, ya dauketa cak sai kan big bed
dinsa, rungumesa tayi ta fara masa kukan shagwaba tana cewa "Ni dai a'a pls" Nan ta
kara birkita mutumin.... Da asuba a nan dakin suka yi sallah tare saboda ruwan da
aka fara tun karfe hudu saura har zuwa lokacin sallah bai tsaya ba, bayan sun idar
ya juya yana kallonta taki barin su hada ido, murya can kasa yace "Good morning
Heart" ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba, yayi murmushi ya dawo kusa da
ita a hankali ya dago kanta yana kallon idonta da ya kumbura, nan da nan hawaye ya
cika idonta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi ya jawota jikinsa a hankali yace "I am
sorry wife, i am very sorry" Ita dai bata ce komai ba sai hawaye da take tana
shessheka a hankali, dagota yayi ya kwantar da ita saman gadon ya ja mata duvet don
garin yayi sanyin sosai, ya zauna gefenta yace "Get some sleep" Yana ta zaune gefen
nata har yaga ta fara bacci wajen karfe shidda, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya
sauka daga kan gadon ya dauke pray mat din da suka yi sallah yayi folding dinsa.
Har da safe karfe takwas bata tashi ba, ya dau makullin motarsa ya fita zuwa
pharmacy don siyo mata magani ya dawo gida, ko da ya shiga dakinsa bai ganta a ciki
ba, ya fita zuwa dakinta jin wanka take a bandaki ya zauna dakin ya jira har ta
fito, suna hada ido ta sunkuyar da kanta ta karaso kan gadon ta kwanta ta lulluba
da duvet don sanyin take ji, ya koma kusa da ita yace "Maran ya daina ciwo gaba
daya?" Ta kallesa ta gyada masa kai, ya dagota yace "I can also make u warm not
only duvet" Yana fadin haka ya lullubesu da duvet din gaba daya yana rungume da
ita, kamshinsa yasa taji warmth din, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace
"But.... did you know i love you?" Lumshe ido tayi, shi ma yayi hakan yana jin
sabon sonta na fizgarsa yace "Ina sonki, ina sonki my wife, fiye da yanda ni kaina
nake zato... I want to be with u till death do us apart....." As if whispering tace
"Me too, i love u" Kissing dinta ya fara yi, duk da tsoronsa da ya cika zuciyarta
amma bata hanasa ba, kuma daga karshe sai da tayi da ta sanin da bata hanasa din
ba, haushinsa da taji na yanzu yafi na jiya da daddare, ya gaji da lallashinta
ganin kamar tunzurata yake kara yi kawai yayi shiru ya kyaleta yana kallonta. Sai
da ya sauko downstairs ya kalli agogo yaga har sha daya saura minti biyar, ya tafi
kitchen ya hada mata shayi don shi kam babu abinda ya iya bayan wannan, ya kusa
minti daya tsaye bakin kofar dakin ya kasa shiga kamar dai yana shakkarta, daga
karshe dai ya tura kofar a hankali, durkushe ya ganta jikin gadon, ya karasa ciki
da sauri ya ajiye shayin yace "Are you okay?" Cikin kuka tace "It's paining me" Ya
dagota ya zaunar da ita gefen gadon yace "I am sorry dear, pls ki sha Shayin ga
magani na siyo maki nan" Da kyar ya lallabata ta sha shayin ƙadan sannan ya bata
maganin da ya siyo mata daxu ta sha, tayi ta juye juye har kusan 12 kafin bacci ya
dauketa, ya mike ya fita daga dakin zuwa nasa. Karfe uku na yamma bayan ya sa ta ci
abincin da ya siyo mata ya sauko downstairs tare da ita, gaba daya baya jin dadin
ganinta cikin yanayin da take ciki yanzu, and he promise him self zai kyaleta har
sai ya gano cause of ciwon maran nata, ta zauna kan kujera tana kallon tv dake
aiki, yayi kasa da murya yace "U are angry at me ko?" Taki ce masa komai, ya zauna
gefenta yace "Kiyi hakuri plss ba laifina bane Baby" Ta wani kallesa, murmushi yayi
ya ja hancinta yace "To mu je kiyi strolling compound for some minutes, you will
feel better" Bai jira cewarta ba ya dagota suka fita daga parlon, yace "kin taɓa
zaga Backyard din gidan nan kin ga flowers da na shuka maki kuwa?" Ta girgiza masa
kai, yace "Ohk now, zan rufe idonki in kai ki har wajen and u chose the best flower
da kika fi so, da kaina zan dinga watering din maki shi, sauran kuma masu aiki su
dinga yi" Ta ɗan buda ido tace "Toh idan naje na fadi kasa fa?" Tun da garin Allah
ya waye sai yanxu ta bude baki tayi masa magana, yaji dadin haka yace "Ta ya zaki
fadi bayan ga mijinki, ain't u secured when with me?" Ita dai bata ce komai ba,
bayan sun sauka matakalan bakin entrance din gidan ya zaga ta bayanta ya tsaya ya
rufe mata idonta a hankali da hannunsa, sannan ta tafiya a hankali yayi leading
dinta har zuwa Backyard din gidan, ita dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login