Showing 36001 words to 39000 words out of 268471 words
fito daga
bangaren Mumy, Nihad ta nufeta tana huci tace "Ke mahaukaciyar wace gari ce da xaki
rufe min kofa bayan kinsan na fita?" Hafsah tace "Ayya kiyi hakuri wllh ban san
baki shigo ba, na xata kin bi ta gaba kin shigo" Nihad ta mata tsawa tace "Aa ta
hancinki na bi na shigo" Tsaki ta ja ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama.
Umma dai ta bi ta da ido, direct dakin Nihal ta tafi, Nihal har ta gama shiryawa
tana kallon Nihad tace "Ohk baxa ki rakani din ba" Nihad tace "Nihal idan na fara
yi ma wancan driver din rashin mutunci ke ce ta farko da ke fara jin haushi, wllh
duk abinda na masa kar ki ga laifi na, don haka tun wuri ki je ki samesa ki amso
min wayata da jakata dake wajensa" Nihal dake kallonta with confusion tace "Me ya
kai jakarki da waya wajensa kuma?" Nihad tace "How will i even know?? I mistakenly
dropped my bag at the gate jiya, ko sani ma ban yi ba...." Nihal ta katseta tace
"How will u mistakenly drop a whole bag not even purse Nihad?" Nihad ta hade rai
tace "And that is none of ur concern, kawai abinda nace maki shine ki amsar min
kayana a wajensa kar in fara rashin mutunci na, don wllh idan bai yi hankali ba sai
na gaura masa mari kuma ba abinda xai faru" Dariya ta ba Nihal, sai dai bata yi ba,
tace "Ke yanxu wa yace maki shi ya dau maki jaka?" Nihad tayi saurin cewa "Aminu ne
ya gaya min, kuma don't forget wayana na ciki" Nihal tace "Amma ai ba yaki bane, xa
ki iya samunsa politely ki tambayesa jakar, na tabbata xai baki" Nihad ta yi wani
dariyar rainin hankali tace "Koh? To sannu, shi drivern xan je in sama politely
sbda ina tsoronsa ko? To abinda baki sani ba, Aminu ce min yayi satar jakar yayi
niyyarsa yayi shiru, bai kuma san Aminun ya gansa ba, to idan yana sata sai ya fara
ta kan kayana a gidan nan? Kaii amma mutumin nan ya kara bani tsoro wllh" Nihal ta
dau karamin handbag dinta tace "Yamma na yi, xan tafi shopping" Nihad ta hade rai
tace "Ohk baxan raka ki ba kenan?" Nihal tace "Oh na xata kince ai baxa ki ba"
Nihad ta harareta tace "Yaushe nace maki haka?" Nihal tace "Toh dauko hijab dinki
mu tafi" Nihad bata ce komai ba ta juya ta fita, Nihal ta bi bayanta, babban
dalilin da yasa Nihad xata shopping din nan kawai don Nihal ta amsar mata jakarta
da wayanta gun khalil, Nihal na fitowa parlor Umma tace "Har kin shirya auta?"
Nihal tace "Eh na shirya" Umma tace "To kar dai ki manta turarena" Nihal tace "Toh
baxan manta ba" Umma tace "To ya kika tsaya, ga yamma na yi" Nihal tace "Ina jiran
Nihad" Umma ta kalleta tace "Nihad? ita tace maki xata?" Nihal tace "Eh" Umma tace
"Ke da xaki yi maza kije kiyi abinda xai kai ki ki dawo, meye kuma sai kun yi zuga
kamar yan matan amare Nihal" Nihal tace "Aa nafi son mu je tare" Umma tayi shiru
bata kuma cewa komai ba, Nihad ta fito sanye da Hijab ita ma, Tana kallon Nihal
tace "Mu je" Nihal ta kalli Umma tace "Sai mun dawo" Umma tace "Allah ya tsare"
Nihad tace "Umma xa a taho maki da wani abu ne?" Umma tace "Aa babu komai, Allahj
ya tsare" Fita suka yi daga parlon, Nihad ta hade rai ganin khalil da Aminu, Nihal
ta nufesu tana kallon khalil tace "Idan baka yin komai xa mu iya tafiya yanxu?" Ya
mike yace "Ohk" Motar ya nufa, Nihad ta bi sa da wani shegen kallon tsana, duk
Aminu na lura da ita, Nihal ta bude front seat xata shiga Nihad tayi saurin cewa
"Me xa ki yi a gaba ke kuma?" Nihal tace "I prefer seating here" Nihad ta ja tsaki
ta bude back seat ta xauna, Tuni mai gadi ya bude gate din suka fita compound din,
Khalil yace "Wani supermarket din xa mu Hajiya?" Nihal tace "Ko wanda ya fi kusa"
Nihad tace "Kai Malam mu tafi Sufi Mart" Khalil dai driving dinsa kawai yake, next
thing kawai Nihad taga ya dau hanyar wani store din daban, ta kankance ido tace
"Wai kai kurma ne baka ji inda nace ka kai mu bane?" Driving dinsa kawai yake kamar
bai san da shi take ba, Nihal ta juya ta kalleta tace "But ai duk daya ne Nihad"
Nihad ta galla mata harara tace "To da ke nake ke kuma?" Nihal ta dauke kai bata ce
mata komai ba, A Danja Khalil ya sauke glass din motar ya amshi facemask hannun
wani yaro sannan ya basa kudi ya kulle glass din, Nihad ta kyabe baki, sai kuma ta
ja tsaki ba dai wanda yace mata komai a motar. Parking Khalil yayi a inda aka
tanadar don parking a harabar Supermarket din, ya kashe motar yana kallon Nihal,
tace "Baxa mu dade ba in sha Allah" Nihad tace "Toh da kike cewa haka wa xai dauko
kayan idan mun gama siyayyan? Ai sauka shi ma xae yi daga motar ya kwaso kaya ba
wai zama xae yi a driver seat ba" Nihal ta kalleta tace "But the staff in there
will do that, it's not necessary" Nihad tace "Wallahi u have a very big problem,
what is then the use of him? Why then did he have to drive us here if he can't come
out and help? Sannu good Samaritan" Nihal ta kalli khalil tace "Sae mun fito" Yace
"Toh a fito lafiya" Ta bude motar xata sauka yace "Amma bari in sa maki number ta
idan kin gama sae ki kirani in dau maki kayan" Tace "Akwai masu daukan kayan a ciki
kar ka damu" yace "Toh idan da wani abun sae ki kirani" Tace "Toh" wayarta ta mika
masa yayi dialing number din sa sannan ya mika mata, amsa tayi ta kira number,
karamar wayar dake aljihunsa ya fara ring, tace "Nagode" daga haka ta bude motar ta
sauka, Nihad dake ta kallon ikon Allah ta ja tsaki me tsayi sannan ta sauka, ko
barin wajen motar basu yi ba tace "Me ye na wani exchanging digit da driver idan ba
kaskantar da kai ba Nihal? Me yasa ke kin fiye over sabi a rayuwarki? Ni ban san me
yasa ke da Mumy ku ke yin haka ba wllh" Nihal taki tanka mata, Nihad tace "Though
wannan ba damuwata bace, my problem is ban ji kin masa maganar jakata da wayana
ba?" Nihal tace "Xan yi" Suna shiga mall din, Nihal ta fara daukan abubuwan da ta
xo siya tana xubawa a cart Nihad na tura mata cart din, duk inda suka gifta sae an
kallesu don babu wanda bazai ce su ba yan biyu bane, they look so cute, beautiful
and adorable, kawai dai Nihad ta fi Nihal haske da tsayin hanci with more cute
lips, ita kuma Nihal ta fi Nihad cika, though she isn't chubby but ta fi Nihad
warce iska me karfi idan aka yi xae iya tafiya da ita... Lol, tsayinsu daya haka ma
shape din large eyes dinsu, sae dai kana kallonsu kasan Nihad tafi Nihal wayewa
nesa ba kusa ba, ganin Nihad isn't taking anything Nihal tace "But kince kema xa
kiyi shopping kin fasa ne?" Nihad ta yatsina fuska tace "I won't shop here" Nihal
bata kuma ce mata komai ba, har ta gama
daukan duk abinda xata bukata a makaranta, sannan ta dau ma Umma turarurrukan da
tace, wani tsadadden turare da ta san Nihad na so ta daukar mata, Nihad ta amsa
tace "Thank you" Daga haka ta saka shi cikin cart din, Nihal ta dau wayarta tayi
dialing number da Khalil ya sa mata with the intention of asking him a question,
can kuma dae kawai ta katse ta fasa kiran nasa sbda Nihad dake ta kallonta, wasu
turarurrukan biyu ta deba ta sa a cart sannan tace "Shikenan na gama" Nihad ta tura
cart din suka nufi counter. Suna tsaye counter din Nihad tace "Na manta xan dau
Sanitary Napkin" Daga haka ta juya zuwa in da zata dauka, khalil ya shigo cikin
mall din with facemask, yana hango Nihal a counter ya nufi wajen yana kallonta yace
"Naga kiran ki..." Nihal tace "Oh bansan ya shiga ba" Yace "Ohk, sun gama in dau
kayan?" Xata yi magana kawai wata yarinya kamar balarabiya ta nufosu tana kallon
Khalil closely tace "KJay?" Juyawa yayi da sauri, Ta wara ido kafin ta ce komai
yace "Ohh Nadiya, daga ina haka?" Ta kyalkyale da dariya tace "How wonderful i
recognized u upon the nose mask KJay..." Ya kalli Nihal da sauri yace "erm, yi
hakuri don Allah minti daya..." kawai yace "Mu yi magana a waje Nadiya" yana fadin
haka ya bar wajen da sauri, Sai a sannan Nadiyar ta kalli Nihal dake ta kallonta
daga sama har kasa, Nadiya ta daga mata hannu tace "Hi" Nihal tayi murmushi ta daga
mata hannu ita ma, juyawa tayi ta bi bayan khalil da har ya fita mall din, Nihal ta
bi ta da kallo, har gadon baya ta saki dogon baΖin gashin kanta, daga ganinta kasan
half cast ce, sae ga Nihad ta ajiye Sanitary Napkin din a kan counter, tana kallon
Nihal sai kuma ta kalli inda take ta kallo amma tuni Nadiya ta fita daga mall din,
Nihad tace "What are u staring at?" Nihal ta dauke kanta da sauri tace "Nothing"
ma'aikatan wajen ne suka kwasar masu kayan xuwa mota bayan an biya kudin kayan,
Khalil na jingine jikin mota ya rungume hannunsa, ganin sun fito ya xaga ya bude
booth din motar, wanda ya tayasu fito da kayan ya shigar cikin booth, Nihal ta bude
handbag dinta ta dau dari biyar ta basa, yayi mata godiya sannan ya wuce, tuni
Nihad ta shige bayan mota, Nihal ta xauna gaban motar, ya tada motar suka bar
shopping mall din. Tunani iri iri ke yawo a xuciyar Nihal, she can't even think
straight, Nihad kuma ta kasa kunne taji Nihal tayi ma Khalil maganar wayarta amma
shiru, har ta shirya rashin mutuncin da xa tayi mata suna shiga gida don dab suke
da isa gidan kawai ta ga Nihal ta kallesa tace "Ina son xan maka magana don Allah"
Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace "Toh ina jin ki Hajiya" Ina a polite state
tace "Jakar Nihad yana wajenka ko?" Yayi Ιan yi shiru kamar baxai ce komai ba,
Nihal dai kallonsa kawai take, sai kuma yace "Eh yana wajena" Tace "Toh xaka bani
don Allah idan mun isa gida" Yace "Toh ba damuwa, in sha Allah" Nihad ta galla masa
wani tsinannen harara ta kauda kai, da yace baxai bada ba ya gani mana, suna isa
gida yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta tsaya nan parking space babu yabo
babu fallasa tana jiran jakarta. Nihal ta sauka ya bude mata booth ya saukar da
kayan kasa, xagawa tayi xuwa gun Nihad tace "Ki tafi ciki, ai xan amsar maki" Nihad
tace "Nooo, Baxan tafi ba, ina nan ina jira" Khalil dake jin abinda tace, ya dai
kwashi kayan Nihal gaba daya ya kai mata can bakin kofar shiga main building din
gidan ya ajiye, Nihal na tsaye har ya dawo yana kallonta yace "Anjima da daddare
xan baki jakar idan na shiga can bangaren kenan" Nihad tace "Ban gane anjima da
daddare ba, kai ko kunyan sata baka ji ba a ranka, to tun wuri ka shiga yanxun nan
ka fito min da jakata kar in tara maka mutanen gidan nan, wallahi rashin mutunci
xan maka don ma kaji in gaya maka" Khalil ya kalleta yace "Toh" Daga haka ya tafi
wajen mai gadi yayi xamansa, a fusace Nihad ta kalli Nihal tace "Kina dai gani ko,
wllh sai na nuna masa wacece ni yau kar ya fito min da jakata" Nihal tace "Ba sai
da nace ki shiga ciki xan taho maki da shi ba, toh ai gashi nan kin ji" Nihad tace
"Na ji me? Ai jakata baxata kara minti biyar a hannunsa ba, bari ya gani" Tana
fadin haka ta juya fuuu ta wuce cikin gida, ita damuwarta kar ya ba Nihal jakar ta
bude taga kayan Husnah dake ciki, Nihal ta nufe Khalil dake kusa da mai gadi ta
mika masa ledan hannunta tace "Gashi nan na daukar maka kai ma, amma don Allah kayi
hakuri ka bamu jakar yanxu" Yana kallon ledan yace "Nagode sosai Hajiya, Allah ya
saka da alkhairi.... Bari in dauko maki jakar" Daga haka ya mike ya nufi chalet, ta
bi sa da kallo sannan ta bi bayansa, da ya lura tana biye da shi, sai yayi slowing
pace dinsa, tana isa kusa da shi tace "Ina son xan maka tambaya" suna ci gaba da
tafiya ba tare da ya kalleta ba yace "Ohk ina sauraronki?" Tace "Tell me... who are
you?" Ya Ιan yi jim sai kuma yayi saurin cewa "Ban gane abinda kike nufi ba" Tace
"Nasan ka gane" Yace "Da gaske ban gane ba" suna isa Chalet din kafin tace komai,
yayi maza yace "Ina xuwa in dauko jajad yanxu" daga haka ya shiga ciki ta bi sa da
kallo, ba a dau lkci ba ya dawo rike da jakar Nihad, a bude zip din jakar yake, ya
mika ma Nihal ta amsa, babu abinda idonta ya fara cin karo da sai kwalban Codeine
da prophylactics da ke saman jakar, lkci daya ta rude apart from being shock, bata
san sanda ta rungume jakar ta juya da sauri xata bar wajen ba, yace "Ga wayarta"
Nihal ta juyo da kyar amma ta kasa barin su hada ido, ta dai amshi wayar da yake
mika mata ta juya ta bar wajen tana tafiya da sauri, tana shiga gida direct dakin
Nihad ta wuce, Nihad xata fito daga dakin kenan suka kusa cin karo, Nihad ta koma
baya, Nihal ta shiga dakin ta jefa mata jakar a kasa tana girgiza kai sadly tace
"Nihad meye wannan a cikin jakar ki??" Nihad ta kalli jakar lkci daya gabanta ya
fadi, Nihal ta karasa cikin dakin ta xauna gefen gado ta dafe kanta, Nihad dai sai
kallon jakarta take tana tunanin abinda xata ma khalil taji sanyi a ranta, ko daxu
da ta bude jakar bata ga abubuwan nan a saman jakar ba, wato shi ya daura su saman
jakar ya bar zip a bude don Nihal ta gani, Bayan kusan minti daya Nihad ta kalli
Nihal, hawaye ta gani idonta, Nihad tace "Look Nihal wllh wllh ba kayana bane na
Husnah ne, haba don't u trust me?? kema kinsan i can neva posses such stuffs, i
swear to God na Husnah ne, shi kuma munafuki algungumin da ya daura a saman jakar
ya jira ya ga abinda xai faru da shi a gidan nan" Tana fadin haka ta durkusa ta hau
tattara abubuwan dake cikin jakar ta kulle, Nihal dai bata ce komai ba ta mike a
sanyaye ta ajiye mata wayarta a gefen gado sannan ta fice daga dakin.
βπ»
07087865788
ππ *NIHAAD*ππ
βπ»
By _Khaleesat Haiydar_
13.....
Zaunawa Nihad tayi ta dau wayarta ta bude, nan ta ga miss calls da ya wuce misali,
ta shiga call logs ta ga kiran Aliyu guda daya wanda yayi mata tun da safe, bata
san sanda ta sauke wani ajiyar xuciya ba, so he did call her, wani Murmushi tayi,
tayi dialing number sae da ya kusa katsewa ya daga, tayi kasa da murya tayi masa
sallama ya amsa, jin yayi shiru a hankali tace "Can you hear me?" Yace "Yea ina ji"
tace "You called da safe, bani da lafiya shi yasa ban samu dagawa ba" Yace "Baki da
lafiya? Me ya sameki?" Ta langwabar da murya tace "Na tashi da xaxxabi ne" Yace
"Subhanallah, how are u feeling now?" Tace "Da sauki shi yasa har na samu na
kiraka" Yace "Since when were u sick?" Tace "2 days ago" Ya dan yi shiru, sai kuma
yace "I am sorry, Allah Ubangiji ya baki lafiya" Ta lumshe ido tace "Ameen" Yace
"Hope kina iya cin abinci?" Tace "Ehh daxu na samu na ci" Yace "Get well soon dear"
Ta dan yi shiru sai kuma tace "Kayi hakuri da abinda ya faru few days back" Yace
"Nihad" Tace "Na'am" yace "Daga ina akayi employing driver din nan?" Tace "Wllh ban
sani ba i just saw him over night a gidan" Yace "Ya sunansa?" Ta gyara xama tace
"Halilu" Yace "Good, yana gidan har yanxu ko?" Tace "Yana nan wllh, rashin mutunci
kuwa sae abinda yayi gaba, i have just decided in dinga hawa adaidaita from
henceforth idan xan je makaranta" yace "You don't worry, i will bring an end to
everything" tayi wani Murmushi tace "Trust u dear" Yace "A gidan yake permanently
ko yana xuwa ya tafi ne?" Tace "Aa a nan yake permanently ba inda yake xuwa" Yace
"Ohk, gobe xan shigo kano in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, i
will call u back later" Tana Murmushi tace "Alright dear" daga haka ya katse wayar
ta lumshe ido ta bude cike da farin ciki, at last they will bring an end to this
forsaken driver, tasan tun da har ya shiga trap din Aliyu kuma ya shiga uku. Nihal
na ta xaune parlor a dining area har kusan karfe tara na dare, she her self don't
even know what exactly she is sitting down there for, har Umma sai da tayi mata
magana ta tafi ta kwanta ita da xata yi tafiya gobe, amma bata bar wajen ba, Farooq
ya shigo parlon ganin ita kadai yace "Me kike yi a nan?" Ta kirkiri murmushi tace
"Ba komai kawai ina duba waya ne" Yace "Ohk, xo ki amshi sako ki ba Aminu" Tace
"Toh" Mikewa tayi ta bi bayansa har xuwa bedroom dinsa ya dauko wani takalminsa ya
mika mata yace "ki kai masa" Ta amsa tace "Toh" Yace "Gobe da yaushe xa ki tafi?"
Tace "Da safe in sha Allah" Yace "Ohk" Juyawa tayi ta bar wajen, tana fitowa
compound ta tafi bakin gate inda Aminu yake, Bata ga Aminu a wajen ba sai khalil,
yana ganinta yace "Barka da yamma Hajiya" Ta gyada kai kawai tace "Ina Aminu?" Yace
"Ya Ιan fita xai dawo yanxu" Tace "Ohk, ba nisa yayi ba?" Yace "Ehh ban san ko yyi
nisa ba" Ta koma gefe ta tsaya tace "Ok i will wait" shi dai Khalil bai ce komai
ba, but from all indication he was uncomfortable with her by his side, bayan kusan
minti daya tayi breaking silent din tace "Daxu na maka tambaya baka ce min komai
ba" ya ki kallonta yace "Ohh, yi hakuri Hajiya wani tambaya kenan?" Tace "Kawai
cewa nayi, xan iya sanin ko kai waye?" Yayi shiru na few seconds, sai kuma yace
"Ohk amma ina son ya kasance tsakanina da ke, don ba kowa nake ba labarina ba"
Nihal tace "In sha Allah nayi alkawarin rike maka sirrin ka" Murmushi yayi ya gyara
xama yace "Kinyi alkawari har yar uwarki baxa ki