Showing 246001 words to 249000 words out of 268471 words

Chapter 83 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

baki tace "Lokacin basu san da aurenki da khalil ba?" Dariya kawai
Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Jamila tace "Ikon Allah, to dama yasan khalil
din ne?" Ta girgiza kai tace "Kilan sai daga baya, nasan Aunty Maryam ce zata gaya
masa Abbana ya rasu shine zai ce zai zo gaisuwa, dama dai yana shigowa Nigeria but
a Uk yake zama" Mumy tace "Allah sarki, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya bashi
lada" Khalil bai dawo gidan ba sai dare, nan Aunty Jamila ta sanar masa gobe ya dau
Nihad su tafi gida, ya dai yi shiru bai ce komai ba, komawa daki tayi wajen er
uwarta, Khalil ya kalli Nihal dake juya abincin gabanta a parlon, yace "Ina wayarki
Nihal?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tace "Yana dakina" Yace "A kunne yake?" Ta
girgiza masa kai don for more than a month now bata kunna wayarta ba, Yace "Ki
kunna za a kiraki....." Ta dai yi shiru tana kallonsa, yace "Kin ji?" Ta gyada masa
kai kawai, Nihad ta shigo parlon rike da abinci ta kawo masa, ta ajiye gabansa ta
zauna tana facing dinsa sannan ta dau plate tana debar masa abincin, shi dai
kallonta kawai yake babu ko kiftawa, Nihal ta mike ta dau abincinta ta shiga dakin
Mumy, a hankali Nihad tace "Should i add more?" Yayi kasa da murya yace "I want to
feed on u, not rice and stew"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah



Ur evidence via 07087865788




Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun
turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin
kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki
ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin
sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta
dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp
09084473900

75
Nihad tayi murmurshi kawai ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba ta kara masa
nama akan abincin da ta zuba, shi dai kallonta kawai yake kasa kasa, can yayi kasa
da murya yace "Baki ce komai ba...." Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa tana mika
masa abincin tace "Fara cin wannan" Dariya ta basa, a hankali yace "Are you
serious?" Ta gyada masa kai, ya amshi abincin ya fara ci, ta koma ta jingina da
kujeran ta kusa da inda yake zaune tana kallon tv dake aiki a parlon, lokaci lokaci
take satan kallonsa ta gefen ido sai taga shi ma kallonta yake, taji yayi kasa da
murya yace "When are we leaving tomorrow?" A hankali tace "Sanda kace" Yace "Da
safe?" Tace "Allah ya kai mu" Bai wani ci abincin da yawa ba ya ajiye ya dau ruwa,
ta daga kai tana kallonsa ganin ɗan abinda ya ci tace "Bai maka dadi bane?" Cikin
whisper yace "When it's not you...." Hararansa tayi ta gefen ido, yayi murmushi ya
sha ruwan da zai sha ya ajiye sauran yace "Let me not over stay my welcome, bari in
tafi sai da safe" Tace "Toh Allah ya kai mu..." Tashi yayi yace "Kice ma su Mumy na
tafi sai da safe" Nihad ta mike ta dau gyalen Nihal ta yafa a jikinta, shi dai
yana tsaye yana kallonta, ganin kallon da yake mata irin na mamakin nan ta ɗan buda
ido a hankali tace "Ko baka son rakiyan ne?" Ya wara ido yace "Idan baki rakani ba
ma ai bazan tafi ba sai dai in kwana parlon nan" Ta ɗan yi murmurshi ta dau wayarsa
dake saman kujeran, ya nufi kofa ta bi bayansa, sai bayan da suka fito daga main
parlor ya kama hannunta suka nufi gate walking slowly ko wanne da tunanin da yake a
ransa, Aminu na zaune bakin gate din har sannan shi fa bai gama dawowa dai dai ba
kai kace shine Farooq ko Usman, Nihad ta zame hannunta a hankali daga na Khalil
ganin Aminu, ta nufi gate ta fita, khalil ya tsaya wajen Aminu, ba a dau lokaci ba
Khalil ya fito kofar gidan ya ganta jingine jikin motarsa, ya karasa har kusa da
ita ya tsaya yana facing dinta yayi kasa da murya yace "Till tomorrow?" A hankali
tace "Allah ya kai mu lafiya" Yana kallon eye balls dinta yace "Ko mu tafi in dawo
dake gobe da safe?" Ta zaro ido tace "Aa ni dai bazan iya ba" Yayi murmushi yana
bin layin da kallo, wanda babu kowa cause it's few minutes to 10pm, murya can kasa
yace "Can i kiss you love?" Ta sunkuyar da kanta kawai tayi murmurshi, shi dai
kallonta kawai yake babu ko kiftawa da lumsassun idonsa, sai kuma yaga ta ɗan bi
layin da kallo, ganin babu kowa ta gyada masa kai a hankali, ya hade goshinsa murya
can kasa yace "With stew in my mouth" Daga haka ya fara kissing dinta, and he did
that for almost a minute, underneath his breathe yana lumshe ido yace "I love you
so much" Lumshe ido tayi, kawai yaga ta shige jikinsa a hankali tace "Same" Yace
"Same what?" Da sauri ta ajiye masa wayarsa kan motar ta juya ta nufi gate, dariya
ta basa sosai, ya bi ta da kallo har ta shige gidan ta kulle gate. Washegari Nihad
na tashi wajen karfe tara bayan tayi breakfast ta fara harhada duk kayanta dake
dakin Mumy, Aunty Jamila dai sai bin ta da kallon mamaki take don bata ce masu
komai ba kawai ta hau hada kaya kamar warce ake jira a kofar gida, Ita kanta Mumy
bin ta kawai take yi da kallo, tana kokarin rufe trolly dinta kamar ance ta daga
kai taga duk kallonta suke a dakin har Nihal dake dakin, kunya taji ya lullubeta ta
rufe fuskarta da trolly din da sauri tana turo baki, Aunty Jamila tayi dariya tace
"Duk wannan azarbabin tafiya ne haka kamar muna koranki Nihad?" Ita dai bata ce
komai ba kuma bata dago kanta ba but she is so ashamed, Aunty Jamila na murmushi
tace "Karfe nawa za ku tafi?" Ba tare da ta dago ba a hankali tace "Aa ni bai ce
min yaushe ba, kawai dai naga kayan are scattered ne shi yasa nake gyarawa fa
Aunty" Aunty Jamila nata murmurshi tace "Eh naga alama, kayan kam are scattered"
Fasa zuge zip din Nihad tayi daga karshe ta mike kawai ta fita daga dakin ta koma
dakin Nihal ta shiga bandaki tayi wanka ta shirya cikin kayan da ta cire a akwati,
riga da skirt ne da babban mayafi wanda Aunty Maryam tayi mata a Abuja, bata taɓa
sa shi ba dama sai yau, tana gama shiryawa ta kwanta gefen gado kawai... Karfe sha
daya Nihal ta shigo dakin, tana kallonta tace "Ur husband is around" Nihad ta daga
kai ta kalleta sai kuma ta mike zaune, Nihal tace "Bari in daura maki dankwalin"
Daga haka ta dau dankwalin ta tafi gaban madubi ta jawo stool tana kallon Nihad
tace "Dawo nan" Nihad ta mike ta tafi gaban mirror din ta zauna, eye pencil kawai
ta saka a idonta sai lip balm da ta saka a lebbenta amma zaka yi tunanin har powder
ta shafa, she looks so beautiful, ga shi ta ɗan marmaro daga raman da tayi, Nihal
tayi mata dauri me kyau ba kuma me hayaniya ba, ya zauna dass a kanta, sosai kyanta
ya kara fitowa, Nihad na kallonta a hankali tace "Thank you" Nihal na Murmushi tace
"You look beautiful sweet sis, nasan bazai gane ki ba" Nihad dai murmushin kawai ta
mayar mata, Nihal ta dauko mata gyalenta ta mika mata ta amsa sannan suka fita daga
dakin tare, tun da suka shigo parlon Mumy Khalil ke kallon Nihad babu ko kiftawa
don at first bai gane ita bace duk da na kwalliya tayi ba a fuska amma bai taɓa
ganinta da daurin dankwali ba, ta zaune tana kallonsa a hankali tace "Ina kwana" Ya
lumshe ido ya bude a hankali yace "You look beautiful dear, how was ur night?" Tana
wasa da fingers dinta tace "Alhamdulillah" Ita dai Nihal na zaune a parlon ta maida
hankalinta kan tv, Khalil yace "Ur box?" Nihal na jin haka ta mike ta tafi dakin
Mumy don dauko akwatin Nihad ta fita main parlor da shi, Aunty Jamila ta shigo
parlon tana kallonsu tace "Toh ku yi ma yan gidan sallama dai kafin ku fita" Khalil
yace "In sha Allah" Aunty Jamila tace "Kafin in koma Jigawa in sha Allah za mu taho
da lefen nata Abujan, inna ta kai su can gidan ta ajiye a dakinta" Khalil yace
"Allah ya kai mu Aunty" Aunty Jamila tace "Ameen, a gaida mana su Hajiya da
General, mun gode kwarai Allah ya bar zumunci" Khalil yace "In sha Allah" Nihad ta
mike ta tafi dakin Mumy, ta sameta zaune saman darduma, ta duka gefenta murya can
kasa tace "Mumy za mu tafi" Mumy na kallonta tace "Toh Nihad, Allah ya tsare, Allah
ya baku zaman lafiya, ki dau iyayensa tamkar naki sai ki zauna lafiya a rayuwa kin
ji, Allah ya baku zuri'a dayyaba" Ita dai Nihad kanta na kasa, Mumy tayi shiru bata
dake cewa komai ba, don bata son hawayen dake taruwa idonta ya zuba, she knows she
is so much going to miss her daughter most especially in this trying time, banda
Aunty Jamila na nan da bata san kuma ya zata yi ba, Nihad ta goge hawayen da ya
kawo idonta a hankali tace "Allah ya ji ƙan Abba ya basa aljanna...." Sai kuma ta
fashe da kuka, Mumy da hawaye ya fara sauka idonta tace "Ameen, ta shi ki je" Cikin
rawan murya tace "Idan su Sudais sun dawo ace masu na tafi" Kai kawai Mumy ta iya
gyada mata saboda bata son tayi breaking, Nihad ta mike ta nufi kofa Mumy ta bi ta
da kallo tana share hawayen dake sauka idonta, Aunty Jamila ta bi Nihad da kallo
bayan ta fito daga dakin, can ta mike ta tafi wajen Mumy, ba a dau lokaci ba ta
fito tare da Mumy da ta tsaya jikin kofar dakin nata tayi ma Khalil sallama cikin
sanyin murya, ya kasa kallonta yace "Ameen Mumy, Allah ya kara hakura" Ta amsa masa
da Ameen, sannan ta juya ta koma daki, Tare da Aunty Jamila suka fita main parlor,
Nihal na zaune main parlor din tana jiran fitowar su, ba don ran Nihad ya so ba
suka nufi bangaren Umma da khalil, shi ma kawai don Nihal na zaune ne bazata iya ce
masa a'a ba da yace mata za su shiga wajen Umma, banda haka da bazata ba wllh,
Kamila na zaune parlon Umma, ta gaida Khalil ya amsa mata da murmushi, ita dai
Nihad wasa kawai take da gefen mayafinta, Amina kuma ta shiga dakin Umma, sai ga
Umma ta fito ta zauna nan bakin kofar dakinta rike da carbi, Khalil ya gaisheta ta
amsa cikin sanyin murya, yace "Za mu koma ne yanzu in sha Allah Umma" A hankali
Umma tace "Toh Allah Ubangiji ya tsare hanya, Allah ya kai ku lafiya, ya kuma baku
zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya rabaku da sharrin masu sharri" Kansa a
kasa yace "Ameen" Ita dai Nihad bata kalli Umma ba, Umma ta ɗan kalleta, sae kuma
cikin sanyin murya tace "Toh Nihad, Allah ya kai ku lafiya.... Allah ya ji ƙan
mahaifinku ya gafarta masa...." Ba tare da Nihad ta kalleta ba don har hawaye ya
cika idonta tace "Ameen" Khalil ya mike yace "Toh Allah ya ƙara hakuri Umma" Umma
tace "Toh Khalil, a yayyafe... Allah kuma yasa muna da rabon ganawa, Allah ya
kaddara saduwan mu" Yace "In sha Allah, Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Nihad
ta mike ta nufi kofa ta fita, Khalil ya bi bayanta, Umma ta kalli Kamila tace "Toh
ki raka su ko" Mikewa Kamila tayi ta bi bayansu har zuwa main parlor, Khalil na
kallonta yace "What did u study in school?" Tace "Microbiology" Yace "Ohk maa sha
Allah, kuma duk Cv's dinki na nan ai" Tace "Eh suna nan" yace "Toh bari mu shiga
muyi ma Inna sallama kafin mu fito ki dauko min" Tace "Toh" Suna shiga dakin Inna
suka sameta ita kadai tayi backing kofar dakin tana ta faman aikin kirgan uban
kudaden da aka bata, har ta jawo zani zata boye ganin Khalil ne da Nihad ta bar su
a sarari, ta marairaice fuska tana kallon Khalil tace "Sannu Halilu" Ya zauna kasan
Carpet yace "Ina kwana inna?" A hankali tace "Lafiya lau Halilu, ya gajiya" Yace
"Alhamdulillah Inna" Nihad ta durkusa gefen gado tace "Ina kwana" Inna ta kalli
Khalil tace "Daga ita har Nihal sai sun ga dama suke shigowa su gaisheni su ce min
ya hakuri kuma sun san ina gidan nan, kai kace ni na kashe Ibrahim din" Khalil ya
ɗan buda ido yace "Aa gaskiya basu kyauta ba" Inna tace "Atohh bayan wanda ya hada
ma Allah ya daukesa ya bar duniyar da kalubalen dake cikinta kadai ta ishi bawa, ai
nasan in sha Allahu yana kyakkyawan masauki tunda shi din ba mutumin banza bane,
don haka tsakanina da su kawai kowa ya kama kansa, dama babu abinda na hada dasu
har ga Allah...." Khalil ya ɗan yi murmushi yace "Kiyi hakuri Inna" Nihad dai bata
kalli inda Inna take ba, Khalil yace "Dama za mu koma Abuja ne yau, shine muka
shigo mu yi maki sallama" Inna tace "Kai, kaga da anyi arba'in ai sai in bi ku
inje na musamman in ma Janar da mahaifiyarka godiya don ba ko wasu surkai ne za su
yi abinda suka yi ba, mutanen kirki wllh, sannan kuma duk abi da ni gidan abokansa
da suka zo har nan in masu ban gajiya, babu wanda bai ban dubu dari ba a cikinsu,
kaga yanzu nake ta hada kan kudaden ko rijiya ce in sa aje kauye a haka ma bayin
Allah, duk wanda ya sha ruwan Allah ya kai ladan gun Ibrahim dina" Khalil yace
"Gaskiya ne inna, hakan abu ne me kyau kuwa" Inna tace "Wallahi abinda nake so in
yi kenan, shi yasa na fito da kudaden yau nake kirgawa, sannan filayena biyu a
siyar a gina dankareren masallaci a bakin titi da sunansa, in sha Allahu abinda zan
yi kenan, idan Allah ya kara hore min har gidan marayu sai na gina da sunansa wllh,
to idan ban masa ba wa zai masa?? Sai dai ko yayansa Abubakar, balle ma Abubakar
din ya dauke nauyin karatun kananun yaran da ya bari wato Sudais da Fadil, ita
Amina naji ance ta gama sakandarin amma fa yace bazata jami'a ba, ni dai nace ko wa
aka samu kawai ayi mata aure ta bar gidan nan don babu ruwana kuma wllh, mai gadi
ma kaga Abubakar ne zai dinga biyansa albashi daga yanzu, da nace a kori ko me
gyaran fulawan da sharan tsakar gida a bar me wanki da guga kada kudin yayi ma
Abubakar din yawa sannan fa ga albashin dreba me kai kananun mazan nan boko da
islamiyya amma yace duk zai iya ba sai an kori kowa ba, cefanen gidan kuma Farooq
da Usman sai su dage, duk da buhunhunan shinkafa sun kusa goma yanzu haka a store
wanda abokan Marigayi da yan wajen aikinsa da yan anguwa suka harhada aka kawo, ga
jarkan mangyada manya manya har biyar, indomie ma da na kirga katan 11 ce wllh, ga
taliya, kuskus, macaroni, kai har fa da gero da masa ko wa zai ci?? Sannan ga
buhunhunan sugar, flawa, kai mu je ma in nuna maka store din ka gane ma idonka
kawai, wllh ko kwakkwaran spes babu a store din ya cika makil da kayan abinci"
Khalil yace "Duk na gani ai Inna, ina nan duk aka kawo" Inna tace "Toh banda shi
mutumin kirki ne waye zai ma iyalinsa haka? Ko nan da shekara biyu bana tunanin
kayan abincin nan za su kare, kawai fatana kada su yi espaya kawai" Khalil yace
"Baza su yi ba in sha Allah" Inna tace "Allah ya sa, sannan lefen matar nan in sha
Allahu idan zan taho godiya da bangajiya da su zan zo" Khalil na Murmushi yace "Toh
Allah ya kai mu inna, bari mu je kada jirgin ya tashi babu mu" Da sauri Inna tace
"Maza ku je, Allah ya tsare" Dubu hamsin ya ajiye mata, tayi ta godiya tana sa masa
albarka ta rakosu har main parlor, Kamila na tsaye tana ta jiransa da takardun
nata, ya nufeta ya amsa tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi" Yace "In sha Allah,
zan kai ma Abbana" Tace "Toh Allah ya kai ku lafiya" Gaba daya yan gidan suka
rakosu gun mota banda Mumy da Aunty Jamila sai Umma, Inna ta dinga cewa "Allah ya
kai ku lafiya, Allah ya kiyaye hanya...." Khalil ya bude motar yace "Ameen Inna,
Allah ya saka da Alkhairi" Aminu ya gwalo ido ganin wanda ke tahowa a mashin dinsa,
shi kansa khalil tsayawa yayi yana kallonsa, Inna tace "Waye wannan kuma da mashin
duk ya cika anguwa da ƙara" Yana isa dai inda suke ya kashe mashin din ya sauka ya
fashe da kuka sosai, Aminu ma ya rushe da kuka kamar jira yake, Inna ma sai ta
fashe da kuka tace "Habibu?? In gaya maka Habibu Allah yayi ma Ibrahim rasuwa"
Habibu ya nemi dakali ya zauna yana rusa kuka Aminu ya zauna gefensa yana tayasu,
Kamila tace "Don Allah meye haka, ku da za ku dinga bin sa da addu'a" Habibu yace
"Haka ne, Allah Ubangiji ya gafarta ma Alhaji, wallahi na shiga Nijar saro ma
yayana kaya sai jiya na dawo labarin nan ya riskeni, Allah sarki Alhaji har yau
gashi ina ta cin moriyar shagon da ya bude min har na gina gidana a birni" Inna
tace "Toh in kai me hankali ne sai ka duba marayun da ya bari kanana idan ko ba
haka ba Allah sai ya tsine maka wllh" Habibu ya dinga cewa "Haka ne inna, gaskiya
ne Inna" Kamila ta daga ma Nihad hannu ta juya kawai ta shiga ciki, Amina ma tace
"Allah ya kiyaye Aunty Nihad" Daga haka ita ma ta shiga ciki, Nihal ta mata side
Hug cikin sanyin murya tace "I will miss u sweet sis" Daga haka ita ma ta koma
cikin gida, Habibu ya taso yana kallon Nihad da ladabi ya gaisheta yace "Ya hakuri
Hajiya" Nihad ta sauke idonta tace "Alhamdulillah" Inna tace "Idan ka gama da su
sai ka shigo kayi ka su Maryam gaisuwa" Sai kuma ta kalli Khalil tace "Bari in
shiga Halilu, Allah ya kai ku lafiya" Ta juya ta shiga gidan, Habibu na kallon
Khalil yayi kasa da kai yace "Oga ya muka ji da hakuri?" Khalil yace "Hakuri mun
gode Allah Habibu" Habibu yace "Sau da yawa ina kiran layin nan naka da nake da shi
don in gaisheka amma bana samunka oga" Khalil yayi murmushi yace "Ina da numberka
ai, zan kiraka da main line dina" Da ladabi Habibu yace "Toh Oga godiya nake"
Khalil

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login