Showing 99001 words to 102000 words out of 268471 words
gunjin kuka take tana kallon wata
nurse dake mayar da kayan aikinsu mazaunin su tace "Aunty Nurses babu wani abu da
za a shafa min?" Nurse din tace "An rubuta maki magani da za ki sha, Allah ya
sauwake" Daga haka ta fita, Nurse din ta kawo ma Khalil magungunan tana kallon
Husnah tace "Allah ya kiyaye gaba, za ku iya tafiya yanxu ga magunguna da
prescriptions a jiki" Daga haka ta juya ta bar wajen, Khalil ya daga kai ya kalli
Husnah, share hawayenta tayi ta sauko daga kan gadon da take a hankali kamar me
gudun kar ta fama wani ciwo a jikinta, duk sun yayyaga mata kayanta wandon ne kawai
basu karasa ba, amma daga saman cikinta duk a bude yake, Khalil zai juya ya bar
wajen cikin kuka tace "Wallahi baxan iya tafiya ba ko Nihad ce ka turo ta kama min
hannu" Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo, da sauri ta karaso kusa da shi ta kama
hannunsa, ya dake ya fara tafiya tana dingishi tana bin sa har suka fito reception
din, har suka isa mota Husnah ta shiga baya ta zauna Nihad bata fito ba, Khalil na
tsaye jikin motar for almost 5 mins ganin bata fito ba still ya koma reception din,
hade rai yayi yace "Malama ke muke jira" Ko Kallonsa bata yi ba ta tsura ma Tvn
dake aiki a reception din ido, yace "Ohk ga kudin mota duk sanda kika zaman sai ki
dawo gida" Ya ciro dari biyar ya mika mata, zuwa lkcn nurses din sun fara kuskus ko
kishiya da kishiya ne, can ta mike ta fice daga reception din fuskarta a daure,
juyawa yayi ya bi bayanta sai yaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga motar shi
ma suka bar asibitin, suna hawa saman titi Nihad tace "Hostel za a kai ki ko ina?"
Husnah tace "Wallahi kin bani mamaki Nihad har in kone a gidanki amma ki kasa budan
baki ki min sannu? Sai yanxu ki wani bude baki kice hostel xa a kai ni ko ina?"
Nihad tace "Saboda ai sai da nace ki bari in dafa kika ki, Yanzu idan wani abu da
yafi wannan ya sameki su Mumy da Abba suka ji bayan sun hana in kawo kowa gidan fa?
What did u want me to tell my parent? Ni yanzu dai hostel za a kai ki ko ina, kin
dai ga dare yayi" Khalil yace "Kinsan dare yayi kike kira mata hostel yanzu? Ba
kwana ta zo maki ba dama?" Nihad ta wani jefa masa kallo tace "Ni bata ce min zata
kwana ba, salon mu koma gida wani abu da yafi wannan ya sameta in shiga uku? Kawai
ta koma hostel ko gobe sai in kai mata jakarta can din" Kallon Nihad kawai Khalil
ke yi, Husnah tace "To baxan wani je hostel ba jakana na gidanki kuma ID card dina
na ciki, kuma ai soyayya ce tasa na zo gidanki ba wani abu ba, me yasa su Naf da
Zully basu zo ba, amma ba komai Nagode da walakancin da kika min Nihad" Khalil dai
ya nufi hanyar gida, bayan ya shiga ciki yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka
ta wuce ciki, Husnah ta sauka ita ma ta shiga gidan Khalil ya bi su da kallo,
jingina yayi da motar ta ta6e baki. Husnah na shiga dakin Nihad ta fashe da kuka
sosai tace "I never expect this from you, in wani yace min zaki min haka wallahi
baxan yarda ba, saboda wannan mere Drivern ya taimakeni ya kai ni hospital kike jin
haushi Nihad?" Nihad tace "Ya baxan ji haushi ba mutumin da ko magana bana yi masa
za ki ja min raini a wajensa ya zata ya mana alfarma, ko kadan i am not happy with
what happened da kawai kirawoni kika yi na fita waje na nemo mana taimako akan
wannan yaron da kika kula, yaron da ya tsaneni nima na tsanesa shine har zaki yarda
ya wani kai ki asibiti?" Husnah tace "Tohh idan mutum na cikin azaba ai baya ma
tunanin komai, kawai burinsa a fitar da shi daga axaban da yake ciki, to situation
din da na tsinci kaina kenan, amma ni kaina ina ni ina wani driver can" Nihad bata
sake cewa komai ba, Husnah tace "Shikenan, tunda har kika koreni bari in yi
tafiyata ko hotel ne in kwana don a hostel na riga nace masu baxan dawo yau ba"
Nihad tace "Ni fa bance kar ki kwana ba, kawai haushin yaron can ne yasa nace mu
kai ki hostel" Tana kai wa nan ta mike ta cire Hijab din jikinta tace "Bari in mana
boiling din spaghetti din yanzu, daga can xan gyara kitchen din" Tana fadin haka ta
fita parlor ta wuce kitchen tsaye taga Khalil yana kokarin mopping din kitchen din,
ta wani hade rai, yana ganinta ya ajiye mop din ya fice daga kitchen din ya shiga
dakinsa, bayan few minutes da fitar Nihad Husnah ta leko daga dakin tana lekan
parlor amma bata ga Khalil a ciki ba, komawa dakin tayi ta cire yagaggen wandon
jikinta da riga ya rage daga ita sai bra da skin tide ta dau after dress dinta ta
saka tayi buttoning dinsa sannan ta fito, ta fi second goma tana kallon kofar da
take tunanin dakinsa ne sai kuma ta murda, dago kai yayi suna hada ido ta sunkuyar
da kai ta shiga dakin ta tura kofar tana tsaye bakin kofar tace "Dama nace bari in
maka godiyan dawainiyar da kayi da ni, Allah ya saka da
Alkhairi.... kuma don Allah abinda ya faru kwanaki ina sake neman yafiyarka don
wancan ranan baka ce min komai ba da na baka hakuri" Kallonta kawai Khalil yake,
can ya ajiye lemon kwalin dake hannunsa yace "Ohk, kawarki ki ce ta aikoki ki bani
hakuri kenan?" Husnah ta zaro ido tace "Waaa?? Ai inda muka bambanta da ita kenan,
da ita ce baxa ta ta6a baka hakuri ba, kasanta da taurin kai da kafiya, yanzun ma
bata san na shigo nan ba da baxata bari ba, amma ka sani wllh tunda muka maka
wannan rashin kirkin bana samun nutsuwa saboda ba halina bane" Yace "Ohk ai na zata
duk ku ke sa ta a hanyar walakanta mu talakawa" Husnah ta dafe kirji ta karasa
cikin dakin tace "Waa?? Halin kishiyar mamarta ne ta dauko, kasan duk abinda ta
sata tayi shi take yi, amma basu san da talaka da mai kudi duk Allah ne yayi su ba,
ka gan ni nan babana yalo yake siyarwa a kawo kaduna, ni ba er kowa bace shi yasa
nasan mutuncin ɗan adam" Khalil yace "Ohk, ai ina ce er kano ce" Husnah tayi wani
dariya tana jujjuya ido tace "Wallah er kaduna ce ni gaba da baya, Zully da Naf ne
yan kano" Yace "Toh naga makarantar taki ta masu kudi ce" Husnah tace "Ehh wallahi
wani saurayina ne ya biyamin tun daga level one har karshe, wata kawar mu zully ma
saurayinta ke biya mata, Naf ce dai iyayenta ke biya mata don su ma masu kudi ne"
Khalil ya gyada kai yace "Allah sarki" Husnah ta zauna gefen gadon tace "Amma ina
jiye maka zama gida daya da Nihad, yanda bata kaunarka ta tsaneka kullum a
makaranta cikin tsine maka take wai kana matsayin driver kana nuna mata isa, bayan
anyi auren nan har ikirari tayi wai zata kasheka, nan kuwa kai jahadi kayi, halan
baka hawa social media? Ina nufin baka da babban waya?" Ya girgiza kai yace "Bani
da" Husnah ta gyada kai tace "Allah sarki, kawai dai ka saka ido sosai kada kiyayya
yaje ya kaita ga aikata abinda ba shi kenan ba, in sha Allah in xan sake dawowa
nayi maka alkawarin babban waya" Khalil yace "Toh Nagode, amma kawar taki bata da
saurayi ne?" Husnah ta rike ha6a tace "Ita kuwa take da saurayi wanda ita ta makale
masa ba shi ba, kana jin janaral jikamshi?" Khalil yace "Eh nasan shi, ko ba wani
babban soja ba?" Husnah ta dafa kafarsa cike da kissa tace "Yauwaaa, Toh shi fa....
ɗan sa kwaya daya take so kamar ta kashe kanta, tun yana basar da ita har dai ban
san sanda suka dinke ba, mu dai mun fi zargin bashi kanta tayi, don kawai lkci daya
muka ga ya fara kiranta ba kakkautawa a maimakon ita da ke yawan kiransa" Khalil ya
sauke idonsa kasa daga kallon da yake ma Husnah, Husnah tace "Kuma fa duk wannan
abun sau daya ya zo wajenta a nan kano suka hadu a wani waje, kamar dai kar su hadu
shkkn ya makale mata, kasan mu mata idan muna son abu babu abinda baxa mu yi kan
abun ba, to tun dai daga sannan ya fara kulata sosai, kuma kar kace fa yana zuwa
gidansu, aa sam... duk xuwan da yake yi wajenta nan kano sai dai su hadu a wani
waje su yini sannan yayi tafiyarsa, toh kwanaki can ban san ya aka yi ba yaje
gidansu wai xai tura iyayensa, mu dai ko gaya mana bata yi ba gaskiya sai daga
baya, ai ko muna ta murna xa mu hade da 'ya yan manya mu ma a dama damu tunda
abokanansa duk 'ya yan manyan kasar nan ne kawai wai sai ga videon tsaraicinta ya
bazu a duniya, ni takaicina daya da ba a bari sai da muka hadu da abokansa ba, har
yau mun rasa ta ina video din nan ya fita, muna dai tunanin garin yawace yawacenta
ne aka mata video din nan" Khalil bai kuma cewa komai ba, lkci daya kuma duk mood
dinsa ya canza, Husnah ta shafa kafarsa a hankali tana kallon kwayar idonsa tace
"Sai kaji babu dadi ace videon tsaraicin warce aka aura maka na ta yawo a duniya
ko? A ranka kana tunanin an cuceka ko?" Kallonta Khalil yayi, tana Murmushi ta
janye hannunta a hankali tace "Toh Nagode bari in je inyi wanka" Daga haka ta mike
tana juya manyan mazaunanta ta nufi kofa, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai
har ta fita dakin, karo ta kusa ci da Nihad, Nihad ta tsaya tana kallonta daga sama
har kasaasa, Husnah tace "Ke yace min maganin na wajenki kuma ni ban gansa a
dakinki ba" can kasa kasa Nihad tace "Ba ya wajena" Daga haka ta shige dakinta,
Husnah ta tafi parlor ta dau magungunan nata ta dawo dakin Nihad. Nihad dai na ta
zaune gefen gado, Husnah tace "Wai taliyar bata yi bane Nihad?" Sai a sannan Nihad
ta kalleta tace "Mu je mu duba" Husnah tace "Ohk" Daga haka ta mike ta fita Nihad
ta tashi ta bi bayanta, tana tsaye parlor har Husnah ta shiga kitchen, a hankali ta
bude kofar dakinsa ta leka taga baya ciki, ta kalli kofar bandaki sai kuma ta kulle
kofar dakin, entrance din fita ta kalla bata ga takalminsa ba, ta karasa jikin
window ta tsaya ta bude labulen a hankali tana lekan waje, yana tsaye balcony ya
rungume hannunsa, can ta ga ya nufi dakalin da yake son zama ya zauna kana ganinsa
kasan he is moody, Husnah ta fito daga kitchen tace "Me kike nema a waje" Nihad
tace "Ba komai, kin zubo taliyar?" Husnah tace "Ehh na zuba, ashe har kin sauke"
Nihad tace "Toh dauko mu je daki" Husnah ta koma ta dauko suka wuce dakin, bayan
sun gama cin abincin Nihad ta fitar da kwanukan ta sake leka waje taga har sannan
khalil na zaune inda yake staring into space, kafin Nihad ta dawo Husnah ta jawo
jakarta ta fito da kayan mayenta ta sha sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta
kwanta, Nihad na dawowa dakin ta zauna gefen gado, tana son shiga bandaki tayi
wanka amma ta kasa tashi, Wajen karfe sha daya da rabi Husnah ta mike Nihad na
kallonta tace "Ina za ki?" Husnah tace "Ruwa zan dauko kitchen" Nihad ta dauko wani
bottle water dake daya side din gadon ta mika mata, Husnah ta amsa ta koma ta zauna
tana sauke numfashi a hankali, ita fa dama kwana biyu duk samarin nata basa Kano
gaba daya a takure take dama, daga karshe dai Husnah ta kwanta ta kulle ido duk da
ba bacci tayi ba, Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad ta mike daga kwancen da take
ta nufi kofa ta sa makulli sannan ta ciro, Da mamaki Husnah ta mike zaune tana
kallonta tace "Me yasa zaki kulle mu har da cire makulli Nihad?" Nihad tace "Saboda
duk dare haka nake yi dama" Husnah bata kuma cewa komai ba ta kyabe baki ta koma ta
kwanta, Nihad ta saka makullin cikin pillow ta kwanta kai. Washegari da sassafe
bayan sun yi sallan asuba sun koma bacci kiran Umma ya tashe su, Bayan Husnah ta
daga jin muryar Umma tace "Auu Umma ce, ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau Husnah
baki yi saving number na har yanzu ba ko?" Husnah tace "Yanzu xan yi Umma, ya
gida?" Umma tace "Alhamdulillah, ina Nihad din?" Husnah ta mika ma Nihad waya ta
koma ta kwanta, Bayan Nihad ta gaidata, Umma tace "Ya, kin gano sunan iyayen nasa
kuwa Nihad?" Nihad tace "Aa Umma, dama sai yau" Umma tace "Kin ji irin shiriritar
taki ko? Ke da tun jiya nace kisan yanda kika yi ya gaya maki amma sbda shashanci
baki yi ba? Ko dai kin fi son kiyi ta zama da dreban nan ne Nihad?" Da sauri Nihad
tace "A'a Umma, in sha Allahu yau xan gaya maki" Umma tace "Toh kar ki bari Husnah
ta bar gidan nan sai kin gano kin sanar min ta wayarta tukunna" Nihad tace "Toh
Umma" Umma tace "A handsfree wayar yake ne naji maganata na dawo min?" Nihad tace
"Aa" Umma tayi kasa da murya tace "To dai ki xama me rike sirrinki a ciki, ciki da
kike gani ba don tuwo kadai aka yi sa ba, ko da mun gana waya kawarki ta tambayeki
me muka ce kice mata ba komai kawai daddawa da kuka nace xan bada a kawo maki, don
ba komai ake sanar ma k'awa ba, wa ya sani ko da hadin bakinsu aka saki video dinki
a duniya" Nihad tace "Aa Umma ba haka bane gaskiya" Umma tace "Toh shikenan, ina
sauraronki zuwa anjima" Nihad tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, Husnah na
kallonta tace "Wai me ya faru?" Nihad tace "Aa ba komai, abubuwan da zata kawo min
ne take tambayata" Husnah tace "Ohk" Komawa tayi ta kwanta, Nihad ta mike ta dau
Hijab dinta ta daura kan kayan baccinta ta nufi kofa Husnah ta bi ta da kallo har
ta fita, Nihad na murda kofar dakin Khalil taji an sa makulli, ta fi minti daya
tsaye bakin kofar, can ta juya ta tafi parlor ta zauna, tana fitowa da minti biyar
sai ga Husnah ma ta fito ta zauna parlon, jan Nihad ta dinga yi da hira, daga
karshe wajen karfe tara Khalil ya fito daga dakinsa, babu warce ya kalla a cikinsu
ya fita daga gidan, Husnah na ji ya fita da mota ta kalli Nihad tace "Lallai ke me
hakuri ce da har kika kai warhaka da mutumin nan a gidan nan, Dubi fa yanda ya wani
zo ya wuce mu ko gaisuwa babu, kai kana talaka da kai kayi ta yin abu isa isa?"
Nihad ta kyabe baki tace "Ke ma kika lura da mutum ya zo ya wuce ta nan, ai ni ban
ga kowa ba" Husnah ta kyalkyale da dariya tace "Ahh lallai kam" Nihad tace "Tashe
mu je ko irish ne mu soya da kwai, ni dai na fara jin yunwa" Husnah ta mike suka
wuce kitchen din, har kusan la'asar Khalil bai dawo gidan ba, kiran Umma uku duk
sai Nihad tace mata ai bai dawo ba, kiran karshe da Umma tayi mata da ta kara sanar
mata har sannan bai dawo ba, Umma tace "To kar ki yarda ki bari Husnah ta bar
gidan, don tana tafiya babu ta inda xa mu yi communicate" Nihad ta kalli Husnah da
ita dama bata ga alamar xata tafi ba tace "Toh Umma" Labari har da na kauyensu
Khalil sai da Nihad ta ba Husnah dake ta kyalkyalewa da dariya har da faduwa kasa,
tace "Kice ke kika ga asalin dreba ganin idonki?" Nihad tace "Hmm... I wish xaki ga
kauyen nan Husnah, wllh with millons baxa ki yarda kiyi minti sha biyar a garin nan
ba, it's hell on earth" Husnah dai sai dariya take, sai ga Naf ta kira Husnah,
Nihad da wayar ke kusa da ita tayi saurin dagawa ta kai kunne, Naf na jin muryar
Nihad tace "Amma Husnah munafuka ce shine bata gaya mana ba tayi tafiyarta ita
kadai" Nihad tace "Wallahi nima ban ji dadin da baku zo gaba daya ba, gashi
throughout today I wasn't lonely, muna ta hira da Husnah" Husnah ta fixge wayar
tace "Toh ai naga xaku fita ne shi yasa bance maku mu taho ba Naf, amma meye a ciki
next time idan xan zo ai sai mu taho gaba daya, ba wani tashin hankali bane" Naf
tace "No but like seriously kinsan indai kince mana wajen Nihad xa ki babu abinda
xai hanamu binki, kuma banji dadin abinda
kika mana ba, yanzu ma kawai xa mu iya tahowa da zully tunda babu abinda muke"
Husnah ta dinga cewa Hello hello, daga haka ta katse wayar tace "Ji shegen network
din ya dauke" Hirar da take ma Nihad ta ci gaba da yi mata, Nihad tace "Kinga
lokaci na wucewa me xa mu ci da daddare Husnah?" Husnah tace "Ni yanzu xan fita in
amso wani sako na, ko indomie ce ma ci da daddaren, Hijabi kawai xan sa in je in
dawo" Nihad na kallonta tace "Kar fa ki ki dawowa Husnah" Husnah ta zaro ido tace
"Me xai hanani dawowa kuwa, cabb ai kamar na dawo kinsan yanda nayi kewar ki kuwa,
to a nan ma xan bar wayata, amma kar ki cire min a flight mode har in dawo" Nihad
tace "Toh" daga haka Husnah ta sa hijab ta dau handbag dinta ta bar gidan, ko da ta
dawo bayan kusan awa daya Nihad ta dinga kallon hannunta ganin ba leda tace "Ina
sakon?" Husnah ta ja tsaki tace "Wai ashe sai gobe, shine suka bari naje nayi
asaran kudin motata na dawo" Daga haka ta shiga dakin Nihad. Sai after Magrib
Khalil ya dawo gidan, Husnah da fitowarta daga wanka kenan ta dauki mai zata shafa
ta rike ha6a tace "Dama haka yake yi ya fita tun safe sai dare kamar me siye da
siyarwa a kasuwa" Nihad ta kyabe baki tace "Ohk ya dawo ne" Dariya kawai Husnah
tayi bayan ta gama shafa cream dinta tace "Ke baxa ki yi wankan bane" Nihad ta mike
tace "Zan yi" Daga haka ta shiga bandaki, mikewa Husnah tayi da sauri ta bude kofar
dakin tana leka parlor, ba kowa parlon sai leda da ta gani a ajiye na eatry, ta
dawo daki ta dau handbag dinta sannan ta fice tana waige waige kamar munafuka ta
shiga kitchen ta bude handbag dinta ta