Showing 33001 words to 36000 words out of 268471 words
galla masa wani harara tace "Ai ba ni na kawo motar ba
balle ka bar min makullin" tana gama fadin haka ta bude motar ta sauka ta ki kulle
door din tayi tafiyarta, ya bi ta da wani kallo, sai kuma ya sauka ya kulle sannan
ya hau motar ya tafi.... Husnah na ganin Nihad tace "Shine nake ta kiranki kike
danna min busy Nihad?" Nihad ta sauke ajiyar xuciya amma ta ki bata amsa, ta nemi
seat ta xauna, wato dai a takaice drivern nan ne ya dau jakar tunda gashi har
Husnah ta kira ana ta danna mata busy, lallai mutumin nan raini me karfi ya shiga
tsakaninsu, bayan dauke mata jaka sbda guts har bude jakar ma yayi kenan, muryar
Husnah ya dawo da ita daga tunanin da take, tace "Ina magana kin min shiru, dama ba
komai bane ce maki xanyi ki taho da jakar da kika je birthday jiya da shi, don
akwai abubuwana a ciki" Nihad ta kalleta tace "Abubuwanki kamar me?" Husnah tace
"Kwalban Codeine dina da Naff na ciki, sai prophylactics, ni ina jin kamar ma har
da lingerie dina a jakar, don na duba ban gani ba...." Nihad ta zaro manyan idonta
tace "Duk a cikin ina???" Husnah tace "Jakarki mana, kinsan yana da girma" Nihad
bata san sanda ta mike ta dafe kirjinta ba tace "Na shiga uku...." Da mamaki Husnah
tace "Kin shiga uku kuma? Me ya faru?" Nihad tayi narai narai da tace "Wayyo Allah
na, Me yasa xa ki min haka ki ajiye abubuwan nan a cikin jakata Husnah? Me yasa xa
ki min haka? Gashi yanxu jakar ta fadi a bakin gate ban san wanda ya dauke min ba"
Husnah ta gwalo ido tace "Kaiii, garin yaya kika yarda jaka a bakin gate Nihad?"
Nihad da abun duniya ya isheta ta koma ta xauna ta cije yatsa tace "Na shiga uku"
Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh kinsan wa ya dau jakar ne?" Ta kalli Husnah
tace "Wallahi wannan driver din nake zargi don shi kadai ya gan ni sanda na dawo da
asuba don a bayan flowers dake kofar gida na fara buya as a result of people coming
out from the mosque after subhi prayer" Husnah ta rike ha6a tace "Ji tsiya, Driver
kuma?" Nihad ta kasa cewa komai tayi tagumi, Husnah tace "Tabb shine kika yi shiru,
to me kike jira da har yanxu baki tambayesa ba?" Nihad tace "Toh me xan ce masa?
Bayan ban ga sanda ya dauka ba, Har wayata fa na cikin jakar, idan ba sata yake son
yi ba ai xai ba Aminu ya ajiye min" Husnah tace "Ehh lallai wannan mutumin ya rika,
shi ke ta ja min busy kenan? Wato dai har ya bude jakar" Nihad ta xaro ido tace "Na
shiga uku, gashi kin xuba abubuwa kika ce cikin jakar" Husnah ta mata wani kallo
tace "Ke dalla to meye, koma me ya gani cikin jakar ba shi ya ga duhu ba, kuma ma
bansan uban me kike jira da har yanxu baki tambayesa jakarki ba, ko tsoronsa kika
fara ji? ai ba ma tambayarsa xa ki yi ba wai ko ya ga jaka ko bai gani ba, kawai ce
masa xa ki yi ya baki jakar ki da ya dauka kar kiyi masa rashin mutunci, kuma kada
ya sake ta6a maki kayanki ko da kuwa a titi kika yar don baki aikesa ba" Nihad dai
ta rasa abun cewa tunani iri iri ke yawo a ranta, Husnah ta kyabe baki tace "Ni dai
ki adana min prophylactics din nan foreign ne ba na kasar nan bane kuma tsada ke
garesu, Codeine din kuma shi ma nasan ba kya sha, kar ki je ki xubar ki adana mana
gaskiya" Tashi Nihad tayi ta bar mata wajen ta koma seat din baya abun duniya ya
isheta, yanxu mutumin nan duk ya ga abinda Husnah ta saka mata a jaka? To amma ya
ma yi mugun rainata gaskiya, waye shi da har xai bincika mata jakarta?? A daddafe
Nihad ta yi lectures daya tace xata tafi gida, Husnah tace "Ke don Allah ki saki
ranki, ko Abba ne ya ga jakar nan ya dauka ya bincika ai sai haka, me xai dameki
akan wani shegen driver dinku ya bude jakar ki? Ae rashin mutunci mafi muni xaki
masa idan kin koma gida anjima, ni abinda ya fi damu na ma wayarki ne wllh, don
matsiyacin sai ya iya dauka yace xai je ya siyar bai san wayar nan sai ta siye duk
yan kauyensu ba, yanxu kawai ki xo mu je police station, cikin lokaci kalilan xa
ayi tracking" Nihad ta zaro ido tace "In tona ma kaina asiri kenan, kin zata na
gaya ma kowa cewar na yarda jaka da waya a ciki? To har Nihal bata sani ba" Husnah
tace "In kince ayi cikin sirri babu tonon asiri ai sai ayi hakan, duk fa mutanena
ne, amma wllh so nake a walakanta sa idan aka ga wayar a wajensa, a nakada masa
shegen duka" Nihad tace "Husnah bari in je gida ko xan ji saukin abinda ke damuna,
i can't endure anymore" Husnah ta ta6e baki tace "Wllh kina da sa ma kai damuwa,
duk ki bada space din da lamarin driver xai dinga damunki haka, to wai shi wannan
driver din daga ina ya xo yake abu isa isa da gadara haka?" Mikewa Nihad tayi tace
"Duk yanda ake ciki xan kiraki da wayar Nihal ai tana da number ki" Daga haka ta
fice daga hall din, tun da ta fara school din bata ta6a trekking da kafafuwanta har
bakin titi ba sai yau, haka nan ta tsayar da adaidaita shi ma xata iya kirga iya
sau nawa ta hau sa a rayuwarta, suna isa gida ta sauka ta bude jakarta ta basa kudi
sannan ta shiga gidan, Aminu ne kawai bakin gate, ta Ιan bi compound din da kallo
sai kuma tayi kasa da murya tace "Aminu baka tambayar min driver din can ko ya ga
jakata ba kuma?" Aminu yace "Anya, don ina da yakini da ya gani xai nuna min, ai
shi mutum ne me gaskiya da amana" Ta wani galla masa harara tace "Dallah Malam rufe
min baki, duka duka kwananku nawa tare xaka san yana da gaskiya da amana, ashe kai
dolo ne ma ban sani ba? To bari ka ji wayata ce ta kusan miliyan daya da rabi a
jakar nan" Driver ya gwalo ido yace "Subhanallahi, subhanallahi...." Nihad ta saci
kallon wanda ke tahowa ganin driver din ne ta daure fuska ta juya ta nufi cikin
gida da sauri, xaunawa Khalil yayi gefen Aminu ganin yanda yake
zaro ido kamar mara gaskiya yace "Me ya faru kake buda ido haka" Aminu yace "Ba
nace maka ta yarda jakarta ba daxu har tana tambayata ko na gani, to wllh wai har
da wayarta na miliyan biyu da rabi a cikin jakar" Khalil ya ciro karamar wayarsa
yace "To ta huta..." Aminu yace "Atoh dai, Ta kuwa huta wllh, don yau tana sa uban
a gaba ya siya mata sabo wallahi sai ya siya, sai dai uwarta ta hana amma tsaf in
dai ita ce xai siya mata, kai kaji waya har miliyan uku, ni yanxu na samu irin
kudin nan ai kauye xan koma in tada gini malam, inci me kyau in sha me kyau, sannan
in kara mata biyu...." Khalil na kallonsa yace "Haba?" Aminu yace "Wllh tllh,
albashin namu fa Hajiya ke amsowa a wajensa ta bamu, Ni dai ban san ko nawa yake
bata ba amma dubu 50 50 take bamu, kuma da farkon xuwana akwai wani lkcn da ya ta6a
bani da kansa wllh dubu 70 ya bani, to kilan dai har da kyautatawa ce irin tasa ban
dae sani ba" Khalil dae bai ce masa komai ba. Nihad na shiga cikin parlor ta tafi
dakinta direct, xaunawa tayi gefen gado ta rafka tagumi abun duniya ya isheta, tun
da shegen mutumin nan ya xo gidan nan bata da kwanciyar hankali, bude kofar dakin
aka yi Nihal ta shigo da sallama, Nihad ta daga kai tana kallonta, Nihal ta karaso
ta xauna gefenta tace "Amma ba ki jira ku gama lectures din yau ba kika taho ko"
Nihad ta yatsine fuska tace "I am tired, kawai shine na dawo" Nihal tace "Toh ki
kwanta ki huta, xuwa yamma sai ki rakani shopping din, kinsan gobe sunday xan tafi
fa" Nihad tace "Wa xai kai ki shopping din??" Nihal tace "Khalil" Nihad ta juya ido
tace "Waye haka?" Nihal tace "Driver..." Nihad ta bude baki ta rike ha6a tace "Wai
khalil? Shi uban wa ya basa wannan suna yana driver? Ni fa na xata kinyi wani
saurayi ne Khalil ban sani ba, shi driver din ne yace maki sunansa khalil?" Nihal
dai kallonta kawai take, Nihad ta gyada kai tace "Tabdi, ana iskanci a duniya, shi
yasan ma'anar Khalil din ma kuwa?? Yau naga mutumi da karfin hali, ke kuma wawuya
shine kika yarda sunansa Khalil, to wllh karya yake ba abinda ya hadasa da wannan
sunan" Nihal tace "To ko ma dai meye sunan Abbanmu garesa, ko so kike in kira sunan
Abba gatsau?" Nihad tace "Toh meye don kin kira tunda ba sunan Abban kika kira ba?
Meye don kin ce masa Ibrahim ba shine sunan nasa ba? Wato dai ke kika makala masa
khalil din kenan?" Nihal tace "Aa, yace haka ake kiransa dama, ni bani na sa masa
ba" Nihad ta bude baki tace "Ji shegen karya, to karya yake munafuki, uban wa ke ce
masa haka? Amma fa mutumin nan yayi mugun raina maki wayo ma dai, a kauye wa yasan
wani khalil, dama Halilu yace shine xan yarda, to wai tsaya ma tukun, fira ku ke
har yake gaya maki sunansa khalil??" Mikewa Nihal tayi tace "Woo na gaji da
question and answer din nan, Ko ma meye sunansa ba abu bane da za mu tsaya muna
bata lkci akai, ni dai anjima ki shirya mu je Sahad store din" Nihad tace "Allah ya
kiyaye in dai can xaki wllh baxan je ba, ga wajaje irinsu wellcare kice min Sahad,
ai kowa da kowa ke xuwa Sahad" Nihal ta juya ta kalleta, sai kuma ta girgiza kai
kawai ta fita daga dakin. Nihad ta rike ha6a tace "Ji maye wai khalil, shi a lallai
ya xo gidan masu kudi bari ya maida sunansa irin na yan gayu wai khalil, aa Khalo
ba khalil ba" Ta ja tsaki ta mike ta shige bandaki. Ta a fitowa ta koma gefen gado
da take xaune ta xauna, tunani ta shiga yi a ranta, to ko dai taje can chalet din
da kanta ta duba jakarta ne? Ta kalli agogo lkci daya ta mike ta fito main parlor
Umma tace "Aa har kin dawo er baba" Nihad ta gaisheta sannan ta fita balcony har
sannan taga yana xaune tare da Aminu a bakin gate, komawa ciki tayi ta shiga
kitchen sannan ta bude kofar kitchen din da xai sada ka da back yard din gidan
wanda ta nan ma xaka iya xagawa har xuwa Chalet, ganin yanda Hafsah ke kallonta ta
sha kunu tace "Ya dai da kallo haka ke kuma?" Hafsah ta kauda kanta, Nihad ta fita
da sauri ta xaga ta baya sai Chalet, bata ga takalmin kowa a bakin kofar ba alamar
su Isiyan ma duk basa nan kenan, a hankali ta bude kofar tana leka parlon sannan ta
shiga, da sauri sauri ta fara dudduba parlon, har xuwa dining area bata ga alamar
jakarta ba, har bandakin dake parlon sai da ta bude, wanda sai da ta kusa amai, ta
kullo da sauri tana yatsina fuska ta yi hanyar dakunan chalet din, duk dakuna biyun
dake a bude sai da shiga tana tottoshe hancinta tsabar tsami da doyi, na ta bincika
kaf Ghana must go da ta gani a dakunan amma bata ga jakarta ba, dakin da khalil ke
ciki ta murda ta ji a kulle, to ko dai nan dakin aka ajiye jakar nata shine har da
kullewa da makulli, tunanin inda xata fara nemo spare key ta shiga yi, can ta zare
key din dake jikin kofar su Isiya ta juya ta fita da sauri ta xaga ta koma kitchen,
sai da ta wanke hannunta da morning fresh ta hada har key din tana yatsina fuska
sannan ta shigo parlor, har wani tashi taji xuciyarta ke yi sbda warin da ta dinga
inhaling, kazami irin wannan har shi xai takura mata a gidan nan ya dinga shiga
gonarta, dubi wajen da suke kwana wanda ita ko pig take rearing baxata bari yayi
rayuwa a irin wannan kazantaccen wajen ba, tana wannan tunanin ta faki idon Umma
dake waya ta shige bangaren Abbanta, direct dakinsa ta wuce bayan ta shiga parlor,
nan ta hau bude duk wani drawer da ke dakin, a bedside drawer ne ta ga bunches of
spare keys na gidan, tayi murmushi ta kalli na hannunta sannan ta hau duba irinsa,
kaf irinsu guda uku dake wajen duk sai da ta dauka incase of necessity sannan ta
mayar da drawer din ta kulle ta mike ta fice daga dakin, kitchen ta sake bi ta xaga
xuwa Chalet din, da sauri ta shiga ciki ta nufi hanyar rooms din, dakin dake kulle
tayi facing, ta hau gwada makullen hannunta da sauri da sauri, lkci daya ta bude
dakin, wani farin ciki ne ya lullubeta, ta shige ciki ta kulle tana bin ko ina da
kallo gabanta na faduwa? Banda kamshi babu abinda ke tashi a dakin, rigarsa da ta
gani saman gado ya sa ta gane shine a dakin, rike ha6a tayi.... to gidan uban wa ya
samo wannan turaren da ya xuba a dakin haka, bata daina bin dakin da kallo ba ta
karasa middle of the room, the room look so different kamar ba a chalet din ba,
babu tarkace da kaya kamar irin na su isiya sannan everywhere looks so neat and
tidy, ta kyabe baki without bothering ta hau yin abinda ya kai ta dakin, Duvet ta
gani kamar an rufe abu da shi ta tafi da sauri ta daga sai ga jakarta a ajiye saman
gadon, xaro ido tayi wani farin ciki ya lullubeta, ta bude jakar tana bincikawa da
sauri, banda abubuwan da Husnah ta xuba mata a jakan sai nata tarkacen bata ga
alamar wayarta a ciki ba, nan kuma ta marairaice tana bin dakin da kallo, a ina to
ya ajiye mata wayar?? Sake jakar tayi ta nufi tasa jakar kayan dake dakin, sai bin
jakan take da kallo kafin ta durkusa ta xuge zip din, ko karasa bude zip din bata
yi ba tayi ido hudu da wayarta, babu bata lkci ta dauka, dai dai nan kuma aka bude
kofar dakin, tsabar rudewa da tsorata da tayi bata san sanda ta mike ta saki wayar
jikinta na rawa tace "Wayyoo... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
βπ»
07087865788
ππ *NIHAAD*ππ
By _Khaleesat Haiydar_βπ»
12.....
Tsaye Khalil yayi bakin kofa yana kallonta with a weird facial expression, bata
sake yarda sun hada ido ba banda faduwa babu abinda gabanta yake, sai kuma ta hade
rai xata durkusa ta dau wayarta da ya fada saman jakar, yayi hanzarin shiga cikin
dakin ya sa kafa yayi changing position din jakar yana kallonta, tana ganin haka ta
bi jakar cike da tsiwa tace "Wai kai yaushe na fara wasa da kai a gidan nan ne da
xaka dinga raina ni haka? ina ruwanka da kayana ko a saman titi na jefar da xaka
ta6a min, how dare you?" Tana fadin haka ta ja tsaki ta kara dukawa zata dau wayar,
ya dauke jakar a wajen, buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, sai kuma ta nufesa
da nufin cakumosa yanda ta saba amma ganin kallon da yake mata sai kawai ta tsaya
tana harararsa, cike da rashin kunya tace "Wallahi idan baka mika min wayata a
dakin nan ba xan maka sharrin da har abada baxa ka mance ba, ka bani wayata
nace..." cikin kakkausar murya yace "Idan kin fasa..." Ta kankance ido tana
kallonsa da mamaki jin abinda yace, ji take kamar ta kifa masa mari, da a waje ne
wllh ba abinda xai hanata marin sa, Yana mata wani kallo ya ajiye jakar a gabanta
yace "Idan kin isa ki ta6a" A fusace tace "Toh wai kai idan kana sata sai ka rasa
wayar warce xaka sata sai tawa a gidan nan? A kaina satarka xai kare? Idan na ta6a
uban me ka isa ka min? Wllh sai na ma sharrin da baxaka ta6a mantawa da ni ba" Duk
wannan babatun da take bata yarda ta ta6a jakar ba, banda faduwa kuma babu abinda
gabanta yake barin da ta ga irin kallon da yake mata, jakarta dake gefen gado ya
nufa ya dauka ya dawo inda take ya jefa mata a gabanta yace "Dauki ki fita...
Abubuwanki dake ciki xa su fi wayar muhimmanci gare ki" Kamar xata yi kuka tace "Ni
wllh ka bani wayata kar in hadaka da Abbana da yayana" Da Husky voice yace "Dauka
jakar ki nace ki fita" Bata ce masa komai ba ta tafi ta dau jakarta tana jin kamar
ta fashe da kuka, ta nufi kofar tana tafiya a hankali, ta gefen ido ta saci
kallonsa sae kuma ta dawo da gudu ta fixgo jakarsa ta nufi kofa a guje kamar an
aikota, tana shiga parlorn plate din da su Isiya suka ci abinci suka bari a wajen
ta take sai da ta tafi tsuuu kamar xata tashi sama sae ga ta a kasa timm, jakarsa
kuma yayi can hanyar kofar fita, nata kuma yayi wajen Tv, gwalo ido tayi tana
numfashin wahala da kyar tace "Wayyoo Abbana, wayyo bayana ya karye" tsaye yayi
bakin corridor din dakunan ya rungume hannunsa ya jingina da pillar din wajen yana
kallonta irin dai dai kenan, ta fashe da matsanancin kuka tana jujjuya kanta tace
"Wayyo Allah na a zo a taimakeni bayana ya karye, baxan iya tashi ba" karasowa
cikin parlon yayi zai tafi ya dau jakarsa, tana ganin haka ta yunkura ta tashi ta
nufi kofar da gudu ta figi jakar tasa, a dari da sittin ta fice ko bin ta kan nata
jakar bata yi ba a parlon, bai san sanda ya bi ta ba, tuni har ta dau hanyar
kitchen yace "Keeeee dau wayarki ki ajiye min jakata" haba da ya kara tuna valuable
dinsa dake jakar kawai ya bi ta, tana isa kofar kitchen ta murda ta ji sa a kulle,
ta gwalo ido tace "Na shiga uku, Hafsahhhh uban wa yace ki kulle" tana ganin ya
nufota kawai ta ajiye jakar a kasa tana kallonsa xuciyarta na bugawa, yana isa
gabanta ya duka ya dau jakarsa sannan ya bar wajen. Nihad bata san sanda ta fashe
da kuka ta sulale wajen ba tana cewa "Wallahi sai na maka rashin mutunci a gidan
nan, kawai mutum kamar maye ya sa min ido a gidan ubana duk ya bi ya takura ni" Sai
kuma ta mike ta xaga ta shiga cikin gidan, Umma dake parlor ta kalleta daga sama
har kasa tace "Lafiya?" Nihad tace "Ina Hafsah?" Sai ga Hafsah ta