Showing 171001 words to 174000 words out of 268471 words
Mami tayi tace "Kana ina?" Yace "Ina kano" Tace "Ohh
kanon ka bi ta? Kana nufin kanon ka kama hanya ka tafi ko gaya min baka yi ba? To
ka kyauta, maza maza ka nemi next flight ka taho Abuja yanzu" Yace "Ba jirgin da
zai tashi yau saboda weather" rai bace Mami tace "To wannan kai ta shafa ka biyo
mota kawai ka dawo na gaya maka" Daga haka ta katse wayarta, cike da fada tace
"Banda ma lalacewa tunda yarinyar ta zo gidan daga uwar har uban babu wanda ya taɓa
kira muka yi magana da su, don su ma ji ya yarinyar take, kawai ga ta nan dai kamar
bata da iyaye, kana da ya mace har hankalinka zai kwanta idan bata gabanka, babu
wanda fa ke bibiyar lamarinta nake gaya maki, duk ina lura da komai, kinga ai
saboda tsabar yanda idonta ya bude ai Kano ta kama hanya tayi wucewarta daren jiya,
wanda bai saba ba ai baxai yi haka ba, ko tsoron dare bata ji ba, dama can ta saɓa
abunta ne, Allah ya shirya" Hajiya Safeenah ta sauke ajiyar zuciya, Mami tace "Tun
farko da ya samu matsala da uban Yemen nace ya tafi ya ki, na dawo nace ko zai je
Uk nan ma yaki, all that while ban san yana kano ba na dai san yana Nigeria, to
gidan wasu irin mutane ne ya zauna wa enda basu da kula haka? Ka sakar ma duniya
yar ka mace a wannan zamanin, sannan ga dai abinda yarinyar nan tayi ko wata uku ba
ayi ba amma har ku sakankance baku bibiyar lamarinta, a'a ban taɓa ganin haka ba
tun da nake" Hajiya Safeenah tace "Yanzu dai Hajiya Fatima kiyi hakuri, a bi komai
a sannu ki kirasa ya bar zuwan nasa gobe tunda yace ba jirgi, biyo mota daga kano
zuwa Abuja ai aiki ne babba yanzu, kawai ki masa hakuri ya bari har gobe, bari in
kirasa" Daga haka Hajiya Safeenah ta kira Khalil, nan ta sanar masa kawai ya bari
gobe sai ya biyo jirgin safe, bayan ta katse wayar Mami tace "Dama yana dawowa duk
zan amshe takardun in mayar ma uban baxan iya fitina ba, idan jiƙawa zai yi ya
shanye sai ya jika ya shanye, babu abinda zai raga Khalil da shi" Hajiya Safeenah
tace "Aa kar kiyi haka, ki bar wannan issue din tsakaninsa da ubansa kawai kar kiyi
involving kanki, gaskiya kar kiyi haka, kamar yanda ya fada ke baki amsar masa ba
kuma ya amsa sai kice xaki mayar?" Mami tace "Wallahi mayar masa shine kadai mafi
alkhairi gare mu gaba daya, sai kace baki san General ba, ni duk wani abun tashin
hankali bana so wallahi, har fargaban zuwa asibiti nake yanzu yanda nake ji a
jikina sai ya iya yiwuwa jini na ya hau" Hajiya Safeenah tace "Allah ma baxai sa
hakan ba, kawai kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, komai zae zo da sauki"
Mami ta taɓa baki tace "Ya batun programs na bikin, kun gama shawaran da Hajiya
Hauwa?"
Bayan Azahar ganin Khalil bai shigo ba Mumy na kallon Nihad tace "Ki je kiyi masa
magana ya shigo ya ci abinci" Nihad da tunda tayi sallah take zaune saman darduma a
bedroom din Mumy ta mike ta dauke darduman ta linke sannan ta fita, Hijab ne har
kasa jikinta don ta shiga bedroom dinta ta kwaso sauran kayanta ta kawo bangaren
Mumy ta ajiye, har zuwa sannan kuma Umma bata dawo gidan ba, babu kowa main parlor
din ta fito compound ta gansa zaune tare da Aminu, ɗan zaman da Khalil yayi a wajen
babu abinda Aminu bai sanar masa ba da ya faru a gidan bayan tafiyarsu sai wanda ya
manta, dawowar Kamila gida, matsalar da Usman ya samu wajen aikinsa, rashin
walwalan Abba a ko da yaushe tun tafiyarsu, yanda Umma ke fita ta dawo dab da
magrib kafin Abba ya dawo motarta duk jan laka, zuwan karshen da Inna tayi gidan ta
zauna nan compound tana ta tikar kuka wai an rabata da Nihad an daura mata aure da
ɗan kauye tana can ita ma ta zama er kauye, sabon dreba da aka kawo me warin baki
da warin hammata ga shegen gulma, murmushi kawai khalil ke yi yana kallon Aminu da
ke basa labaran nan with passion babu abinda yake tsallakewa a labarin, in details
yake badawa, he is so good in it, in wanda xai yi demonstrating ne sai ya tashi
yayi demonstrating sannan ya koma ya zauna, yana cikin basa labarin yanda banki
suka zo suka kulle gidan dake can karshen layi saboda bashinsu da ya ci na fitar
hankali sai ga Nihad ta karaso, duk abinda Aminu ke cewa Khalil baya apprehending
tun fitowar Nihad, don ainahin kamshin da ya santa da shi ne ya cika wajen still
dai bai daga kai ya kalleta ba, Aminu ya mike yana washe baki yace "Sannu Hajiya,
sannu da karasowa...." Nihad tace "Sannu Aminu" Daga haka ta kalli khalil tace
"Mumy tace ka shigo ka ci abinci" Sai a sannan ya kalleta kamar baxai ce komai ba
sai kuma yace "Kawo mana nan" Tayi shiru tana kallonsa, can ta juya ta bar wajen ya
bi ya da ido har sannan kamshin na dukan hancinsa, sai da tayi nisa Aminu ya koma
ya zauna yace "Kai mutumina, amma kayi jahadi wajen dawo da yarinyar nan hanya mai
bullewa, wallahi duk jikina yayi sanyi kamar ba Nihad din da na sani ba a baya,
dubi fa yanda ta zama ta gari, ko da dai dama wannan matar uban nata ce ke zugata
duk mun sani, wani nutsuwa na musamman fa take da shi yanzu, shi yasa jiya da
naganta ta dawo ita kadai na maza na kiraka inji ina kake don na zata guduwa tayi,
ashe dai ta nutsu, sannan ga...." Khalil ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Ina
jinka, sai bankin suka kulle masa gidan" Aminu ya gyara zama yace "Wallahi kuwa in
gaya maka, bawan Allahn ya fito yayi ta birgima a layin nan duk muka taru kansa, ga
matansa da ya'yansa a gefe abun dai zar tausayi, an fa ce caca yake yi, kuma ɗan
giya ne....." Khalil ya dinga kallon Nihad da ta fito, hakan yasa Aminu yayi shiru
yana ɗan murmushi ganin Khalil bai ma san me yake cewa ba, har ta iso inda suke da
tray din abincin ta durkusa gabansa ta ajiye, shi dai kallonta kawai yake, ta mike
tace "Me sanyi ruwan za a kawo?" Sae a sannan ya dauke idonsa yace "Duk wanda kika
kawo" Juyawa tayi ta bar wajen still ya bi ta da ido, the perfume is just something
else, Aminu dai sai wani murmushi yake irin na rubabbu, yau wai Nihad ce ke kawo ma
Khalil abinci har ta durkusa ta ajiye masa a gabansa yarinyar da har hana a basa
abinci tayi a gidan, Aminu ya rike haɓa uwa ɗan daudu yana nazari... Sai bayan
la'asar Khalil ya shiga cikin gidan shi ma Sudais ne ya zo yace masa Mumy na
kiransa, parlor ya samu Mumy, Mumy tace "Kana ta zama a waje Ibrahim" Ya ɗan yi
murmushi yace "Muna tare da Aminu ne" Tace "Kuma ba rana" Yace "Aa babu" Tace "Toh
ko bayan magrib ne sai ku tafi can gidan Inna ku gaisheta" Yace "Toh Allah ya kai
mu" Bai wani jima a parlon ba tunda ba wai hira suke da Mumy ba ya fita ya koma gun
Aminu, Mumy ta koma parlonta tana kallon Nihad tace "Me yasa baki je dakin er
uwarki ba Nihad?" Nihad dake game da wayar Mumy tace "Naga kamar bata son magana
ne, i don't want to inconvenience her" Mumy ta zauna tana kallonta tace "Amma ai ta
shigo nan har sau nawa saboda ke Nihad" Nihad tace "Ko ta shigo ba magana take ba,
i don't know why she is silent" Mumy bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes
tace "A ina kuke a Abujan?" Nihad tayi shiru, sai kuma ta daga kai ta kalli Mumy
ganin kallonta take, ta sauke idonta a hankali tace "Maitama" Mumy ta ɗan bude ido
tace "Maitama kuma? Akwai wani maitaman ne bayan wanda na sani?" Nihad ta girgiza
mata kai tace shi wannan din ne, da mamaki Mumy tace "Wajen wa a Maitama?" Ita dai
farooq yayi assuring dinta sosai yace ta kwantar da hankalinta Nihad is doing very
fine, idan ya zo kano za su yi magana, iyakar abinda ya gaya mata kenan amma bai
gaya mata anguwan ba ko inda take, Mumy tace "Kin yi shiru" Nihad ta ajiye wayar
hannunta a hankali tace "Gidan iyayensa" Mumy look so confuse, tace "Wani iyayen
nasa kuma?" Nihad ta sauke idonta tace "He is the son of General Jikamshi" Kallonta
kawai Mumy take, can tace "Are you okay Nihad?" Nihad ta kalli Mumy, a hankali tace
"He disguise himself, I don't know his reasons, I don't know.... but they are rich,
he is the son of General Abubakar" Mumy da duk kanta ya daure tace "Ke ban gane ba,
wani general din? Sannan ba Aliyu bane ɗan gidan General? Kanki daya kuwa Nihad, ko
dai zaki je ki kwanta ne...." Nihad tayi wani murmushi kawai, can ta girgiza kai ta
goge hawayen da ya taru idonta tace "Aliyu lied to me, ba shine yaron jikamshi ba,
Jikamshi is just his uncle which is Khalil's father" Sai kuma ta fashe da kuka
cikin sanyin murya tace "Mumy naga abubuwan iri iri in just 3 months from every
angle, Khalil isn't who we thought him to be, i don't know his intent of coming to
our house, I don't know his intent of coming here as a driver, they are super rich,
his father is a General, his mum is from Yemen, i don't just...." Sai kuma ta hade
kai da gwiwa tana kuka a hankali bayan ta tuno abubuwa da yawa, Mumy was
speechless, ta ma rasa me xata ce, sai kallon Nihad din take inna State of
confusion, kuma har cikin ranta taji bata yarda da abinda Nihad ta fada ba, seems
bata da lafiya, Mumy ta mike ta dagata tace "You need rest, go and have some rest"
Har dakinta ta kai ta ta kwantar da ita saman gado, Mumy na ta kallonta har ta rufe
ido sannan ta juya ta fita daga cikin dakin.
Bayan Magrib Nihad ta gama shiryawa ta sa Hijab dinta har kasa, tun labarin da ta
ba Mumy da la'asar Mumy bata dawo dai dai ba kuma ba wai ta yarda da zancen Nihad
bane, a'a kawai gani take kamar ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa ne as a result of all
what she passed through, gani take she isn't in her right senses, gani take kawai
sambatu take ba wai don tasan abinda take fada ba, Mumy ta nuna mata inda Makullin
motarta yake, Nihad ta dauka, a hankali tace "Sai mun dawo Mumy" Mumy bata iya ta
ce mata komai ba ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin, Mumy ta jingina da
kujera rai ba dadi, ita dai tasan Nihad bata da lafiya don sanyin nata ma yayi
yawa, Mumy bata san sanda ta fashe da kuka ba tana fatan kada ace ƙwaƙwalwarta ne
ya samu matsala. Khalil na tsaye parking space bayan ya gaisa da Abba, sae dai Babu
yabo babu fallasa Abban ya amsa masa har ya shiga ciki, yana ta jiran Nihad har ta
karaso ta mika masa makullin motar ya amsa yana kallonta, ita dai bata bari sun
hada ido ba duk da ta dai ga ya canza kayan jikinsa, ta zaga ta bude kofar gaba
zata shiga yace "Aa koma normal spot din ki...." Ta ɗan yi jim sai kuma ta sauka ta
koma back seat, ta madubin mota yake kallonta har ya tada motar yayi warming suka
bar gidan, She doesn't look like the normal Nihad anymore, seems abubuwa da yawa
suna damunta a zuciya, this is a new Nihad he is seeing for 2 months now, har suka
isa gidan Baffanta bata sani ba don tayi nisa a tunanin da take, yayi parking yana
kallonta, ta dago kai ta kalli anguwan da suke da sauri, sai kuma ta bude motar ta
sauka shi ma ya sauka. Tana gaba yana bin ta har suka shiga gidan, Hamid na zaune
parlor Nihad bata kallesa ba ta shiga bangaren da Inna take, Khalil ya karasa har
inda yake ya basa hannu sannan ya juya ya nufi bangaren Inna, Inna ta tsaya rike da
darduman hannunta tana ta kallon Nihad, sai kuma ta fashe da kuka kamar yar yarinya
ta ajiye darduman hannunta a gefen gado, ta zauna kasa tace "Allah ya isa tsakanina
da duk wanda yayi sanadin rabani da ke, ko ma waye Allah ya saka min, Allah ya
walakanta shi...." Sai kuma ta kalli Khalil da ya durkusa bakin kofa, ta wani tsuke
fuska tace "Kai kuma haka ake yi kawai ka dau yar mutane ka tafi da ita kauyen
Nijar saboda Allah ya ci da kai an aura maka ita babu ko sisinka, yau ga karfin
hali ni patu, kai ba kowan kowa ba dillalin kashi a leda zaka dau min jika ka mayar
kauyenku? Ashe haka buzaye suke basu da kamun kai basu da lissafi bamu sani ba, yau
ko da kudinka aka aura maka ita zaka dauketa ka kaita kauyen ku balle babu
kwandalarka, ina ma kaga kudin aurenta, wato ka samu xukekiyar yarinya a bagas
shine ka tafi kana ta fafa da ita a kauyenku kai ga ɗan banza" Shi dai khalil kansa
na kasa sai ɗan murmushi yake, Nihad kuwa banda hararanta babu abinda take tana
turo baki, Inna ta rike haɓa tace "Tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin wannan
azababben karfin halin ba, banda kaddara me Nihad zata yi da kai ɗan nan, ai kai ba
ajinta bane tafi karfinka ta ko ina, iyaka kayi aikinka na dreba ka kama gabanka
amma ina kai ina auran yar masu gida banda ƙaddara da ta riga fata, ɗan gidan
Habubakar Jikamshi ne saurayinta fa wannan dai da kayi ma walakanci kwanakin baya,
wanda da ba don mutuncina da na ubanta ba da ya daureka har karshen rayuwarka ka
rube a gidan yari, wallahi mun sha gaisawa da shi yafi a kirga ta waya, abinda idan
bashi da number mutum ma baya samunsa ba ko wani gaja yake waya da ba, sai in shi
ya yi niyyar kiran mutum" Nihad tayi karfin halin cewa "Dama gaisheki muka zo yi"
Inna tace "Toh ya tashi ya tafi sai kin huta haka kuma, wato ga ki ya sameki a
banxa sai dai Ibrahim ya tura masa kudi kaca kaca, shi gashi ai sai kyau yake yana
kara budewa uwa kirjin zai yage, ke kuma duk kin tsamure kin kanjale ke da kudin
ubanki, da kyar idan kina samun abinci ma kina ci sau uku a rana" Khalil ya daga
kai yana kallon Inna, a hankali yace "Toh bari muje ta debo kayanta Inna" Inna ta
masa wani shegen kallo tace "A ina??" Yace "Gidan da muka ajiye kayan" Tace "Wani
gidan ne?" Yace "Nan cikin gari" Tace "Toh wai da daga ina ku ke?" Yace "Kauyenmu"
Ta buda baki tana kallonsa, can tace "Toh maza maza tafi ka debo mata kayanta,
kauyen uban wa, kaga tayi kalar yar kauye banda dai baka tsoron Allah duk girmanka,
kaiii Ibrahim ma dai sai Allah yayi masu hisabi da Nihad, don ya cuceta ya gurbata
mata rayuwa, wallahi ya cuceta" Khalil ya mike yana kallon Nihad dake ta kallonsa,
yace "Za muje ki debi kayan ne, don ban san wanda zaki bukata ba" Mikewa tayi, Inna
tace "Ta debi me, Bawan Allah dukka zaka tafi ka kwaso mata ka kawo nan inyi jinyar
jikata ko zata marmaro, shi kuma Ibrahim yaje hakkinta ma baxae bar sa ba duk da ni
nace na yaɓa da hankalinka kawai a aura mata kai, bansan kai ma mugu bane, ashe
kauyen da dadi ka gudo ka dawo birni ka nemi tukin mota, maza tafi ka kwaso mata
kayanta" Nihad tace "Toh ai ni xan je in xaba kayan, ba dukka nake sa wa ba fa"
Inna tace "Duk da haka kuje ki kwaso su gaba daya, baki ji yace wajen ajiya kayan
suke ba, idan aka kwashe maki kaya ta ina za a fara...." Nihad tace "Toh" Khalil na
kallon Inna yace "Sai anjima" da sauri tace "Toh" Juyawa yayi ya fita ta bi sa da
harara, Nihad ta bi bayansa, Inna tace "Maza kiyi ki dawo" Har suka iso mota babu
wanda yace komai cikinsu. Bayan sun bar layin ya juya ya kalleta yace "Kala nawa
zaki debo kayan?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ko dukka za a debo?" Ta hade
rai tace "Ni nace maka zan koma ne?" Yace "Ai ban sani ba" bata kuma ce masa komai
ba bayan tafiyar kusan minti talatin ta gansu gaban wani hotel, ta kallesa, ya
fiddo wayarsa dake ring ganin Mami ke kiransa ya jinginar da kansa jikin kujeran
motar, can dai ya daga ya kai kunne a hankali yace "Ina yini?" Daga daya ɓangaren
ba tare da ta amsa ba a takaice tace "Karfe nawa zaka taso goben?" Yace "Da safe"
Tace "Ai dai ka ji inda nace kaje idan ka sauka ko?" Yace "Toh saboda me?" Mami
tace "Ohh kace saboda me? To in baka da hankali ka shigar masa gida idan ka shigo
Abuja, wai ma in tambayeka kana da wani kudurin na daban ne a ranka da yasa ka dage
sai ka amshi takardunka dake wajensa bayan babu abinda ka rasa yanzu?" Ya ɗan yi
shiru, sai kuma yace "Ba komai, just in case of necessity" Mami tace "Toh kana
sauka Abuja xaka bani in mayar masa kuwa" Khalil ya bude baki yace "Ki mayar masa
kuma Mami?" Tace "Haka nace" Shiru yayi, yana jin ta kashe wayar ya ajiye, bayan
few seconds ya kalli Nihad yace "Mu je ki dau wasu kayan naki da kika bari a Abuja
na taho maki da su" Yana fadin haka ya bude motar ya sauka, ta bi sa da kallo sai
kuma ta sauka, sai da ya kulle motar sannan ya nufi cikin hotel din ta bi bayansa,
makullin dakin ya amsa tana biye da shi har zuwa dakin da ya sauka dazu da safe, a
hankali take tafiyar har ta shiga cikin dakin ya kulle kofar, taga ya shiga bandaki
ya dauro alwala ya fito, nan dakin ya shimfida darduma zai yi sallan don an idar a
masallaci, Nihad dai ta dinga bin dakin da kallo don bata ga alamar jaka balle kaya
ba, can dai ta nufi bandakin ita ma tayi alwala ta fito, ta dau wani darduman ta
shimfida xata yi sallan...
Bayan ta idar da sallan ta kallesa don kwanciya yayi kan gadon ya rufe idonsa kamar
me bacci nan ko ba bacci yake ba, kawai neman mafita yake na chakwakiyar nan da
yake ciki, he don't even know where to start from, it's doesn't look easy at all,
definitely yasan ko harbesa Abba zai yi baxai mayar masa da takardunsa ba, to shi
wannan ma ba damuwarsa bane, babban tashin