Showing 141001 words to 144000 words out of 268471 words

Chapter 48 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

sani ba don tayi
nisa tunanin da take, Mimi ta kamo hannunta tace "Dear" Firgit Nihad ta dawo, Mimi
tayi murmushi tace "Mun iso" Nihad ta kalli mutumin da ya bude masu motar yana
jiran su sauko, ta sauka daga cikin motar, sannan Mimi ma ta sauka, kallon wajen
Nihad ta dinga yi tana imagining duk nan saloon ne? How big and beautiful, ganin
yanda ta tsaya Mimi tace "Mu je" Nihad ta bi bayanta ta kasa daina kallon saloon
din har suka shiga ciki, nan taga fararen mata ne masu gashi har gadon baya ke zuwa
gyaran gashi wajen, har turawa da larabawa, kana ganin cikin saloon din kasan ba
karya, Mimi tace "Ke ma kiyi gyaran gashinki" Nihad dai bata ce komai ba, da Mimi
ta sake mata magana tace "Ohk" sai da suka 6ata kusan awa daya da rabi a saloon din
daga karshe suka fito, har sannan kuma wanda ya kawosu na jiransu a motar, har suka
isa gida Nihad na duniyar tunanin da ta fada, mamakin Khalil kawai take.... why
then did he disguise himself and come to their house as a driver? What might be his
mission? And who were those villagers he took her to and claimed they are his
parent? Tambayoyin da take ta ma kanta kenan amma babu amsa, ta kuma rasa amsan,
kenan Nihal ta san wanene shi shiyasa take kulasa har da exchanging number? Nan
abubuwa da yawa da suka faru tsakaninta da shi a gidansu suka hau dawowa mata
vividly, lkci daya tayi saurin kawar da tunanin daga xuciyarta don ko tunawa bata
son tana yi, a haka har suka isa gida... Basu tarda kowa a Main parlor ba Mimi ta
raka Nihad har dakin da aka sauketa, Nihad na kallonta a hankali tace "Thank you"
Murmushi kawai Mimi tayi mata ta juya zata fita, Nihad tace "Wait plss, ina son xan
maki tambaya" Mimi ta juyo tana kallonta tace "Ohk" a hankali Nihad tace "I have
this female friend, a guy came to stay in their house... he showed he was a nobody,
i mean he disguised him self, he hide his identity, so all through his stay a
gidansu yana mata abubuwa gadara gadara, sannan he don't have an atom of respect
for her as per somebody that came to stay and work under them, shikenan ita kuma
sai bata raga masa, shi ma kuma bai fa sa walakanci da gadara da yake mata ba, to
cut everything short har dai ya bar gidan, ita kuma it now happens tana nasu gidan
da zama for just a while, and he wasn't what
she took him to be, she saw him a different person in his parents house, idan ke
ce a shoes din kawar nan tawa tell me how u will handle everything...." Mimi ta
fashe da dariya sosai, ta zauna gefen gado tana kallon Nihad still laughing tace
"Really?" Nihad dai fuskarta babu yabo babu fallasa tace "Tell me how u will handle
it" Mimi ta sauke ajiyar xuciya tana murmushi tana gyada kai tace "Ohk, if i should
be in this shoe gaskiya xan ji kunyarsa sosai...." Nihad tace "Mind you, sanda yake
gidansu baya respecting dinta sannan walakanci da gadara kawai yake mata da gaya
mata bakar magana, ya sha hadata da parents dinta har ya kai ya kawo nobody is even
supporting her again in their house, shi kuma ba a ganin nasa laifin, kullum shine
me gaskiya ita kuma ayi ta mata fada" Mimi dai murmushi kawai take tana kallon
Nihad tace "Amma ita bata masa walakanci ko cin mutunci ko cin zarafinsa ba, or
even gori during his stay?" A takaice Nihad tace "Tayi mana, tunda ae shi ya ja
komai" Mimi dai ta kasa daina murmushi, can tace "Ohk in ni ce, to make peace reign
xan samesa a gidan nasu in basa hakuri ince let by gones be by gones plss, we just
misunderstood ourselves amma yayi hakuri komai ya wuce" Nihad ta katse ta tace
"Idan baxa ta iya basa hakurin ba fa?" Mimi tace "Then ko hanya baxan dinga barin
yana hadani da shi a gidan nasu ba, i will try all possible best to be avoiding him
sbda duk sanda na gansa a gidan xan dinga tuna abubuwan da suka faru a baya and i
might be feeling guilty for everything.... So idan ni ce i will prefer in basa
hakuri a wuce wajen, saboda with all that have happen baxan samu peace of mind din
xama a gidan ba" Mimi na Murmushi ta kare maganar, Nihad tace "Ai shima duk abinda
yake mata bai ta6a bata hakuri ba" Mimi tayi dariya tace "Toh shikenan, sai kawai
tayi ta avoiding dinsa, that's just it" Nihad tace "Thank you for ur advice to her"
Mimi tace "Welcome dear" Daga haka ta juya ta fita, Nihad ta koma gefen gado ta
zauna a hankali. Bayan Magriba Nihad ta tafi bangaren Mami ta dalilin kiran da Mimi
ta shigo tayi mata wai Mami na kiranta, kwance ta ga khalil a parlon farko waya na
kare kunnensa, ta kalli Mimi ganin ta shiga next parlor din, ta nufesa trying her
possible best to be calm tace "Ka bani wayata da Aunty Maryam ta bani...." Ko
kallonta bai yi ba, from the way yake magana har ta gane da warce yake wayar, ganin
yayi banza da ita tace "Magana nake maka" Ya katse wayar da yake ya mike zaune yace
"Why are interrupting my call?" Taki ce masa komai, mikewa yayi ya bar ta a wajen
ya fice daga parlon ta bi sa da wani kallo, can ta shiga daya parlon. Mami na
kallon Nihad bayan ta shigo ta gaisheta tace "Ba dai wani matsala ko? And i hope u
are comfortable a dakin?" Nihad tace "Eh Mami nagode" Mami tace "Good, if there is
anything u let me know" Juyawa Nihad tayi ta fita. Washegari da safe Nihad ta fito
wanka kenan Mimi tayi Knocking, ta saka hijab dinta ta tafi ta bude mata kofar,
Mimi ta sakar mata murmushi tace "Good morning Neehad" Nihad ta mayar mata da
murmushin tace "How was ur night" Mimi tace "Alhamdulillah, Aunty Maryam wants to
speak to you on phone" daga haka ta mika mata wayar tace "Idan kun gama ki sameni
parlon Mami" Nihad ta gyada mata kai ta juya ta koma cikin dakin, wani farin ciki
taji jin muryar Aunty Maryam, bayan sun gaisa Aunty Maryam tace "Ina wayar da na
baki Nihad?" Nihad tace "Ban kara ganinsa ba Aunty" da mamaki Aunty Maryam tace
"Baki gansa ba kuma? Ba a jakarki kika sa ba?" Nihad tace "Ehh na duba kuma ban
gani ba" Aunty Maryam tayi shiru, can tace "Waye ya dau maki jakar?" A hankali
Nihad tace "Shi...." Aunty Maryam tace "Khalil?" Nihad tace "Ehh" Aunty Maryam tace
"Ohk, shikenan xa mu yi magana" daga haka tayi mata sallama ta katse wayar, Aunty
Maryam na katsewa Khalil ta kira, bayan ya daga ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tace
"Bawan Allah akan wani dalili ka dauke wayar da na ba Nihad?" Khalil dake kwance ya
mike zaune ya buda ido yace "Waya kuma... Ita tace maki haka? Beside Aunty ai ni
ban ma san da wata waya ba" Ta dakatar da shi tace "Kar ka raina min hankali Malam,
babu wanda zai dau wayar nan sai kai, yanzu dalilin da ka dauke wayar kawai nake
son ji, period" Ya koma ya kwanta yace "Because kamata yayi tayi concentrating a
kararunta yanzu ba ta rike waya ba...." Aunty Maryam ta saki baki tana sauraronsa,
sai da ta bari yayi shiru sannan tace "Toh dauki wayar ka mayar mata, xan kirata da
shi nan da minti goma...." Shiru yayi bai ce mata komai ba tace "Baka ji abinda
nace bane?" Yace "Na ji" Tace "In kuma kana son mu samu matsala da kai ka kara
dauke wayar nan daga wajenta ka ga, ai kana ji sai da nace maka na ba wani number
layin shine xaka wani kama waya ka ɗauke, jaririya ce ita da baxata rike waya ba ko
kuma waye ya ta6a xuwa jami'a ba waya?" Khalil dai bai ce mata komai ba, tace
"kamar yanda nace nan da minti goma zan kira wayar bana son jin sa a kashe, sannan
kuma ita nake son jin ta daga kiran" Daga haka ta katse wayarta ya taɓe baki, bayan
few minutes ya sauka daga saman gadonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya dau
shirt dinsa ya saka ya dau wayar sannan ya fita. Nihad ta gama shiryawa ta dau
gyalenta ta fita zuwa parlon Mami, dai dai corridor that will lead to the parlor
suka hadu da shi yana zuwa ta opposite dinta, taki yarda su hada ido har ta iso
kofar xata bude taji ya fixgo hannunta ya bar bakin kofar, zaro ido tayi tana bin
sa tace "Meye kake ja na haka?" Bai saurareta ba yana ta tafiya da ita, Balcony din
part din ya shiga tare da ita, Ta dinga bin domain din wajen da kallo, kai baxaka
ce ba a kasar waje bane, can ta kallesa tace "Why will you drag me this way??" Yace
"Bana jin wannan yaren" Ta wani kyabe baki ta dauke kai tana kallon titi, a takaice
yace "Zan baki waya kamar yanda aka ce in baki, amma ina son tunasar maki cewa shi
aure ko ma wani iri ce daraja ne da shi sannan ba abar wasa bace, ba ruwan Allah da
auren soyayya ko auren kiyayya ko auren hadi, so abu kadan zaki yi yanzu ki sa6a ma
Allah, ki ja ma kanki fushinsa...." Da mamaki Nihad ke kallonsa har da bude baki,
bai bata space din cewa komai ba ya ci gaba yace "Dama kawai ina mutunta iyayenki
ne shi yasa har yanzu ban raba auren da ke tsakanina dake ba ina jiran appropriate
time din yin hakan, sannan i have conscience baxan iya sakin ki a halin da kika
shiga days back, don a sanda mahaifinki ya nuna baya bukatar ni dake a garin da
yake, a sannan ya kamata ace na rabu dake na kama gabana don dama saboda shi nake
zaune dake, amma ban yi hakan ba, tausaya maki da nake ne dalilin da yasa har yanzu
aurenki ke kaina.... So a halin da ake ciki yanzu bazan so a rubuta maki zunubi ta
dalilina ba, don haka idan na lura baxa ki daraja martaban aure ba kuma zaki janyo
ma kanki fushin Allah to zan raba auren dake tsakaninmu don sama maki sauki, dama i
was hoping to do that in the rightful time a lokacin da ya kamata, probably idan
kinyi nisa karatunki kin kusa kammalawa, kinyi reconciling da mahaifinki, kinyi
kokarin amending few damages that u did to ur self, kin kuma sake fahimtar rayuwa,
kin fahimci duniya da mutanen dake cikinta da kyau, but i Sense duk wannan won't be
possible saboda hanyar da aka daukar maki na rike waya, and communicating with a
guy...." Nihad dai kallonsa kawai take, yace "So how ever u chose it to be is left
to u, ina maki abubuwa da yawa ne ba don kin cancanci in maki ba, sai ɗan darajan
iyayenki..." Yana gama fadin haka ya ciro wayar aljihunsa ya mika mata yana
kallonta yace "I will decide on what to do in few days time" ta sa hannu ta amshi
wayar, ya juya ya bar wajen.... Nihad ta shiga parlon Mami ta tadda Mimi na jiranta
su yi Breakfast, bayan ta zauna shayi kawai ta iya sha sai irish kadan, ta na dai
zaune idonta na kan tv abubuwan da Khalil ya gaya mata na ta dawo mata, tabe baki
kawai tayi, aka bude kofar duk suka daga kai, Aunty Hassana ce ta shigo parlon,
bata amsa gaisuwar Nihad ba tana kallon Mimi tace "Ke ina uwarki?" Mimi ta mike ta
shiga dakin Mami, Aunty Hassana ta dinga hararan Nihad, a hankali Nihad ta mike ta
nufi kofa ta fita daga parlon don haka kawai ta ji tana tsoron matar, Aunty Hassana
ta bi ta da harara, tana ta tsaye har Mami ta fito, Mami na kallonta tace "Mun
tashi lafiya Aunty Hassana" Aunty Hassana ta dakatar da ita tace "Ba wannan ya kawo
ni ba, ina ce ai ko ba komai Hajiya Fatima yanda xa ki mutunta uwar mijinki da tana
raye haka nima ya kamata ki girmamani ki mutunta ni don ni din ba banza bace, Da
mijin nan naki da kike takama ya sha nono ni ya sakar ma, amma naga baki da warce
kika raina sama da ni, yanzu ace wannan yarinyar da ta zo gidan nan tun jiya har ta
kwana zuwa yau ya dace ace baki turata ta gaidani ta gaida Amina a gidan nan ba?
Idan ita Amina bata isa ba nima din ban isa ba kenan? Kawai yarinya ta shigo gidan
mutane tsabar ba a nuna mata matsayin wa enda ta samu a gidan ba sai ta wuce ka
wuce bata gaida ka ba, ko daga kai baxata yi ta kalleka ba, to akan wani dalili?"
Mami ta kalli Mimi tace "Mimi je ki kai ta ta gaishesu" a fusace Aunty Hassana tace
"Aa bama bukata, taje ta gaida wa? kawai dai ina kara baki shawaran ki daina abinda
kike, in raini kike ji a gidan nan to karki matso da shi inda nake, don ni ba
abokiyar yin ki bace Fatima" tana kai wa nan ta fice daga dakin kamar iska, Mimi ta
kalli Mami tace "Why is she always creating issues out of nothing? From this to
that, is she normal?" Mami tace "Jeki ki kaita nace ta gaishesu ban iya wahala da
safen nan Mimi, da nasan abinda ya kawota kenan ma ni cewa xanyi kice mata ina
bacci" Mami na kai wa nan ta juya ta koma dakinta. Khalil na zaune parlon Abbansa,
ya jira har ya gama wayar da yake na kusan minti goma, Abba na kallonsa bayan ya
gama a takaice yace "May i help you?" Khalil ya gyara zama yace "My Curriculum
vitae, the key to my houses and their written document, my land title, my car....
Ina bukatarsu gaba daya, and I also want my business account unfrozen" Kallonsa
kawai Abba yake, can ya mike yana kallonsa da kyau yace "Till u pay ur debt of
800m, idan ba haka ba duk assets din nan da ka lissafo ina me tabbatar maka siyar
da su zan yi, kuma basu kai biyan bashin ba ma, shi kuma Cv din in kona, after all
i sponsored you...." Khalil ya dinga kallon mahaifin nasa, Abba yace "So Now get
out before i shoot ur leg" mikewa Khalil yayi ya nufi kofa kamar xai tashi sama ya
bude, sai kuma ya juyo yace "But dad, I can't pay for what I know nothing
about...." Yana fadin haka ya fice daga parlon, direct bangaren Mami ya tafi, Mami
na ganinsa ta mike tace "Lafiya" Yana huci yace "Mami me yasa har yanzu Abba ke
danganta 800m dinsa da ni?? Ina zan kai har 800m" A hankali Mami tace "Saboda kai
ya ba, a hannunka yasan kudinsa" A fusace Khalil yace "Toh ni ban san komai kan
kudin nan ba, why is he not believing me?" Mami tace "Yanzu me ya kawo maganar
kudin?" Yace "Naje na samesa xan amshi abubuwa na da ya amshe min" Mami tace "Amma
ai na hanaka ko? What are you lacking now without them?" Khalil na girgiza kai yace
"Baxan iya ci gaba da zama bana aiki ba Mami, ya sa anyi sacking dina a inda nake
aiki, to ya bani Cv dina in nemi aikin a wani waje mana?" Mami tace "Idan da ka
saurareni da baka je masa da maganar wani Cv ba Khalil, me kake bukata da baka samu
a yanzu haka? Baka fi wani me aikin samu ba duk da haka? Every month ina tura maka
300k banda wanda kannena ke baka, so me xaka yi da Cv yanzu" a fusace Khalil yace
"Ni neman auren Nadeeyar ma bana son yaje min, xan samu kawu kawai su je" yana
fadin haka ya nufi kofa a fusace, Mami ta buda baki, sai kuma tace "Toh ai mun yi
magana da shi jiya yace next week xai tura representative nasa su je neman auren,
kar ka fara xuwa wajen kowa idan ba ɓacin ransa kake son gani ba" Tuni khalil ya
fice daga parlon. Hajiya Amina ta shigo bangaren Aunty Hassana tace "Aunty Hassana
kin ji abinda Oga yake ce min daxu kuwa?" Aunty Hassana tace "Me yace?" Hajiya
Amina tace "Wai satin da xa a shiga xai tura a nema ma Khalil auren yarinyar nan
dai, ita fatimar ta masa maganan hakan..." Aunty Hassana ta gwalo ido tace "Da
gaske?" Hajiya Amina tace "Wallahi, kafin ya fita yake sanar min" Aunty Hassana
tace "Ai ko bai gaya min ba kuma na shiga gaishesa daxu" Hajiya Amina tace "Toh dai
shine nace bari in zo in sameki" Aunty Hassana tace "Toh bari inyi wanka zan fito
yanzu" Hajiya Amina tace "Toh sai kin fito" Daga haka ta juya ta fita, Aunty
Hassana ta mike da sauri ta dau wayarta ta shiga daki tayi dialing number
aminiyarta, tana dagawa tace "Ke kuma haka ake Chamo daga cewa kina zuwa sai in ji
shiru" Daga daya bangaren aminiyar tata ta kece da dariya tace "Ke dai bari na
shiga rububi ne, ai da ma sai dai ki gan ni yau to kuma sai tafiya Kaduna ya
kamani, ya gida ya su Sajida" Aunty Hassana tace "Lafiya lau, ni baki gaya min
yanda ku yi da mutumin nan kan maganar da muka yi dake ranan ba har yanzu" Chamo
tace "Wallahi yace daga dubu dari tara da hamsin ko biyar baxai sake ragewa ba,
kuma ke ma dai kin shaida aikinsa, ba fa kowa yake ma aiki ba don shi aiki ma yawa
yake masa" Aunty Hassana tace "Shikenan, don wallahi yanzu Amina ta shigo take gaya
min satin da xa a shiga ma xa aje neman auren yarinyar" Chamo tayi wani dariya irin
ta bosawa tace "Wuyarta ba a tura masa kudi an fara aiki ba, ke dai turo kudi kawai
aminiya" Aunty Hassana tace "Toh Sadiya, yanzu kuwa zan saka maki, so nake da kansa
zai birkice masu yace ya fasa bai sonta, kuma dab da xa a kai kudin" Chamo tace "An
gama, sako kudi yanzu" Aunty Hassana ta katse wayar ta tura mata kudin.


ki biya ki karanta cikin salama hankali kwance.

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788....


44

Da daddare Mimi na parlon Mami tana ta danna wayarta bayan sun gama cin abinci da
Nihad, kallo daya zaka ma Nihad ka gane she is moody, gaba daya she is
uncomfortable da zaman gidan, Noor ta shigo parlon tana kallon Mimi tace "Hey Madam
Dad yana kiranki..." Mimi tace "Ohk" Daga haka ta mike ta kalli Nihad tace "I am
coming" Nihad ta gyada mata kai, ta nufi kofa Noor na biye da ita, Nihad ta bi su
da kallo, a hankali ta kwantar da kanta jikin kujera tana jin kewar nata Abban,
bayan sun fita Noor

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login