Showing 123001 words to 126000 words out of 268471 words
da idanuwanta da suka yi jajir, ya
kasa ci gaba da kallonta ya sauke idonsa yace "Kiyi hakuri, take ur breakfast now"
A hankali ta dinga subsiding kukan da take amma tana jin xuciyarta na mata zafi, Ya
sauka ya koma inda take without looking at her ya dau cup ya zuba mata ruwan shayi,
ya haɗa mata shayin, ya ajiye side dinta, ita dai goge hawayen da yaki tsaya mata
kawai take tana kallonsa, Bude kofa yaji anyi a other parlor din, ya dau shayin
yace "Tashi mu je ciki kiyi breakfast din" Mikewa tayi da sauri ta bi bayansa zuwa
bedroom din Mami, ya ajiye mata shayin sannan ya koma zai dauko sauran abincin,
Mami ce ta shigo parlon, ganin Nihad bata parlon ta sauke ajiyar xuciya, juyawa
khalil yayi bayan ya dau abincin ya nufi Bedroom da sauri saboda muryoyin wa enda
yake ji, Mami ta zauna parlon har Hajiya Amina ta karaso ta zauna, Sai Hajiya
Hassana ma ta shigo ta zauna, Hajiya Amina tace "Yanzu tun jiya dama Khalil ya dawo
gidan nan aka ki sanar mana? Sai kace wani mugun abu, sannan kuma ya ki zuwa ya
gaida mu?" Mami tace "Jiyan ai ba da wuri ya dawo ba" Hajiya Amina tace "Toh ai bai
wuce duk mu yi barka ba, mu bama bakin ciki da abun alkhairi, daxu su Farhana ke ce
min ya dawo nace to ai haka dama ake so" Hajiya Hassana dake girgiza kafa tace
"Yana ina yanzu?" Mikewa Mami tayi ta wuce bedroom dinta, duk suka kalli juna suka
ta6e baki a tare, Mami na shiga dakin ta kulle kofar, Khalil na zaune ya sa Nihad a
gaba tana shan shayin hannunta da kyar, yana ganin Mami ya mike ɗan yana durkushe a
gabanta ne, Mami tace "Ka fito ku gaisa" khalil ya kalleta ya ɗan hade rai yace "In
gaisa da wa?" Mami tace "Ka rufa min asiri, minti nawa ne kun gaisa ka juyo" Ya
girgiza kai yace "Aa kiyi hakuri Mami, wallahi baxan fita ba" kasa cewa komai Mami
tayi tana kallonsa, ya koma saman kujera ya zauna yace "Saboda me xan gaisa da su,
sanda xan tafi sallama muka yi da su balle mu gaisa yanzu da na dawo, i am sorry
Mami i am not going out" Mami sai kallonsa take, can tace "Toh ko bakin kofa ai sai
ka tsaya Khalil, kai baka gudun abun magana ko?" Yace "Aa gaskiya bana gudu Mami, i
am not moving an inch from here, ita Aunty Hassana dama a shirye nake da ita na
dawo gidan nan, she shouldn't dare cross my part" Mami dai duk jikinta yayi sanyi
ta kasa ce masa komai, daga karshe Khalil ya tashi ya bude bandaki ya shige, A
hankali Mami ta juya ta fita ta koma parlon tana kirkiran murmushi tace "Shiryawa
yake, idan ya gama duk xai je ya gaishe ku" Hajiya Hassana ta daga mata hannu ta
dakatar da ita da sauri tace "Aa ba sai kin karesa ba Fatima, ai bamu isa ya fito
ya gaida mu ba ne, mu a su wa?" Mikewa tayi tana kallon Hajiya Amina tace "Taso mu
je Amina" Hajiya Amina ta mike suka nufi kofa Mami ta bi su da kallo har suka fita,
Mami ta sauke ajiyar xuciya ta zauna. Daga karshe ta mike ta fita daga parlon nata,
ba a dau lokaci ba ta dawo rike da kayan Mimi, ta shiga dakinta ta ajiye gefen gado
tana kallon Nihad tace "Shiga bandaki kiyi wanka yanzu" Khalil dai na zaune yana
kallon Mami, Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta fito parlor, biyota yayi ya
zauna kujeran kusa da ita yayi kasa da murya yace "Don Allah ki saurareni Mami"
Mami tace "Sauraran me xan maka Khalil" Yayi gathering courage xai yi magana aka
bude kofa duk suka juya, Farhana ta shigo parlon tana kallon Khalil tace "Yayanmu
wai kaje Abuu yana kiranka" Yayi shiru yana kallonta, Mami ta hadiye abu da kyar
tana kallon Farhana tace "Ki je yana zuwa" Juyawa tayi ta bar wajen, Mami ta
kallesa da damuwa tace "Ka je kaji kiran da yake maka" Khalil bai iya yace komai
ba, can ya mike ya fita, slowly yake tafiya har ya isa bangaren Abba, yayi sallama
sai da aka amsa masa sannan ya shiga, Abba na tsaye ya shirya alamar zai fita,
Khalil yayi ma Aunty Hassana kallo daya ya zauna kasa, a hankali yace "I am here
sir" Abba yana nuna masa Aunty Hassana yace "Who is she to me?" Khalil bai iya yace
komai ba, Calmly Abba yace "Tambayarka nake" Khalil ya kallesa yace "Ur sister"
Abba yace "Good, kasan da haka ka dawo gidan nan baka je ka gaida ita da Hajiya
Amina ba" Khalil yayi shiru, Aunty Hassana tace "Aa yaya, uwar ce ta sa shi hakan
ba kowa ba, ita ce xata hanasa ya shigo ya gaida mu saboda ba mu isa ba, sannan
still mun tashi mun je har can bangaren nata don ganinsa amma kememe yaron nan ya
ki fitowa ta wani fito tana karesa, ita Amina da abu kadan ke sa ta kuka muna
fitowa ta kama kuka wai ai wannan cin mutunci ne, ni kuma kasan halina bana daukar
nonsense shine yasa ma na zo na sameka yanzu, yaron da a haife na haifesa? Sau nawa
nake saka ka a gaba ina cewa kayi hakuri ka bar sa ya dawo gidan nan, shine zai
dawo ya saka min da haka?" Abba dai yayi shiru yana safa da marwa a babban parlon
nasa, Khalil ya jefa mata wani kallo ta gefen ido, Can Abba ya juyo yana kallonsa
da kyau yace "Bata hakuri, sannan duk ka bi su bangarensu ka gaishesu kace masu ka
dawo" Khalil ya kalleta a takaice yace "Yi hakuri" Daga haka ya mike ya fice daga
parlon, Da ido Abba ya bi sa, Anty Hassana ta saki baki ita ma ta bi sa da kallo,
Can ta kalli yayan nata xata yi magana yace "Tashi ki je Hassana, xan nemesa anjima
idan na dawo" Aunty Hassana ta dinga kallonsa da mamaki, sai ma taga ya nufi wajen
takalmansa ya zauna yana kokarin sa wa, tashi tayi daga karshe ta fice daga parlon
kamar xata tashi sama, Khalil na fita ya koma bangaren Maminsa, Mami na tsaye tana
kallon Nihad dake sa mayafin Mimi da ta amso mata, Mami ta fesa mata turaren
hannunta tana kallonta tace "Baki taho da dankunne ba?" Nihad ta girgiza mata kai
kawai, Gaba daya in ka kalleta sai ta baka tausayi, duk ta fita hayyacinta, Khalil
dake tsaye bakin kofa kallon Mami kawai yake ya ma rasa abinda xai ce mata, lokaci
daya jikinsa yayi sanyi don bai san what she is up to ba, Mami ta dauko ma Nihad
wani dankunnen gwal mara nauyi ta mika mata tace "Sa wannan" Nihad ta kai hannu a
hankali ta amsa tace "Nagode" sannan ta saka dankunnen, Mami ta dau nata mayafin ta
yafa a shoulder tana kallon Nihad tace "Mu je" Nihad ta nufi kofar ta bi gefen
Khalil ta fita, Mami na isa bakin kofar ya matsa a hankali ya bata hanya, makullin
motarta ta mika masa tace "Mu je" Yayi karfin halin cewa "Where Mami?" Mami tace
"Amshi makullin a hannuna ko?" A hankali ya kai hannu ya amsa, Mami ta fita Nihad
na biye da ita. Har suka fito compound din gidan babu wanda suka hadu da a hanya
kamar dai babu kowa gidan, Nihad ta dinga bin compound din da kallo, it's soo
beautiful and big, Khalil ya nufi Ride din Maminsa yana tafiya a hankali, gaba daya
ya rasa tunanin da xai yi, Mami ta dinga amsan gaisuwan da securities din cikin
gidan ke mata, Nihad dai sai binta take tana satan kallonsu, back seat Mami ta bude
tana kallon Nihad tace "Shiga" Nihad ta shiga motar a hankali, Mami ma ta shiga
sannan ta kulle motar, bayan few minutes Khalil ya ja motar ya fita compound din
bayan an bude masa wagegen gate din gidan, slowly khalil ke driving din har suka
fita anguwan, sai a sannan yana kallon Maminsa ta madubi cikin sanyin murya yace
"Where are we going Mami?" Mami tace "Take me to Maryam's house" Ya d'an sauke
boyayyen ajiyar zuciya sannan ya nufi gidan Aunt dinsa, Nihad sai kallon anguwanni
masu kyau take, amma kana mata kallo daya zaka san she is worried, suna shiga
estate din su Aunty Maryam basu dade suna tafiya ba suka isa gidan, Khalil yayi
horn bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Mami ta sauka tana kallon Nihad
tace "Sauko" Nihad ta sauko, ta bi bayan Mami zuwa gidan, Aunty Maryam ta rungume
Khalil tana welcoming dinsa cike da farin ciki tace "Idon son dina kenan nake gani
haka?? Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah" Murmushi kawai yayi ya gaisheta, ta
amsa tana
kallonsa daga sama har kasa, Lokaci daya er fara'ar fuskarta ya bace tace "Welcome
son, Allah Ubangiji ya saka maka abinda aka maka" Murmushi kawai shi dai yake,
Aunty Maryam na rike da hannunsa ta nufi parlor tana gaida Mami da ladabi, murmushi
dauke fuskarta tace "Har kinyi Kumari yar uwa, Allah Ubangiji ya raba mu da mugun
ji da mugun ganin" Murmushi kawai Mami tayi, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take
don ita ma kana kallonta kasan halfcast ce, fara ce kal kamar Mamin khalil, sannan
ita ma ga gashinta da tayi packing har kusan gadon baya, Aunty Maryam ta kalli
Nihad don sai sannan ta lura da ita tace "Sannu da zuwa yan mata, shigo ki zauna"
Nihad ta sauke kanta ta zauna kasa a hankali ta gaisheta, Aunty Maryam ta amsa tana
Zaunawa gefen yayarta, tuni mai aikin Aunty Maryam ta cika gabansu da ruwa da lemo
da kayan maqulashe, Aunty Maryam ta kasa daina kallon Khalil tana murmushi, she is
so happy seeing him, can dai ta kalli Mami tace "Ya gida Aunty?" Mami tace
"Alhamdulillah, kira mai aikinki ta shiga da bakuwar nan ciki ta bata breakfast
naga bata wani yi a can gida ba" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Ayya, to bari in
kirata ta zo" Aunty Maryam ta kira mai aikinta a waya sai gata ta taho tace "Gani
Hajiya" Aunty Maryam tace "Ki shiga da bakuwar nan guess room ki hada mata
breakfast yanzu" Yarinyar tace "Toh Hajiya" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Tashi
ku je yan mata" Nihad ta mike a hankali ta bi bayan mai aikin da tayi wani bangaren
daban da ita. Mami na kallon Khalil tace "Ko da za ayi sati admission letter din
bai fito ba xata zauna nan har ta karba sannan ta koma gidansu" Khalil ya dinga
kallonta ya kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Who is she Aunty?" Mami tace "Tare
ya zo da ita" Aunty Maryam ta kallesa tace "Wacece ita din" yayi kasa da murya yace
"Yarinyar mai gidan da na zauna a kano" Aunty Maryam tace "Allah sarki, Admission
take nema nan din?" Ya gyada kai kawai, Aunty Maryam tace "Lallai ya yarda da kai
tunda har ya bar ka da yar sa har ku ka taho tare, Allah Ubangiji ya saka masa da
alkhairi" Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace "Ameen" Mami ta kalli Aunty Maryam
tace "Yaushe tafiyar naku, naji shiru baki ce komai ba" Tace "Ohh wllh yace sai
yayi settling a can kafin mu bi sa, may be nan da sati biyu in sha Allah" Mami tace
"Toh Allah ya kai mu" Aunty Maryam tace "Ameen" Khalil yayi kasa da murya cike da
karfin yace "Mami about that video.... yan dakinsu ne a makaranta suka mata bata
sani ba, sannan suka saki a social media... the Case is silently in court now,
mahaifin nata yayi sueing dinsu gaba daya, so that's why zai canza mata makaranta
yanzu, since the incident yake processing admission dinta a nan garin so
coincidentally xan taho sai yace mu taho tare da ita" shiru yayi cause he him self
knows he sounds so stupid, there is nothing making sense in what he is saying, Mami
tace "Toh ni ka ji nace wani abu Khalil? Allah dai ya tsare mana zuri'a gaba daya,
kawai ta zauna nan har sanda xa ta amshi abinda ta zo amsa sai ta koma gida, ae
shikenan ko...." Aunty Maryam dake ta kallonsu tace "Wai me ke faruwa?" Mami ta
sauke ajiyar zuciya briefly tayi mata bayanin abinda ya faru daxu da safe da yara
suka shigo, Aunty Maryam ta saki baki da mamaki looking speechless, can ta kalli
Khalil tayi kasa da murya tace "Wai kana nufin wancan ita ce yarinyar da video
dinta yayi trending weeks ago?" Khalil bai iya yace komai ba, Aunty Maryam ta
girgiza kai hankali tashe tace "Amma ta bata wayonta, tayi tarnishing image dinta a
idon duniya, ta kuma yi ma kanta ta6on da goguwansa sae wani ikon Allah, duk yanda
aka yi bata ji, banda bata ji meye zaki zauna daga ke sai skimpy inner wears a daki
har maki video kina dariya, kai ai abun nan bai min dadi ba wallahi, Allah Ubangiji
ya tsare mana zuri'a, amma wannan ta6on ai baxai gogu ba har tsawon rayuwarta sai
ma ta tashi aure zata gane hakan barin idan tana da mahassada" Kallonta kawai
Khalil yake baya cewa komai, Aunty Maryam ta rike ha6a cike da jimami tace "Kaii,
sai kawai naji bata burgeni ba don bana son yaro mara kamun kai, don da tana da
kamun kai da babu yanda xa ayi tayi abinda tayi, babu yanda xa ayi hakan ya faru da
ita, wallahi ranan da naga videon ta sai da nayi tashin dare nayi addu'a Allah ya
kare mana xuri'a da al'ummar Musulmi baki daya, abun sam babu dadi, gashi babu inda
wannan videon bai je ba, kuma kun ga wllh ban ganeta ba ni banda kun yi magana, to
ma banda abun uban nata ai aurar da ita kawai ya kamata yayi a yanzu ba wai ya sake
biya mata makaranta a wani wajen ba, tana kanon ma a gabansu tana shakiyanci ina ga
ta hadu da yan matan garin nan ai kuma sai abinda hali yayi, gata wata sumu sumu
kamar bata magana... To kai garin yaya kasan mahaifin nata?" Khalil ya sauke idonsa
kasa, Mami dai sai kallonsa take, Aunty Maryam tace "Kayi shiru" Ya dago ya kalleta
a hankali yace "A sanda na sauka a kano bani da kowa bawan Allahn ya rike ni tamkar
dan sa, yayi accomodating dina, yayi feeding dina without knowing who i am,
mahaifiyarta mace ce mai kirki warce saboda ita nayi dadewar da nayi a tare da su,
ina jin ta kamar ke da Mamina a gidan, yayyinta maza kuwa zaman mutunci da girmama
juna muka yi da su, basu ta6a nuna min ni ba dan gidan bane, haka sauran yan
uwanta mata dake gidan, abinda nake so ku gane, ba wai na je masu da real identity
dina bane, i went der as a nobody, babu wanda yasan wanene ni har yanzu da nake
maku magana banda ita yarinyar yanzu, amma suka min karamci a irin wannan zamanin
da muke ciki, i know i can never repay them their good deeds, kuma yace in taho
tare da yarinyarsa ta amshi admission letter saboda wani mistake nata sai in ki?"
Aunty Maryam ta sauke ajiyar xuciya tace "Baxa ka ki ba kam, amma surutun yan gidan
nan naku ake gudu" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "That is it dear, abinda na guda
kenan na kawota nan gidan har ta gama abinda ya kawota ta koma, banda mu da muka
san wannan labarin da ka fada a kan gidansu yarinyar waye ya sani? Nobody, kai ko
sun ji cewa xa su yi karya kake, don haka duk abun magana gudunsa nake nan da ka
gan ni, daxun ma da suka shigo ba saboda Allah bane, gulma ce ta kawosu, yarinyar
kawai suka zo gani, ita kuma wannan yarinya ta bata wayonta don waje daddaya ne
xata je aki ganeta, Allah dai ya kiyaye ya tsare mana zuri'a, ya bata mijin da xai
aureta yayi overlooking mistakes dinta ya rufa mata asiri duniya da lahira, da da
mijin ma da auren kawai yayi mata ta ci gaba da karatun nata a dakin mijinta don
hakan zai fi mutunci, Allah dai ya takaita mata gori a duk inda xata kasance"
Khalil dai kallonsu kawai yake, Aunty Maryam tace "Ameen, da ganin wannan lamari
kasan influence na bad friends ne hade da rawan kai irin na yaran yau, saboda haka
ne ya kamata mu kara sa ma yaranmu ido sosai" Wayar Mami ya fara ring ta daga ta
kai kunne, bayan sun gaisa tace "Lahh ai gani a gidan Maryam, kin fito ne?" Mami
tace "Yauwa to, kawai ki taho nan din idan kin fito, shima yana nan ai" Daga haka
ta katse wayar, Aunty Maryam na kallonta tace "Wacece?" Mami tace "Hajiya Safeenah
ce" Aunty Maryam tace "Allah sarki, taji sauki kenan" Mami tace "Aa da sauki sosai,
3 days ago ma ai taje can gida wajena" Aunty Maryam ta mike tace "Bari inje in
sanar ma mai aikin can tayi mata wani abun kafin ta iso" Daga haka ta bar parlon,
Mami na kallon Khalil tace "Wai fasa tafiyar kayi yau Khalil?" khalil na danna
wayarsa yace "Sai na shirya Mami" Aunty Maryam ta ɗan tsaya kitchen din tayi
assisting mai aikinta bayan da ta gama hada komai ta bar mata ta fito parlor, duk
bata tarar da su a parlon ba, har zata wuce sama sai kuma tayi bangaren guess ta
kara ganin Nihad, don kawai abun ya tsaya mata a rai tun daxu, bude kofar dakin
tayi ta shiga ta ganta zaune kasa ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam na
kallon abincin dake ajiye tace "Baki yi breakfast din ba?" A hankali Nihad tace "Na
koshi" Aunty Maryam tace "Toh fito parlor kiyi kallo, yara sun jogane kayan kallon
nan din sai an gyara" Nihad dai bata ce komai ba ganin Aunty Maryam ta juya ta mike
a hankali ta bi bayanta, har suka fito parlor tare, nan din ma a kasa ta zauna,
Aunty Maryam ta tafi ta kulle kofa sannan ta wuce sama wajen Mami, Khalil na kwance
saman kujera Mami na basa labarin abubuwan da suka faru baya nan, Aunty Maryam ta
zauna kenan aka kira Mami, Mami ta daga tace "Kin iso ne?" Sai kuma Mami tace "To
bari a bude" Katse wayar tayi tace "Kin kulle kofar parlon ne Maryam?" Aunty Maryam
ta kalli Khalil da sauri tace "Dr ka bude mata kofa, yanzu kuma na kulle kafin in
hauro" Ya mike ya fita daga parlon ya sauka downstairs, Nihad na zaune ta k'ura ma
Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi a ciki take ba, kallo daya yayi mata ya
nufi kofar parlon ya bude, Da ladabi ya gaisheta yayi mata sannu da zuwa, da fara'a
tace "Maa sha Allah, ka dawo lafiya Khalil?" Yace "Alhmdlh mum" Tace "Toh
Alhamdulillah, sannu, Allah Ubangiji yayi maka albarka" Yana murmushi yace "Ameen"
Sannan ya koma gefe ta shigo parlon, ya juya ya nufi inda remote yake