Showing 75001 words to 78000 words out of 268471 words

Chapter 26 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

tsayawa bakin
kofar dakina ma baxa ki samu ba balle ki gwada min halinki na rashin tarbiya...
bari kiji ba bakin kofar dakina ba har bangarena ma sai ya haramta gare ki wataran
wallahi...." Sai kuma ya mike ya nufeta, sosai gabanta ke faduwa ganin yanda ya
daure fuska amma ta dake ta tsaya bakin kofar, ya tsaya dab da ita yace "Kinsan me
yasa baxan ke kulaki ba idan kina nuna rashin tarbiyar ki? Saboda ke din ban dauke
ki a bakin komai ba, ban dauke ki mace ba, ba kuma kallon mace nake maki ba, kallon
yar titi kuma er bariki nake maki, na dai girmama mahaifinki na amshi tayinki da
yayi min don shi din mutum ne me daraja da kima a idona, banda haka ko da duk
arxikin duniya aka hadani da ke wallahi wallahi baxan aureki ba don ni ba ajinki
bane ta ko ina na fi karfin ki...." Nihad ta zaro ido hade da bude baki tana
kallonsa, sai kuma ta cakumo kwalarsa cike da tsiwa tace "Ni kake ce ma yar titi
kuma er bariki??" Shaketa yayi ya hadeta da kofa ba shiri ta sakesa gabanta na
mugun faduwa, ya dinga kallonta fiercely yace "ina me baki shawara da kakkausar
murya, Kar ki sake gigin kai hannunki jikina, idan ko kika sake yin wannan kuskuren
to xaki sha mamakin abinda xan maki a gidan nan" Yana gama fadin haka ya turata
waje ya kulle kofarsa, kiris ya rage ta fadi, tana huci bayan tayi regaining
balance dinta tace "Kai din banza zaka bani shawara da kakkausar murya, aa sai dai
karyayyen murya, waye kai kuma me kake takama da shi, kuma wallahi ni ba er titi
bace don ina da gatana kuma da arxikin iyayena, kai kuma fa? Naga sai kayi tuki
kake samun na xubawa a aljihu?" Sai kawai ta fashe da kuka ta shige dakinta ta fada
kan gado tana rera kuka, duk Abba ne ya ja mata yau wai driver din gidansu ke
kiranta yar titi kuma yar bariki, kuka take kamar ranta xai fita, gaba daya ta
mance da wata Husnah, sai da taji ana kiran magrib sannan ta tashi ta goge idonta
ta xauna saman gadon, tana jinsa ya fita masallaci, banda muguwar tsanarsa babu
abinda ya cika xuciyarta, wallahi ta tsanesa, she hate him with passion, tana jin
ya fita masallaci ta mike ta dau mayafinta ta fita xuwa baya wajen Husnah, wayam ta
ga wajen, ta juya ta koma ciki, wayarta ta fiddo can kasan jakarta ta hau dialing
number Umma, Sai da ya kusa katsewa Umma ta daga, bayan sun gaisa ta fashe da kuka
tace "Umma ya farooq ya zo har gida ya zane ni saboda na tafi makaranta wai" Umma
ta bude baki tace "Shi farooq din?" Cikin kuka tace "Ehh Umma" Umma tace "Yi shiru
xan yi maganinsa don ubansa" Nihad na shessheka tace "Toh Umma yace kada in sake
fita makarantar kuma" Umma tace "Ai ba shi ya haifeki ba da xai hanaki xuwa
makaranta, kanki tsaye gobe ma ki shirya kiyi tafiyarki duk inda xa ki ba ma
makaranta kadai ba, ki kyaleni da shi kawai xan yi maganinsa" Nihad tace "Toh" Umma
tace "Kar ki sake asaran hawayenki a banza, kinji abinda nace maki" A hankali Nihad
tace "Na ji" Umma tace "To sai da safe" Daga haka ta katse wayar, mikewa tayi
direct ta tafi dakin farooq, luckily ta samesa xai fita Masallaci, strictly tace
"Farooq daga yau sai yau in har ba baki kake son in maka ba bana son in sake kara
ganin ƙafafuwanka a hanyar gidan Nihad, kuma babu ruwanka da harkarta da abinda
take yi, in dai ba so kake in ce maka je ka ka gani, kai ko a waya na haneka da
kiranta" Da mamaki Farooq ke kallonta, tace "Ni dai na gaya maka, kana kiranta ko
da a waya ne Allah ya isa, balle har ya kai ka taka har gidanta, daga yau bana son
magana ya sake hadaka da ita ko a ina kuwa" Tana gama fadin haka ta juya fuuu ta
fice ya bi ta da kallo, a parlor ta tadda Amina xata fita, tace "Ke kuma ina xa
ki?" Amina tace "Umma kati xan amso" Umma tace "Ban hanaki fesa turare haka ba idan
xa ki fita? Kuma ba nace maki wannan hijabin bana son kina sa shi ba? Meye amfanin
hijabi da xai dinga nuna surarka? Maza koma ki dau wani hijabin"
Amina ta juya tace "Dama kyautar da hijab din xan yi Umma, kawai bana son daukan
gogagge ne shi sa na sa shi yanxu" Umma tace "Maxa ki bayar idan ba haka ba in
kona, bana son sake ganin ɗan iskan hijabin nan a gidan nan" Amina ta juya ta koma
daki, Umma ta wuce ɓangarenta. Karfe tara da wani abu Nihad ta gama shirinta xata
kwanta, har sannan taki daina kukan maganganun da Khalil ya gaya mata, wai er titi,
sannan har da cewa tayinta Abba ya basa, takaici kamar ta hadiye xuciya, can ta
mike ta fita daga dakin nata, a parlor ta gansa xaune yana kallo, tana harararsa
tana huci tace "Ba dole ka sa tv a gaba ba tunda babu a house" Shi dai bai ko
kalleta ba, tace "Kuma da kake cewa Abbana tayina yayi maka, in ka cika ɗan halas
ka sakeni yanxu yanxu mana..." Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta maka masa
wani harara tace "Idan kuma baka da takarda da biro ni ina da su" Bayan few seconds
yace "Ohk ashe dai kinsan da aurena a kanki?" Ta wani kyabe baki tace "Oho dai" Ya
gyada kai yace "Kar ki damu akwai lokaci, kawai mu jira lokacin, ina son sai sanda
kika fahimci ni ba sa'an aurenki bane sannan xan sake ki...." Tace "Aikin banza
kenan, yanxu ya kamata ai, don tun yanxu nasan ni ba class dinka bace, kuma baxan
ta6a xama class dinka ba" Khalil bai sake tanka ta ba, ta juya fuuu ta koma ciki,
wayarta ta dauka a karkashin pillow tayi dialing number Aliyu, amma ta kasa samunsa
sbda ba shi da number, Naf ta kira tace "Naf don Allah ki kira Aliyu kiyi mashi
sending wannan number nawa yayi saving i want to talk to him" Naf tace "Ohk" Daga
haka ta katse wayar, bayan wani lkci Naf ta sake kiran Nihad tace "Nihad na tura
masa number taki yace xai kiraki" Nihad tace "Toh nagode sosai" Nihad na kwance
tayi lamo kan pillow tana ta jiran kiran Aliyu, sai ga kiran nasa, farin ciki ne ya
cikata ta mike xaune da sauri ta daga kiran, a hankali tayi masa sallama, ya amsa
yace "How are you?" cikin sanyin murya tace "Alhmdlh" Yace "Are okay?" Lokaci daya
hawaye ya kawo idonta tace "No" Da damuwa yace "Me kuma ya faru?" Tana girgiza kai
hawaye na sauka idonta tace "Baxan iya jure xama waje daya da wannan drivern din
ba, Har xagina sai da yayi daxu fa" Aliyu yace "Ya zage ki?" Cikin kuka tace "Ehh,
wai ni ya ce ma er titi, er tasha, har da cewa Abbana tayina ya basa" Aliyu yace
"Shi Drivern?" Tace "Ehh" kasa cewa komai Aliyu yayi, can yace "Wait u mean driver
ne ya gaya maki wa ennan maganganun?" Nihad tace "Wallahi" Rai bace yace "Har ya
kira ki da er titi?" Cikin rawan murya tace "Haka yace" Aliyu ya fuzar da iska yace
"Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki, xan dawo Nigeria soon, and everything will
soon come to an end in sha Allah" Tana share idonta tace "Nagode" Yace "Kar ki sake
xubar da hawayenki, sai yayi da ya sanin zagin nan da yayi maki wallahi" Nihad tace
"Sannan nace ya sakeni ya ki" Aliyu yace "He just have to, cause u are not meant
for him...." Ɗan murmushin jin dadi tayi, yace "Are u on WhatsApp?" Tace "Aa xan
bude yanxu" Yace "Idan kin bude, ki kirani" Tace "Ohk" Daga haka ya katse wayar,
sosai hankalinta ya kwanta da abubuwan da Aliyu ya gaya mata, bayan ta bude
WhatsApp din Video call suka yi da Aliyu har kusan karfe dayan dare, tun bayan da
Video dinta ya tafi viral sai ranan tayi bacci cikin dadin rai. Cikin dare taji
kamar ana daga pillow din da ta daura kanta, ta bude ido da sauri, bata ga kowa ba
banda duhu dake dakin, gabanta ya dinga faduwa don da gaske taji kamar ana daga
pillow dinta, ta mike xaune tana bin ko ina da kallo duk da duhun dake dakin,
hannunta ta kai xata yi switching wutan dakin taji ta daura a kan hannun mutum,
wani ihu ta fasa a mugun tsorace xata sauko daga kan gadon taga an kunna wutan
dakin haske ya gauraye ko ina, yana jingine jikin bango kusa da bed side drawer,
tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa a mugun tsorace kuma da mamaki, ya daga
pillownta ya dau wayar dake ƙarƙashi, xaro ido tayi ta taho da sauri tace "Wallahi
kar ka kuskura ka ta6a min...." Wani mugun kallo yake mata yace "Kar ki matso kusa
da ni" Ta fashe da kuka sosai tace "Wallahi ka bani wayata, kaga ba kai ka siya min
ba, ba kuma da sisin ka aka siya ba" Kofa ya nufa ta koma gefe tana kuka tana
kallonsa har ya fice daga dakin, da sauri ta bi sa dakinsa tana cewa "Wallahi ka
bani wayata" Bude kofar bandaki taga yayi tana kallo ya tara ruwa a bucket sannan
ya cilla wayar a ciki ya fito ya sa ma bandakin makulli, saboda shock kasa ce masa
komai tayi ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, bai ko kalleta ba ya kashe wutan
dakin yayi kwanciyarsa saman gado.... Har gari ya waye Nihad bata yi wani bacci ba,
ta ci kuka har ta gode Allah, ta sake tabbatar da cewa bata ta6a tsanar mutum a
duniya irin khalil ba, karfe takwas saura taji kamar ana welding a bakin gate, ta
mike da kyar ta fito parlor ta tafi kofar fita parlorn, tsaye ta gansa a compound,
ga kuma me welder da me canza lock din gate suna ta aiki a bakin gate, juyawa tayi
da sauri hawaye cike idonta ta koma dakinta, ta xauna gefen gado tana shessheka, ta
shi tayi ta tafi dakinsa ta bude kofar bandakin ta duba bucket din da ya jefa
wayarta taga babu wayar a ciki, ta fito ta ga karamar wayarsa a gefen gado, da
sauri ta dauka ta fito ta shige dakinta, Call logs ta shiga taga number anyi Saving
da Nadeeyah with love Emoji, kallon Number ta dinga yi sai kuma tayi scrolling xuwa
kasa taga number Nihal wanda ko jiya ma sun yi waya, shiga tayi taga maganar minti
nawa suka yi taga kusan minti goma, dialing number tayi yana fara ring Nihal ta
daga, Rai bace Nihad tace "Ban san ke munafuka bace kuma algunguma sai yanxu Nihal,
kuma in sha Allahu ke abinda xai sameki sai ya fi wanda ya sameni ki rubuta ki
ajiye, don naga kamar farin ciki kike da condition din da nake ciki, banda kina
farin ciki da abinda ya sameni wayar me xaki dinga yi da enemy din nan nawa? Me
yake gaya maki, me kike gaya masa?" Nihal tace "Haba Nihad, what is this u are
saying? Da kinsan wayar da nakeyi da shi da baki kirani kina gaggaya min wa ennan
maganganun ba, kema kinsan baxan ta6a farin ciki da bakin cikin ki ba..." A fusace
Nihad tace "Babu abinda xa ki gaya min da xai gamshe ni, kuma xan ga ta inda xaki
sake waya da shi" Nihal tace "Toh shikenan, amma ki sani ko na kirasa ke nake cewa
ya ba waya sai baxai baki ba" Nihad tace "Oho wannan ke da shi ya shafa" Nihal tace
"Jibi xa mu yi hutu, and we need to talk idan na dawo Nihad" Nihad bata kuma
sauraronta ba tayi ending call din, Yanxu tasan xamanta da kowa a duniya, Abba ne
oo, Mumy, Ya farooq, Nihal, duk ashe ba sonta suke ba, kuka sosai ta saki, sai kuma
tayi blocking number Nihal a wayar sannan ta bi duk calls din ta goge, Kallon
Number Nadeeyah ta dinga yi ganin how special the line is with multiple 2's, can ta
ja wani tsaki ta danna masa block sannan tayi deleting shi ma gaba daya a call
logs, sai kuma ta tuna cewar she needs to tell Aliyu cewar ya amshe mata waya
incase zai yi ta nemanta, dialing number Aliyu ta fara yi, ko digit hudu bata sa ba
sai taga number ya fito barau barau amma ba tare da suna ba, still tayi tana ta
kallon screen din karamar wayar baki bude da mugun mamaki, to ko dai jiya da ya dau
wayarta ne ya kwashe number??? lkci daya ta juya da sauri jin taku, wani irin
faduwa gabanta yayi ganinsa a bakin kofar dakin yana kallonta, cikin rikicewa ta
ajiye wayar hannunta gefen gadon gabanta na faduwa, shigowa dakin taga zai yi, ta
marairaice ta koma can karshen bangon dakin xuciyarta na bugawa tana kallonsa amma
hakan bai hanata hade rai ba, ya kalli wayarsa sannan ya kalleta, daukar wayar taga
xai yi ta nufi kofa a guje yayi saurin fixgota, kuka ta saki ta rirrike hannunsa
tace "Ni wallahi ka sakeni, me kaga nayi kuma again, ba yar uwata na zo inyi magana
da ba na dade ban ji muryarta ba...."




Nihaad is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via👇🏻


07087865788✍🏻

25

Khalil na ganin number dake saman screen dinsa ya kalleta da sauri, bai san lkcn da
ya saketa ba ya shiga call logs dinsa hurriedly to check if tayi sending kiran,
Nihad tayi using opportunity din saketan da yayi ta fice daga dakin a guje ta shige
nata ta kulle, jingina tayi da kofar tana maida numfashi with surprise written all
over her face, why did Aliyu's number appeared on his phone daga fara dialing, how
will that be? lokaci daya tayi assuring kanta cewa ai jiya ne ya kwashe number a
wayarta bayan ya dauke mata wayar, karasawa tayi ta zauna gefen gado da tunani iri
iri a ranta, does it mean bayan ya jefa wayar cikin ruwan cirowa yayi ya busar
kenan ya shiga call logs dinta ya dau number Aliyun? Dama kuma da Aliyu da Umma sai
su Husnah kadai tayi magana da a sabon wayar, numbobinsu kadai ne a wayar, tsaki ta
ja ta mike ta tafi kusa da window ta tsaya, why will she even be stressing her
self, takaicinta guda yanxu da bata tsoma wayar tasa cikin ruwa ta fito da sauri
ba, yunwan da ya addabeta wajen karfe sha biyu ya sa ta bude kofar dakinta a
hankali ta fito parlor, bata gansa a parlon ba ta saci kallon kofar dakinsa sai
kuma ta shige kitchen da sauri, ta bayan windown kitchen din ta hangosa xaune saman
farin kujera yana waya, kasa kunne tayi amma babu abinda take ji saboda window din
kitchen din dake a kulle, idan kuma tace xata bude xata yi drawing attention dinsa,
juyawa tayi ta fice daga kitchen din ta nufi kofar fita parlor, cikin sanda ta isa
har ta wajen da yake ta tsaya inda baxai hangota ba don backing wajen yayi, kawai
tana son tabbatar da cewa da Nihal yake waya kafin ta san irin rashin mutuncin da
xata mata sannan kuma ta hadata da Umma, ji tayi yayi kasa da murya yana cewa "Amma
Baby me yasa kike tunanin ina Nigeria?? Wani yace maki ya gan ni a Naija ne?" Gwalo
ido Nihad tayi ta bude baki tana kallonsa, murmushi taga yayi yace "Ranan da na
dawo ai bayan wajen Mamina wajen ki xan taho har sai kince min in tafi, kinga ko
abinci ma kadan xan ci na Mami.... Naki ne xan ci in koshi" Nihad dai ta kasa rufe
baki sai kallonsa take da mugun mamaki, cikin cool voice dinsa yace "Nasani
Nadeeyah.... In sha Allah ina dawowa babu bata lokaci kuma kamar yanda na maki
alƙawari xa mu yi aure...." Sai a sannan Nihad tayi wani dariya tana tafe hannu
tace "Yau naga ikon Allah, babba da shirga karya" juyawa yayi da sauri yana
kallonta, ta wani hade rai tace "Katon mutumi da kai baka ji kunyar irin wannan
karyar da ka zauna kake laftawa ba? Wato ba a Nigeria kake ba, na shiga uku ku ji
wai baya Nigeria, to a wani kasar kake? ko da yake ita ce babban mahaukaciyar da ta
tsaya take sauraronka har kake fesa mata wannan mugun karya haka..." Tuni khalil ya
katse wayar ya mike yana mata wani kallo yace "Kar ki sake kiranta da mahaukaciya"
A fusace Nihad tace "Ance mata mahaukaciyar me xaka yi? idan waya xaka yi da ita ka
fita titi kayi mana ai dai naga nan gidan Ubana ne ko? Ko Abbana ce maka yayi ka zo
ka dinga masa waya da mata a gidansa?" Khalil yace "Zaki gane ke ce mahaukaciya ba
ita ba" Cike da tsiwa tace "Sai dai ku ne mahaukata ba ni ba wallahi, kuma kar ka
sake kiran wata banzan mace a gidan Abbana" Bai kuma ce mata komai ba ya gyada kai
kawai ya bar wajen, ta bi sa da wani harara, sai kuma ta ja tsaki tace "Wai baya
Nigeria, kai har kana da kudin fita nan nan Niger ma balle wata kasar?? Ai har ka
mutu ko kamshin airport baxa ka ta6a ji ba don ma kaji in gaya maka" Shi dai tuni
ya bar wajen don Nadeeyah na ta kiransa a waya, Bin bayansa Nihad tayi tace "Dama
idan waya xaka yi ka fita can titi kaje kayi ba dai a gidan Abbana ba na gaya maka"
kafin ma ta shigo parlorn har ya shiga dakinsa ya kulle da makulli, ta ja tsaki
tace "Aikin banza" kitchen ta tafi ta dafa indomie, tana kitchen din taji ana
kwankwasa gate, ta ɗan leka parlor sai gashi ya fito daga dakinsa ya fita compound,
kashe gas din tayi da sauri ta fito daga kitchen din ta shige dakinsa, gun wayarsa
dake saman gado ta nufa, sbda tsoro har wani rawa hannnunta yake ta dau wayar ta
shiga call log don taga da warce yake waya har yake karyan ba a Nigeria yake ba,
Nadeeyah ta gani, mamaki ne ya cika ta don ai tayi blocking number jiya, ai ko yau
sai ta tona masa asiri ba dai baya Nigeria ba, xai ga aiki da cikawa yanxun nan,
dialing number tayi har ya gama ring ba a daga ba, ta sake kira nan ma yana ta
ringing no response... Khalil na isa gate din ya bude, Husnah ce tsaye bakin gate
din tana sanye da Hijab har kasa, ta ɗan yi murmushi tana kallonsa tace "Ina yini?"
Babu yabo babu fallasa yace "Daga ina kuma wa kike nema?" Tana Murmushi still tace
"Ba lallai dama ka nuna ka gane ni ba duk da nasan ka gane ni, dama ba wani abu ya
kawo ni nan ba illa in baka hakuri akan abinda muka maka shekaranjiya ni da
kawayena, tun ranan wallahi ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login