Showing 195001 words to 198000 words out of 268471 words

Chapter 66 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

kulle gate din na taho, ga su can suna ta buga
gate din" Ai ko rufe baki bai yi ba Farooq ya nufi kofa da sauri, a tsorace Inna ta
mike tace "Ina za ka farooq??" Umma ma ta daka masa tsawa amma tuni ya fice daga
parlon, da gudu Inna ta bi sa tana kiransa a gigice, yana tafiya ya fiddo wayarsa
dake ring a aljihu yaga Khalil ne ke kiransa, dagawa yayi khalil ya sanar masa suna
waje, Farooq ya karasa bakin gate din ya bude, Khalil ne tsaye bakin gate din sai
sojojin dake kewaye wajen ko wanne da bindiga a hannu, sai a sannan Janar ya sauko
motar tare da abokinsa, Inna ta gwale ido uwa munafuka ganin Khalil ga sojoji sun
zagayesa, sai kuma ta fashe da kuka ta saki salati tace "Dama sai da na fada, sai
da nace ɗan kinnafa ne su Ibrahim suka gwaleni suka maida ni wawa....." Sai kuma ta
kalli Janar da sojojin dake wajen suna kallonta tace "wallahi ranka shi dade bamu
taɓa saninsa ba, ce maku yayi ya san mu? Ɗan Nijar ne fa" Sai kuma ta juya da gudu
taje ta gaya ma Abba ya buya, gaba daya ta rikice ta gigice, Farooq sai kallon
Janar yake wondering if Lieutenant General Abubakar I Jikamshin da ya sani ne
wannan yake gani a gabansa or just kamanni ne, shi dai Janar was patiently
standing, su Mami kuma basu kai ga sauka daga motar ba, Khalil yayi kasa da murya
yana kallon Farooq bayan ya shiga compound din da sauri yace "He is my Father"
Muryan sojan dake tare da Janar suka ji yace "Is this how u treat ur guess?" Yana
kallon Farooq yayi maganar babu yaɓo babu fallasa, Da sauri Farooq ya gaishesu a
daburce yana welcoming dinsu ya bude gate din sosai ya basu hanya, nan su Mami da
Aunty Maryam suka sauko daga motar, Khalil dai kansa na kasa, walking fast ya fara
leading din Janar da abokin nasa zuwa entrance din main parlor ganin kamar Farooq
ya rikice and at anytime Janar zai iya exploding ya masu kwarkwar gaba dayansu a
wajen barin yanda aka barshi a tsaye, Nihad taji kamar taje ta rungume yayan nata,
she is so happy seeing him, A balcony Khalil ya hadu da Abban Nihad, a bit confuse
Abba ya dinga kallon Janar dake tahowa like the soldier he is, Abba ya kalli Khalil
sae kuma ya sake kallon Janar with his friend, kamar Janar Jikamshi yake gani a
gabansa, ko idonsa ne ke masa gizo, lokaci daya sojojin da suka biyo bayan Janar da
abokinsa suka nemi each and every angle of the compound suka tsaya, hakan dai bai
sa Abba ya fasa ba Janar hannu ba yana masa sannu da zuwa, sannan ya ba daya sojan
ma hannu kafin yayi leading dinsu har cikin Main parlor, Saminu da Isiya sai
wuwwurga idanuwa suke daga Chalet suna jiran suga an fara kwashe kowa na gidan har
su, har sannan kuma Aminu na makale a inda ya durkusa a parlon tun dazu, Hajiya
Inna kuma na can kuryan dakin Mumy bata ma san sanda ta isa nan ba tsabar gigicewa
sai salallami take tana cewa ya cucemu ya cucemu, dama sai da nace masu ban yarda
da shi ba hankalina bai kwanta da shi ba aka maida ni wawa.... Khalil ya daga kai
ya kalli Umma da ta koma bayan kujera ita ma sai zare ido take a tsorace, Mumy na
tsaye kofar kitchen da Aunty Jamila, ko wanne zaka ga Fargaba karara kwance a
fuskarsa, sunkuyar da kansa yayi kawai, Bayan Janar da abokinsa sun zauna ya nuna
ma Abba ganin bai zauna ba yace "Bismillah Alhaji" Abba ya kirkiri murmushi ya
zauna yace "Barkan ku da zuwa, amma sai dai ban san me ke tafe da ku ba, ina kuma
fatan Allah ya sa
lafiya" Nihad ce ta shigo parlon su Aunty Maryam na biye da ita, duk suka zauna a
parlon, Mumy da Aunty Jamila suka dinga bin su da kallo, lokaci daya gaban Mumy ya
fadi, what's happening??? Umma dai kamar idanuwanta za su fito tsabar yanda take
gwalesu tana bin sabbin occupant din parlon da kallo, Farooq ne kawai ke ta masu
sannu da zuwa a parlon da fara'arsa, ya tafi ya dinga jido pack din ruwa da lemo,
Nihad ta kasa ci gaba da zama kawai ta tafi da sauri ta rungume Mumy cike da farin
cikin ganinta duk da basu wani dade da ganin juna ba, but she is having a new
strong love for her mum now, Mumy ta hadiye wani abu da kyar, murya can kasa kasa
tace "Su waye wa ennan Nihad? Why are they here??" Yanda zaka san kowa a tsorace
yake ko gaida su Mami da Aunty Maryam babu wanda yayi a parlon ana dai jiran aji
abinda ke tafe da su, most especially Abba da hankalinsa ya tashi sosai, kawai dai
bai nuna bane a fuska, Muryar Janar dake kallon Abba suka ji yace "Babu wani abu
dake tafe da mu sae alkhairi Alhaji, kuma muna me ba kai da iyalanka hakurin yanda
muka shigo maku gida kai tsaye, may be without any notice.... and most important of
all, i hope kai ne Alhaji Ibrahim??" Abba ya gyada kai yace "Kwarai ni ne" Janar
yace "Sunana Abubakar Ibrahim Jikamshi...." A hankali Abba yace "Lieutenant...
General.... Abubakar Jikamshi" Janar yace "Haka ne" Umma ta dafa kujeran kusa da
ita tana sake kallon Janar da kyau kamar idanuwanta za su fito, kwarai kuwa sai
yanzu ta ganesa, Ita kanta Mumy da Aunty Jamila kallonsa suke babu ko kiftawa with
shock, Janar ya nuna ma Abba Khalil yace "Few abinda ka sani game da wancan mutumin
nake son kayi briefing dina Alhaji..." Sosai gaban Abba ya fadi, ya daga kai yana
kallon Khalil da ya sunkuyar da kansa kamar mara gaskiya, lokaci daya har hawaye ya
kawo idon Mumy..mm Kasa cewa komai Abba yayi, Janar yace "Muna sauraronka Alhaji" a
hankali Abba yace "Toh, ya dai zo gidan nan yau shekara daya da yan watanni, ya
nemi aikin driving na kuma basa, yana kai min yarana makaranta, sannan duk wani
aike na cikin gida ana aikensa" Cike da karfin hali Abba ke maganan, only Farooq is
looking so calm a parlon, Janar ya gyada kai cikin gamsuwa yace "Shikenan?" Abba ya
girgiza kai yace "Na kuma basa auren 'ya ta, bayan da naga shi me gaskiya da rikon
amana ne, sannan na yaɓa da hankalinsa da nutsuwarsa...." Janar ya dinga gyada kai,
Shi dai Abba kallonsa kawai yake, Janar yace "Amma kai ta yaya kasan yana da
gaskiya da rikon amana?" Abba yace "Ehh to, na sha gwadasa ta fanni daban daban
akan abubuwa da yawa da suka shafi kudi, and i never find him guilty of any, a
yanda ma yayi min maintaining motar da na basa ban taɓa driver da yayi min haka
ba...." Janar yace "Nawa ne Albashin da kake basa?" Abba yace "Na kan basa dubu
hamsin ko dubu sittin duk wata...." Janar yayi shiru sai kuma yace "Amma kai baka
bukaci sanin iyayensa ba kafin ka basa auren yar ka?" Abba yace "Har wajen iyayen
nasa naje a kauyen getso, kuma da yardansu na aura masa 'ya ta ba kai tsaye aka yi
hakan ba ranka shi dade" A tare Janar da su Mami suka daga kai suna kallon Khalil
with surprise, shi ko ya ki dago kansa, Janar dai ya kasa daina kallon sa, wato har
feigning iyaye yayi a kauye, Janar ya kalli remote dake gefen kujeran da yake
zaune, dauka yayi lokaci daya ya harbi Khalil da shi, duk yanda Khalil ya so
dodging remote din sai da ya taɓa sa, ni ko nace ya mance ba Major bane ya harbesa
da yake kokarin dodging, Nihad ta rufe bakinta da sauri don wani dariya ne ya kusa
taho mata, Khalil ya sosa kansa with a smile on his face, wai fa duk wannan abun da
ake Inna na makale jikin kofa ta kasa fitowa, banda hawaye babu abinda take, ta
tsine ma Khalil yafi sau hamsin, su Saminu da Isiya na tsaye bakin window ta waje
suna jiyo komai, Aminu dai har ya gaji da gwale ido kamar wanda yayi ma sarki
karya, Janar na kallon Abba bayan shirun few seconds da yayi yace "To ɗa na ne
Ibrahim, ni na haifesa.... Ba komai kuma ya sa na xo nan ba sae don in tabbatar da
gaskiyan lamarin auren nasa, ina kuma farin cikin hada zuri'a da kai Alhaji
Ibrahim, na kuma ji dadin yanda ka yarda da shi har ka basa auren er ka, and I will
forever be grateful for that" Ba Abba ba kowa na parlon sae da yayi stiff a inda
yake for some seconds, da wani expression Abba yace "Ɗan ka kuma??" Janar yace "Ɗa
na ne, and he is my only son" Aunty Hassana da ke ta girgiza kafa a parlon ta kalli
Janar da sauri jin da tayi yace his only son, Abba ya daga kai yana kallon Khalil
babu ko kiftawa, Aunty Jamila tayi saurin riko Mumy wanda ta ji wani jiri tayi baya
kamar zata fadi, Aunty Maryam dai sai kallom Mumy take cike da tausayinta don taga
kamanninsu da Nihad, Khalil bai iya ya dago kansa ba ya karaso har cikin parlon ya
durkusa gaban Abba cikin sanyin murya yace "I am sorry i wasn't truthful to you
sir, i had no choice but to hide my identity.... Ina kuma neman yafiyarka, i never
took u for a fool, bani da option ne...." Inna da ta kusa minti daya baki a bude ta
fito parlon da sauri bayan ta goge hawayenta tana kallon Janar tace "Wai ɗan da ka
haifa a cikin ka ko kuma yaron aikin gidanka kake nufi?" Janar na kallonta yayi
murmushi ya nuna mata Mami yace "Ga Mahaifiyarsa can, ita ce uwargida na" Mumy da
Aunty Jamila suka daga kai da sauri suka kalli Mami, hawaye masu zafi ne suka hau
sauka idanuwan Mumy ta jingina jikin kanwarta saboda yanda taji tsayuwar na neman
gagararta, ganin abubuwan take kamar a mafarki, Umma ta dinga bin kowa na parlon da
kallo babu ko kiftawa tana ta wani irin murmushi kamar warce tayi recovering daga
hauka, Inna ta rike kai tace "Habaa waaa, to kalleni nan" Janar dai sai kallonta
yake, ta nuna masa Abba tace "Ni na haifi Ibrahim, kuma tsakanina da Allah tun da
yaron nan Halilu ya xo gidan nan na gaya masu ba banza yake ba, wallahi tun ranan
da na fara ganinsa hankalina ya kwanta na amince da shi, yaushe ake samun mutum da
nutsuwa da ladabi da sanin ya kamata haka a zamanin nan, uwa uba ga kyauta, wallahi
apple ya siyo min ranan ya fi na dubu biyar daga cewa yaje yaji nawa nawa ake
siyarwa, Allah ne ya kaddara zaman sa a gidan nan amma ni ce sanadi, kuma ni na
bada goyon baya aka aura masa jikata ka tambayi kowa, amma dai kai ko wani lalacewa
ya sameka kamar me bakin uwa kana babban soja a kasa zaka bar ɗan ka a gantale?
Yanzu da bai shigo hannunmu ba fa? Ayi magana ta tsakani da Allah fa" Juyawa duk
suka yi da sauri jin an fadi timm a kasa, Mumy da Aunty Jamila da Farooq suka
karasa gun Umma da sauri, Abba ya mike, Mami ta nufi wajen tace "Subhanallah, is
she okay" Aunty Maryam dai ko motsawa bata yi ba don tuntuni take lura da yanayin
da Umma ta shiga a parlon, kuma a kan idonta ta tafi luuu sannan ta fadi timm, tuni
jini ya fara bulbulowa daga goshin Umma tsabar yanda ta buge da tiles, Farooq da
Khalil suka yi waje da ita bayan Janar yayi instructing sojan dake bakin kofa a
tafi da ita hospital with the convoy....



Waje aka yi da Umma za a saka ta a mota zuwa asibiti don jini ba na wasa bane ke
zuba a goshinta kamar an bude pampo, Inna tayi gate da gudu tana ce ma sojojin dake
bakin gate din su bude su bude, Kasake inna tayi ta bude baki ganin layin ba
matsaka tsinke da jama'a, ke kya ce rabon daloli ake, Inna ta toshe hancinta da
sauri don tear gas kawai sojojin ke sakar masu ba kakkautawa amma sun ki gudu, ashe
duk yan Khaleesat palace ne da suko taho ayi komai a gabansu, shine sojoji suka
hanasu shigowa gidan Abba, can na hango Mrs Bello ta ci damara, Mom twins da Aunty
Zahrah rike da katon Banner an rubuta masu gudu su gudu, Daga daya bangaren kuma
Chamo na hango tayi bake bake a gaba tana tura masu son mata overtaking ga Fu'ad
goye a bayanta duk ta hada zufa, Deejah me lamurje kuwa sai bi take tana rabon
lamurje a gora, ashe abinda yasa basa jin zafin tear gas din kenan, A kusa da Chamo
na hango Aunty Inna sanye da hulan lauyoyi tana cewa sai tayi sue din sojojin idan
basu bari sun shiga gidan ba, they have no right, turanci dai har da wanda ban taba
ji ba a bakin inna in gaya maku, Sai kuma na hango Mardiyya rike da microphone
cikin daga murya take cewa ita ewr jarida ce, ita fa ewr jarida ce, don haka tana
da right din shiga ta dau wrahotu, they have no wright to stop her, Safiyya Usuman
da Aunty Amzaj kuwa babu abinda suka mance basu gaya ma sojojin ba na cin mutunci
ga hawayen tear gas sai zuba yake a idonsu, Damsel, Aisha Bela, da Aneesah da Mom
Asas, kuwa na rike da speaker da ya cika anguwar da wakar rarara ta masu gudu su
gudu, daga can bayan yan Khaleesat palace na hango yan Nihad conversation su ma
suna ta nasu taɓarar su, a bayansu kuma ashe yan bati ne ko wacce da banner dinta a
hannu, duk suka tare layi babu ta inda za a fitar da Umma dake ta zuban jini xuwa
asibiti, ji kake tas tas tas tas tas a sama, kamar kiftawar ido layin ya dawo ba
kowa sai gorunan Lamurje, warin takalmin jama'a da zanin goyon chamo a kasa, sai
hular lauyoyin inna, sai banners din yan bati, sai a sannan aka samu aka yi asibiti
da Umma....
🥸🥸



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788


59

Ana fita da Umma zuwa asibiti Inna ta dawo parlor, tana kallon Aminu dake zaune
jikin kujera sai cilla ido yake, cike da mamaki tace "Kai baka da hankali ne kake
zaune tsamo tsamo cikin manyan mutane kana kallon bakinsu, tarbiyarka kenan? aa to
baka da tsoron Allah" Aminu ya mike da sauri ya fita daga parlon, Inna ta bi sa da
wani kallo, can ta karasa gun Janar tace "Mu ma kawai ba mu suman bane saboda
taurin zuciya amma gaskiya mun girgiza da wannan lamari, kishiyar uwarta ce fa amma
tafi uwar sonta, ita ta raineta tun tana karama har kawo girmanta, yanda take sonta
ma ko ya yan da ta haifa a cikinta bata so, kaga kuwa dole ta girgiza saboda farin
ciki har ta suma" Janar yace "Ikon Allah... To Allah ya bata lafiya" Nihad dake ta
kallon Inna ta mike ta bar parlon, Inna tace "Ameen ameen, to alfarma ta farko da
nake nema a wajenka a matsayinka na ɗa na shine a hadani da sojoji ko da basu kai
ashirin ba, wani tantiri aka aura ma jikata sai kaga yanda ya bi ya canza mata
halitta da duka, don da a hanya na ganta bazan fahimci jikata bace...." Abba dai ya
kasa dago kansa saboda takaici, a ransa kuwa yaji dama bata zo gidan ba baƙin suka
zo, ita kanta Mumy kanta a kasa yake, Aunty Hassana ta dinga ma Inna wani kallon
rainin wayo, can tace "Toh Hajiya banda abunki mu ga abinda ya kawo mu daban sai
kuma ki shigo da wani al'amari...." Inna ta juya tana kallonta da sauri tace "Amma
dai daga jin wannan zancen naki ba lallai kina da alaka da Janar ba, to ke kuma a
wa? Ina ce yace mana ga matarsa can wato uwar Halilu wancan kuma dake zaune kusa da
ita ko makaho ya shafa yasan kanwar matarsa ce, to wacece ke kuma?" Janar yace "Shi
mijin a ina yake Baaba?" Inna ta juyo tace "Ina dai zuwa" Daga haka ta tafi dakin
Umma don can Kamila ta makale duk budurin nan da ake saboda yanda fuskarta ya
kumbura suntum, ga bakinta da ya dawo kamar na rakumi, kana ganinta kasan tana jin
jiki, Inna tace "Daure ki tashi mu je parlor, ga sojoji nan Allah ya kawo mana daga
sama ba ko sisinmu, mu je su ganki don a san irin dukan da xa a ma matsiyacin,
Kamila ta wani kalli Inna tace "Baxan je ko ina ba" Inna tace "Amma dai ke
walakantacciya ce, ga dai za a bi maki hakinki kina neman gantalar da ni, tun dazu
nake ta wahala a kanki" Kamila ta kwanta ta juya mata baya, Inna ta dinga kallonta
can ta fita, kafin Inna ta dawo parlon Abba yayi saurin ce ma Janar ai mijin baya
nan amma ya riga ya gama magana da yan uwansa ba wani abun tashin hankali bane,
they will sort everything out, tana fitowa Janar yace "Shikenan Baaba, mun gama
magana za aje a samesa in sha Allah" Inna tace "Toh Allah yayi maka albarka, Allah
ya sa ka gama da duniya lafiya, mu kuma Allah ya bamu ladan rikon da muka ma ɗan
ka, rikon amana babu ha'inci, cin sa, shan sa, suturarsa, wajen kwanansa, duk bamu
gaza ba, kai har mota sai da muka basa yana zuwa duk inda ya ga dama kansa tsaye,
ni kuma duk sai na gwammaci Halilu a kan jikokina maza don ya fi jin kai na a
kansu, yanzu sai aje a ajiyeni gidan babban ɗa na in taho da shi har nan ya
gaisheka shi ma cikin girmamawa" Janar yace "Eh toh yanzu dai ana jirana Baaba,
kafin dai in koma Abuja za mu hadu da shi in sha Allah" Wani hararan tsana Hassana
ta dinga yi ma Inna, duk ta kagu taga sun fice daga gidan taje ta san ta inda zata
fara don wannan duk bata mata lokaci kawai ake, su Mami da Aunty Maryam dai sai
kallon Innar suke su ma kamar sun ga alien, Mumy kuwa kunya kamar ta nutse a wajen,
inna ba kamun kai, Masallaci Janar suka fita tare da Abba da abokinsa saboda
lokacin azahar yayi.... Mumy na kallon su Aunty Maryam tace "Mu je ciki ku yi
sallah Hajiya" Aunty Maryam ce ta fara tashi ta bi bayan Mumy, Inna ta lallaba ta
bi bayan Aunty Maryam bayan sun shiga parlon tace "Amma ita wancan figaggiyar da ku
ka zo da wacece ita? Naga babu ta inda take kama da ku ko Janar din, amma kuma take
son kawo min raini" Aunty Maryam na murmushi tace "Kanwarsa ce kaka" Inna ta gwale
ido tace "Kanwarsa kuma? To na ganta baka shi kuma fari, babu kuma kamanni in za a
fadi saboda Allah" Aunty Maryam tace "Uwarsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login