Showing 225001 words to 228000 words out of 268471 words

Chapter 76 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

daya Alhajin ya maki ai ko?" Hawaye na
sauka idon Umma tace "Ehh" Hajiya Turai tace "Toh babban abinda za a fara aiki a
kai yanzu shine duk yanda za abi Alhaji ya maida ki dakinki, bayan ya maida ki sai
a koma kan Nihad...." Da sauri Umma tace "Wacece Nihad, ga matsaloli kaca kaca a
gabana kina kira min Nihad Turai, bayan dai an maida ni ayi kokarin duk yanda za
ayi Kamila ma ta koma dakinta wallahi sai kinga rashin darajar da take min a gidan
nan yanzu, bata ma damu da halin da nake ciki ba, dazu da safe ke kyace dukana zata
yi daga nace tayi kokari ta rage baccinta ta dinga tashi tsakar dare tana gaya ma
Allah matsalolinta, Turai bata da aiki yanzu sai waya da manyan mata wanda ko ni
sun fi karfina, kusan kullum sai ta fita ta dawo da kayan ciye ciye tace Hajiya
wancan ce ta bata ko tace Hajiya wancan ce ta bata, har iphone ta dawo da shi gidan
nan wai macece er uwarta ta bata, idan ta fita tun safe sai dare take dawowa fa
wllh, ke dai kinsan irin tarbiyan da na basu Turai ko nan da gate idan ba
kwakkwaran dalili ba bana barin su fita, duk wani sa ido da uwa zata ma 'ya yanta
na masu bakin gwargwado Allah kuma ya gani, to wani hali ne wannan kuma Kamila ta
tsiro da? Wannan ai ba tarbiyata bane, tsorona ma kada taje su sakata harkan
lesbian, da farko ne mutuwar auren ke damunta har ta rame ta fita hayyacinta amma
yanzu kam manyan mata kawai take bi Turai, shine hankalina ya kara tashi wllh,
sannan sai a koma kan Nihal ita ma ayi duk kokarin da za ayi ɗan ministan nan ya
dawo ace yau ita ma tayi aure tana dakinta Turai, sannan Usman shi ma Allah ya
taimakesa ya samu wani aikin ko da ba na Abujan ba, wallahi yana cikin damuwa shi
yasa ma ya fita Nijar ba dangin uwa ba na uba a can, kinsan yanda samun aiki yake a
kasar nan idan ba kasan wanda ya san wani ba, Amina ma ayi addu'a Allah ya fiddo
mata da miji wllh babu me zuwa wajenta abun har tsoro yake bani, hatta Hafsat din
nan me aiki ana zuwa zance wajenta amma banda Aminata, abu na karshe wannan
yarinyar Husnah a yi duk me ma za ayi kada Allah ya kara kado ta gidan nan don
girman Allah, wllh wannan su ne babban matsalolin dake gabana a yanzu dai Turai, da
su nake kwana nake tashi" Hajiya Turai tace "Duk kar ki ji komai zan aiko a amshi
zoben, idan ma da ciko ni zan maki wallahi don kin fice haka a wajena Sumayya,
banda rashi ai da ba sai nace ki bada zobe ba ni me maki ne ko da miliyan zan
kashe, to bani da shi bani da dalilinsa Sumayya" Umma tace "Allah ya rufa asiri ni
dai ki min kokari Turai, bani da me min wannan abun banda ke" Nan suka yi sallama
Umma ta ajiye wayar ta jingina da gado abun duniya ya taru ya mata yawa, duk ta
rame tayi baƙi babu kyan gani. Kwankwasa kofar dakinta aka yi tace "Wanene?" Amina
tace "Ni ce" Umma tace "Ya aka yi? Ba nace kada wanda ya shigo min nan ba ina
bukatar hutu" Amina tace "Nihal ce zazzaɓin ya sake dawo mata Umma" Umma ta sauka
daga kan gadon da sauri ta tafi ta bude kofar tace "Tana ina?" Amina tace "Can
dakinta" Umma tace "Tun yaushe zazzaɓin ya dawo?" Amina tace "Abinci ta ci, sai
tace cikinta na ciwo sosai daga nan kuma sai amai" Umma tace "Wannan yarinya wannan
yarinya da shegen taurin kai take, nace mu je asibiti taki to ya zan mata, tana ta
zazzaɓi a tsattsaye yaki ci yaki cinyewa me maganin Chemist zai mata fisabilillahi"
Suna isa dakin Nihal suka tadda Mumy zaune gefen gadon tana mata sannu, Umma tace
"Me yasa kin fiye taurin kai ne Nihal, nace aje asibiti su maki treatment me kyau
kin ki, to ya kike son inyi dake?" Mumy tace "Nima yanzu maganan da nake mata
kenan, nace ta shirya mu je asibiti wai sai ta huta" Ko kallonta Umma bata yi ba
don tun bayan da Abba ya saketa ta daina kula Mumy a gidan, ko taje dubata a can
ɓangarenta duk sannun da zata mata ba um ba um um sai dai tayi ta sauke ajiyar
zuciya, Umma tace "Tashi sa Hijabinki mu tafi asibiti" Nihal ta daga kai ta kalleta
da kyar tace "Toh a bari anjima mana Umma" Umma tace "Anjiman ubanki, kin tashi kin
shirya ko kuwa, dubi yanda kika lalace kamar warce ta shekara tana zazzabi" Mumy
dai bata sake ce masu komai ba, Nihal ta mike zaune cike da karfin hali tace "Don
Allah ki bari Anjima Umma wllh bacci nake ji kuma yanzu" Umma tace "Toh tashi ki
koma bangarena ki kwanta" Nihal ta tashi tsaye ta fita daga dakin, Umma da Amina
suka bi bayanta, ta koma dakin Nihad dake bangaren Umma ta kwanta, Umma na kallonta
tace "In kin tashi daga Baccin sai Amina ta raka ki asibitin, ko dai kin ji za a
sakar maku result ne a makaranta, tunda ke haka kike da kinji za a saki result kin
fara zazzabi ba ji ba gani" Nihal ta gyada mata kai da sauri tace "Ehh" Umma tace
"Ko da naji, to Allah ya sa a ga alkhairi" Daga haka ta juya ta koma dakinta. Karfe
biyu da rabi na ranan Nihal ta shigo dakin Umma, Umma na zaune kan darduma rike da
carbi, tun da ta idar da sallahn azahar wajen karfe daya da wani abu take zaune
saman darduman take ta jan carbi, da taji hawaye ya zubo idonta sai tayi sauri ta
goge, Nihal ta zauna gefen gadonta, Umma na kallonta ganin yanda ta rame tace "Anya
baza kije asibiti a maki thorough Checkup ba Nihal? Kin ga yanda kika koma kuwa?" A
hankali Nihal tace "Toh ba final exams bane da muka yi Umma" Umma tace "Toh naga
ramar tayi yawa ne, and u look pale" Nihal tace "Umma zan je gidan Coursemate dita
dake rijiyar zaki, ita zata duba mana result din ni bazan iya ba" Umma tace "Har an
saki?" Nihal ta gyada kai a hankali tace "Eh" Umma tace "Toh Allah ya baku sa'a, ya
baku nasara ya rabaku da spill over" Nihal tace "Ameen" Umma ta jawo jakarta ta
ciro dubu daya daga cikin dubu sha biyar din da Farooq ya bata kafin ya koma aiki,
tace "Ki rike wannan a hannu, ai driver ne zai kai ki ko?" Nihal ta gyada mata kai
ta amshi kudin sannan ta mata godiya ta mike ta fita daga dakinta sai da ta fara
zuwa bangaren Mumy ta sanar mata zata fita sannan ta bar gidan, Raliya Coursemate
dinta ce kuma zata girmeta da kusan 4 years amma ko sau daya bata taɓa zuwa gidansu
ba sai dai Raliyan ta zo wajenta, duk da dai sai a level 4 ne ma suka saba da ita
har ta zo gidansu, bata da wata kawa da take zuwa wajenta a kaf garin kano, yawanci
ko yan islamiyyarsu sai dai su zo gida wajenta amma ita kam bata xuwa, Suna isa
kofar gidansu Raliya ta kirata a waya tace "Ina kofar gida" Raliya tace "Anya kin
gane address din da na tura maki kuwa Nihal?" Nihal tace "Toh ai driver ne ya kawo
ni" Raliya tace "Toh gani nan fitowa, Allah ya sa ba wani wajen daban ku ka je ba"
Sai ga Raliya ta bude gate din gidansu, Nihal ta sauka daga motar tana kallon
drivern tace "Kawai ka tafi idan na gama zan kiraka baba" yace "Toh Hajiya" Daga
haka ya ja motar ya bar layin, Raliya ta rungume Nihal cike da farin cikin ganinta
tace "Ya naga sai kara ramewa ma kika yi maimakon ki ciko da kika koma gida" Nihal
ta mata murmushi kawai, Raliya ta kama hannunta suka shiga cikin gidan nasu, babban
gida ne sosai, sai da Raliya ta fara kai ta ta gaida Mum dinta da Stepmom sannan ta
tafi dakinta da ita, Nihal ta zauna gefen gadonta, Raliya tace "Kinji result nan da
sati biyu za a saki?" A hankali Nihal tace "Allah ya kai mu" Mai aikinsu Raliya ta
kawo mata ruwa da small chops, Raliya tace "Naji dadin ganinki wallahi, dama baki
taɓa zuwa gidanmu ba sai dai ni in je naku, to yau dai ga ki a gidanmu and i really
appreciate it" Nihal tayi murmushi amma bata ce komai ba, Raliya tace "Na gan ki
wani iri, ko baki da lafiya ne dai Nihal?" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Nihal,
Raliya ta koma gefenta ta zauna da mamaki tace "What's wrong dear?" Bayan few
seconds Nihal tayi karfin halin cewa "Ni bani da kawa, and i have no one to confide
with, kawai naji na yarda dake Raliya, For two months now.... ban ga period dina ba
Raliya" Raliya was shocked ta koma baya ta dinga kallon Nihal tsoro fal idonta, a
kaf department dinsu babu mutum da kana ganinsa zaka masa kallon holy somebody
kamar Nihal, ita ko magana da maza ma bata yi sai taga dama, sannan bata shigar
banza ko da bazata sa hijab ba bazaka taɓa ganinta da karamin gyale ba sai dai
babba da zai rufe jikinta, sannan she is one of the loveliest soul da ta taba
haduwa da warce bata san walakanci ba, abunta bai rufe mata ido ba sannan ga ta da
tausayi, Raliya ta sauka daga kan gadon tana kallon Nihal still shocked tace "Ban
gane ba Nihal? What are you trying to say now?" Kuka sosai Nihal take kamar ranta
zai fita tace "Kin dai
san halina duk da bamu wani dade tare ba Raliya, even male frnds i don't keep,
wallahi wallahi wallahi ni ban taɓa zina ba...." Sai kuma ta kasa ci gaba ta hade
kai da gadon Raliya tana kuka sosai, cikin rawar murya tace "I wish Allah zai dau
rayuwata yanzu, Allah ne shaidata ni ban taɓa zina ba, i was betrayed Raliya,
yaudarata aka yi...." Raliya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma don
baki ga period ba ai u don't have to conclude u are pregnant wani lokacin period na
haka, ko nima last 3 months sai da nayi kusan wata biyu banyi period ba daga baya
sai gashi ya zo, do not conclude Nihal" Nihal ta girgiza kai tace "Ni ban taɓa yin
haka ba" Raliya ta ma rasa abinda zata ce mata don gaba daya kanta ya kulle, can
tace "Abinda zai faru, ki tashi yanzu mu je mu siyo Pt test strip a chemist kiyi
amfani da shi don mu tabbatar" Nihal ta goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan
murya tace "Toh" Raliya ta dau hijab dinta bayan ta je ta gaya ma Mum dinta za su
je siyo abu su dawo ta fita tare da Nihal, ba a chemist din unguwansu ta siya ba
sanin halin jama'a, sai da suka bar anguwan kwata kwata sannan suka samu wani
chemist suka siya, Raliya ta tare masu ɗan adaidaita ya maida su gida, ba Nihal me
test din ba, ita kanta Raliya gabanta faduwa yake sosai, ta dinga addu'a a
zuciyarta Allah ya sa negative za su gani, ai ko Nihal na gama dubawa suka ga
positive, Raliya was so shock ta zauna gefen gadonta ta kasa cewa komai, kuma bata
hana Nihal kukan da take ba kamar zata shide, Raliya ta dinga tunanin wani taimakon
zata iya ba Nihal wanda asirinta bazai tonu ba, gashi dai ita kanta ba wai idonta a
bude yake ba, tana dai cin life amma gaskiya bata shashanci, wata kawarta warce
tasan duniya, duniya ya santa ce ta fado mata, ta kalli Nihal cikin sanyin murya
tace "I have this friend Zaliha nasan zata hada mu da Dr da zai cire cikin...." Ko
rufe baki Raliya bata yi ba, Nihal ta dago da sauri ta girgiza kai hawaye na sauka
idonta cikin rawar murya tace "Bazan cire ba, laifi biyu a lokaci daya Raliya?"
Raliya tace "But kin ce yaudaranki aka yi Nihal, koma laifin ne astagfirullah sai
dai daya na cire ciki amma ba na zina ba since yaudaranki aka yi" Kuka Nihal sosai
take kamar ranta zai fita tace "Baxan cire ba, i can't" Raliya ta zaro ido da
mamaki tace "How did u want to face ur parents with this Nihal?? So kike ki sa masu
heart attack? Ya kike son mahaifiyarki tayi? Ta yaya zaki fuskanci mahaifinki idan
aka gano wannan cikin? Ohh no think about this plss" Kuka kawai Nihal take ta ma
rasa abinda zata ce ma Raliya amma ita dai tasan bazata taɓa cire cikin nan ba
Allah yayi fushi da ita, cire cikin will be the last thing she will do on earth,
Raliya tayi tagumi duk ranta babu dadi, this is so sad, bayan few seconds tace
"Since ni dai baza ki dauki shawarata ba, don't you have any other person that u
can confide in, ko namiji ko na mace wanda u are close with kiji shawaran da zata
baki ko zai baki??" Nihal tayi shiru tana goge idonta tana nazarin who will that
person be.....


*Manage this pls, bana jin dadi ina mura*


Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788

68

Tun daga nesa Khalil ke kallonta har ta karaso ta ajiye masa tray din hannunta me
dauke da drink da glass cup sannan ta zauna tana danna wayarta, bayan few seconds
yace "Nadeeyah" Ta daga ido ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Do u have anything
in mind that u are hiding away from me?" Tace "Iike?" Yace "You act strange this
days, i don't understand u anymore" Tace "Really?" Yayi shiru yana kallonta, ta
karyar da kai tace "I am not acting strange, kawai dai ina baku enough space da ku
ke bukata ne da kai da matarka" a hankali yace "But ai kema matata ce to be...."
dariya kawai tayi bata ce masa komai ba, sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, yace
"Nadeeyah" Ta daga kai ta kallesa, yace "Seriously bana jin dadin abinda kike min,
you are making me feel kamar i am wronging u without me knowing" Ita dai kallonsa
kawai take, can tayi murmushi tace "Ohk sai yanzu ka gane hakan?" Yayi kasa da
murya yace "But how? Ta yaya nake wronging din ki?" Lokaci daya hawaye ya kawo
idonta bata dai ce masa komai ba, yace "Don Allah kiyi min magana" Ta daga kai ta
kallesa hawaye na sauka idonta tace "You should have told me to move on Kjay, da
baka ci gaba da ɓata min lokaci ba kana ce min in jira ka, you wasted my time for 4
years, i neva double dated because of u, da kayi aurenka da tun sannan ka gaya min
in ci gaba da rayuwata...." Ya dakatar da ita yace "Haba Nadeeyah, why are u saying
all this pls, how many times do i have to explain things to you, wallahi wallahi
ban je gidansu da niyyar aurenta ba, hasalima ni bn santa in person ba naje
gidansu, hadin mahaifinta ne aurenmu and i can't say no to him, kawai Allah ya
kaddara aurena da ita ne, i neva bargained for it" Cikin kuka tace "Yanzu ai da son
ranka kake zaune da ita, kuma kana sonta fiye da yanda kai kanka kake tunani yanzu,
saboda son nata da gudun bacin ranta yasa kayi kamar baka gan ni ba a airport ai"
Ya buda baki yana kallonta da mamaki, can ya kwantar da murya yace "Amma fa kinsan
ke na fara so Nadeeyah, kuma har a yanzu ina sonki fiye da tunanin ki, babu abinda
ya ragu a son da nake maki, don Allah ki cire Nihad a ranki Nadeeyah, you are my
first love and u will remain my first love, and kowa yana da matsayinsa a zuciya
ta" Ita dai kuka kawai take, ya dafe kansa don shi baya son wannan kukan nata, can
ya dago yana kallonta yace "If Nihad is just ur problem now shikenan ke zaki zauna
a nan Abuja ita kuma ta zauna either in kaduna or Kano, kinga babu ta inda za ku
fara ganin juna, is that okay by u?" Ta goge idonta tana kallonsa, yace "No say
something, idan da yanda kike son ayi sai ki gaya min" A hankali tace "I am not to
tell u what to do Kjay, and i will neva do that, kawai dai ni nasan i have no bad
intention against her, and i am trying my best to be friends with her amma she is
taking me for a foe, tun asali dama bata so na, even before i know she is ur wife"
Ya girgiza kai da sauri yace "Aa it's not that bata sonki Nadeeyah, kawai dai she
is a kind of person da bata sakin jiki lokaci daya da mutum, tana dadewa bata saba
da mutum ba, that is just it" Ɗan murmushi Nadeeyah tayi tace "No, ba haka bane,
tana min kallon kishiyarta, ni kuma bana mata wannan kallon har cikin raina, duk da
we were together before u met her, amma ni ban ji haushinta don ta aureka ba, i
have nothing against her" Yace "I will talk to her about that i promise, gradually
nasan zata saki jiki da ke in sha Allah" Murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba,
yace "Ni nasan baki da matsala Nadeeyah, u are a good girl kamar yanda na san ki a
ko da yaushe...." Wayarsa dake ajiye ne ya fara ring, ya dauka yana duba me kiran
nasa, ganin Nihal ce ya daga ya kai kunne, ya amsa sallaman da tayi masa jin
yanayinta yace "Are you okay?" Daga daya bangaren tace "Alhamdulillah, ya Nihad?"
Ya ɗan yi shiru jin kamar her voice is shaking yace "Hope everything is fine
Nihal?" Tace "Lafiya lau, ina son zan maka magana ne...." Yace "Oh ok, zan kira ki
zuwa dare don bana gida yanzu" jin tayi shiru yace "Hello" Sai kuma tace "Allah ya
kai mu, Nagode" Daga haka ta katse wayar, Nadeeyah dai sai kallonsa take, Yace
"Hope everything is settled now dear?" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "Can we
go out for shopping?"
Karfe shidda na ranan Nihal na kwance dakin Nihad don Umma ta hanata zuwa dakinta
yanzu, zazzaɓi ne me karfi ya rufeta, tun dawowarta daga waje Raliya bayan la'asar
take kwance dakin nata, da Umma ta shigo ta tambayeta result din makaranta sai ce
mata tayi ai ba a saki nasu ba, duk da tana jin zazzabin tun a lokacin amma bata
nuna ma Umma ba, kawai ce mata tayi bacci zata yi, Umma ta fita ta bar mata dakin
shine take ta kwance, Mumy ce ta shigo dakin ganin tun dazu bata ga ta fito parlor
ba, ta cire duvet din da ta kulle jikinta tace "Nihal jikin ne..." Shiru Mumy tayi
jin yanda jikinta yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login