Showing 15001 words to 18000 words out of 268471 words

Chapter 6 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

duk wani abu na cin mutunci da cin
fuska shine dai dai a wajenta, ai wannan ba rayuwa me kyau bane, har take cewa ka
sallamesa, da yayi me? Ruwa fa ta dauka gun me kayan marmari ta watsa masa a jiki,
kawai dai ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, haka ta sa Habibu a gaba daga baya
ta gaji ta saukar da kanta, mai aikin gidan nan ba dadin Nihad take ji ba, Nihal
kuma ba haka take ba, na rasa wannan baƙin hali irin na Nihad ni kam, ni dai ba
haka taga nake mu'amala da jama'a ba balle tace, kai kanka ba haka mu'amalar ka da
jama'a yake ba, to halin wa ta yo haka, idan ba shiga hakki ba wllh kar ka fara ce
ma bawan Allahn nan komai, a kan me xata ce sai ya bata makullin motata ta tafi
gantalinta da yamma sbda rashin kunya ma bata yi shakkar cewar motar tawa bace,
kuma naga ai ba ita ta basa makullin ba ni na basa, to a kan me xai bata..." Abba
dai yayi shiru bai ce komai ba, ganin ta gama fadin abinda xata fada yace "But that
doesn't warrant u to slap her publicly Maryam, why not ki bari idan kuka dawo gida
ki hukunta ta?" Mumy tace "Wato na goyi bayanta kenan Yallabai, ai yanda tayi
rashin kirkinta a bainar jama'a gwara nima na hukuntata a cikin jama'ar dai dai
kenan, ni fa i am not in support of walakanta d'an Adam Yallabai, kuma babu wani da
ya fi wani a wajen Allah sai wanda yafi tsoronsa, idan ma xaka share xancen nan ka
je ka huta to gwara ka share" Abba bai kuma cewa komai ba, Mumy tace "Can i excuse
my self?" Yace "Alright" ta mike tayi masa sai da safe sannan ta fita, Umma ta fito
daga bedroom din Abba don duk ta ji yanda suka yi da Mumy, tana ta6e baki tace "Yau
ni naga neman suna kiri kiri gun talakawa, ita a neman sunan ma ta rasa inda xata
dinga yi sai wajen talaka? Ai kamata yayi ta dinga kutsa kanta cikin manyan mutane
ana yi da ita, ta nan ne neman suna xai mata rana, amma ke kice duk abinda talaka
yayi dai dai ne, a dole sai kin burge?" Abba ya mike ya fita daga parlon, compound
ya fito, dai dai nan khalil ya fito daga dakin mai gadi ya amshi omo, ganin Abba ya
nufesa ya gaida shi da ladabi, Abba ya amsa yana kallonsa yace "Ibrahim, a dinga
hakuri da yaran nan don Allah, sannan duk sanda Nihad ta sameka da batun amsan
makullin mota kana da number ta ka kirani, idan wanda xaka bata ne sai ince ka
bata, don ba wai bata iya driving ba, tana driving to where ever she wants to, just
sbda security purpose ne bana barin suyi driving din da kansu, so kar kayi zaton
bata iya driving din bane, and u gat respect them all kamar yanda xaka yi
respecting dina ka ji" Khalil da kansa ke kasa a hankali yace "Toh in sha Allah
Alhaji" Abba yace "Sun baka daki a can boys quarters din ko? Don nasan akwai empty
room da Habibu ya bari" Khalil yace "Ehh an bani" Abba na kallon omon hannunsa yace
"Wanki xaka yi da omo?" Yace "Eh xan wanke bandaki ne" Abba yace "Ohk good, wannan
ai yayi kadan, no problem xa a kawo maka daga cikin gida yanxu" Yace "To nagode
Alhaji" daga haka Abba ya juya ya koma cikin gida, khalil ya koma can boys quarters
din. Abba na komawa part dinsa ya kalli Umma yace "Ki ba ko Sudais ne blanket with
some detergents ya kai boys quarters" Umma tace "A kai ma wa a can?" Abba yace
"Driver" Umma tace "Aa da dai kaje gun uwar dakinsa ta bada a kai masa, ni kam bani
da old blanket, kaji Alhaji da wani xance, shine yace ka basa blanket din?" mikewa
Abba yayi ya fita, ya tafi bangaren Mumy, tana daki ya sameta yace "Maryam blanket
xaki ba Sudais with some detergents ya kai ma driver din can" Mumy tace "Sudais ai
yayi bacci yallabai" Abba yace "To bani" Wani blanket dinta ta dauko, sannan ta dau
pack din omo da sabulu with toothpaste ta hada ta ba Abba, Abba ya amsa ya fita
dakin, a stairs ya hadu da Nihal xata dakinsu, tace "Abba where are u going with
the blanket" Yace "Boys quarters xa a kai ma drivern can" Nihal tace "Ohk, bari in
kai Abba" Abba yace "Good" Amsa tayi daga hannunsa don dama da Hijab a jikinta ta
juya ta koma downstairs ta nufi kofar fita main parlor, boys quarters din ta nufa,
tayi Knocking duk da kofar a bude take, isiya ne ya karaso ganinta ya gaisheta da
ladabi xai amshi blanket din yace "Wanki ne Hajiya?" Tace "Aa, ina sabon driver
yake?" Jin haka Khalil dake bandaki xai fara wankewa ya fito ya nufi kofar,
kallonta ya dinga yi don da farko ya xata Nihad ce, amma sai yaga ba itan bace don
wannan fuskarta bai rabo da murmushi, ya amshi abinda take mika masa, yace "Nagode
sosai" Juyawa tayi ta sauka chalet din, ya koma cikin parlon yana kallonsu Isiya
yace "Ku yi kokari ku bar barin kofar nan a bude sbda sauro" Da ido duk suka bi sa,
lkci daya suka kya6e baki, ya ajiye blanket din ganin omo, sabulun wanki da na
wanka sannan ga Toothpaste ya kwashe su gaba daya ya wuce bandakin, ya bata fiye da
minti talatin yana wankin bandakin don sae da omon yayi rabi, lkci daya bandakin ya
dawo hayyacinsa, wanka yyi ya fito, ya kulle bandakin da makulli sannan ya cire
makullin ya koma dinning area, ya shimfida babban bargon wanda laushinsa ba a cewa
komai, ya bude window dake wajen sannan ya kwanta ya rufe ido, bayan minti sha
biyar yaji ana magana, ya bude ido ya ga Saminu tsaye a kansa, shiru yayi yana
kallonsa, Saminu yace "Makullin bandaki da ka kulle xaka bada" Khalil yace "Ohk,
dama kuna amfani da bandakin kenan?" Saminu yace "Yo me xai hana" Khalil yace "Ohk,
shine ku ka bar shi yanda na samesa?" Bai jira Saminu yace komai ba, yace "Amma dai
kamar babu bandaki a dakunan naku iya wannan kadai ne ko?" Saminu yace "Akwai mana,
amma wannan din muke shiga gaba daya ai" Khalil ya ciro makullin da ya ajiye a
aljihun gaban rigarsa ya mayar aljihun wando sannan ya gyara kwanciyarsa ya rufe
ido, xuwa yanxu daga Isiya har Shafi'u na tsaye parlon suna kallonsa gaba daya,
Saminu yace "Toh wai kai gayen nan me kake nufi tukunna ma dai" Mikewa Khalil yayi
ya tsaya sai ga Saminu ɗan tsut a gabansa, Khalil na kallonsa da kyau ya tsaya dab
da shi yace "Baxan bada ba nake nufi" Shafi'u ya koma ya xauna haka ma Isiya suna
kikkifta ido, sui sui Saminu ya bar dinning area din shi ma yana gwaggwale ido.




✍🏻
07087865788

6️⃣
💖💖 *NIHAAD* 💖💖




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




~~~~~~


Washegari Monday har karfe tara Nihad na ta kwance a dakinta, karfe tara da rabi
aka bude kofar dakin, ta juya ganin Umma ce ta shigo ta mike xaune a hankali, Umma
tace "Baxa ki makarantar bane Nihad, naga yau Monday" Nihad tace "Lectures din
karfe goma ne, Nihal ta tafi islamiyya?" Umma tace "Tun yaushe, ke dai kam na san
ba xa ki ba" Nihad bata ce komai ba, Umma ta juya ta fita, sauka tayi daga saman
gadon ta shiga bandaki, nan ma sai da ta bata kusan minti arba'in sannan ta fito,
shiryawa tayi cikin tsadadden bakar Abaya, wurin shirin ma ta 6ata kusan minti
talatin, banda kamshi babu abinda ke tashi a ko ina na jikinta, sosai Abayar ta
amshi farin fatarta kai kace balarabiya ce, ta dau karamin handbag ta sa flat shoe
sannan ta fito daga dakin bata kulle ba don Hafsah xata shiga tayi mata gyaran
dakin sannan ta wanke mata bandaki, tana tafiya kamar bata son tafiyar ta tafi part
din Mumy ta bude kofar parlon, xaune ta ganta parlon tana waya, ta cire takalminta
nan bakin kofa ta karasa ciki a hankali, ta xauna saman kujera fuskar nan nata babu
yabo babu fallasa, har Mumy ta gama wayar sannan ta gaisheta, Mumy ta amsa mata ita
ma a dakile without looking at her, mikewa tayi tace "Xan tafi makaranta" Mumy tace
"Allah ya tsare" fita tayi daga parlon ta wuce part din Umma, Umma tace "Ashe dai
za ki, toh Breakfast din fa?" Tace "Xan yi a makaranta" Umma tace "Toh Allah ya
tsare" Kamar xata yi kuka tace "Umma ni gaskiya baxan iya shiga mota daya da wannan
yaron ba" Umma tace "Toh yanxu ya xa ayi, idan na tafi na amsar maki makullin kin
san anjima xa a dauko yara a makaranta" A hankali Nihad tace "Toh pls Umma zaki
bani makullin motar ya Farooq" Umma ta rike ha6a tace "Farooq, to bari dai in dauko
maki" cike da farin ciki Nihad tace "Yauwa Umma, karfe hudu xan dawo in sha Allah
baxan wuce haka ba" Mikewa Umma tayi ta fita daga parlonta ta wuce dakin First son
dinta, makullin dake jikin kofar ta murda sannan ta bude ta shiga ciki ta dauko
makullin motarsa ta fito, farin ciki sosai Nihad tayi ta mashi makullin tana
murmushi tace "Umma nagode" Umma tace "Toh ki tafi a hankali dai, kar ki kwarzane
masa mota mu shiga uku" Nihad tace "A hankali xan tafi Umma" Daga haka tayi ma Umma
sallama ta fita daga parlon cike da murna, ta fitowa compound taga mai gadi xaune
tare da Khalil, lokaci daya ta wani murtuke fuska, ta nufi mai gadi tana juya
makullin hannunta tace "Hey Bude min gate xan fita" Tashi yayi da sauri ya tafi xai
bude gate din, ta nufi motar yayanta, ta gefen ido khalil ya bi ta da kallo, har ta
shiga motar, bayan ta gama warming tayi zoom off out of the compound duk don ta
tada k'uran interlock, Mai gadi ya daga mata hannu yace "Allah ya tsare Hajiya" ko
kallonsa bata yi ba balle ta tanka, ta ja motar tayi gaba, kulle gate din yayi ya
dawo yana kallon khalil yace "Hajiya ce xata bata motar Farooq da yake baya gari,
kuma ina tabbatar maka uwarta bata sani ba, dama Umman ke daure mata tayi ta abinda
ta ga dama a gidan nan ai, kai kam huta roro" Khalil yayi murmushi yace "Yanxu ina
xata haka?" Mai gadi ya xauna yace "Wai Makaranta mana, kasan jami'arta shegen
tsada ke garai" Khalil yace "Ita er uwarta fa?" Mai gadi yace "Baiwar Allah, ba
daxu ka ajiyeta a islamiyya ba, hutun makaranta ta dawo, amma kaga kullum sai taje
islamiyya abunta..." Khalil yace "Wacce makarantar take ita?" Mai gadi yace "Ba
nace maka a Zaria take, Ahmadu Bello" Khalil bai kuma cewa komai ba. Nihad na
driving tayi dialing number Husnah, Yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad tace
"Kin shiga school ne?" Husnah tace "Me yasa kika kashe wayarki jiya bayan munyi
dake kina tahowa?" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "It's a long story, but ya na
ji muryarki haka, are you okay?" Husnah tace "Partially" Nihad tace "Where are u at
now?" Husnah tace "Ni'ima guest palace" Nihad tace "Really? To bari in taho nan
kawai, nima I'm not even in the mood of attending lectures today" Husnah tace "Sai
kin xo" Katse wayar Nihad tayi ta dau hanyar Ni'ima guest palace din. Nihad na isa
tayi parking ta kirata, nan Husnah ta sanar mata room number dinta, Nihad ta sauka
motar ta shiga ciki, Knocking tayi kofar dakin, Naf ta bude, Nihad ta d'an buda ido
ganin Husnah a kwance ta lulluba, ta kalli Naf tace "Is she okay?" Naf tace "Shigo
in kulle kofa" Nihad ta shiga ta karasa gun Husnah, ta xauna gefen gadon tana kai
hannu jikinta tace "Ya dai Husnah?" Husnah ta mike xaune tana ta6e baki tace "Ashe
Yaks d'an iska ne duk bamu sani ba" Nihad ta ɗan bude ido tace "Me ya faru?" Husnah
tace "Kawai yaje ya sha kwayoyinsa jiya in gaya maki yayi assaulting dina" Nihad ta
xaro ido tace "Really?" Husnah tace "Wllh ke dai in gaya maki, ban da abunsa ai i
wouldn't have denied him" Nihad tace "Where was Nafee then?" Husnah tace "Ita suna
tare da saurayinta, kin san shi ma ya zo" Da mamaki Nihad tace "Yaks??" Husnah tace
"Ai kuwa baki ga yanda ya dinga tambayarki ba, nace kina hanya duk ya damu baki iso
ba, ke gwara ma da baki xo ba din, kilan rashin xuwanki ya sa haka ya faru," Nihad
tayi shiru, can tace "Tabdi, kuma a Tahir guest palace din?" Husnah tace "Wane
Tahir, ai ba a can muka yi birthday din ba, ke kinga haduwar birthday din nan kuwa
Nihad?? Gaskiya na jima ban ga birthday da yayi haduwar na Maska ba, it was light"
Nihad tace "Ni xancen yaks ne ya tsaya min a rai, Shi yasa fa kike ganin bana kula
clique dinsu, bana harka da maza marasu aji" Husnah tayi dariya tace "Ni kawai way
of approach dinsa ne ya kona min rai, amma what's there? norms ne ai, someone that
i have been crushing on from day one" Nihad tace "To karfe nawa ku ka bar wajen?"
Husnah tace "Kai dare yayi fa sosai, ke ni fa wllh gwara ma da Allah ya hanaki xuwa
nace maki, don da ban san ya xan yi da ke ba a wajen ga uban daren da muka yi, cabb
to wa ma xai saurareki, gaskiya birthday din nan yayi armashi, ai da naga daren
yayi sosai shine na fasa komawa hostel kawai muka kama daki a nan ni da Surayya,
ita Naf fa sai yau da safe ta xo nan ta same mu" Nihad ta kyabe baki ta ajiye
handbag dinta tace "I am jet hungry banyi breakfast ba, me suke siyarwa a nan?"
Husnah tace "Ke bamu dade da waya da Ayman ba xai taho mana da abinci yanxu, bari
in kirasa ince plate uku xai kawo, shi ma jiya ya dawo daga Egypt" Daga haka Husnah
ta kirasa ta sanar masa ya dado wani plate din, bayan ta ajiye wayar tana kallon
Nihad tace "Amma jiyan me ya hanaki xuwa don Allah?" Nihad ta sauke wani ajiyar
xuciya irin na takaici tace "Husnah in gaya maki wani sabon driver Abba ya dauka,
kin san ai ya bude ma Habibu Shago" Husnah ta gwalo ido tace "Don Allah, kina nufin
yanxu babu Habibu? Allah sarki, kai amma xaki yi kewan Habibu, sau da yawa fa da
shi kike hada baki, gashi duk inda kika ce ya kai ki kai tsaye yake kai ki, har ma
ya jira ki" Nihad ta marairaice tace "Ke dai bari, ai ni aka yi ma da Habibu ya bar
driving, sau nawa yake kai ni Tahir ko Bristol or prince hotel, kuma ya jirani
komin dadewar da xa mu yi, sau nawa xa mu fita in amshi mota a hannunsa shi ya tafi
harkar gabansa nima inyi tafiyata, sai na gama xan kirasa mu hadu a busstop mu koma
gida, Yawanci ba shi nake aika ya siyo min duk abinda nake bukata ba, ai har kuka
sai da nayi da naji Abba ya bude masa shago, Habibu ai mutum ne" Husnah tace "Amma
fa ya ci kudinki ba karya" Nihad tace "I wish Allah xai ta6a xuciyar Abba ya dawo
mana da Habibu kawai" Husnah tace "Toh shi sabon da aka dauka fa?" Nihad ta gyara
xama tace "Ai shi xan baki labari yanxu, wato wani tatattcen d'an iska, mara kunya
Abba ya dauko mana as driver Husnah, kinsan jiya a kansa sai da Mumy ta mareni har
sau biyu a titi cikin jama'a? Husnah as i am talking to u now i am boiling inside,
tun shekaranjiya nake cikin ɓacin rai da bakin cikin mutumin nan, daga fara aiki
shekaranjiya har ya raina ni baya girmama ni, ina masa magana sai yayi min banxa ko
kuma ya kalle wanda ke kusa da shi irin dai kamar ba da shi nake ba da na kusa da
shi nake, ko kuma ya kara min sheggun kunnuwansa gaba, irin dai na raini da
tantiranci, Husnah yayi mugun raina ni wllh, yanxu maganar da nake maki motar ya
Farooq Umma ta bani makulli na fito da shi, baxan juri xama a mota ni da shi yana
driving dina ba...." Tuni har hawaye ya cika idonta, Husnah dake ta sauraronta da
mugun mamaki ta gyara xama tace "What?? Shi ordinary driver din yake duk wannan
abinda kika lissafo min kuma kika kyalesa? Ta yaya kika basa wannan fuskar ya
rainaki daga fara aikinsa Nihad? Waye shi haka, kuma a ina Abba ya samo sa?? Wai ma
garin yaya kika yi creating room for this bullshit" Nihad na shessheka tace "Baxa
ki gane ba, wllh irin yan iskan nan ne yaron, cikin ruwan sanyi yake raininsa da
rashin mutunci, idan kin gansa ma xa kiyi xaton baya magana nan ko katon ɗan iska
ne, yanda fa kika san motarsa haka yake jin kansa daga fara aiki" Husnah ta rike
ha6a tace "Tabdi... to kuwa xa mu yi maganinsa, but what did Abba say about it? Ko
baki kai kararsa ba har yanxu?" Nihad tace "Babu wani action da Abba ya dauka tunda
Mumy ta zuzzuga sa, har Umma ma ta saka baki amma Abba yaki daukan kwakkwaran
action, the painful part of it is that Mumy supporting dinsa take kamar ta ta6a
saninsa, kinsan yanda take abubuwanta dai, to wllh a kansa ta gaggaura min mari
jiya a tsakiyar Hotoro dalilin da yasa na fasa xuwa Tahir palace kenan, to wannan
ne har xan dinga basa kudi yana kai ni duk inda nake so ba tare da yayi casting
dina ba wataran? Ina ai baxai yiwu ba, bana harka da fitsararrun yara ni...."
Husnah tace "Calm down besty, shi karamin kwaro ne wllh, kuma xa mu yi maganinsa,
Clique dinmu kadai mun ishesa" Naf dake ta sauraronsu ta kyabe baki tace "Lallai
wnn ɗan iska ne number 1, daga wani kauyen aka samo maku shi halan? Shi a yan
kauyen ma shege ne fa" Nihad tace "How will i even know, wlh d'an rainin wayo ne na
karshe, gashi baya wani magana nake gaya maku, yanda kuka san kurma, cikin ruwan
sanyi yake rashin mutunci da raini, ga wani ji da kai, to kana aiki karkashin
mutane
kana driving ina wani ji da kai??" Kwankwasa kofar aka yi, Husnah tace "Ayman is
here..." Naf ta nufi kofar ta bude, wani matashi ya shigo dakin rike da takeaway
uku with many drinks da bottle water, Ya ajiye ledan yana kallon Nihad yace "Manyan
mata, ashe dai kina kasar nan Nihad?" Nihad tace "To an zuga Abbana ya ki kai ni UK
karatu ba dole a gan ni a kasar ba" Dariya yayi yace "Gaskiya ne, to ya kwana da
yawa, kinsan ku manya ne ba kowa ku ke replying ma chat ba both WhatsApp and IG"
Nihad tace "Not at all" Husnah ta mike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login