Showing 237001 words to 240000 words out of 268471 words
nuna
maki bazai iya ba, yar gwal ce ita da za a siya mata kayan daki kusan miliyan goma
a zamanin nan??? Sannan Nihal da kike cewa bai damu da al'amarinta ba ta ina ya
shaku da ita yarinya duk kiwuya kowa ta maida shi dodo?? Ina ce har ni bata yadda
da ni a sanda take karama? Kuma har yanzu da girmanta kin ga tana zuwa wajena? A
ina kika taba ganin yaro me kiwiya an shaku da shi? Ai sai dai uwarsa, don haka duk
sharrin da kika laka ma ɗa na Allah ya saka masa, Allah ya isa tsakaninsa dake,
Wato har bedio da aka ce yana ta yawo na Nihad har da sa hannunki kenan??" Sai kuma
ta fashe da matsanancin kuka ta koma ta zauna, Nihad dai sai kallon Umma take
hawaye na sauka idonta, shi kam Abba was speechless, Khalil ne ya fara tashi ya bar
dakin, Inna tace "Aa dole ka tashi ashe duk ga warce ta gurbata rayuwar matarka tun
yana er yarinya bamu sani ba" Sai kuma ta rushe da kuka tace "Allah na tuba ka
yafeni da hadin bakina fa aka dauke Nihad daga wajen uwarta aka ba Umma ashe matar
da sharri take nufinta bamu sani ba" Alhaji Abubakar sai share zufan da ke keto
masa yake yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" A hankali Abba ya lumshe ido
with tears in his eyes yace "I have failed as a father"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
71
Khalil na fita dakin Abba ya kira Farooq, Farooq bai daga wayar ba ya mike kawai ya
bi bayansa, he is so heartbroken, main parlor ya samesa tsaye, ya tsaya shi ma yana
kallonsa bai ce komai ba, Khalil yace "This is not the rightful time for that
conversation saboda condition din sa, u have to stop it plss, it's not appropriate
for his health" Farooq dai bai iya yace masa komai ba sai kallonsa yake, Khalil ya
juya ya fita daga parlon, Farooq bai sake komawa dakin Abba ba, ya nufi dakinsa
walking slowly yana ganin kamar mafarki kawai yake. Inna na ganin hawayen da Abba
yake ta rushe da matsanancin kuka cike da takaici tace "Wallahi kin cuce mu
Sumayya, kin cucemu, Allah ya isa bamu yafe maki ba, ashe duk ke kika lalata masa
gidansa duk kokarin da yake na ganin ya ba 'ya yansa tarbiya nagari, duk kokarinsa
na ganin 'ya yansa sun zama na kirki kin tarwatsa masa, daga me Video dake yawo a
gari sai warce aure ya mutu an korota gida sannan uwa uba wai yau cikin shege a
zuri'armu, cikin shege fa?? ya ya zaki yi da wannan hakkin sumayya? Kuma saboda
karancin tsoron Allah kike nema ki alaqanta duk wannan abun da Ibrahim, dama can
kafura ce ke kawai wacce babu Allah a ranta, to bazan boye maki ba a gaskiya
zamanki ya zo karshe a gidan nan, ni kaina baxan jure ci gaba da ganinki ba balle
shi wanda kika cuta ga har ciwo ya kama sa, ki tattara yanaki yanaki ki kama
gabanki kawai Sumayya, ganinki kadai ya isa yasa Ibrahim yaki warkewa wallahi, ki
je duk inda za ki mu kuma baza mu hana yaranki zuwa gareki ba tunda ke kika
haifesu, alhakin abinda kika so ma Nihad ne ya sauka kan er ki, Sumayya kin cuci
Ibrahim don Nihal din ma er sa ce ba abinda zai canza hakan, shi yasa aka ce in
zaka gina ramin mugunta ka ginasa karami, ke ko baki yi wannan tunanin ba..." Umma
dai bata ce komai ba sai kuka take ta dafe kanta, Mumy ta kasa dago kanta ita ma
hawayen ne ke sauka idonta, Nihad kuwa gaba daya ta shiga rudani jin Inna ta ambaci
cikin shege, waye kuma yayi cikin shege, Nihal?? No it can't be Nihal, Tashi Usman
yayi ya fita daga dakin cause he can't endure it anymore, Umma ta mike tana share
hawayenta da zumar fita ita ma, taji muryar Abba a hankali yace "One more thing
Sumayya...." Ta juya ta kallesa, yace "Tell me what u know about Nihad's Video...."
Ta ɗan yi shiru na few seconds, sai kuma hadiye kukan da take tace "Kawayenta ne
suka yi drugging dinta sannan suka mata video din suka kuma saki a duniya..." Mumy
ta daga kai da sauri tana kallon Umma, Inna ta sake salati tana zaga dakin hankali
tashe, Alhaji Abubakar dai is totally speechless, a hankali Abba yace "U asked them
to do that?" Umma ta girgiza kai tace "Sai bayan da suka yi ni nasani, i never
asked them to do that..." Yace "Shikenan, Kije... ni kam na yafe maki, a duk zaman
mu idan akwai inda na kuskure maki ko yaranki ina neman gafara, Allah ya yafe mana
baki daya" Tana share Idonta tace "Ameen, ni baka taɓa min komai ba, Allah ya baka
lafiya" Daga haka ta juya ta nufi kofa inna ta bi ta da sauri tana hawaye tace "Ai
komin dare ana samun a kori kura, aje a samo ki kwashe kayanki Sumayya kada abu ya
lalace mana ni da ke cikin dare" Mikewa Kamila da Amina suka yi suka bi bayan
uwarsu ko warce da hawaye fuskarta, Abba ya kalli Mumy dake kallonsa tana hawaye
ita ma, cikin sanyin murya yace "I am sorry i never played my role well as a
father, i am sorry i broke my family..... I am sorry for everything" Alhaji
Abubakar yayi karfin halin cewa "Kar kace haka Ibrahim, komai kaga ya faru a duniya
Allah ne ya tsara hakan, stop thinking u failed ur family, u never failed them, u
were and will always remain a good father..." Da kyar Abba na kallon Mumy yace "Ki
kira min Nihal" Alhaji Abubakar ya dafasa yace "Noo, not now Ibrahim, sai ka kara
samun lafiya sosai, yanzu a bar wannan maganar haka, u need rest for now pls" Abba
bai kuma ce masa komai ba, Mumy ta share hawayenta ta mike ta nufi kofa a sanyaye
ta fita daga dakin, Nihad dai ta kasa tashi a inda take sai kuka take a hankali,
ganin Abba kallonta yake ta mike cike da karfin hali ta tafi can kusa da shi ta
durkusa cikin rawan murya tace "Abba kayi hakuri, all this is happening because of
me, i caused all this, i am sorry Abba, May be you shouldn't have...." Kasa ci gaba
tayi tana kuka sosai, Abba dai sai kallonta yake ya kasa cewa komai, nan kuwa tuna
irin yanda Allah ya dora masa sonta a zuciyarsa tun tana er yarinya yake, wanda tun
a sannan bai iya boye son nan ba har girmanta, kaf 'ya yansa babu warce yaji har
ransa kamar ita, and Umma used that against him by helping him to love her whereas
ba haka bane a zuciyarta, Umma used that to runined him and his family, Hawaye
Nihad ta gani a idonsa ta fashe da kuka sosai ta ma rasa abinda zata ce masa ta
daura kanta a jikinsa cikin rawan murya tace "I am sorry Abba, i am so sorry Abba"
murya can kasa yace "I will always love and Cherish u Nihad, you still remain my
favourite, Allah ya baki zaman lafiya da mijinki, Allah ya baki ikon yi masa
biyayya kamar yanda mahaifiyarki ta min, Allah ya baku zuri'a dayyaba, at last
everything turns out to be in ur favor.... " Ganin irin kukan da take yi Alhaji
Abubakar ya mike ya dagata yace "Tashi ki je Mamana, Allah ya maki albarka" Har
kofar fita parlon ya rakata sannan ya koma gun kanin nasa. Har kusan karfe sha biyu
Nihad bata hakura da kukan da take ba, gani take kamar saboda ita duk abubuwan nan
suka faru, and condition din da Mumy ta gaya mata Nihal ke ciki contributed wajen
kara daga mata hankali ta kasa daina kuka, tsabar yanda hankalinta ya tashi bata
iya ta je dakin Nihal din ba, she don't even know what to say to her, it's till
hard to believe wai she is pregnant, Mumy ta fito parlor ta dalilin wayarta dake
ring ta duba taga Khalil ne ke kiranta, dagawa tayi tare da yi masa sallama, daga
daya bangaren ya amsa yace "Mumy hope ban tashe ki bacci ba" Mumy tace "Aa ban
kwanta ba tukun" Yace "Dama zan ce maki magungunan ta na cikin akwati ne" Mumy tace
"Ohk bari in duba" Daga haka yayi ma Mumy sai da safe ta katse wayar, ta mike ta
nufi akwatin Nihad ta bude ta ciro magungunan sannan ta duba prescriptions din ta
bata ta sha,Tana shan maganin ba a dau lokaci ba bacci me nauyi ya dauketa. All
through the night Mumy bata wani rintsa ba, to ina ma taga kwanciyar hankalin
bacci, lokaci lokaci kuma take shiga dakin Nihal ta dubata sannan ta dawo ta ci
gaba da sallanta, Inna kuwa na parlon Abba a nan aka mata shimfida da bargo don
taki bin Alhaji Abubakar gida, ita ma dai bata yi baccin kirki ba sai sallah take
tana roka ma ɗan ta lafiya a wajen Allah, duk a daren ta yanke shawaran kawai ta
dau Nihal ta kai ta Bauchi wajen kanwarta har Allah ya sauketa a can don idan har
uban na ganinta a gabansa da kyar ya samu lafiya har ya tashi, gwara kawai ta
nesantata da shi, ta kai ta can inda bata san kowa ba tayi rainon cikin tunda taji
ance baza a zubar ba, Umma ma dai yanda taga rana haka taga dare nan babu ko digon
bacci a idonta, yanda take ji kuma a jikinta tasan jininta ya kara hawa, a daren
nan tayi mugun da ta sanin duk abubuwan da ta aikata, tayi da ta sani ya fi a
kirga, kamar yanda Inna ta fada babu abinda yaranta suka rasa gun Abba kawai son
zuciya ne ya kai ta ya baro, duk da baya nuna masu irin son da yake ma Nihad din a
fili amma basu taɓa kawo bukatunsu ya ki yi ba ko ya hanasu, Nihal ce dama bata iya
tambayarsa abu, komai take so sai ta bi ta hannun Umman, shi ko Abba idan baka
tambayesa ba he will assume u don't need it, Nihad kam kullum cikin tambaya take
kuma kullum cikin bata yake, Usman da Farooq throughout the night suna tare da
Abban nasu a dakinsa, Khalil dai lokaci lokaci yake shiga ya duba jikinsa a cikin
daren, idan ya dubasa kuma ya koma dakin Farooq, Mumy na son shiga ta duba Abban
amma ta kasa zuwa sanin Inna na parlon nasa sannan su Farooq na bedroom dinsa.
Karfe hudu da yan mintuna Mumy ta samu ta kwanta bacci ya dauketa, 4:30 Khalil ya
fito daga dakin Farooq ya nufi bangarem Abba, duk da an hour ago ya shiga ya dubasa
last, kwance ya samu Inna a parlon tana bacci har da minshari, wanda daxu da ya
shigo idonta biyu tana ta sallah, walking gently don kar ya tasheta ya nufi dakin
Abba, dazu da ya shigo Farooq ne kawai ke bacci Usman idonsa biyu, amma yanzu kuwa
duk bacci suke saman Carpet din dakin, ya karasa saman gadon yana kallon Abba don
ba a position din da ya bar shi dazu ya samesa ba ya karkace kansa dake kan pillow,
dukawa Khalil yayi murya can kasa yace "Abba ya jikin?" Abba bai ce masa komai ba,
ya kai hannu zai gyara masa kwanciyar saboda kar wuyarsa yayi ciwo sannan ya danne
hannunsa me matsala, Khalil ya fi 20 seconds yana kallon Abba babu ko kiftawan
kirki, can ya kwantar da shi da sauri ya cire pillow din da yake kai gefe yana duba
every pulse that he can check a jikinsa, ji yayi kafafuwansa sun kasa ci gaba da
daukarsa, bai san sanda yayi kneeling down nan kasa ba yana ci gaba da kallon
Abban, lokaci daya ya hade kansa da gefen gadon hawaye na sauka idonsa a hankali
yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, Muryar Farooq yaji yace
"Ohh i slept off...." Khalil dai bai iya ya dago kansa ba, Farooq ya mike ya dawo
kusa da su yace "Ya samu baccin?" Hawaye kawai ke sauka idon Khalil ya kasa ce masa
komai, Farooq ya kalli position din da Abba yake sai kuma ya kalli Khalil da sauri,
lokaci daya yaji gabansa ya wani fadi, ya duka gaban Abba da sauri ya riko hannunsa
yana jijjigawa yace "Abba... Abba" Yaga ko motsawa Abba bai yi ba, kiran da Farooq
ke ma Abban ne da karfi ya tada Usman, ya tashi tsaye da sauri, Farooq ya kai kansa
chest din Abba jikinsa na rawa and he heard nothing like heartbeat, ganin abinda
Farooq yayi Usman ya nufosa hankali tashe yace "What is the meaning of that???" Shi
dai Khalil ya kasa dagowa ya kallesu, he was weak all over, hawaye ya kasa daina
zuba a idonsa, Farooq ya hade kai shi ma da jikin gadon hawaye na sauka idonsa yace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" hayaniyar
Usman ne dake ta jijjiga Abba yana kiransa ya tada Inna, da gudu ta shigo dakin a
rikice, jiki na rawa tace "Menene kake kiransa haka Usuman??" Usman ya fashe da
kuka ya durkusa nan kasan dakin, Inna ta tafi saman gadon da sauri ko ina na
jikinta na bari tana cewa "Ku gaya min me ya samesa, me ya samu ɗan nawa? Wayyo
Allah na ku gaya min don Allah" Ganin babu me shirin bata amsa, ga Khalil da Farooq
sun ki dago kai, Usman kuma yayi zaman dirshan a kasa ya rike kai yana kuka, ta
fashe da matsanancin kuka da gudu ta fice daga bangaren ta shigo main parlor a
gigice ta saki salati da duk karfinta, sai kuma ta fasa ihu ta daura hannu a ka
tana zaga parlon, Mumy ce ta fara fitowa da sauri daga ɓangarenta a tsorace, Sai ga
Umma ma ta fito da su Kamila, Nihad ma ta fito daga parlon Mumy, Inna na kallon
Mumy ta kara kwala ihu tana girgiza kai tace "Na shiga uku Maryam, wayyo Allah na
Maryam, na shiga uku na lalace, su ce min wasa suke min, Innalillahi wa inna ilaihi
raji'una...." Sai kuma tayi collapse nan kasa, Umma dai jikinta sai rawa yake ta
kasa karasowa cikin parlon, Mumy bata kara kallon Inna ba ta yi bangaren Abba duk
jikinta na rawa ta shiga, Nihad bata san sanda ta bi bayanta ba ita ma da sauri,
dai dai sanda Khalil ya mike ya ja ma Abba abun rufansa ya rufe har kansa Mumy ta
shigo dakin, Banda kuka babu abinda Farooq da Usman suke, Mumy taji wani jiri ya
debeta ta fadi a sume nan kasan dakin, wani kara Nihad ta kwala da karfi ita ma ta
sulale nan kasa.... Kafin wayewar gari gidan Abba ya cika babu masaka tsinke da
jama'a, ko wajen parking babu a layin, abokansa na wajen aiki, yan uwa da abokan
arziki, makota, wa enda ya taimaka a rayuwa, childhood friends duk dai gasu, babu
wanda bai ji mutuwarsa ba, da yawa al'umma sai da suka yi kwalla, shaidar da Abba
ya samu kuwa ba a cewa komai, an masa shaidan mutumin kirki me rike ibada sannan me
tausayi da taimakon talaka, Aminu kuwa kai kace Mahaifinsa ne ya rasu don can bayan
gidan ya tafi ya dinga kuka yana buga kai, haka Saminu da Isiya, karfe takwas saura
Janar da abokansa biyar suka iso gidan tare da Mami da su Mimi.... Mami was more
than shock ta kasa kallon Mumy ta nemi waje a parlon dake cike ta zauna tana nanata
Innalillahi wa inna ilaihi raji'una a zuciyarta zuwansu gidan da kuma position din
da Abban ya zauna cikin parlon yana magana cikin girmamawa cike da dattako kawai
take tunawa, irin kukan da Umma ke yi a parlon dole a tausaya mata, duk ta birkice
ta dawo kamar wata tabaɓɓiya, Mumy dai ba um ba um um sai hawaye don zuwa lokacin
sumanta uku, Aunty Jamila dake gefenta tana ɓata baki cikin nutsuwa ita ma dai
kukan take, haka frnds dinta su hudu da ko wacce kokarin kwantar mata da hankali
take, Karfe tara aka tafi kai Abba makwancinsa, a sannan ne Mumy ta kara realizing
da gaske tayi loosing mijinta forever and she couldn't endure it any longer, hakan
yasa su Aunty Jamila suka shiga da ita part dinta. Bayan an dawo daga kai Abba Mami
ta samu Khalil a compound tana tambayansa Nihad don tun da suka zo bata ganta ba,
tana son tasan halin da yarinyar take ciki, bai iya ya daga kai ya kalli Mami ba
yace "Tana asibiti tare da wata Aunt dinta, she miscarried the pregnancy...." Mami
ta kasa cewa komai tana kallonsa, can tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,
hope she is fine amma?" Yace "Yanzu zan je can din, an mata alluran bacci ne tun
wajen 6" Mami ta kasa cewa komai, she really pitied the family sosai, a hankali
tace "Toh ka je, Allah Ubangiji ya bata lafiya, ita ma mamarta da alluran baccin
aka samu aka yi mata" Yace "Bari dai in je asibitin in dawo, kakarta ma na asibiti"
Mami tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Juyawa Khalil yayi ya nufi gate, a
sanyaye Mami ta koma cikin gidan....
*Barrister yace harba masu haka nan ko ba yawa su yi maneji* 😟
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
72
Nihad ta daga kai tana kallonsa har ya karaso cikin dakin, ya zauna kusa da ita
yana kallonta a hankali yace "My father wants to speak to you Nihad" Ta sauke
idonta hawaye na saukar mata bata ce komai ba, ya goge mata hawayen ya mike ya
dagota suka nufi kofa don da Hijab har kasa a jikinta, It is around 5pm na yamma,
kuma ranan aka yi sadakan ukun Abba, har a sannan kuma akwai jama'a sosai a gidan,
tana biye da shi kamar iska zai hureta ta fadi har suka iso parlon Abba, Janar na
zaune da frnds dinsa a parlon sai yan uwan Abba biyu da amininsa da wasu Colleague
dinsa, Nihad ta karasa har kusa da Janar ta duka kasa ta gaishesa cikin sanyin
murya hawaye na zuba idonta, yayi patting shoulder dinta cike da tausayinta ya
kwantar da murya yace "Kiyi hakuri daughter, take heart dear, a yanzu ur dad needs
nothing from u than prayers, baya bukatan wannan kukan naki, ki yawaita yi masa
addu'a that is all he needs now...." kai kawai ta gyada masa hawaye wani na bin
wani a fuskarta, ya dai yi mata nasiha masu kwantar da hankali da kara hope,
Sojojin dake parlon da abokan Abba na taya sa, shi dai khalil na tsaye bakin kofa
yana kallonta, he is full of pity for his wife, he wish he can take all her pain
away, so kawai yake ya samu space din lallashinta yanda ya kamata don har yanzu bai
mata lallashin da ya gamshesa ba, daga karshe Janar ya daga kai ya kallesa yace
"You can leave with her" cikin rawan murya Nihad tayi masu godiya ta mike ta nufi
khalil, Abba yace "I want to speak with the