Showing 126001 words to 129000 words out of 268471 words

Chapter 43 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ya dauka don
rage volume din Tvn, a hankali Nihad ta gaisheta ta amsa da fara'a, Khalil Yace
"Suna sama Mumy" Upstairs ta nufa, Kamar ance ya juya ya ganta ta jingina da kofar
parlon tana kallonsa tana murmushinta me kyau, wara ido yayi kafin yace komai ta
taho da sauri ta rungumesa ta lumshe ido a hankali tace "I have missed you so much"
Daga kai Nihad tayi ta kalleta, shi kam yayi stiff a wajen da yake duk ya daburce
cause she took him unaware, Lokaci daya ta lura da Nihad dake wajen da sauri ta
sakesa ta koma baya tana mata murmushi tace "Sannu, sorry i just badged in,
Assalamu alaikum" Nihad dake kallonta daga sama har kasa ta dauke kai kawai, Khalil
ya bude palm dinsa with surprise yace "But you didn't say u are coming with Mum" Ta
langwabar da kai smiling at him tace "Surprise" Kallonta kawai yake, a hankali
hawaye na taruwa idonta tace "I missed u so much..." Ya mata wani kallo yace "Come
off it dear" Lokaci daya
Nihad ta mike ta fice daga parlon zuwa guess room da take ciki daxu, Nadeeyah ta
bi ta da kallo, sai kuma ta kallesa tace "Dear Wacece ita? Ko dai taji haushin
yanda na shigo ko? Wallahi i was just overwhelmed" Khalil ya daga kafada yace "No,
kece dai kika ga haka...." Tace "Ohk, tayi hakuri in ma taji haushina ne, where is
Mami?" Ya nuna mata sama tace "Let me go and greet her" yace "Ohk dear" Tana barin
wajen ya bi ta da kallo har ta haura sama.....



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788


Assalamu alaikum manyan mata!!

For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of
jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰


Join my WhatsApp group for beautiful samples.

Contact https://wa.me/c/2349090591769


39

Bayan Azahar Aunty Maryam ta sakko downstairs tana kallon mai aikinta dake parlor
tace "Kin kai ma bakuwar can abinci kuwa?" Mai aikin ta tashi da sauri tace
"Wallahi na manta Hajiya" Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta tace "Amma ai
baki mance naki cikin ba" Da sauri mai aikin tayi hanyar kitchen, Aunty Maryam ta
nufi guess room, bude kofar dakin tayi taga Nihad zaune saman darduma, Aunty Maryam
ta shiga dakin, Nihad ta daga kai tana kallonta, Aunty Maryam tace "Kiyi hakuri
ashe wancan gantalalliyar bata kawo maki abinci ba ni ina can sama ban sani ba"
Nihad dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kika ki
zama parlon kiyi kallo?" A hankali Nihad tace "Ba komai" Aunty Maryam bata kuma
cewa komai ba, Sai ga Murja ta shigo da abinci dakin ta ajiye ma Nihad, Aunty
Maryam na kallonta tace "Ki karo lemun" Da sauri Nihad tace "Aa ya isa Aunty" Aunty
Maryam tace "Toh zuba abincin ki ci" Daga haka ta juya ta fita daga dakin, All
through Khalil na compound wajen shan iska tare da Nadeeyah, kana ganinsu kasan
they really missed each other, abincin ma waje aka kai masu suka ci tare, bayan
Nadeeyah ta zuba masa drink din kwalin gabansa yana kallonta yace "Thank you" Tayi
murmushi tace "Continue... ina jin ka" Ya É—an buda ido yace "Me xan ce kuma,?" Tace
"Ba labarin stay dinka a kano kake bani ba, ai baka gama ba" Yayi murmushi yana
shafa kansa yace "Shikenan, all the household are very nyc, i think that's the most
important of all" Tace "To ita wannan yarinyar da na ganku tare, yar gidan ce?"
Yayi shiru, sai kuma yace "Nihal!! Of course yarinyar mai gidan ce..." Nadeeyah
tace "Allah sarki, wani school take?" Yace "Ahmadu Bello" Nadeeyah tace "Ohk, but
kasan har yau yan gidanku basu san inda kake ba all those while, a lot of time
Farhana da Sajida suna yawan tambayata about u, irin dai suna son su san ko i know
about your whereabout" Yayi murmushi bai ce komai ba, tayi sipping drink din
gabanta tace "Kasan everything happens for a reason, may be don kaje ku hadu da yan
gidan ku kulla zumunci shi sa Allah ya kaddara zaka je kano har kuma ka je gidansu,
kaga ai baxa ka manta halaccinsu ba" Ya gyada kai yace "Haka ne" Tace "And you mean
har yanzu basu san kai waye ba har bayan da ka dawo Abuja?" Ya girgiza kai yace
"Basu sani ba" Tayi murmushi tace "Za su yi mamaki kuwa idan suka san kai wanene,
but menene ya ja ra'ayinka har ka je gidan nasu ka zauna bayan baka ta6a saninsu ba
sannan ba rasa wajen da zaka zauna a kano kayi ba, infact ko hayar nawa ne nasan
xaka iya affording, u can even decide to stay in the hotel don duk da ba salary
kake samu ba sannan babu wani source of income don duk Abba ya toshe hanyar but
still nasan u neva ran out of cash all that period, Mami na tura maka, Aunty
Maryam, Aunty Hamida even though bata kasar...." Murmushi yayi yana kallonta murya
can kasa yace "And even you yourself" Ta hararesa tace "A'a ni ka cireni a lissafi
don anything mine is urs" Ta tallabi chin dinta ta ci gaba tace "So how did u even
know about them? And me yasa kayi deciding zaman gidan?" Yayi shiru yana kallonta
kamar baxai ce komai, can kuma yace "I will tell u some other time Nadeeyah" Tace
"Why?" Yace "I don't want to talk about it now" Ta langwabar da kai a hankali tace
"Amma ka ta6a saninsu ne?" Ya girgiza kai yace "Nace xan baki labarin some other
time" Tace "Ohk, but ya kamata ko Mami ka hada da yan gidan su gaisa a waya, su ma
za su san kayi appreciating dinsu" Yace "I will do that dear" a hankali tace "But
why did u keep on telling me kana USA?" Yace "Saboda nasan xa ki iya cewa xaki zo
kano saboda ni, shi yasa ma ranan da muka hadu nace maki in few hours time flight
dina xai tashi, don kar ki saka ran za mu hadu" Murmushi kawai Nadeeyah tayi tana
kallonsa... sai kusan la'asar suka shiga cikin gida, Nadeeyah ta haura sama shi
kuma ya zauna parlor, ko minti biyar bai yi zaune parlon ba Nihad ta fito rike da
warmers na abinci da mai aikin Aunty Maryam ta kai mata, tun da suka hada ido sau
daya bata sake kallon direction dinsa ba, sai dai kuma bata san hanyar kitchen ba
don tayi zaton zata hadu da mai aikin ne a parlor, juyawa tayi ta koma inda ta
fito, sai ga Mami ta sauko downstairs tare da Mum din Nadeeyah da Aunty Maryam,
Mami tace "Khalil xaka ajiyesu gida daga can mu tafi gida, xata kira driver nace ba
sai ta kirasa ba mu ma yanzu za mu tafi gwara mu tafi gaba daya" Khalil ya mike
yace "Ohk" Mami ta nufi Aunty Maryam dake answering call tayi kasa da murya tace
"Kai ni mu yi sallama da ita, ina ga ai daga nan zata wuce in ta amshi abinda xata
amsa" Aunty Maryam ta nufi bangaren da Nihad take Mami na biye da ita a baya, Aunty
Maryam ta bude kofar, kwance suka ganta a kasa, Aunty Maryam ta katse wayar da take
tace "Me yasa xaki kwanta a kasa ga gado?" Nihad ta mike zaune bata ce komai ba,
Mami tace "Naga bata da sabo ne da wuri" Mami na Murmushi tace "Ya sunanki?" Nihad
bata iya ta dago kanta ba a hankali tace "Fatima amma ana kirana Nihad" Aunty
Maryam ta kalli Mami, Mami tace "To maa sha Allah Nihad, yaushe xa a baki admission
letter din?" Sai a sannan Nihad ta daga kai tana kallon Mami, Mami tace "Yaushe
suka ce?" Cikin sanyin murya tace "Nima ban sani ba" Mami tace "Toh jiya me suka ce
maki a makarantar" Ta sauke idonta kasa tace "Shi ne dai suka gaya ma ba ni ba"
Mami ta kalli Aunty Maryam, Sai kuma tace "Toh, ya dai ce kafin sati za ki samu,
idan na zo nan din kafin ki tafi to, idan kuma ban zo ba xan bada sako a kawo maki
kin ji? Sannan ki gaida su mamanki da kyau" Nihad ta gyada mata kai kawai, Mami
tace "Toh sai anjima" Cikin sanyin murya Nihad tace "Nagode" Tana fadin haka ta
fara cire dankunnen dake kunnenta tace "Ga dankunnen" Mami tace "Aa, na baki ne ki
dinga sa wa Nihad" Nihad ta mayar tace "Toh Nagode, Allah ya saka da Alkhairi" Mami
na Murmushi tace "Ameen" Daga haka tace "Mun tafi" Ta juya ta fita dakin, Aunty
Maryam ta bi bayanta ta kullo kofar dakin. Khalil kadai ke jiransu a parlon,
Nadeeyah da Mum dinta kuwa sun fita compound, Mami na kallon Khalil tace "Ina
suke?" Yace "They are outside" tace "Toh mu je" Ya kalli Aunty Maryam yace "Na sa
wayata caji idan na ajiyesu xan dawo in dauka anjima Aunty" Mami tace "Ji wani
wahalar da kai, ka dau wayar mana idan mun je gida ka sa a cajin" Aunty Maryam tayi
dariya tace "Baki ga yanda na saki baki ina kallonsa ba" Ya É—an yi murmushi yana
sosa kai yace "Haka ne" Gun wayar ya nufa, Mami ta juya ta fita daga parlon, ya
juya ya kalli Aunty Maryam yace "Kawai bari in bar shi Aunty, ai bamu gama hiran ba
dama" Aunty Maryam tace "Toh je ka ajiyesu ka dawo, akwai abinda kake so ayi maka
kafin ka dawo" Yace "Aa coffee kawai xan sha idan na dawo" Tace "Toh sai ka dawo
son" Daga haka ya fita parlon da sauri zuwa parking space. Wajen karfe biyar da
wani abu Nihad ta fito parlor, Aunty Maryam dake zaune parlon tana rungume da
autanta Mus'ab ya dawo makaranta ta kalli Nihad tace "Kin fito" Nihad na wasa da
fingers dinta tace "Eh, akwai aikin da xa ayi Aunty?" Aunty Maryam tayi murmushi
tace "Aa Nihad, Murja ta ma kusa gama girkin ina ji yanzu, karaso ki zauna" Nihad
ta karaso cikin parlon ta zauna a kasa, Aunty Maryam tace "Hau saman kujera mana"
Nihad ta girgiza kai tace "Aa nan ya isa" Mus'ab dake kallonta yace "Ummi is she
our visitor?" Aunty Maryam tace "Yes dear, sauka kasa ka gaisheta" Ya sauka daga
jikin mamarsa yace "Good evening" Nihad na kallonsa tayi murmushi don mate din
Fadil dinsu ne tace "How are you?" Ya koma jikin mamarsa yace "Fine" Har Bayan
magrib Nihad na parlon tare da Aunty Maryam, aka bude kofa Khalil ya shigo da
sallama, Aunty Maryam ta amsa masa tana kallonsa tace "Sai yanzu?" Ya karaso cikin
parlon ya ajiye jakar hannunsa yace "Eh Aunty, good evening" Tace "Evening welcome,
wannan jakar fa? Ko na ta ne?" Ya nufi wayarsa yace "Eh nata ne" Ya dauko wayar ya
dawo ya zauna, Aunty Maryam na kallon Nihad tace "Dauka ki kai can dakin" Tashi
Nihad tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta dau jakar ta wuce ciki, Aunty Maryam
tana kallonsa tace "A kawo maka abincin ko coffeen dai" Yace "Na sha a gida Aunty"
Tace "Ohk, Mami tace xaka yi tafiya, yaushe ne tafiyar?" Ya É—an yi shiru sai kuma
yace "Nan dai da kwana biyu idan na gama shirye shirye" Tace "Toh Allah ya kai mu"
Wayarsa yake dubawa ya ga missed calls din Farooq, ko jiya ya kirasa, Khalil yayi
dialing numbersa ya kai kunne, Farooq na dagawa suka gaisa, Farooq yace "Har yanzu
baka turo ba Khalil" Khalil ya shafa kansa yace "Nace kar ka damu Yallabai, da da
bukatar hakan xan tura maka" Farooq yace "Ehh naji, amma kawai ka turo min"
Murmushi Khalil yayi yace "Toh shkkn, Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Farooq
yace "Fatan dai kuna lafiya?" Khalil yace "Alhmdlh" Farooq yace "Zariyan a wani
anguwa ku ke, ina ga in shigo ko jibi weekend" Khalil yace "Ohk zan tambaya" Khalil
yace "Ohk, tana kusa?" Khalil yace "Bari in bata" Mikewa yayi yana kallon Aunty
Maryam dake ta kallonsa ya mata alamar yana zuwa sannan ya tafi inda Nihad take,
saman gado ya sameta kwance, ya karasa ya mika mata wayar, ta mike zaune tana
kallon Iphone da yake mika mata, ta kai hannu ta amsa tana kallon screen din taga
number ya farooq don a haddace yake a kanta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace
"Ya farooq" Daga daya bangaren yace "Na'am Lil sis ya kike" Lkci daya har hawaye ya
kawo idonta tana goge idonta cikin rawar murya tace "Lafiya lau" Yayi shiru, sai
kuma yayi kasa da murya yace "Yanzu kukan me kike? Ko akwai damuwa ne?" Ta kasa ce
masa komai, yace "Nihad" Tana goge idonta tace "Na'am" Shi dai khalil na tsaye yana
kallonta, Ya Farooq yace "Bana son wannan kukan naki Nihad, shi yasa ko na kirasa
bana cewa ya baki, kukan nan yana damuna idan kina yi" A hankali tace "Toh na daina
yaya" Yace "Good girl, kiyi hakuri in sha Allah komai xai wuce, komai yayi farko
xai yi karshe in sha Allah, don haka ke dai ki zama me biyayya ku zauna lafiya da
mijinki, sannan ki rike Ibada sosai, may Allah guide
and protect you for us" Cikin sanyin murya Nihad tace "Ameen yaya" Yace "Har yanzu
baki da atm card ko?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Hello" Tace "Ehh
bani da shi" Yace "Toh shikenan, in sha Allah on Saturday xan zo, na gaya masa ma"
Nihad tace "Ina zaka zo yaya?" Yace "Wajenku idan Allah ya kai mu, be a good girl
always, Allah ya maki albarka" Tace "Ameen yaya" yace "Give him the phone" Mika
masa wayar tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai kallonta kawai yake,
bai kuma amshi wayar ba, ita kuma taki yarda ta kallesa, ganin still ya ki amsar
wayar ta ajiye masa nan gefen gado ta koma tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya
shafa beard dinsa, sai kuma ya dauki wayar ya juya ya fita ya kulle mata kofa.
Wajen karfe tara da rabi Aunty Maryam ta bude kofar dakin da Nihad ke ciki, zaune
ta sameta saman darduma ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam tace "Sai yanzu
kika yi isha'in? Nihad ta girgiza kai tace "Aa tun daxu nayi" Aunty Maryam tace
"Toh baxa ki kara abinci ba ko?" Nihad ta gyada mata kai tace "Ehh Aunty nagode"
Aunty Maryam tace "Toh shkkn, tunda ga kayanki ya kawo ki yi wanka sai ki kwanta,
ga zani kiyi amfani da shi don towel din bandakin ba a wanke yake ba" Nihad ta
nufeta ta amshi zanin da take mika mata tace "Nagode" Aunty Maryam tace "Ni xan
tafi daki, Allah ya tashe mu lafiya" Nihad tace "Toh sai da safe" Juyawa Aunty
Maryam tayi ta rufo mata kofar ta bar wajen, Nihad ta koma gefen gadon ta ajiye
zanin, sannan ta cire Hijab din da tayi sallah ta linke ta ajiye don a dakin ta
gani. Ta kalli jakar da ta shigo da shi daxu dakin, can ta nufi gun jakar ta
durkusa ta bude zip din a hankali tana kallon ciki, Hijab da aka yi packaging a
leda ta ciro har guda hudu, sai kuma Abaya kala biyar da undies masu yawa, sai
kayan shafe shafe with perfumes kala biyar, da nighties su ma biyar, kulle jakar
tayi ta mike ta bar wajen. Duk da Nihad felt secured a gidan Aunty Maryam amma
wannan daren ma ta nemi bacci ta rasa, for almost 4 days now bata bacci da daddare
ko tayi a firgice zata farka bayan wasu mintuna, or is she been traumatic, bata
taɓa jin tana kewar Mahaifiyarta yanda take ji yanzu ba, maganganunta na karshe ya
kasa fita daga ranta da zuciyarta, she could vividly remember every single word shi
told her a rananta na karshe a gidansu, and she wish she could hear more of such
from her, Magana da tayi da Ya farooq daxu shi ma yayi contributing a rest of mind
dinta but she still couldn't sleep, gaba daya idanuwanta sun kekyashe daga jin
bacci, daga karshe ta tashi a hankali ta kumna switch din dakin ta ga karfe biyun
dare, cike da karfin hali ta nufi bandaki tana jan kafa, har kusan karfe uku da
rabi Nihad bata yi bacci ba tayi sallan har taji bata da sauran strength kawai ta
jinginar da kanta da gado tana daga zaune kan darduman, sai a sannan taji hawaye na
sauka idonta, cikin rawar murya tace "Ya Allah duk wanda yayi min wannan abun ka
tona asirinsa cikin gaggawa, come to my aid ya Allah, Allah ka kawo min mafita
alfarman ma'aiki" Kuka take sosai tana roƙon Allah, wanda tun faruwan abun yau ne
ta kwantar da hankali take kai kukanta wajen Allah cikin nutsuwa, ko jin sanda aka
bude kofar dakin bata yi, cause she is really hurt, sae yanxu take ganin she needs
to know who is this that betrayed her, she needs to know who did this to her da ya
tarwatse farin cikinta ya rabata da Abbanta ya bata mata suna yayi tarnishing image
dinta a idon duniya, Aunty Maryam dai sai kallonta take tana tsaye bakin kofa, dama
ka'idarta ce duk in Allah ya farkar da ita cikin dare ko dab da asuba ko da baxata
yi sallah ba sai ta fito ta dudduba condition din yaranta idan suna gidan, har
dakin mai aikinta takan bude ta dubata, in ma da wani bako gidan in dai ba babba
bane xata bude dakin ta duba, sai in Allah bai farkar da ita ba wanda hakan ma ya
zame mata jiki dole ko yaya sai ta tashi saboda ta maida shi daily routine dinta a
gidan.... (Yana da kyau iyaye mata su sa ido su yi kokarin dinga yin hakan ko da ba
kullum ba barin idan kana da yara yan mata teenagers, kai har ma da yara mazan, its
very very important, i have this aunty that kullum da daddare sai ta leko ku taga
halin da ku ke ciki a daki, ya ma riga ya zame mata jiki, da Mumyn Nihad na kokarin
yi ma Nihad haka ko da ba a bangarenta take ba da abubuwa da yawa basu faru ba
kamar zuwa night parties da take, wasu yan matan sai su kai har karfe daya ana
video call da saurayi kasa kasa, ko chatting din banza, wasu kuma a wannan lokacin
xa su samu daman shiga internet su yi kallace kallacen banxa, wasu masturbation da
dai sauransu, duk kina can kin shanya baki hangangan kina bacci, Allah Ubangiji ya
kare mana zuri'a ya raba mu da mugun ji da mugun gani) Duk abubuwan da Nihad ke
fada Aunty Maryam na jin ta don daga karshe ma kulle kofar dakin tayi a hankali,
wanda hakan ne yayi distracting Nihad ta juya da sauri, sai da gabanta ya fadi
ganinta tsaye bakin kofar, ta hau goge idonta da sauri, Aunty Maryam ta karaso
cikin dakin tana kallonta ta zauna gefen gado tayi kasa da murya tace "It's okay
dear, tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login