Showing 165001 words to 168000 words out of 268471 words
ta rungume hannunta ta hade rai alamar she isn't moving an inch, Ya
jingina gefenta yayi kasa da murya yace "Ohk, How about we spending the night at
the hotel together" Ta kallesa da sauri, ya dage mata gira, ta dauke kai tana jin
gabanta na faduwa, ya kamo hannunta a hankali yace "Kinsan Mami ce tace ku zo nan
yau, so it won't make sense in maida ke gida ince kince baxa ki zauna ba for now
reason, so kawai mu tafi hotel" yana gama fadin haka ya bude mata back seat yana
kallonta yace "Ur usual spot" Nihad dai ta kasa cewa komai kuma ta ki shiga motar,
wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Mimi ce, dagawa yayi tace "Yayanmu Kai Mumy ke
jira fa bata wuce sama ba, or ain't you coming in again" Da sauri yace "Ohk, ohk
I'm coming" Daga haka ya katse wayar, yana kallon Nihad yace "Bari in je mu gaisa
da mutanen gidan, idan na fito sai mu tafi hotel din" yana fadin haka ya nufi cikin
gidan, Nihad ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta,
why will they bring her to this house, gidansu wannan er iskar yarinyar, tasan
baxata bi sa hotel ba but she will surely not stay in this house... Khalil na shiga
ya tadda Mum din Nadeeyah xaune a parlor, ya gaisheta da ladabi ta amsa da fara'a
tace "Ina bakuwar?" Yace "Yayanta ne ya kira take magana da shi a waje" Nadeeyah
dai sai kallonsa take, Mumy tace "Allah sarki" Khalil ya kalli Nadeeyah dake zaune
saman kujera suna hada ido ta dauke kai, tunawa yayi bai yi sallah ba ya mike da
sauri yace "Mumy xan yi sallah in dawo yanzu" Mum din Nadeeyah Tace "Toh je kayi...
Ga abinci xa a zuba maka kafin ka dawo...." Kofa ya nufa ya fita yana kallon
parking space, bai ga Nihad a wajen da ya bar ta ba, yayi still yana bin compound
din da kallo amma babu alamarta, cikin few seconds ya karasa gun mai gadi dake
bakin gate yana kallonsa da sauri yace "Wata ta fita gidan nan yanxu ne Malam?" Mai
gadin yace "Ehh bata dade ma da fita ba" Khalil ya zaro ido with shock yana kallon
mai gadin ya kasa ce masa komai, sai kuma ya fice da sauri daga gate din, at first
ya ma rasa ina zai bi don hanyoyi ne daban daban a area din, kawai ya dau hanyar
titi, cikin minti kadan ya iso main road din duk da nisan shi, amma bai ga alamar
Nihad ba, ya dinga bin ko ina da kallo zuciyarsa na bugawa, lokaci daya yaji wani
xufa na keto masa at the same time ƙafafuwansa suka masa nauyi.... Sai da Nihad ta
tabbatar tayi nesa da anguwan sosai sannan ta tsaya, ta cikin layuka tayi ta tafiya
har ta ganta a wani babban titi, wanda hakan yasa ta gane she is very far away from
the area she just left, tana ta tsaye bakin titi tana bin lafiyayyun motocin dake
wucewa da kallo ta rasa next step din da xata dauka, she stood there for more than
15min a bakin hanyar kafin wani mota yayi parking kusa da inda take tsaye, ta koma
baya tana kallon motar, wani mutumi da baxai wuce shekara 55 ba ya sauke glass yana
kallonta yace "Yan mata ina zuwa? Ki shigo in rage maki hanya mana kina ta tsayuwa
a nan" Nihad dake ta kallonsa taki cewa komai, yace "Haba yan mata ya kika yi
shiru, naga tun daxu kike ta tsaye a nan, har na shiga wancan supermarket din na yi
siyayya na fito" Sai a sannan Nihad tace "Bani da kudin mota ne, na yar da jakata"
Yace "Subhanallahi, to shigo in ajiye ki inda za ki ko, Allah ya tsare gaba" Nihad
tace "Sai dai ka bani kudin motar" Dariya yayi yace "Toh nawa ne kudin motar" Ta
ɗan yi shiru sai kuma tace "Ko nawa ne ka bani" Yace "Toh amma me yasa baxa ki
shigo in ajiye ki ba, ba fa ɗan yankan kai bane ko ɗan Kidnapper, Kinga dare yayi
bai kamata mace kamarki na tsaye bakin hanya a wannan lokacin ba" Tayi shiru ta ki
cewa komai, yace "Toh bari a baki kudin motar tunda baki yarda da ni ba, amma wani
anguwa kike?" Tace "Can gaba ne" Ya ciro kudi ya mika mata hade da wayarsa yace "To
sa min number wayarki yan mata" Ta amshi kudin ta ajiye masa wayarsa kan kujera me
zaman banza tace "Nagode, amma bani da waya wallahi" Tana gama fadin haka ta ci
gaba da tafiyarta da sauri, ya bi ta da kallo baki bude. Tafiya kawai Nihad take
amma bata ga alamar adaidaita sahu ko daya unguwar ba, gashi ta gaji sosai abun ka
da bata saɓa da tafiyar kafa ba, har lokacin kuma bata duba nawa mutumin ya bata
ba, daga karshe ta ganta a gaban wani babban supermarket, a nan taga wani me
adaidaita ta nufesa da sauri tace "Tasha zan je" yace "Wani tasha?" Tace "Inda ake
hawa motar kano" yace "Toh mu je" tace "Nawa ne?" Mutumin yace "Dubu biyu" Nihad ta
kalli kudin hannunta ta fara kirgawa taga dubu biyar ne, ta shiga adaidaitan, ya
tada suka bar wajen, Nihad na isa tashan bayan ta ba mai adaidaita sahu kudin ta
shiga ciki, ai ko ta samu mota da xai kama hanyar kano a lokacin, nan ta tambayi
nawa ne kudin mota aka ce mata dubu takwas, tayi kuri da ido ta kasa ce masu komai
don dubu uku kadai ne a hannunta, can ta koma gefe ta tsaya kamar munafuka, dreban
motar yace "Hajiya nawa xaki bada?" Tayi shiru sai kuma tace "Ni bani da kudi amma
idan na baka wannan xaka karba?" Tana magana tana kokarin ciro dankunnen kunnenta,
duk da akwai haske a wajen sai da mutumin ya kunna fitilar wayarsa yana haska ɗan
kunnen da kyau, can ya kira wani abokin aikinsa shi ma ya duba, Mutumin na kallonta
yace "Ai kawai ki fadi nawa zaki siyar ba cuta ba cutarwa sai a baki kudinki ki
cire kudin mota" Nihad tace "Ai ban san nawa zaka siya ba" Yace "Kin siyar dubu
talatin?" Nihad dai tayi shiru sai kuma tace "Toh" Mutumin yace "Toh ina zuwa" Can
sai gashi da cash din dubu talatin ya mika mata, Nihad ta amsa ta kirga dubu takwas
ta basa, sannan ta shiga motar wanda duk maza ne a ciki, suka bar mata jikin window
ta zauna.... Mami ce tsaye parlor tare da Mum din Nadeeyah suna kallon Khalil dake
zaune saman kujera ya ki ce masu komai, kana ganinsa kasan yana cikin tashin
hankali, Mimi sai hawaye take, Noor dai na zaune saman kujera don tare da Mami suka
zo gidan, Nadeeyah kuma na tsaye can kusa da dinning area, Mami tace "Magana fa
nake maka ka min shiru Khalil, ina kake tunanin yarinyar mutane zata tafi da
daddaren nan? Lokaci fa na wucewa" Mikewa yayi without looking at them yace "Nima
ban sani ba" Daga haka ya nufi kofa, Nadeeyah ta bi sa da kallo har ya fice daga
parlon, Mumy ta saki salati tace "Wallahi duka duka ko minti goma fa basu yi da
shigowa gidan ba, har nake tambayarsa tana ina da naga ita bata shigo parlon ba
yace tana waje tana waya da yayanta, ina yar mutane ta shiga ni Safeenah" Mami dai
ta kasa cewa komai don hankalinta ya tashi ita ma, where are they going to start
from, kasa ci gaba da tsayuwa tayi ta nemi kujera ta zauna tana furta innalillahi
wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta.... Ko barin Abuja Nihad basu yi ba bacci ya
dauketa a motar, Khalil bai jin ya taɓa shiga tashin hankalin da ya shiga a wannan
lokacin, ko abinda Abbansa yayi masa bai daga masa hankali irin wannan ba, ganin
abun yake kamar a mafarki fa, ya ma rasa wani tunanin zai yi, sai da yaga karfe
goma yayi tashin hankalinsa ya fara fitowa sarari, tun takwas su Mami suka koma
gida don barinsu ma yayi a gidan yayi wucewarsa, amma saboda yanda hankalin Mum din
Nadeeyah ya tashi haka ta sake bin su gidan tare da Nadeeyah, Duk suna zaune
parlorn Mami wajen karfe goma da yan mintuna khalil ya shigo parlon ta dalilin
kiran da Mami tayi masa, Mami tayi karfin halin cewa "Nace ka kira gidansu ka ki,
nace ka kira yayanta ka ki, to wai ya zan yi da kai, in ma baxa ka kira ba ni ka
bani numbersu mana, wannan wani irin tashin hankali ne" Khalil that was trying all
possible means to be calm yace "In kirasu ince masu me Mami? I should call and tell
them I can't find their daughter cikin daren nan? In kirasu ince masu an kasa rike
yar su a gidanmu saboda kanwar Abbana tace baxata zauna ba kuma Mamina bata da
abinda xata iya yi game da hakan? Mami ni na zata akan yarinyar nan sai inda
karfinki ya kare, i thought zaki yi repaying good deeds din da iyayenta suka min ta
hanyar riketa just like su Mimi, ina ce you will always be there for her, if not
for her family i would have been depressed by now, right in front of u Abbana sent
me away from his house and u couldn't do anything about it, kina gani na bar gidan
nan baki iya yin komai a kai ba, naje inda suka rikeni ba tare da sun san ni ba har
suka damka min amanar dukiyarsu amma ta haka za muyi repaying dinsu mu kasa rike
masu tasu er?" Mami dai kallonsa kawai take ta rasa abinda xata ce amma duk jikinta
yayi sanyi, juyawa yayi ya fice daga parlon Nadeeyah ta bi sa da kallo babu ko
kiftawa, Hajiya Safeenah ta nemi kujera ta zauna tace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un" Wajen karfe biyu da rabi na dare Nihad suka shigo garin Kano, tayi bacci
har ta gode Allah a hanya, mamaki ya cikata ganin adaidaita har sannan a tasha,
tana kallon
wanda ke tambayarta inda xata tayi shiru, tana tunanin ko dai kawai taje hotel ta
kwana tunda tana da kudi kuma tasan prices din hotels na Kano, nan ta gaya masa
hotel dai dai kudinta ya tafi da ita kuwa, tana sauka ta basa kudinsa ta shiga
ciki, ta biya kudin daki aka bata makulli ta wuce zuwa dakin, wanka ta fara yi a
bandaki sannan ta dauro alwala tayi magrib da isha ta kwanta, amma ta kasa bacci
sai juye juye kawai take, babu wanda ke ranta kuma a lokacin sai Nadeeyah, she just
hate her with passion, bata son ganinta kwata kwata, da tasan gidansu zasu je da
tun daga gidansu Khalil ta gudu don ko haduwa da ita bata so har cikin ranta....
Karfe takwas saura na safe Nihad ta tashi daga baccin da ta koma bayan tayi sallan
asuba, ta fita waje zuwa supermarket dake kusa da hotel din ta siyo brush da
maclean ta koma ciki, kafin karfe tara har ta gama shiryawa ta fito ta tare
adaidaita yana tambayarta inda xata tayi shiru, don sai a sannan gabanta ya fara
faduwa don bata san me xata je ta tarar a gida ba, kilan ma Abba ya koreta idan
taje, amma a haka ta dake ta gaya masa inda xata sannan ta shiga adaidaitan a
sanyaye, ya kama hanyar gidansu, tunda suka dau hanya gabanta bai daina faduwa ba,
bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso gidan, at first kasa sauka tayi daga
cikin adaidaitan ganin ya juya yana kallonta, tayi karfin halin sauka ta basa
kudinsa ta nufi gate tana tafiya a hankali, she is so afraid, daurewa kawai take,
bude gate din tayi taga Aminu zaune bakin gate da er radio a hannunsa, yana ganinta
ya zare ido ya mike da sauri yace "Hajiya" Ta ɗan yi murmushi tace "Aminu" Bakin
Aminu har kunne ya dinga mata sannu da zuwa, sai kuma ya nufi waje da gudu duk
zatonsa tare take da Khalil, Nihad dai ta ci gaba da tafiya gabanta na faduwa ganin
motar Abbanta a parking space, taga motar ya Usman ma alamar yana gidan, har ta isa
balcony dinsu ta kasa daga kafarta da kyau, tsoro ne fal zuciyarta, ta kusa minti
daya a tsaye kafin ta murda kofar a hankali ta shiga ciki tana kallon parlon, Umma
ta fito kitchen kenan rike da breakfast din da ta hada ma Nihal tayi sororo bakin
kofa tana zaro ido tace "Wa zan gani kamar 'ya ta Nihad?" tun da Nihad ta mata
kallo daya ta dauke kai ta nufi bangaren Mumy tana tafiya a hankali, Umma ta buda
baki with shock ganin abinda tayi mata ta bi ta da kallon mamaki, tuni Nihad ta
bude kofar Parlon Mumy a hankali ta shiga, Mumy ta fito dakinta kenan tayi ido hudu
da Nihad, still tayi bakin kofar dakin tana kallonta with surprise, Nihad ta tafi
da gudu ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy dai ta kasa motsi, can tayi
karfin halin dago kanta tace "Daga ina?" Nihad na Murmushi tace "Gida Mumy" Mumy
tace "Ke da wa??" Nihad tace "Ajiyeni yayi yaje ya dawo" Bude kofar Parlon aka yi
duk suka daga kai, Umma ta shigo, Nihad na ganinta ta shige dakin Mumy ta kulle
kofar, Umma tayi kasake a inda take tsaye, Can tayi karfin halin cewa "Ko ba Nihad
bace?" Mumy ta kirkiri murmushi tace "Ehh wallahi, yanzun nan ta shigo na ganta
nima" Umma tace "Allah sarki, to sannunta da zuwa, ina jin ta gaji ne" Daga haka ta
juya ta fita daga parlon, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri tana kallon Nihad
tace "Me yasa kika yi mata haka ta zo ganinki Nihad? Why did u leave the parlor"
Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mumy tace "Why didn't u greet her?" A
hankali Nihad tace "I need rest, and beside ke na zo gani" Mumy dai ta kasa cewa
komai ta dinga kallonta, Nihad tace "Mumy ina jin yunwa" A hankali Mumy ta juya ta
fita daga dakin don kawo mata breakfast, Mumy na fita ko minti uku ba ayi ba Nihal
ta shigo dakin....
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
52
Nihal ta karasa har inda Nihad take tana kallonta ta zauna gefenta with smile all
over her face, a hankali tace "Welcome sis" Nihad ta sauke idonta tace "Thank you
Nihal" Nihal tace "Ina Khalil din?" Nihad ta kalleta tace "He is fine" Nihal tace
"Ohk ba tare ku ke ba?" Nihad tace "Ajiyeni yayi kawai" Nihal tace "Ohk, kinyi kyau
sosai sis" Ta karasa maganar tana murmushi, Nihad dai bata ce mata komai ba, Nihal
ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "And i miss you so much" Nihad tace "Same
here" Nihal tace "I am happy u are home" Shiru Nihal tayi bata ce komai ba, can
Nihal ta mike a hankali tace "Zan je inyi wanka" Nihad tace "Ohk" Daga haka ta nufi
kofa Nihad ta bi ta da kallo har ta fita, Tana fita da few minutes Mumy ta shigo
dakin rike da tray, Hafsah na biye da ita da flask, cike da murna Hafsah tace
"Sannu da zuwa Aunty Nihad" Nihad ta kalleta tana ɗan murmushi tace "Ya kike
Hafsah" Hafsat tace "Alhamdulillah Aunty" Nihad tace "Ya aiki?" Hafsah na washe
baki tace "Lafiya lau, munyi kewarki sosai Aunty" Nihad dai tayi murmushi kawai,
Mumy dai ta zauna sai kallon Nihad take cike da mamaki, yaushe har ta wani san da
zaman Hafsah a gidan balle har ta mata fara'a haka har da tambayarta ya aiki,
Hafsah ta juya ta fita daga dakin, Nihad ta sauko ta zauna saman Carpet ta dau cup
ta debi ruwan zafi, bayan ta gama hada shayin ta daga kai ta kalli Mumy taga
kallonta take, Nihad tace "Mumy Nihal tayi rashin lafiya ne?" Mumy tace "Me kika
ga?" Nihad tace "Aa kawai naga ta rame" Mumy tace "Tun dai kwanaki a school but
she's better now, kawai stress din makaranta ne, you know she is in her final year"
Nihad bata ce komai ba, bayan few seconds cikin sanyin murya tace "Su sudais sun
tafi school?" Mumy tace "Ehh..." Shiru Nihad tayi tana juya shayin gabanta, Mumy
tace "Ya yan uwan mijin naki gaba daya?" Nihad tace "Duk suna nan lafiya, suna
gaishe ku" Mumy tace "Toh maa sha Allah, shi xai shigo nan ne a hada masa
breakfast?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa sai anjima" Mumy tace "Toh shkkn" Mikewa
tayi ta fita ta bata waje don ta karya comfortably don taga kamar duk a ɗari ɗari
take. Nihad na gama breakfast din ta dau tray din ta fita main parlor, har ta mance
yaushe rabon tayi breakfast cikin dadin rai haka, Zaune ta ga Nihal da Mumy a
parlor, Hafsah dake goge goge ta taso da sauri tace "Bari in kai maki kitchen
Aunty" Nihad tace "Aa Nagode, ci gaba da aikinki xan kai" Daga haka ta wuce kitchen
din Nihal ta bi ta da kallo haka ma Mumy, Dai dai nan Umma ta shigo parlon daga
bangarenta kamar warce aka hankado rike da makullin mota, ko lura da Mumy bata yi
ba tana kallon Nihal tace "Idan Abbanku ya fito kice masa jikar Hajiya Turai ta
fada cikin ruwan zafi yanzu aka kirani na tafi gidan, bana son tashinsa yana bacci,
sannan don Allah ki tafi dakina zaki ga kayana saman gado duk na birkito ki jera
min, sauri nake shi sa ban maida su ba" Nihal tace "Toh Allah ya sauwake" Mumy dake
ta kallonta tace "Subhanallahi, ayi masu sannu don Allah" Tuni Umma ta fice daga
parlon cikin hanzari ba tare da ta ma san Mumy na wajen ba. Nihad ta fito kitchen
kenan sai ga Abba ma ya fito daga parlonsa jin tashin motar Umma don ba bacci yake
ba, hada ido suka yi da Nihad, Sosai gabanta ya fadi ta makale jikin kofar kitchen
din ko ina na jikinta ma rawa, Ita kanta Nihal dake zaune sai da gabanta ya fadi,
Mumy dai ta sunkuyar da kanta kawai, Abba dai kallon Nihad kawai yake babu ko
kiftawa, Nihad ta sauke idonta kasa, lokaci daya taji hawaye ya cika idonta, Abba
ya dauke idonsa daga kallonta yana kallon Nihal yace "Ina Baabarki ta tafi?" Nihal
tace "Wai jikar Mama Turai ce ta fada cikin ruwan zafi shine ta tafi" Juyawa Abba
yayi ya koma parlonsa, Nihad ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa Mumy
tayi ta bar parlon ta shiga nata duk jikinta a sanyaye, Nihal ta karasa kusa da
Nihad ta kamo hannunta a hankali tace "Mu je ki gaishesa" Nihad dai bata ce komai
ba hawaye sai bin fuskarta suke, haka Nihal ta nufi parlon Abba da ita tana rike da
hannunta, Zaune suka gansa parlon ya jinginar da kansa jikin kujera, Nihad ta ki
barin su hada ido ta durkusa daga nan bakin kofar tayi gathering courage muryarta
na rawa tace "Abba ina kwana" Yana kallonta bayan few