Showing 192001 words to 195000 words out of 268471 words

Chapter 65 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

yayi ya sauka ya nufi motar don me motar ma yayi
parking ya sauko, hakuri ya dinga ba mutumin, Allah kuma ya so me saukin kai ne, ya
koma motarsa kawai, Khalil ya koma nasa motar ya shiga, ya jinginar da kansa jikin
kujeran motar ya sauke ajiyar zuciya, Nihad dai sai kallonsa take, irin kamar wanda
baya ganin gabansa din nan don ma Allah ya takaita, ya juya a hankali ya kalleta,
sai ta wani hade rai ta dauke kai, murya can kasa yace "Will u mind driving the car
pls?" Sai kuma ta juyo ta kallesa, ya girgiza mata kai a hankali yace "Baxan iya
ba" Shiru tayi bata ce komai ba, Sai taga ya bude motar ya sauka, a hankali ta bude
side dinta ta sauko ita ma, suka yi exchanging seat, ya sa mata driving direction
din a Google map a wayarsa ya ajiye mata, sai daga baya Nihad ta fahimci dalilin
kasa tukin nasa, don kuwa har suka iso gida kallonta yake, even for a second bai
daina kallonta ba as if his life depends on that, Ita dai tayi concentrating kan
driving da take kawai, ganin bai sauka ya bude gate din ba duk da sun iso gida ta
juya ta kallesa, wani murmushi me narka zuciya ya sakar mata, ta kasa daina
kallonsa, ya kamo hannunta a hankali, sai kuma ya saketa ya sauka daga motar ya
bude gate din gidan ta shiga ciki da motar tayi parking a parking lot, Bata jirasa
ba ta nufi kofar shiga gidan da sauri, sai dai dole ta tsaya ya zo ya bude kofar,
yana budewa kuwa ta shige ciki ya bi bayanta da sauri ya rikota, bata san sanda ta
fashe masa da kuka ba, ya rungumeta jikinsa sosai, yana jin kukan nata har cikin
zuciyarsa, murya can kasa yace "I am so sorry Nihad, i am very sorry, i am sorry i
hurt you much...." Kuka take tana tuna irin azaban da yayi mata, bata ankara ba
taji ya dauketa ya wuce sama da ita, ta kankamesa saboda tsoro, bai direta ko ina
ba sai saman makeken gadonsa dake master Bedroom ya hau aikin lallashin da bai samu
yayi mata all through that day ba, da ya ga ta hakura da kukan ya shiga bandaki ya
hada mata ruwa a bathtub dinsa, ya dawo ya dauketa zuwa bandakin, he did everything
for her, ita dai ta kasa hada ido da shi..... Daren ranan Khalil bai wani rintsa ba
all his thought was with Mami, kukan da yaga tana yi ya tsaya masa a rai, tun kafin
su kwanta ya so kiranta amma bai ma san me zai ce mata ba, infact ba ma shi da
courage din kiran nata, kawai ya hakura da kiran, all through the night Nihad na
jikinsa bai saketa ba, and she slept soundly. Karfe takwas na safe Khalil ya kira
Ya farooq bayan kiran da Janar yayi masa na cewa su shirya shi da Nihad before 9:30
za a zo a daukesu, wayar na fara ringing Farooq ya daga, bayan sun gaisa farooq ya
tambayesa ya Nihad, Khalil yace "She is fine Alhmdlh, ya Kaduna?" Farooq yace "Ina
kano ai" Khalil ya fara tunanin ta ina ma zai fara sanar masa, can dai yace "Erm...
dama Dad dina ne za su je kano wajen Abba yau su gaisa, so i don't know how it's
going to be...." Farooq yace "Ohk, ba damuwa zan sanar masa in sha Allah, Allah ya
kawo su lafiya" A hankali Khalil yace "Ameen" Don har ya fara jin kunyan Abban
Nihad da Mum dinta, Farooq yace "Kamar karfe nawa kenan?" Khalil yace "Zuwa sha
daya in sha Allah" Farooq yace "Allah ya kai mu" Daga haka suka yi sallama Khalil
ya ajiye wayarsa ya jinginar da kansa da kujera, yau kam bai ma san da idon da zai
kalli Abban Nihad ba, he wish Abbansa zai yarda yaje gidan without convoy, but that
will never be possible, can kuma ya ji dama Abban ya bar sa shi kadai yaje gidan ba
sai anje da shi da Nihad din ba, ya sauke wani ajiyar xuciya ya mike daga karshe ya
nufi sama ya shiga dakinsa, har sannan Nihad bacci take, kana kallonta kasan it's a
peaceful one, ya zauna gefen gadon a hankali yana kallonta ko kiftawa babu, abubuwa
da yawa ne suka hau dawo masa tun farkon da ya fara zuwa gidansu, and he couldn't
help it but smile and he wish she will go back to her former Nihad me tsiwa, wauta,
fada, masifa, amma banda walakanta d'an Adam da bin kawayen banza. Aunty Maryam na
zaune gefen gado a dakin Mami ta jingina jikin gadon tayi
shiru bata cewa komai, can ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Aa Mami kar ki
ce baza ki ba tunda har Janar din da kansa yace ki shirya...." Mami ta dakatar da
ita a fusace tace "Akwai wanda zai tilasta ni in je ne idan nace baxan je ba? To
nace baxan je ba, kuma baxan je din ba" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Ni health
dinki nake jiye maki Mami, don Allah ki kwantar da hankalinki abi komai a sannu,
tun jiya nake gaya maki haka amma kin ki fahimtata" Mami ta kalleta tace "Wallahi
ban ga amfanin zuwanki ba Maryam, na zata da kika zo za ki tayani a san ta inda za
a billo ma lamarin nan, amma sai dai ki zauna ki kura ma mutane idanu baki cewa
komai...." Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Ni so nake abi komai ne
a sannu Mami, ni kaina i am shock, i am really shock don yarinyar bata taɓa ce min
ae da aure tsakaninsu ba kuma ta bude min cikinta sosai during her stay a gidana,
amma dae na fi tunanin shi ne ya hanata fadi ita kuma babu yanda zata yi, ni sai
nake ganin tunda auren yayi ba shashanci ba ae da sauki da dai ace neman mata yake
Mami..." Mami ta dinga kallonta ta ma rasa abinda zata ce mata don takaici, Aunty
Maryam tace "That is just it Mami, wannan ne ma yasa na sa ma kaina nutsuwa ban
daga hankali ba, duk da lamarin akwai shock, but one have to try and reason, though
i am not in support of what khalil did da har zai yi aure babu knowledge dinku,
amma ai sai abi komai a sannu" Mami bata tanka ta ba ta dalilin wayarta dake ring,
ta dau wayar nata, ganin Hajiya Safeenah ce ta dinga kallon screen din wayar, can
dai ta daga ta sa handsfree kawai, nan suka gaisa faram faram, Mami tace "Kina ta
kirana jiya da daddare ban samu dagawa ba Hajiya, wallahi maganin bacci na sha,
bana ɗan jin dadi" Hajiya Safeenah tace "Subhanallah, ya jikin yanzu?" Mami tace
"Aa Alhamdulillah naji dama dama" Hajiya Safeenah tace "Toh zuwa karfe sha daya zan
shigo in sha Allah" Mami ta ɗan yi shiru sai kuma da sauri tace "Koh??? kuma gashi
za mu je kano tare da Janar amma yau din za mu dawo" Hajiya Safeenah tace "Ahh to
shikenan, sae dai kun dawo kenan, ita Nadeeyan sae ta tafi ita kadai kawai, dama
tace min zata gun Noor anjima maganar anko" Mami tace "Allah sarki, to in sha
Allahu muna dawowa zan kira ki" Nan dai suka yi sallama Mami ta ajiye wayar a
hankali, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Aunty Maryam dake ta kallon Mami tace "Kin
ga gwara da kika ce mata haka kar ta zo ta ganki a wannan yanayin da kike ciki"
Mami dae bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Ga kuma Nadeeyah tace zata zo wajen
Noor, kar kuma ta zo ta ga kina nan, ba gwara kawai ki shirya a tafi kanon ba, na
tabbatar idan kika je kanon zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, sai kuma a
san next step da za a dauka" Aunty Maryam na fadin haka ta mike ta shiga
bandaki.... Farooq yayi sallama kofar parlon Abba ya shiga ciki, ya zauna kasa ba
tare da yayi interrupting din Inna dake ma Abba magana ba, Umma ma na zaune parlon
ta rafka uban tagumi sai kallon innar take, Inna na kallon Abba a ɗan fusace tace
"Ya kake kallona haka Ibrahim, ni fa ba kai nace ka dauko masa yan sandan ba, to wa
ma zai sa ka ka lalata mana al'amarin, ni da kaina zanje gidan yan sandan in gana
da ogansu daga nan ya sa a cika min mota daya da kurtaye mu je har gidan nasa su
nakada masa shegen duka shi ma, kafin mu tafi da shi.... Ai ni da kaina zanje ko
ɗan rakiya bana so, don ma dai kaf zuri'a bamu da soja ai da shi zan aika ya ci min
ubansa kafin a kai sa gidan yan sanda" Farooq dai sai kallon Inna yake, Inna tace
"Sai kace er banza ya samu ya doka da za a yi shiru a kyalesa, to ni ba gantalaliya
bace, wallahi sai an bi ma jikata hakkinta" Farooq yace "Duk wannan abun fa
bangarenta kawai aka ji ba aji nasa bangaren ba Inna, ku daina saurin zartar da
hukunci daga jin bangaren mutum daya" Inna ta wani jefa masa shegen kallo tace
"Allah ya tsine masa shi da bangaren nasa, ya nakada mata shegen duka ya hadata da
saki daya kace mu jira mu ji bangarensa?? Anya farooq? to wai ko dai kai ka sa shi
yayi mata wannan abun ne bamu da labari farooq??" Shi dai Abba bai ce komai ba a
parlon, Umma ma ta kasa cewa komai abun duniya ya isheta, Inna tace "Toh kuwa bai
doki Kamila a banza ba sai inda karfina ya kare a wannan kes din wallahi, ga duka
ga saki??" Farooq ya dauke kai yana kallon Abba yace "Abba dama Khalil ne ya kirani
yanzu wai mahaifinsa zai zo gaisheka yau, zuwa karfe sha daya" Inna tace "Waye kuma
Khalil?" Umma ta daga kai daga tagumin da tayi tana kallon Farooq, Farooq na kallon
Inna yace "Mijin Nihad" Sake baki Inna tayi kamar warce ta ji mugun abu, can tace
"Lallai duniya ta tara marasu lissafi, yanzu su yan kauyen zai zauna jira baxai
fita aikinsa ba? Yau ga dai fitina kiri kiri" Abba na kallon Farooq yace "Allah ya
kawo su lafiya" Mikewa Farooq yayi ya fita daga parlon, Inna ta kalli Abba tace
"Kai kuma zaunawa zaka yi ka jira kauyawan?" Shi dai Abba bai ce mata komai ba,
Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanxu inna ya kika ce za ayi?" Inna tace "Kamilar
ta zura Hijabi muje har gidan yan sandan su ga abinda matsiyacin yayi mata, daga
nan su bani mota daya muje su ci ubansa, sannan mu tafi kotu..." Umma tace "Toh ai
bata iya ko tashi Inna" Inna tace "Sai a min hotonta in kai masu su gani"

Wani soja ne ya bude ma Nihad kofar motar dake parke kofar gida, ta juya ta kalli
Khalil dake kulle gidan, yayi mata alamar da ta shiga, a hankali ta shiga cikin
lafiyayyen motar, Khalil ya karaso ya shiga motar shi ma, suka bar anguwan, direct
airport motar ya nufa da su, kusan kuma a tare suka isa airport din da Convoy din
Janar, Nihad dai sai kallon ikon Allah take, Lounge na manyan kasar aka yi
Conveying dinsu kafin tashin jirgi.




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788


58
Farooq na fitowa parlon Abba ya tafi bangaren Mumy, Mumy ta fito daga dakinta jin
sallamarsa yace "Bacci kike ne?" Tace "Aa ba bacci nake ba farooq, ya gajiyan
hanya, jiya sai baka shigo ba har nayi bacci" Yace "Wallahi na gaji ne, i had
issues with my car" Mumy tace "Haka kace, Allah Ubangiji ya tsare" Yace "Ameen"
Mumy tace "Ka samu mijin Kamilar a waya?" Farooq yace "Eh na samesa amma bai daga
ba kuma bai biyoni ba" Mumy ta ɗan yi shiru, can tace "Toh Allah ya kyauta, amma da
ka je gida ka samesa ko?" Ya girgiza kai yace "Aa bazan je ba, duk yawancin abinda
take masa dama ai ni yake kira, kuma sai dai in basa hakuri, so this time around
ban san me tayi masa ba, tunda gashi har ya ga kirana bai biyo ni ba" Mumy tace
"Kai abun ba dadi wallahi, Allah Ubangiji ya daidaita su" Farooq yace "Mumy dama
Khalil ne ya kirani yace yau Mahaifinsa zai zo su gaisa da Abba...." Mumy tace "Yau
din nan?" Farooq yace "Ehh, shine na shigo in gaya maki ko za ayi masu ko da snacks
ne, tunda lokaci ya kure balle ace za ayi girki, yace min zuwa 11 za su zo and this
is past 9" Mumy tace "Toh shikenan, dama Jamila na garin amma yau tace min zata
koma, bari in kirata ko zata bari da yamma" Farooq yace "Ohk to, sai a karo drinks
da ruwa" Mumy tace "Toh shkkn" Yace "Zan siyo drinks din da ruwa" Daga haka ya fita
daga parlon Mumy ta dau wayarta ta shiga kiran Aunty Jamila, babu ɓata lokaci kuwa
Aunty Jamila ta iso gidan suka shiga kitchen da Mumy, Hafsah na taya su, Umma ta
fito ɓangarenta jin yanda kamshin soye soye ya cika gidan ta tsaya kofar kitchen
tana kallon Mumy tace "Wai!! Sannunku da aiki, toh dai Allah ya sa su iya ci, yan
kauye suka san wani Samosa da spring rolls banda abun ki Maryam, dama dai tuwo
miyar kuka kika masu da wannan wahalan ai" Ko kallonta Aunty Jamila bata yi ba tana
ci gaba da aikin da take, Mumy tace "Toh gashi nan dai muna yi, ya jikin Kamila?"
Umma tace "Da sauki...." Daga haka ta juya ta bar kitchen din, sai a sannan ta tabe
baki ta koma bangarenta. Nihad ta kasa hada ido da Aunty Maryam da Mami dake zaune
Lounge din, sai Aunty Hassana da bata yi shawara da kowa ba ta dau gyalenta ta
shige daya daga motocin Convoy, kuma daga Mami har Aunty Maryam babu wanda yace
mata komai, Ita kuwa Hajiya Amina dama sai yanda Aunty Hassana tace mata to bata ce
mata ta taho ba balle ta biyosu, Wani waje sak parlor Nihad ta hango Janar zaune da
wani mutumi sanye da kayan soja suna magana, Nihad bata iya ta dago kanta ba, ta
gaishe da su Mami a hankali, Mami ta amsa ba tare da ta kalleta ba, Aunty Maryam
dae sae kallonta take bayan ta amsa gaisuwan, can ta nuna mata kujeran dake side
dinta ganin gefe ta koma ta tsaya, a hankali Nihad ta karasa ta zauna kan kujeran,
Aunty Hassana ta dinga kallon Nihad tana nazarin abinda Aliyu ya gaya mata, Khalil
dama kin shiga Lounge din yayi, ya zauna a Departure Lounge din kowa da kowa...
first class passengers suka fara boarding din plane din, wanda iyaka ahalin Janar
ne a first class din, sai da Aunty Maryam ta nuna ma Nihad inda zata zauna cikin
jirgin sannan ta zauna, kamar yanda Khalil ke ta avoiding eye contact da Mami ita
ma haka ta dinga avoiding, wani kunyarta take ji, Khalil ne karshen shigowa ya
zauna, Aunty Maryam ta taɓe baki ganin yanda yake wani sinne kai, ita kam ta gama
tsorata da lamarinsa bata jin zata sake yarda da ko wani maganarsa, duk yanda take
da shi amma ya boye mata wannan lamarin..... Karfe sha daya da kusan rabi jirgin ya
sauka a Aminu Kano international airport, sai da suka fara sauka daga jirgin before
the rest class, Nihad ta dinga kallon jerin motocin dake jiransu har da na sojoji
da suka yi bake bake a airport din, tuni wani soja ya bude ma Janar da babban sojan
dake tare da shi motar da za su shiga, Khalil dai sai nesa nesa yake da su kamar
baya son a san tare suke, kai kace karere ne shi a wajen, Aunty Hassana kuwa sai
daga kafada ake ana taku dai dai uwa ita ce matar Janar din, Nihad ta daga kai a
karo na farko ta kalli Khalil tun barin su Abuja, taga ko kusa kusa da family din
nasa bai son matsowa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, wasu abubuwan da tayi
masa a baya ne suka hau dawo mata vividly, irin humiliating dinsa da tayi a
gidansu, and even for once bai taɓa attempting nuna mata ya fi ta komai na rayuwa
ba, yawanci duk abinda take masa sai dai yayi kamar bai san tana yi ba, bata san
sanda hawaye ya kawo idonta, and because of him today she is among this elite,
standing in the midst of them, kamar ya san kallonsa take shi ma ya kalli direction
din da take, suna hada ido tayi saurin kauda kanta, Aunty Maryam ta bude daya daga
motocin dake jere tana kallon Nihad tace "Shiga" Nihad ta shiga mota sannan ita ma
ta shiga, Mami ta shiga wani motar daban, Aunty Hassana ta shiga motar da Mami ta
shiga don me shegen tsada ne, nan suka bar airport din, Khalil da zai yi directing
dinsu zuwa gidan ya hau motar dake gaba, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka
iso Nasarawa GRA.... Nihad na ganin sun shigo layinsu gabanta ya dinga faduwa, Tuni
Aminu ya taso da sauri yana leko gate jin jiniya kamar tashin duniya, ganin jerin
motocin sannan ga na sojoji a gaba ya gwale ido yana jiran yaga sun yi gaba sannan
ya ga gidan wa za su amma sai ya ga sun jeru dai dai kofar gidan, kan kace me
sojojin sun sauka sun zagaye layin, a hankali Aminu ya tura gate din ya rufe ya
saka lock yana zaro ido, to meye kuma suka tsaya masu a kofar gida, ko dai ɓatan
hanya suka yi, A mugun tsorace Aminu ya kalli gate din jin ana bubbugawa, haba kan
kace me sai ga Aminu har cikin parlon gidan ba tare da yasan ya iso ba, Inna da
dawowarta kenan daga police station tana bada labarin yanda aka je har gidan Kamila
ba a tadda tsinannen mijin ba, ta saki baki tana kallon Aminu tace "Me zan gani
haka? waye wannan kuma??" Jiki na rawa Aminu yace "Hajiya wallahi sojoji ne sun fi
hamsin a kofar gidan nan, yanzu haka su ke bubbuga gate din, ban san wa suke nema
ba" Farooq ya mike yana kallon Aminu, Inna tace "Sojoji? Meye su din?" Umma dake
zaune parlon ita ma tana kallon Aminu tace "Sojoji fa kace Aminu" Zufa na keto ma
Aminu yace "Wallahi su Hajiya, da manyan bindigu na gansu sun sauka kofar gidan
nan" Inna tace "Aa to ko dai bariki za su suka yi ɓatan hanya suka shigo ma mutane
anguwa, da ba sai ka leka kace masu ba hanya ba" Abba ya fito daga parlonsa jin
bubbuga gate din da ake ta yi ba kakkautawa, shi dai Farooq na ta tsaye yana kallon
Aminu ya kuma kasa fita waje, ganin Aminu a parlon Abba yace "Lafiya" Aminu ya
durkusa ya makale jikin kujera yace "Wallahi Alhaji sojoji ne sun kusa dari ban san
wa suke nema ba, ni dai shine na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login