Showing 57001 words to 60000 words out of 268471 words

Chapter 20 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

bar
gidan nan na mance an halicce wani mutum me kama da kai a duniya? Toh akan me daga
dawowa ta xaka dinga bi na da kallon raini?" Khalil bai ce mata komai ba cause the
sight of her is making him feel feverish, ga wani tafarfasa da zuciyarsa yake, jin
bai ce mata komai ba ta ja wani tsaki tace "Banza kawai" Daga haka ta fice daga
gidan, Aminu dake lekosu ta dakinsa ya fito yace "kaii, Allah ya wadaran wannan
yarinya"

Ana saura kwana hudu su Aliyu xa su kawo kudi, Nihad na bacci da rana Kasancewar
ranan asabar ce babu lectures wayarta ya fara vibrate, bude ido tayi don Aliyu yace
xai kirata tana jawo wayar taga wata Coursemate dinta Sajida da ba wani shiri suke
ba ce ke kiranta, da kamar baxata daga ba sai kuma ta daga ta kai kunne, Sajidah
tace "Nihad what is this i am seeing on social media?" Nihad ta bude ido tace
"Kamar me?" Sajidah tace "Hau WhatsApp" Daga haka ta katse wayar, sai ga kiran wata
secondary school mate dinta Hafsah, tana ta kallon kiran sai kuma ta daga, daga
daya bangaren Hafsah tace "Nihad what's happening?" Nihad ta mike xaune tace "Ban
gane ba?" Hafsah tace "Ki hau WhatsApp" Nihad na kokarin shiga WhatsApp sai ga
kiran wata warce suka yi islamiyya tare, kawai haka nan taji gabanta ya fadi, ta
dai daga kiran, Badiyya tace "Nihad garin yaya haka don girman Allah??" Hankali
tashe Nihad tace "Wai me ke faruwa?" Badiyya tace "Ki kunna data" Nan Nihad taji
jikinta ya fara rawa, wani kiran ne ya shigo taki dagawa tayi rejecting ta bude
data ta hau WhatsApp din da sauri, messages ta gani rututu na shigo mata, kawai ta
bude wanda hannunta ya kai, Wata school mate dinta ce ta turo mata video tana
tambayar "what is this Nihad??" Hannun Nihad na rawa ta bude video din, kanta ta
gani with just skimpy undies a saman gado ba kuma bacci take ba, sai kuma taga ta
mike tsaye turning all over jefar da wayar tayi jikinta na rawa tana zaro ido tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai kuma ta saki wani kara ta sauka daga kan
gadon ta durkusa kasa, ringing kawai wayarta ke yi amma ta kasa motsawa daga inda
take, bude kofar dakinta aka yi ta daga kai da sauri, Umma ta shigo tana zaro ido
tace "Nihad me ke faruwa a social media yanxu Nihal ta kirani tana kuka, kuma wai
ta kiraki bakya dagawa" Nihad ta kasa cewa komai, bata ta6a zama soo weak all her
life ba kamar wannan moment din, ji take kamar komai na jikinta ma ya daina aiki,
wayar Umma ne ya fara ring ta daga da sauri, Nihal na shessheka tace "Umma ki hau
WhatsApp na tura maki" Umma tace "Tohh" Da sauri Umma ta hau WhatsApp ta shiga chat
dinta da Nihal ta bude video din, salati ta saki bayan ta gama kallon video din har
karshe ta jefar da wayarta kan gado tace "Nihaddd????" Dai dai da second daya wayar
Nihad bai samu breathing space ba, kiran su Husnah ne, Naf, Zully, infact calls
upon calls kawai amma ta kasa kwakkwaran motsi inda take a durkushe balle ta daga
wani waya, sai rufe ido take tana budewa kamar dai warce ke mafarki tana son ta
farka, Umma na tafe hannu ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un, na shiga uku na lalace ni Sumayya, Nihad wa ya maki haka? Garin yaya haka
Nihad?" Bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo da tashin hankali kwance fuskarta,
Umma ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah
mun gode maka ni Sumayya, me xa mu gani haka Nihad" muryan Mumy na rawa tace
"Nihad??" Kawai sai ga hawaye na xuba idonta tana girgiza kai, Wannan ne yasa Nihad
ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace" Kwalban turare da Mumy
ta gani gaban mirror din dakin ta figa tayi kanta amma tuni Nihad ta shige bandaki
ta sa makulli, Umma kuma ta rirrike Mumy tana kuka tace "Aa Maryam ki kai zuciyarki
nesa kiyi ta furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un, nima shi nake yi" A haka ta
ja mumy dake kukan bakin ciki da takaici suka fita daga dakin.
kafin dare kai ka ce mutuwa aka yi a gidan, gaba daya iyalan gidan Alhaji Abubakar
sun iso gidan Abba, makusantan Mumy duk sun xo gidan, Umma ma yan uwanta da
kawayenta duk suna gidan, Aminu sai bin duk wanda ya shigo yake da kallo cike da
mamaki don ba ace masu kowa ya mutu a cikin gidan ba gashi khalil da yake ma gulma
baya nan tun rana ya fita, kowa kuma ya shigo babu walwala yake nufar entrance din
parlor, all the way from Abuja haka Farooq ya biyo flight ya dawo, Usman ma daga
kaduna haka ya taho... Tun faruwan abun nan Umma ke kuka non stop, handkici hudu
duk sun yi jagab a hannunta, Mumy kuwa in ka ganta sai ka tausaya mata she is so
heartbroken, banda kanninta mata biyu da Yaya farooq da suka jibgi Nihad son ransu
babu wanda yayi attempting ta6a ta ko ce mata komai a gidan...... Tashin hankalin
Nihad bai linku ba sai da taga alamar Aliyu yayi blocking dinta ta ko ina,
WhatsApp, IG, Phone call, Twitter, infact all, kawai sai take fatan Allah ya dau
ranta ta huta kawai, gashi har lkcn ta rasa a ina aka mata wannan video din idonta
biyu ba bacci take ba.....


*Ci gaban labari*

A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take yashe da kallo, tsakiyar parlor
ne kuma a kasan Carpet, gashi babu kowa parlon, everywhere looks strange to her, da
sauri ta mike xaune as if trying to recall something, dai dai nan aka bude kofar
wani daki ta juya suka yi ido hudu da shi, sai da numfashinta ya dauke na few
seconds da kyar ta jawo numfashin, lkci daya komai ya dawo mata ta kurma wani uban
ihu jikinta na rawa tana kallonsa, sai kuma ta mike a guje tayi hanyar kitchen
kamar mahaukaciya....




Nan na kawo karshen free pages, sai mu hadu a payment group.

Domin samun ci gaban littafin *Nihaad* it is only 500 via 3276052019 fcmb Hauwa
Bello Jiddah

And u show ur evidence via👇🏻
07087865788
Thank you as u patronize and i am assuring u that Nihad will be counted among my
best In sha Allahđź’–

18
At first tsayawa yayi kamar bazai bi ta ba amma ganin ta kulle kofar kitchen din
yayi saurin bin bayanta, Tsaye ya ganta ta dau table knife tana kuka sosai facing
the knife towards her stomach, ya kalleta daga sama har kasa, sae kuma ya shiga
cikin kitchen din ya dau asalin wuka ya karasa har gabanta ya mika mata yace "In da
gaske kike" runtse ido tayi tana kuka iya karfinta, ya kamo hannunta ya saka wukar
a ciki sannan ya koma bakin kofa ya jingina da wall din wajen ya rungume hannunsa
yana kallonta da wani scorned expression, ta bude ido a hankali ta jefar da wukar
ta sulale kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wayyo na shiga uku na
lalace" sai kuma ta daura hannu a ka ta kurma uban ihu tana kallonsa, juyawa yayi
ya bata waje, Ko sanda aka yi leaking Video dinta bata tunanin tashin hankalinta ya
kai wanda take ciki yanxu, she is still yet to believe who she is seeing, wani ihun
tashin hankali ta kuma kurmawa lkci daya kuma tayi shiru, to ko dai aiko sa aka yi
gidan, tunanin hakan ya sa ta hau share idonta gabanta na bugawa da sauri, lkci
daya tayi assuring kanta kawai aikosa aka yi gidan shine ya shigo masu har ciki, da
kyar ta mike tsaye kamar me tsoron taka kasa ta karasa kofar kitchen din ta leko
parlon a hankali with throbbing heart, zaune ta gansa saman kujera, suna hada ido
ta wani hade rai har sannan gabanta na faduwa tayi karfin halin cewa "Malam idan
aikoka aka yi sai ka shigo ma mutane har cikin nan? Wannan wani irin samun waje ne?
Duk tsakar gida bai isheka ba sai ka shigo har nan" Kallonta kawai yake da wani
stern look a fuskarsa, ta wani kara shan kunu tace "ko shi mai gidan ne ya baka
damar shigo mana har cikin nan?" Ba abinda yace mata still, kuma babu alamar xai ce
mata komai sai ma dauke idonsa da yayi, ta dake ta fito daga kitchen din gaba daya,
tace "Wai baka jin ina maka magana ne ko nan din ma rashin kunyan xaka min?" Yace
"Ok" Yana fadin haka ya mike ya juya yayi hanyar kofar fita daga parlon, wani irin
kwanciya hankalinta yayi, taji ta samu relieve da nutsuwa, sulalewa kan kujera tayi
ta jinginar da kanta da kujerar tare da sauke wani dogon ajiyar xuciya, haba ita
dama ta san aikosa gidan aka yi shine xai shigo ma mutane har parlor saboda samun
waje, shi kam yana fita ya kulle kofar parlon, Nihad ta share hawayen idonta a
hankali tana tunanin to ina wanda aka aura mata din, har yanxu fa bata gansa ba,
mikewa tayi ta nufi hanyar dakuna ta bude wani daki a hankali ta leka ciki taga
babu komai dakin banda katifa, ta kulle ta sake bude wani taga shi ma katifar ce
kawai, toh where is the so called husband, a hankali ta juya ta koma dakin da ta
kwana ta xauna gefen gado, she is just imagining ace abinda tayi tunani daxu a
kitchen gaskiya ne ai da kawai da gaske kashe kan nata xata yi kowa ma ya huta, but
why will she even think that way at the first place, it is something that is neva
and neva going to happen, agogon dake dakin ta kalla taga karfe goma sha daya
saura, har lokacin bata ji tana jin yunwa ba, ita ta ma mance rabonta da cin abinci
a cikinta, tana ta xaune dakin with different thought and imagination a ranta, can
kuma ta mike duk jiki ba kwari tana tafiya a hankali ta koma parlor, windown dake
kusa da kofar parlon ta tafi tana leka compound din, karamin compound ne da xai iya
cin mota uku, ga mamakinta sai ta gansa xaune kan wani dakali a tsakar gidan ya
rike kansa, wani faduwar gaba taji ya dirar mata, but seriously what is this man
doing in this house for God sake, me yake har yanxu bai tafi ba, to ko dai mai
gidan ne yace ya jirasa, this time around ta ma rasa wani takamaiman tunanin xata
yi, duk sai ta birkice taji jikinta na rawa.... amma taki barin ƙwaƙwalwarta ya
fassara mata abinda xuciyarta ke raya mata a lokacin, noooo it can't and will never
be, tasan aikosa gidan kawai aka yi wallahi...... _Har a lokacin da ya gama hada
takalman idon Abba na kansa, ganin xai fita parlon Abba yace "Ibrahim" Juyowa yayi
yana kallon Abba, Abba ya nuna masa waje alamar ya xauna, komawa yayi ya xauna a
hankali yana kallon Abban, Abba ya nisa yace "Kana da mata ne Ibrahim?" Khalil ya
É—an yi jim, amma ganin yanda Abba ya kafe sa da ido yayi saurin girgiza kai yace
"Aa" Abba yayi kasa da murya yace "Ohk! Kana da wani dalilin da yasa baka yi auren
ba har ynxu ko kawai ra'ayinka ne?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Dama da kaka
aka ce xan yi auren idan Allah ya yarda" Abba yace "Kana da yarinyar da xaka aura
ne Ibrahim?" Khalil ya dago ya kalli Abba dake ta kallonsa, sai kuma ya sake
sunkuyar da kai a hankali yace "Aa ban samu ba dai tukun" Abba yayi shiru yana
kallonsa as if thinking of where to start from, kallonsa kawai Abba yake daga sama
har kasa duk da a xaune yake, kamar jikinsa ya basa Abban na kallonsa, sai duk ya
tsargu, upside down ya juya palm dinsa a hankali not wanting to disclose the ring
he is putting on, muryar Abba yaji yace "Ina son xan maka aure, xan kuma yi maka
komai na auren sannan in baka gida ku xauna don na ya6a da nutsuwa da hankalin ka,
bana jin ina da fargaba a kanka Ibrahim.... amma baxan yi hakan ba tare da yardar
ka ba, da kuma yardar iyayenka, ina rokan wannan alfarman a wajenka Ibrahim" Khalil
ya ji komai ya tsaya masa na kusan 10 seconds, lkci daya ya ji he is feeling heat
all over, ya dai yi karfin halin dago kai ya kalli Abba, ganin yanda Abba ke
kallonsa wanda in dai ka san Abba to xaka fahimci yana cikin damuwa wanda baya iya
boyuwa ko min pretence din mutum, Khalil ya kirkiri fara'a a fuskarsa yace "Amma
nagode sosai Alhaji, Allah ya kara girma, Allah ya saka da alkhairi, Nagode Alhaji"
Abba yaji dadin reaction dinsa sosai cause he neva expect that, ya xata xai ce Aa
ko kuma ya kawo wani excuse din, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Ameen
Ibrahim, sai mu je can gun iyayenka yau mu yi magana da su ko? Su ma kuma ina fatan
Allah xai sa su amince" Khalil ya hadiye abu da kyar yace "To ba damuwa Alhaji"
Abba yace "Ka shirya nan da awa biyu mu tafi" Yace "Toh Alhaji" Abba yace "Nagode,
amma sai dai baka tambayeni da warce xan hada ka ba" Khalil kallon Abba kawai yake,
Abba yace "Yar cikina ce ba wata ba, saboda na yaba da komai naka ya sa nake son
hada zuri'a da kai, ni kadai na yanke shawarar nan, kuma idan Allah ya yarda ban yi
abun da xai cutar da kai a gaba ba Ibrahim, xaka yi farin ciki da hadin nan
wataran, kawai tun yanxu ina neman alfarman ka koyi hakuri da ita don yarinya ce,
kuma ita ma nasan watarana xata yi alfahari da xabin da nayi mata, fatana kawai
Allah ya dora ni kan iyayenka" Khalil kam yayi nisa tunanin da yake don bai ma
assimilating maganganun Abba, thousands of thought ne suka yi crossing mind dinsa a
moment din nan, why him of all people, this means disappointing every of his
relative, ko Abba bai fada masa wacece cikin yaran nasa ba ya san wacece, no!!!
they are not and will neva be compatible, how will that even be? Muryar Abba ya
tsinta a tsakiyar kansa ya a ce masa "Xaka iya tafiya, Allah yayi maka albarka" Ko
Ameen din khalil bai iya ya amsa ba ya mike ya kwashi takalman Abba ya fita daga
parlon, lkci daya yanayinsa ya sauya, wasu xufa suka hau keto masa, Yana fita
compound ya nufi mai gadi ya dire masa takalman, Aminu ya mike da sauri yace
"Lafiya na ganka a birkice haka? Me ya faru?" Khalil bai basa amsa ba ya nufi
chalet, har idanuwansa sun kada .... Muryar Nihad ne ya dawo da Khalil duniyar
tunanin da ya fada a tsakar gidan, ya daga kai fuskarsa daure yana kallonta, a
fusace tace "Wai baka ji abinda nake ce maka bane? Ka gaya min uban me ya kawo ka
gidan nan?" Mikewa yayi yace "Ki kira babanki ki tambayesa, don shi ya kamata ya
baki wannan amsan" Kasake tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, har ya juya ya fara
tafiya sai kuma ya juyo, severely yace "Sannan ina me baki shawaran kada ki sake
daga min murya, ko kuma ki sake min wasu tambayoyi a gidan nan" Daga haka ya bar ta
wajen tsaye ya koma cikin gidan walking fast, shikenan abinda take ta hana
ƙwaƙwalwarta fassara mata ya tabbata, shikenan tsoronta da fargabanta ya tabbata,
ta fashe da wani matsanancin kuka me ban tausayi ta sulale kasa ta daura hannu a ka
ta kurma wani uban ihu tace "Na shiga uku na lalace, na banu na lalace, Me nayi ma
Abbana xai min haka, me yasa Abbana xai min haka, me nayi ma yan gidanmu suka min
haka, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka take sosai kamar ranta xai fita, ta
fi minti ashirin xaune kasan interlock ta kasa tashi, she is more than shock, why
her?? Ganin abun ma take kamar a mafarki, Nihad ta ci kuka ta gode Allah a zaune
wajen, daga karshe ta kalli gate din gidan sai kuma ta mike da sauri ta nufi gate
din amma tana kokarin budewa taji key aka sa, sulalewa wajen tayi tana ci gaba da
kuka tana girgiza kanta, nan ma tafi min sha biyar, bata ta66atar da gaske an
tsaneta a gidansu ba sai yanxu, sosai kanta ya fara mata ciwo, jin strength dinta
ya fara karewa saboda kukan da take tayi karfin halin tashi tana layi ta koma cikin
gidan, kitchen ta shiga tana kallon wukar da ya bata ta wurgar daxu, karasawa tayi
ta dau wukar hawaye me xafi na sauka idonta, jingina tayi da cabinet tana kuka a
hankali, to ai in tayi hakan wuta kawai xata, jefar da wukar tayi daga karshe ta
fito parlon tana bin ko ina da kallo hawaye na bin idonta, karamar wayarsa ta gani
saman kujera ta karasa da sauri saman kujeran ta dau wayar ta shige dakin da ta
kwana, xaunawa tayi gefen gado hawaye wasu na bin wani a idonta tayi dialing number
Nihal, tana sa wa sunan Nihal ya fito baro baro, ta kai kunne, yana fara ring ba a
wani dau lkci ba Nihal ta daga, kasa cewa komai Nihad tayi tana kuka a hankali ta
runtse idonta, jin shiru ba ace komai ba cikin sanyin murya Nihal tace "Hello"
Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku Nihal, kinga abinda su Abba
suka min ko, dama ashe har Abba baya so na, dama haka aka tsaneni a gidan nan ban
sani ba? wayyo Nihal wllh da Allah baxai jefani wuta ba yau da na kashe kaina kowa
ma ya huta, zuciyata kamar xata fashe
nake ji yanxu, i can't take this any longer, me yasa su Abba xa su min haka, sun
san ma meye aure kuwa?" Kuka take kamar ranta xai fita, Nihal dai tayi shiru bata
ce komai ba, Nihad na shessheka tace "Pls ki turo min number Husnah yanxu ta nan,
nasan kina da shi send it now plss i need it...." Tana gama fadin haka ta katse
wayar ta fada kan gado tana rera sabon kuka, ko minti daya ba ayi ba Nihad taji
shigowar message a wayar, ta mike xaune da sauri taga number Husnah ne Nihal ta
turo mata, da sauri ta hau kiran number, yana fara ring Husnah ta daga tace "Hello"
Nihad ta rushe mata da kuka tace "Husnah tawa ta kare, Abba na ya tsaneni baya so
na, Husnah kila ma ba su suka haifeni ba wallahi" Da sauri Husnah ta rage volume
din Mp da suka cika a daki tace "Calm down Nihad, kar ki je ki sa ma kanki wani
ciwon mu shiga uku, wllh tsoron xuwa gidan nan naku nake saboda yayanki, babu ta
inda kuma xan san halin da kike ciki tunda bani da number kowa a gidan, Nihal da
nake da number ta tana school

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login