Showing 48001 words to 51000 words out of 268471 words

Chapter 17 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ku ke bari ya xo maku??" Mikewa Mumy tayi ta nufi kofa, Khalil ya
gaisheta da ladabi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhamdulillah" ledan
hannunsa ya mika mata yace "Sakon Hajiya ne" Mumy ta amsa ta juya
ta koma cikin parlon, inna ta hangame baki ganin leda shake da manyan apples tace
"Meye wanan din? a ina naga kudin biyan wannan apple cike a leda, amma dai wawa ne
wannan yaron, maza ciro kwara biyu ga dari biyu ki basa, sauran kuma ya mayar yace
ance baxa a siya ba" Mumy na kallon Inna tace "Wai da na nawa kika ce ya siyo
inna?" Inna tace "Aa ni ban aikesa ya siyo ba, kawai cewa nayi yaje ya tambayo nawa
nawa ne, ni ban aikesa ya kwaso min ba wallahi" Mumy tace "Atoh ina amfanin mayar
da abinda aka riga aka karbo Inna" ko rufe baki Inna bata jira Mumy tayi ba ta mike
ta fixge ledan tace "Ai ba sata nake yi ba da xan siye duk apple din nan, kuma 'ya
yana ba kudin banxa suke samu ba" Tana gama fadin haka ta fita waje da sauri, can
bakin gate ta hango khalil a zaune tace "Yau naga gantalallen mutumi, wa ya bamu
kudin siyan wannan uban apple din, ko don ya ga makeken gida ya zata sata ake yi"
Tana isa kusa da su tayi kasa da murya tace "Ɗan nan cewa nayi ka tambayo nawa nawa
ne, bar ganina haka, wllh rufin asirin Allah kawai nake takama da shi, bani da
komai, maza ka maida masu kace biyu aka aiko ka kaji" Khalil yace "Aa Hajiya na
siya maki ne kawai ki ci" Inna tace "Ka siya min? Ko dai lemo ka kwaso min?" Tana
fadin haka ta kara bude ledan da sauri tana lekan ciki, ai ko taga apple ne ya fi
goma, Inna ta gwalo ido tace "Albashin naka ka kwashe ka siyo min apple din?"
Khalil yayi murmushi kawai, Inna ta rike ha6a tace "Kaii amma wallahi nagode, Allah
yayi maka albarka, ko jikokina babu wanda ya ta6a min haka cikinsu, dari uku uku fa
ake siyar da duk guda daya" Shi dai khalil murmushi kawai yake, Tace "Amshi ledan
mu shiga Maryam ta maka godiya" Da sauri yace "Aa Hajiya" Inna tace "Amsa kawai mu
tafi nace" Amsan ledan yayi tana gaba ya bi bayanta har main parlor, tana ganin ya
tsaya bakin kofa tace "Aa shigo kanka tsaye" Still yaki shiga, Inna tace "Wai ba ni
nace ka shigo ba, ni fa na haifi me gidan" Mumy dake kallonsu tace "Ka karaso"
Shiga parlon yayi da sallama, Inna ta kulle kofa tana nuna ma Mumy ledan tace "Wllh
Maryam ashe siya min yayi da albashin sa, kin dai ga bare ne fa amma yasan kyautata
ma tsohuwa" Mumy tace "Toh Allah ya saka da Alkhairi, maa sha Allah" Inna tace
"Allah sai naji ya fiye min Hamid da su Farooq sau dubu" Mumy dai bata ce komai ba,
Inna ta rike ha6a tace "Allah yayi maka albarka ka ji" Yace "Ameen Nagode" Bude
kofar parlon aka yi Nihad ta shigo, still tayi bakin kofar tana kallon Khalil da
mamaki, sai kuma ta kalli Inna da Mumy tace "Me wannan kuma yake yi har cikin
parlor?" Mumy tace "Uwarki yake yi" Nihad ta hade rai tace "Mumy parlon mu fa,
privacy dinmu, this is uncalled for gaskiya, ko su Aminu da suka yi shekara da
shekaru a gidan nan xa a bari su shigo nan balle wannan driver din..." Mikewa Mumy
tayi tana ganin haka tayi hanyar stairs da sauri, Mumy bata fasa bin ta ba, Inna
tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace "Wallahi duk hakuri muke da ita, duk ta
fi karfin kowa in gaya maka, shi yasa kwanaki da ta je ta kai karar ka gu na wai in
sa a kore ka nace waa? Me ka min xan maka sanadin aikin ka, wllh naki biye mata
shine ta kullace ni har yau, dama dai bansan mugun halinta bane shine xan biye mata
amma ai kaga ban biye mata ba gashi har yanxu kana aikinka cikin rufin asiri har da
siyo min apple, ni duk inda harkar rashin gaskiya take ba ni a ciki, Nihad kam bata
da gaskiya wllh" Khalil dai kansa na kasa, Inna tace "In ji suna baka abinci
isasshe dai?" Yana murmushi yace "Ehh ana bamu" Inna tace "Toh shkkn, can gidan
Habubakar din ma ka iya dinga xuwa kullum, ai yanxu kam ka zama Ι—an gida" Murmushi
yayi yace "Nagode Hajiya" Tace "Yauwa je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon. Da
daddare Nihad na kitchen tana pancake da xata ci kafin ta kwanta Sudais ya shigo
kitchen din, cup din hannunsa ya ajiye a sink yana kallonta yace "Lahh Aunty Nihal
ma tace mana tayi pancake ta ci yau a makaranta" Nihad na juya pancake dinta ba
tare da ta kallesa ba tace "Did u spoke with her today?" Yace "Yess, Uncle driver
ne ya kira mana ita, muna ta magana da ita for long" Juyawa Nihad tayi ta ajiye
spatula din hannunta tace "Who is uncle driver?" Yace "Wannan da yake kai mu
school" Ta bude baki, sai kuma tace "Yaushe ya kira maku ita?" Sudais yace "After
magrib prayer" Sake baki Nihad tayi tana kallonsa, jin kaurin pancake dinta ta
kashe gas din da sauri ta fita daga kitchen din, sama ta tafi bangaren Umma, har
bedroom ta shiga ta sameta tace "Umma kinsan da wa Nihal ke waya yanxu?" Umma tace
"Wa?" Nihad tace "Wai driver, yanxu su Sudais suke ce min ai ya kira masu ita,
ranan da xa mu je shopping ne fa ya amshi numberta, toh a ranan da xa mu kai ta
school ma ya kirata ya fi a kirga, sai ga yanxu su sudais suka xo suna gaya min ai
driver ya kira masu ita" Da wani expression Umma tace "Driver? Wani drivern ni
Sumayya?" Nihad tace "Driver dae da kika sani" Umma tace "Ko dai Nihal ta fara
hauka ne?" Nihad ta kyabe baki ta zauna gefen gado, Umma ta dau wayarta ta hau
kiran Nihal, yana fara ring Nihal ta daga, Umma tace "Nihal kiran me ku ke yi ke da
drivern gidan nan?" Nihal tace "Driver kuma?" Umma tace "Ban sani ba" Nihal tace
"Wallahi ba komai Umma kawai wani lkcn yana ba su Sudais ne mu yi magana da su"
Umma ta kunduma mata zagi tace "Kanin uwarki ko na ubanki? Banda xubar da aji meye
na wani waya da drivern gidanku? Sa'anninki na waya da mutanen arxiki ke kina waya
da driver, ke wace irin yarinya ce? to wllh xan ci kaza kazanki idan baki kama
kanki kin goge number tasa ba, kaji min gantalalliya dai" Nihal dai tayi shiru,
Umma tace "Na dai gaya maki tun wuri ki goge number nan ko in ci maku ke da shi"
Umma na kai wa nan ta katse wayar, sosai ranta ya baci, ita kam wace irin yarinya
ce Allah ya bata, duk abun kaskantar da kai ta iya shi, banda haka meye ya kai ta
dinga waya da driver, Nihad tace "Wllh Nihal is so annoying, how comfortable is she
making call with that wretched man" Umma tace "Ki kyale mahaukaciya mana" Nihad ta
mike ta tabe baki ta fita daga dakin, Zaga dakin Umma ta dinga yi. Nihad na gama
pancake din ta shiga bangaren Abbanta, bayan ta gaishesa tayi shiru saboda Mumy
dake zaune a parlon, Abba ya kalli Mumy, murmushi kawai tayi ta mike ta bar masu
parlon, Abba na kallonta yace "Ya aka yi daughter?" A hankali tace "Abba na tambayi
wata kawata gyaran screen din wai 150k ne" Abba yace "Har 150k?" Ta marairaice tace
"Eh Abba" Shiru yayi, can yace "Ohk gobe zan tura maki, amma baxa ki wajen gyaran
ke kadai ba, ko ku je da farooq?" Da sauri tace "Aa Abba ba kace driver ba?" Abba
yace "Ohk, no problem sae ku je tare, kin gyara account din naki ne?" Tace "Aa sae
next week, I'm busy with lectures throughout this week" Abba yace "Ohk xan sa kudin
a account din Farooq sae ya baki" Ta hadiye abu da kyar sai kuma tace "Abba driver
din bashi da account?" Abba yace "No I don't know" Tace "Abba idan yana da shi
kawai ka sa mashi tunda tare xa mu, ba sae ka tura ma ya Farooq ba" Yace "Ohk,
Allah ya kai mu goben" tace "Ameen" mikewa tayi bayan ta ma Abba sae da safe ta
fita tana Murmushi, tana da kusan 70k a account dinta, ga kuma dala dari biyu da
Aliyu ya bata, now with additional 150k from her father, latest iphone is sure
gobe. Washegari Nihad na ta kallo ta window har Khalil ya tafi ajiye su Amina a
makaranta, Hijab ta saka har kasa ta sauko, gun Aminu ta nufa yace "Barka da Safiya
Hajiya" Tace "Aminu ina son tambayarka ne don Allah" Aminu yace "Toh Allah ya sa na
sani Hajiya" Tace "Yaron nan Driver yana da account number ne?" Aminu yace "Anyaa,
gaskiya ban ta6a jin yace xai cire kudi ba" Ta ta6e baki tace "Okay" Juyawa tayi ta
koma ciki, tun jiya take avoiding ya farooq wannan ne ma yasa ta ki zama a parlor,
ta koma dakinta tana jin dawowar Khalil ta sauko kasa da sauri, hade rai tayi ganin
Ya Farooq a parlor ta gaishesa tayi ficewarta ba tare da ta jira ya amsa ba, Direct
wajen khalil ta nufa babu yabo babu fallasa tace "Ehm ya ma ake kiranka? Abbana
yace ka bada account number" Khalil ya kalli Aminu kamar dai yana jiran Aminu ya
bata amsa, a fusace tace "Malam ai ba Aminu xaka kalla ba, da kai nake ni xaka
kalla" Ya kalleta yace "Ohk, bani da account" Ta masa wani kallo tace "I thought as
much" sai kuma ta ja tsaki ta juya ta koma ciki, Aminu yayi kasa da murya yace
"Alhaji fa ya tambayi account din naka kasan ko ihisani xai maka" Khalil ya girgiza
kai yace "To ai bani da account din ne" Aminu yace "Kashh" Nihad ta daidaici lkcn
fitan Abbanta ta fito parlor da sauri yana ganinta yace "Yauwa kin amso account
din" Tace "Abba bashi da shi, kawai ka sa a na kawata Husnah ita ta ma san wajen
gyaran don nata ma ya ta6a lalacewa kamar nawa, don haka ita xata raka mu" Yace
"Okay, forward the account to me via Sms" Tace "Toh Abba nagode, Allah ya kara
budi" Yace "Ameen" Daga haka ya fita parlon Mumy tayi masa Allah ya tsare, Umma na
tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, Bayan fitan Abba Nihad ta juya da sauri
xata bar wajen Mumy tace "Zo nan me xa a gyara?" Tace "Mumy laptop dina ne yake
bani matsala shine xai tura min kudin gyara" Mumy tace "Toh amma lallai sai an sa
kudi account din Husnah? Me yasa baxa ki je ki gyara account dinki ba, kuma nace
maki bana son alakar ku da yarinyar nan kin ki ji, wai sai na fara nakada maki duka
a gidan nan xaki nutsu Nihad?" Nihad ta marairaice tace "Mumy Coursemate dita ce
fa, dole muna haduwa a class ko ban kulata ba ita tana kulani kuma ita kadai tasan
inda ake gyara laptop din nan tunda nata ma ya ta6a lalacewa" Farooq yace "Dauko
laptop din naki da ya lalace ki kawo min" Juyawa tayi ta kallesa, Umma ta karaso
parlon tace "A saboda ka fara gyaran laptop??" Mumy tace "Ta dai je ta dauko masa
laptop din da ya lalace" Umma tace "Toh naga ai ba shi ya bada kudin gyaran ba da
xai hau tuhumarta" sum sum Nihad ta wuce sama, cikin lkci kankani ta shirya ta dau
jakar laptop dinta ta fito, Umma kadae taje tayi ma sallama Umma tace "Toh Allah ya
tsare daughter" Aminu ya
kalli Khalil bayan ta fita yace "Kai fa yanxu huta roro, adaidaita take hawa xuwa
duk inda xa ta." Nihad bata dawo gida ranan ba sai da sabon Iphone dinta dal a
kwali, babu wanda ta sanar ma ta canza waya banda Nihal da Umma, Umma na jujjuya
wayar tace "Gaskiya ne er daddy, yanxu duk kawayen naki su ma irin wannan ke
hannunsu kenan?" Nihad ta washe fararen hakoranta tace "Ehh wllh Umma, shi yasa
nima na dage sai da na canza, ai abun kunya ce ace ni kadai ce ban canxa waya ba a
cikinsu" Umma tace "Ai ko kina da gaskiya abun ki" Nihad tace "Umma kinsan me?"
Umma tace "Aa sai kin fada" Nihad tace "Umma xa mu fara exams nan da kamar sati uku
kuma wllh ina son in koma hostel don in dinga karatu sosai, nasan Mumy da Ya farooq
xa su xuga Abba kuma baxai bari in koma ba, pls ko xaki taya ni convincing Abbana?"
Umma tace "Gaskiya ya kamata ki koma hostel din don ki maida hankali kiyi karatu
sosai, amma kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Zan ce ma Abbanku Mijin
Kamila xai yi tafiya kasar waje kuma xai yi kusan wata biyu a can, tace ki je ki
dinga tayata kwana idan ya so daga can sai ki dinga xuwa makaranta, ita ma Kamilan
xan sa ta kira Abban naku" Nihad ta wara ido cike da farin ciki tace "Yauwa Ummana,
wannan shawarar taki tayi wllh" Umma tace "Kinga kawai daga nan sai kiyi komawarki
hostel har sanda xa ku gama jarabawan, babu wanda xai san baki gidan Kamila" Nihad
tace "Ai kuwa Umma, don Allah gobe da safe kiyi ma Abba maganar da wuri, on
Thursday ma nake son in koma ni dai" Umma tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu
goben, ai gobe Wednesday" Nihad ta fita dakin cike da farin ciki, shi yasa take son
Umma, haba she will be free for a while, babu me takurata. Da safe babu wani bata
lkci Umma tayi convincing Abba, yace "Toh Allah ya kai mu alhamis din" Umma tayi
murmushi tace "Ameen Yallabai, sai kayi ma Maryam magana da kanka ko?" Yace "Aa
kema xa ki iya yi mata ai, menene a ciki" Umma tace "Aa gwara dai kai kayi mata,
kace mata Kamila ce ta roki alfarman Nihad ta koma wajenta na kwana biyu mijinta
xai yi tafiya" Abba yace "Ohk, amma suna da driver ne a can da xai dinga dropping
dinta school?" Umma tace "Anya, da yake kasan shi yake ajiye kamilan duk inda xata
je" Abba yace "Toh duk safiya sai Ibrahim ya dinga xuwa can yana daukarta ya ajiye
ta makaranta, when ever her lectures is terminating sai ta gaya masa yaje ya
dauketa ya maida ta gida" Umma tace "Hakan ma yayi kam" kafin Abba ya fita aiki ya
shiga bangaren Mumy, nan ya sanar mata abinda Umma tace masa, Mumy tayi shiru
alamar ta ma rasa abinda xata ce, Abba yace "Sai ki gaya ma Nihad din ta fara
shiri" Mumy ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Alhaji idan Nihad taje gidan
Kamila babu me kwaba mata, kasan ta da rawan kai fa, tana nan gida ma ya aka karke
balle bata gida" Abba yace "So what are u insinuating?" Mumy ta girgiza masa kai
kawai, Abba yace "Kar taje ta taya er uwartata xama kenan?" Mumy tace "Ko daya ba
haka nake nufi ba" Abba yace "Toh Maa sha Allah, gobe alhamis ta shirya ta koma can
gidan" Daga haka ya fice daga parlon, har ran Mumy bata son xuwan Nihad gidan
Kamila amma to ya xata yi? Hakan ya sa ta tunani iri iri.




Barka da sallah fams, Allah Ubangiji ya maimaita mana


✍🏻
07087865788


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–



17
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




Har daki Umma ta tadda Nihad tace "Toh Abbanki ya amince sai ki fara hada kayanki"
Cike da farin ciki Nihad ta mike ta rungumeta tace "Nagode sosai Umma" Umma tace
"Sai dai fa Abbanki yace driver xai dinga xuwa duk safiya yana daukarki ya kai ki
makarantar sannan idan kun gama lectures ya maida ki gida" Nihad ta zaro ido tace
"Toh Umma ya xan yi?" Umma tace "To na dai amsa ma Abbanki, amma ke yanxu sai ki
samu Drivern kice masa ba sai ya je ba, xaki dinga tafiya da motar Kamila, should
Incase Abbanki xai masa magana...." Nihad tace "Toh shkkn Umma" Umma tace "Xaki
makarantar yau?" Nihad tace "Ehh ina da lectures karfe sha biyu" Umma tace "Da
sauran lokaci ai, sai ki fara harhada kayanki against tomorrow..." Daga haka Umma
ta juya ta fita dakin, Murna a wajen Nihad ba a cewa komai, she is going to have
enough freedom yanxu, wanka ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta shirya, bayan
ta shirya ta fita xuwa bangaren Mumy, Mumy na gyaran bedroom dinta Nihad ta jingina
da kofar dakin da damuwa tace "Mumy kin ji abinda Abba yace?" Mumy ta kalleta tace
"Na me kenan?" Nihad ta marairaice tace "Mumy ni ba son zaman gidan Aunty Kamila
nake ba, it's so boring there, ni kuma ban san ya xan yi ba" Mumy tace "Then u
speak for ur self Nihad, ni me kike son ince a nan?" Nihad tace "I don't Know what
to tell Abba" Mumy tace "Ki nemi abinda xaki ce masa ai baxai maki tilas sai kin ji
ba" A hankali Nihad tace "Toh" Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakinta, hada
kayanta ta shiga yi a akwatunan ta cike da farin ciki, bayan ta gama ta sauka
downstairs tayi breakfast, sae wajen karfe sha daya da rabi ta fita gidan zuwa
makaranta ranta fari sol, yau ma dai adaidaita Sahu ta tafi ta hau bata bi ta kan
Khalil ba, su Husnah da Naf har sun fi ta murna da ta sanar masu xata dawo hostel
ta kuma gaya masu irin plan din da Umma tayi ma Abbanta, Husnah tayi shewa tace
"Kai amma Allah ya shi ma wannan Umman albarka, Allah tana sonki sosai, ta san kan
komai..." Nihad tace "Ke dai bari, ba don ita ba i will keep on being miserable in
that house ga Yaya Farooq ga Mumy, the house is already a living hell for me, yanxu
gobe xan taho da kayana hostel, har na gama hadawa kafin in fito" Husnah tace "Kuma
albishirin ki, kin san saurayina ya kama mana tsadadden hostel a off K, xuwa next
week xa mu koma wllh..." Nihad tace "Haba dai" Husnah tace "Wallahi, dama ina ta
son xan gaya maki sai in manta, yanxu kinga Da ni, ke, Naf, Zully, da Ummi xa mu
xauna dakin, ita Ummi part time xata dinga xama kinsan tafi zama wajen saurayinta
sai in baya gari ne take xuwa hostel" Nihad tace "But bamu yi yawa ba Husnah?
Kinsan fa bana wani son takura a rayuwata" Naf dake danna wayarta tace "Kin ji ki,
2 bedroom ne fa sannan har da parlor with two toilet, ai baki kai ni rashin son
takura ba" Nihad tace "Ohk that's enough...." Kamar shekaranjiya da jiya yau ma dai
haka suka shiririce a Cafeteria babu wanda ya shiga lectures cikinsu, daga karshe
ma suka fita xuwa cin pizza a cikin gari, suna wajen cin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login