Showing 6001 words to 9000 words out of 268471 words

Chapter 3 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

daki da bandaki, sae
bandakin dake parlor sai kitchen, anyi furnishing gidan babu laifi sai dai
furnitures din ba masu tsada bane, Nihad ta dinga kuka tana cewa ta shiga uku, masu
bata bakin ma har sun gaji sun daina, karfe tara saura suka fara shirin tafiya,
Nihad ta rike hannun Kamila cikin kuka tace "Aunty ynxu tafiya xa ku yi ku bar ni,
don Allah kar kuyi min haka..." Kamila tayi dariya tace "Ae ko dole xa mu yi maki
haka tunda mun kawo ki gidan mijinki kinga ni ynxu sae na koma xan dau jakata inyi
driving xuwa gida, kawai kiyi hakuri ki bi mijinki ku xauna lafiya ko hakan xai
goge wannan ta6on da kika ma kanki" Daga haka ta fice daga dakin don dama ita ce
karshen fita, Nihad ta silalo kasa ta xauna tana kukan takaici, tana jin duk suka
fice daga gidan ta daina jin hayaniyar kowa, nan kuma tunanin ta ya tafi gun wanda
xata gani a matsayin mijinta, tsoho ne, yaro ne, baki ne, fari ne, kato ne, siriri
ne, mummuna ne, kyakkyawa ne, infact duk wannan tunanin ne suka baibaye ranta
gabanta ya dinga faduwa hankalinta ya kara tashi, daga karshe ma daina kukan tayi
banda bugawa babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti ashirin a haka taji an bude
gate, da sauri ta mike ta tafi gun window ta bude labule amma sai taga ba ta nan
gate din ma yake ba balle taga me shigowa, komawa tayi ta xauna can karshen gado
tana jin yanda kirjinta ke heaving, to waye wannan da ko mota ba shi da, bayan wasu
mintuna taji an shigo parlor, daga karshe ta ji kamar an bude wani daki an shiga,
mikewa tayi ta jingina da window with so much fear, har ta gaji da tsayuwa bata ga
alamar xa a shigo dakin ba, komawa tayi ta xauna gefen gado, a kan idonta karfe sha
daya tayi, bacci take ji amma taki kwanciya sbda fargaba, kafin sha biyu bacci
barawo ya saceta. Ba ita ta bude ido ba sae da hasken rana ya sauka saman fuskarta
washegari da safe, a firgice ta mike xaune, sae kuma ta sauka daga saman gadon ta
shige bandaki da sauri, bayan ta idar da sallah ta mike a hankali ta nufi kofar
dakin ta bude ta fita xuwa parlor, ta dinga bin ko ina da kallo xuciyarta na
bugawa, kofar da take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali, wani kara
ta saki ba tare da ta shirya ba ganin mutum a tsaye yayi backing kofar kitchen din
ga ruwa ya daura saman gas, juyowa yayi suka yi ido hudu da ita, wani irin shock ne
ya bayyana a fuskarta ta dinga komawa baya tana kallonsa bakinta ya kasa furta
komai, can ta nunasa da yatsa nan ma words suka yi failing dinta, juyawa yayi ya
kashe gas din don ruwan ya fara tafasa ya juye cikin mug sannan ya bi gefenta ya
fice daga kitchen din ba tare da ya sake kallonta ba, makalkalewa tayi jikin kofa
jikinta na 6ari tana ganin abun kamar a mafarki, sae a sannan bakinta ya bude ta
fasa wani raxanannen ihu, sai kuma ta fara ganin kitchen din na juya mata lkci daya
ta sulale kasa....




_8 months earlier_


Contact me directly via👇🏻 to gain access to the book

✍🏻
07087865788

3
💖💖 NIHAAD💖💖




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_



~~~


Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga sauran membobi yan gurmin Khaleesats Palace, don
gurminsu ya hana in saka sunansu jiya inga ta tsiya, Su Hajiya Aisha Bela, Hajiya
Suwaiba, Hajiya Safiyya Usman😂 Hajiya Mardiyya mandy rice😜, Hajiya Sadiya uwar
Hanan, Uwar Sa'eed, Hajiya Farida me kayan en gayu, Amzaj, Hajiya Zaarah, Wata ana
ce mata me kayi nayi, Hajiya Aisha Macika, Hajiya Billy, Uwar Habee, har dai da
wata me gawayin dare, duk na gaisheku kyauta... Sauran da basu ga sunansu ba a
tsakiyar rubutu xa su gani😁



8months earlier...



Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune
wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da handkerchief din hannunsa, karamar
waya ya fiddo aljihunsa yana duba agogo dake nuni da karfe biyar da rabi, ya juya
ya kalli mai gadi dake xaune gefensa da radionsa a hannu, xai yi magana aka danna
horn, da sauri mai gadin ya ajiye radion ya mike ya isa bakin gate din gidan ya
bude, wata rantsantsiyar mota ce ta shigo compound din, mutumin dake xaune ya bi
motar da ido har ta isa kantamemen space da aka tanadar don parking a compound din,
mai gadin ya dawo bayan ya maida gate din ya rufe yace "Bari in sanar masa kana ta
jira kar ya shige ciki kuma" Daga haka ya nufi parking lot din ya jira har dattijon
dake cikin motar ya sauko yana gyara babban rigar jikinsa, da ladabi me gadin ya
risina yace "Barka da isowa Alhaji" Alhaji Ibrahim yace "Yauwa Aminu... " Mai gadin
yace "Alhaji dama Habibu ya taho da baƙon tun daxu, shi har ya ma tafi yace yau xai
koma, baƙon kuma gashi can yana jiranka tun karfe biyu" Alhaji Ibrahim ya kulle
motar tasa yace "Ohk, to ya karaso" Mai gadi ya koma gun mutumin dake xaune saman
farar kujera da sauri yace "Kaje nayi masa magana" Tashi mutumin yayi ya nufi
parking space din, yana isa ya duka har kasa yana kallon Alhaji Ibrahim yace "Barka
da yamma Alhaji" Alhaji Ibrahim na kallonsa yace "Yauwa kai ne wanda Habibun ya
kawo kenan?" Mutumin yace "Eh ni ne" Alhaji yace "Ya sunanka?" Mutumin ya sauke
idonsa daga kallonsa yace "Sunana Ibrahim" Alhaji Ibrahim ya jinjina kai yace "To
madallah, amma ya ku ke da Habibun?" Mutumin yace "Garinmu daya da shi, ga gidanmu
ga gidansu, babana aminin mahaifinsa ne" Alhaji Ibrahim yace "To ba laifi, ai har
garin naku naje watanni da suka wuce" Shi dai mutumin bai ce komai ba, Alhaji
Ibrahim yace "Shkkn babu damuwa, amma kayi karatu ne?" Mutumin ya girgiza kai yace
"Aa iyakata sakandari, shi ma ban zana waec ba" Alhaji Ibrahim ya daga kafada yace
"Ohk, xuwa kake ganin xaka dinga yi kullum ko kuma yaya tsarin naka yake?" yayi
kasa da kai yace "Duk yanda ka tsara haka xa ayi Alhaji" Alhaji Ibrahim yace "Kaje
dai gobe da safe ka dawo, ni yanxu xan shiga ciki in huta ne, dawowata daga aiki
kenan..." yace "Toh nagode kwarai Alhaji, Allah ya kara girma" Tuni Alhaji Ibrahim
ya nufi main entrance din shiga gidan nasa, ya mike ya bi sa da kallo, sannan ya
kalli building din gidan wanda duplex ce gari guda, juyawa yayi ya koma gun mai
gadi, mai gadin na ganinsa yace "Ya ake ciki?" yace "Yace in dawo da safe" Mai gadi
yace "Ahaf ai ka ma samu, tunda ta hannun Habibu ka biyo, ai Alhaji sun fi shekara
goma sha biyar da Habibu, har kauyensu ya je daurin aurensa kwanaki, in dai baka da
rawan kai sannan uwa uba ace kana da nutsuwa gun aikinka to wllh tuni Alhaji xai ja
ka jiki ka xama kamar d'an gida, ba ga mu ba duk mun dawo kamar yan gidan banda dai
ba halinsu daya da wasu daga ahalin gidan nasa ba, to ya sunan naka?" Mutumin yace
"Sunana Ibrahim" Mai gadi ya rufe baki yace "Yo ai sunan Alhajin kenan" yace "Allah
sarki, Sai goben in sha Allah, xan tafi ynxu" Mai gadi yace "Allah ya kai mu" Gate
ya nufa ya fita daga gidan. Alhaji Ibrahim ne xaune parlonsa, daga gefensa matarsa
kuma amaryarsa Hajiya Maryam, Wasu yan mata ne biyu xaune daga kasa saman lallausan
carpet dake malale parlon, Hajiya Maryam tace "Ayi hakuri Alhaji in sha Allah hakan
ma baxai sake faruwa ba, ita ma Hajiya nasan bata fahimce su bane, amma xa su je su
bata hakuri" Alhaji Ibrahim na kallon yan matan yace "Ku tashi ku bani waje" Duk a
tare suka ce kayi hakuri Abba, yace "Ku fita nace..." Mikewa suka yi a tare suka
fita daga parlon, daya daga cikin yan matan tace "Gaskiya ni ki daina ja min Nihad,
ko me kika yi sai a hada mu a mana fada, da na sani da ban biki ba jiya, haba don
Allah" Tsaki er uwar tayi mata ta bi wani corridor tayi gaba abunta irin ko damunta
abun bai yi ba. Wata mata ce da baxata haura hamsin da bakwai ba xaune wani
lafiyayyen parlor da ba a cika da kaya masu hayaniya ba, cike da ɓacin rai tace
"Toh banda ma fitina da neman magana irin naku dole ne sai kun je? Me yasa baxa ku
xauna inda Allah ya ijiye ku ba, maganinku kenan" Nihad tace "Ae wllh daga yau ko
Abban ne yace mu je ni dai sai dai in fita inyi using opportunity din in xaga gari
in sha iska in dawo abu na, i don't care... baxan sake xuwa ba gaskiya" tana kai wa
nan ta mike ta dau wayarta dake caji ta fita daga parlon, Hajiya Sumayyah tace
"Atoh dai, da ya fi maku, don dama magana ta ce kawai bakwa ji banda haka na hanaku
xuwa tun ba yau ba" Ita dai er uwar Nihad na kwance saman kujera bata ce komai ba,
Hajiya Sumayyah ta bude kofar bedroom dinta ta shiga ta kulle. Washegari asabar
kasancewar yan matan gidan basu da lectures duk suka yi shirin tafiya islamiyya
amma banda Nihad dake kwance parlon step mum dinta tana aikin danna waya, Hajiya
Sumayyah da suke kira da Umma da tace "Ke Nihad kina kallon lkci kuwa, ko baxa ki
islamiyyan bane yau ma?" Nihad tace "Umma sai gobe i have something important to
do" Umma tace "To ita Nihal ma cewa tayi ba xata ba?" Bata rufe baki ba sai ga
Nihal ta shigo har ta gama shiryawa, Umma ta kalli Nihad bata dae ce komai ba ta ci
gaba da abinda take, Nihal tace "Hope u are been cautious of time Nihad?" Tashi
Nihad tayi ta fita daga parlon tana cewa "Ni sai gobe" Mai gadi ne tsaye tare da
mutumin da ya xo jiya, bayan sun gaisa mai gadin yace "Yanxu xaka ga Alhajin ya
fito xai tafi gun motsa jiki, don ma yau bai fito da wuri ba, amma dai bari in
sanar masu a ciki kar kuma ka yi ta jira haka babu dadi" mutumin yace "To nagode"
Xaunawa yayi kan farar kujera yana bin compound din da kallo don ya kayatu da
kyawawan shukoki na flowers har ma da artificial flowers, daga can wani gefe wani
karamin water fall ne me ban sha'awa ruwa na ta xuba ga artificial crocodiles da
kifaye a ciki, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo yace "Ka ga wancan yar barandar?"
ya kalli inda yake nuna masa yace "Eh na gani" Mai gadin yace "Toh kaje can kayi
jiran alhajin, akwai kujeru ma a wajen" Tashi yayi ya tafi wajen yana bin ko ina da
kallo, bayan kujeru masu kyau har da carpet grass malale a kasa daga gefe, ga
artificial flowers da ya kawata wajen, ya xauna saman daya daga kujerun wajen
surveying everywhere with his eyes, bayan kusan minti sha biyar aka bude kofar
parlon, tsaye tayi tana kallonsa daga sama har kasa a bit flabbergasted, ya kalleta
yayi kasa da kai yace "Ina kwana" tace "Wa kake nema Malam? Daga ina haka?" Yace
"Mai gidan nake jira" ta fi minti daya tana masa kallon sama har kasa, ta ma rasa
me xata ce, sai kuma ta sauka kasa xuwa compound din ta tafi gun mai gadi da sauri,
yana gaisheta ta ki amsawa tace "Aminu waye wancan aka bar sa xaune a kofar shiga
parlor? Waye wannan?" Yace "Ranki shi dade baƙon Alhaji ne wanda Habibu ya kawo
jiya, shine sabon...." Ta gwalo ido ta dakatar da shi da sauri tace "Haba Aminu,
Haba Aminu, yanxu kai rashin hankalin naka ya kai haka, a tunaninka ya kamata a bar
sa yaje har can ya jira Abbanmu, privacy din mu ne can din fa? ga dai kujeru a
compound amma har sai yaje balcony kamar xai shiga parlor, a ina aka ta6a haka?"
Aminu yayi kasa da murya yace "Wannan gaskiya ne Hajiya, ayi hakuri anyi kuskure
kam, ayi hakuri" Tace "To tun wuri ka tafi kace ya dawo nan kusa da kai ya xauna ya
jira Abban" Aminu yace "Toh Hajiya" tabe baki tace "Ni dama tambayarka xanyi hope
jiya baku mance feeding din tsuntsaye na ba?" Ya washe baki yace "Haba dai Hajiya,
ai kullum safe rana da dare sai Saminu ya basu, yau ma da asuba ina kallo yaje ya
xuba masu" tace "Yauwa toh nagode, bari in je in duba su, shekaranjiya da jiya duk
bama nan ban gansu ba" Yace "Da yake sai dare ku ka dawo jiya din ma" Tace "Eh fa"
daga haka ta wuce ta xaga ta inda tsuntsayen suke a backyard din gidan wanda nan
dinma duk shuke shuke ne, ta fi minti bakwai tana kallon kyawawan tsadaddun birds
din nata ko wani breeds a cage dinsu daban, birds din iri hudu ne ko wanne me kyau
har kuma da Aku a ciki, ta tafi gun akun da aka yi Seperating da sauran tace "Hello
cutie" The bird was only chirping and flying around the little cage alamar he
appreciates seeing her, bayan wani lkci ta bar wajen xata koma cikin gida, tsaye
taga Abba a balcony bakon nasa kuma ya sauka daga saman kujera ya durkusa kasa yana
sauraren Abba, kallonta kawai Abba yake da mamaki yace "Nihad ke baxa ki islamiyyan
bane?" Tayi gathering courage tayi kasa da murya tace "Abba assignment nake typing
anjima xan yi submitting via...." Abba ya dakatar da ita yace "Why are u skipping
Islamiyya this days Nihad, last week ma na ga baki je ba ko, hakan ba dai dai bane
dear" Sunkuyar da kanta tayi bayan few seconds ta dago, kallon mutumin dake
kallonsu ita da Abba tayi, ta wani daure fuska wondering why he was looking at
them, tana tafiya a hankali ta shiga parlor ta kullo kofar, bayan minti shidda aka
sake bude kofar, har sannan Abba na tsaye speaking with the man, su uku ne duk
sanye da hijab din islamiyya har kasa, Abba ya kallesu, sai kuma yace "Ke xaki yi
driving din?" Tace "Eh Abba ga makullin" Amsa yayi ya mika ma mutumin dake durkushe
gabansa yace "Ka ajiyesu a makaranta, xan jira ka har ka dawo" Ya amsa da ladabi
yace "Toh Alhaji" shi ya fara sauka Balcony din, Autan Mumyn Nihad da ake kira da
Sudais yace "Abba is he our new driver" Abba yace "Yes he is sweetheart" Duk suka
yi ma Abbansu sallama suka sauka xuwa parking lot, sai da suka tsaya dai dai motar
xuwa makarantarsu sannan drivern ya nufi motar shi ma, bayan ya bude duk suka shiga
back seat, ya shiga ya tada motar yana warming, shi dai Abba na tsaye balcony har
sannan yana kallonsu, Drivern na warming motar yaji ance "Ina kwana" ya daga kai
yana kallonta ta madubi da mamaki, sai kuma yace "Ina kwana" Bayan wasu yan mintuna
ya ja motar suka bar gidan xuwa islamiyyan nasu with Fadil and Sudais directing
him. Parking yayi bakin gate din islamiyyan, Nihal ta bude motar ta sauka su Fadil
ma duk suka sauka, bayan ta kulle motar ta kallesa tace "Sai anjima" Yace "Sai
anjima Hajiya" Suka shiga makarantar, reverse yayi ya bar wajen har sannan bai
daina mamaki ba. Yana isa gidan bayan mai gadi ya bude masa gate ya shiga yayi
parking ya kashe motar ya sauka, gun mai gadin ya nufa ya xauna, Mai gadin yace
"Inji ka yi kumallo dai?" Driver yace "Aa" Mai gadin yace "Toh bari inyi ma mai
aikin gidan magana in amso maka" Daga haka ya nufi backyard din gidan xuwa kofar
kitchen dake baya, Drivern dai na xaune yana ta juya makullin motar hannunsa sai ga
mai gadin ya dawo da plate din dankali da kwai da kofin shayi, ya amsa yace "Nagode
sosai" slice din bread ne biyar a gefen irish din da kwai wanda aka matsa ketchup a
gefe shi ma, irish din ya fara ci yana dangwalawa da ketchup din, Mai gadi yace
"Amma xaka dinga tafiya ne da daddare ka dawo da safe ko gidan nan xaka tsaya?" ya
kallesa yace "A ina xan tsaya a nan din?" Mai gadi yace "Ka ji ka, Yo ai har Habibu
ya gama yayinsa a gidan nan kafin Alhaji ya bude masa shagon da ya bude masa na
tayoyi a gidan nan yake komai nasa, duk tare muke, ga can boyis kwata, su Saminu da
Shafi'u masu gyaran pulawa da sharan tsakar gida da Isiya me wanki da guga ai a nan
suke duk" ya dau cup din shayin ya kurba yace "Dakin babba ne?" Mai gadin yayi
dariya yace "Wai daki, to har parlor akwai a ginin, sannan dakuna uku ne ko wanne
da bandaki, kai har ma da kitchen a nan din" yace "To shikenan" Aminu mai gadi yace
"Kai ma kayi xamanka kawai a nan xa ka fi gane kan albashin naka, kaga babu xancen
kashe kudin abun hawa xuwa da tafiya sannan xa a ciyar da kai a nan ba sae ka siya
komai da neran ka ba, duk abinda yan gida suka ci a nan shi mu ma muke ci" Shi dai
bai ce komai ba ya gama cinye irish din tass sannan yace "Toh xan xauna nan din in
sha Allah, nagode da kulawa" Ganin ya ajiye plate din Aminu yace "Ya haka, naga
baka ci kwan ba? Yanxun nan fa ta soya maka" Ya girgiza kai yace "Bana so" Aminu ya
dau plate din yana kokarin cin kwan yace "Allah sarki, wasu haka suke basa cin kwai
sai suce yana masu karni, mu dai kam ko danyensa ne baxa mu ki ci sha ba, wa yaƙi
dadi" Sai da Aminu ya cinye kwan ya mike yace "Mu je ka ga Boyis kwatan" shi ma ya
tashi, yana biye da shi, suka tafi far end of the main building in which stood a
Beautiful Chalet, mai gadi ne ya fara shiga, shi ma ya cire takalminsa bakin kofar
shiga Chalet din kamar yanda mai gadin yayi sannan ya shiga ciki, ba laifi parlon
na da girma, sannan ga kujeru har ma da tv, kaya ne ko ta ina a parlon ga wani
tashi da parlon yake, everywhere looks very untidy, isiya ne tsaye parlon yana ta
faman guga a ironing board, Aminu yace "Ashe kana ta guga shi yasa baka fito ba,
ina Saminu?" Isiya dake ta kallon wanda Mai gadin ya shigo da yace "Suna can daki"
Aminu yace "To ga bako, kun samu karuwa a nan, shine ya maye madadin Habibu a gidan
nan yanxu" Mutumin ya gaida isiya, isiya ya amsa yana ci gaba da gugansa, Aminu na
kallonsa yace "Mu je ka xabi dakin da xaka xauna ko" Isiya yace "Ka dai san dakin
dake daga dama ni ne a ciki, na hagu kuma Saminu, wanda ke jikin na hagun Shafi'u
ne a ciki" Shi dai kallonsa kawai mutumin yake, Aminu dake kallon Isiya shi ma yace
"To ya xa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login