Showing 213001 words to 214217 words out of 214217 words

Chapter 72 - Mutallab Part 1 and 2 by Nimcyluv

Nimcyluv   

05 Jun 2026

57

Wora a cinyarsa kokawa ta fara

dashi tana dukansa da ™arfi idanunta rufe ya tattare hannun rigarsa ya ri™ota ya

jirkito da ita jikinsa kan ta a ™irjinsa, ya dinga shafa kanta ya yi shiru a

hankali ta fara magana "mugu, azzalumi ka cuce ni ka zalunce saboda bani dashi, ka

yaudare ni saboda ina neman abincin ci a wajanka ashe ba don Allah kake yi mini

komai ba, wallahi ba zan yafe ba na tsane ka...,"



"Please Saudah kar ki hukunta ni ta haka kin ji? Na yi kuskure ki bani dama na goge

kuskure na, kin ji Tom?"



"Na tsaneka"



"Saboda na miki fyaWe?"



Ta kuma cewa "Na tsaneka"



"˜addara ta haddasa komai"



"Bana son ganinka"



"Ni ina son ganinki"



"Ka fita daga rayuwata"



"Yanzu na ji na shirya rayuwa domin ki Saudah" Jaheed ya ce a hankali.



"Na tsaneka, na tsaneka, na tsaneka"

"Ina son ki, zan soki, ina kan son ki"



Kuka ta saki sosai ya rungumeta ya ce "Idan kika tsane ni to waye zai so ni? Ba

kisan meke damuna ba ko? Ba ki san yadda nake samu abincin da nake ba ki ba ko?

Yadda kika tsane ni haka na tsani iyayena, domin a karkararmu akwai tsangayoyi

kala-kala amma sukai burus suka ™i sani a can, ina kuka ina cewa bana son zuwa

almajiranci amma Baffa ya™i wai su kamar gado haka zuwa almajiranci yake abin kunya

ne ka haifi Wa ya™i zuwa neman karatu wani wajan, don haka dole zance gashi Baffa

yana yin noma muna da abinci sosai baya yanke mana amma ya kawo ni nan garin daba

uwa ba uba, ba wa ba ™ani, ba mai cewa bari ko ka yi. Ni kam Saudah ki yi mini

uziri, ki yafewa Jaheed Sada"



"Ba zan taSa yafe maka ba, kuma sai na faWawa Malam ka yi mini iskanci, ina cewa

kar ka yi, kar ka yi amma....,"



"Mene kar na yi?"



"Saka abin...,"



"Uhmm Saudah kenan. Ki rufa mini bargon asiri mu magance matsalar tsakaninmu mu

zama abu Waya tamkar kabejin dake cikin kofensa. Give a chance zan goge laifina kin

ji? Idan kika faWawa Malam cewa almajiransa ya yi wa ΄arsa fyaWe da matsala ba

kaWan ba" magana za ta yi ya saurin haWe bakinsu waje guda ta yi shiru tana ji yana

kissing nata smoothly. Bacci ya Wauke ta a jikinsa ya dinga danna mata ™afa a

hankali yana yi mata pictures masu kyau.



Sa™o aka turo masa.



"Dukkan wata Eng Ali wali ya taSa mu'amala dashi da namiji ya nemi wajan Soyewa

domin ya saka a kashe su ko kama su a kai su gidan yari a musanya su da masu laifi,

Šan'yaro ka bar garin nan yanzu na turo maka wannan sa™on saboda wani abu mai

muhimmanci kuma ina som gyara kuskure ne, kabar garin nan"



Da sauri Jaheed ya mi™e tsaye jikinsa na rawa ya juya ya kalli Saudah sai ya sake

kallon sa™on da aka tura masa cikin tashin hankali ya yi waje, ya fice tare da

barin Saudah ™wance a gadon asibiti bayan ya yi mata fyaWen da babu wanda ya sani

daga shi sai ita, sai Allah daya halicce su



*

A can gidan Dig Abdul-Johar Marafa kowa sanda Yasmin take wannan jawabin tun kafin

ta ™arasa Paaahh ya yi saurin sanya hannunsa yana dafe ™ahon zuciyarsa ya fara yin

baya tare da soma tari a hankali ya saka hannunsa ya rufe bakinsa a gigice Aafiyyah

ta yi cilli da wayar hannunta duk da shocke na ganin jaririyar hannun Laylerh.



"Daddy, Daddy!"



Ta ce a gigice tana nufar wajan Paaahh kafin ta ™arasa ya yi saurin zubewa a wajan

saboda wata bugawa da zuciyarsa ta yi a ™irjinsa wani gudan jini ya yi fitar gurbi

daga cikin bakinsa ya sauka a tafin hannun Aafiyyah zaro ido ta yi jikinta na rawa

ta fasa ihu tana yin kasa kamar zata kifa cikin sauri AA MAJ ya ri™ota ta faWa

jikinsa a sume kwantar da ita ya yi a kan kujera. Junaid da Awais da Dr Hash suka

yi kan Paaahh gabaWaya a ruWe suna kiran sunan shi amma baya ji komai nasa ya

Wauke. "Take him to the hospital, yana ciwon zuciya" cewar Ummimi



Ummi tashin hankali da fargaba ya saka ta sulale ™asa ta yi zaman ΄an bori sai

ajjiyar zuciya take saukewa.



"Ciwon zuciya? Daddyn?"

Dr Hash ya furta a kiWime yana Wora hannunsa a ™irjin Paaahh tare da Wan dannawa a

hankali. Paaahh ji yake kamar ana fisgar ranshi zuciyata ya ji ta daina bugawa wani

duhu da gilmawar abu yake gani a cikin idanunsa, ya san idan wani abu ya same shi

tamkar Maamah ya samu, an san cewa babu wani abu da yake zama raunin Aafiyyah sai

an taSa Dig Abdul-Johar shi ya saka aka zaSi wannan hanyar wajan ganin an kashe

Aafiyyah da ranta bashi ake so ya mutu ba, Aafiyyah ake son ganin bayanta.



"Maamah, Maamah"



Yake cewa a hankali yana mi™a hannunsa AA MAJ ya mi™e ya ™arasa ya ce "Sir you'll

be fine in sha Allah"



"Zafi nake ji a nan Wina Aliyu"



"Sannu sir"



Ya nuna musu Aafiyyah ya ce Ina Junaid, Hashim, Awaisu, Aliyu?" Ya kira su, su

huWun ya kama hannunsu ya ri™e cikin nasa ya nuna musu Aafiyyah wacce ta ja

numfashi a fisge kamar mai aljanu tana zabura, daidai lokacin Anty Turai da Wahee

da Zahiderh suka shigo gidan daman daga wajan malami suke aka ce suyo nan mai tsaye

su yi aikinsu akan Aafiyyah. "Subuhanallahi gida ya rikice meke faruwa a nan?" Ta

ce tana nufar wajan da zaratan samarin suke Wahee ta yi jigum Zahiderh kuma ta kafe

AA MAJ da idanu wanda ya Wora kan Paaahh a cinyarsa. Ummimi ta mi™e ta nufi Waki

zata Wakko wayarta cikin rashin sani ba tare da kowa ya ankare ba Aafiyyah ta

zabura kai babu Wankwali ba takalmi ta yi waje idanu rufe mai gadi baya nan sai ya

nufi bakin gate ta fice daga cikin gidan gabaWaya idanu rufe.



A can gidan kuma Paaahh ya dam™e hannayen yaran nasa ya ce "Aliyu ga Junaid da

Awais nan ga dr Hash nan, Aliyu ga Ummi nan, Aliyu ga Zahiyerh nan, Aliyu ga Turai

nan wannan nauyin naka ne na bar maka" ya yi shiru jini yana cigaba da fita daga

hancinsa da bakinsa idan ya tuna cikin Aafiyyah sai ciwon ™irjinsa ya ™ara zafi,

idan ya tuno maganar Wazo ta Yasmin sai ya ji ya sallamawa rayuwa da duniya. Ya

numfasa ya ce



"Safiyyerh"



"Me ya samu Safiyyerh?" Cewar J



"Ku tabbatar ta yi dariya a rayuwarta, ku tabbata babu abin da zai ™ara sanyata

kuka Aliyu ka zama uban Maamah na bar maka wannan matsayin" sai ya fara salati

jikinsa ya saki ihu Anty Turai ta saka AA MAJ ya runtse idanunsa hawaye na sauka a

idanun Dr Hash Awais kuma kifawa kan Dig Johar ya yi yana sakin kuka tare da faWin

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi!"



Mi™ewa AA MAJ ya yi jiri na kwasar shi da nufin Wauke Aafiyyah daga gidan gabaWaya

kar ta farko taga wannan tashin hankali kar kuma a yi biyu babu sai dai babu

Aafiyyah a rikice ya haura upstarts.



Aafiyyah ta yi nisa ™arfarta futu-futu tana tafiya a tsakiyar hanya kamar

mahaukaciya wata mota dake bayanta ta fara yi mata horn din din din amma bata ji.

Wanda ke baya hakimce a motar ya ce "Mene ya faru ne?" Driver ya ce "Sir wata

mahaukaciya ce akan titin ita na kewa horn bata ji amma" Barrister ya ce

"Mahaukaciya kuma?" Ya faWa yana kallon Amsh dake tsalle akan kujerar motar.



"E, mahaukaciya sir"



"Ikon Allah, ka yi parking muga wacece ta ya zamu taimaka mata"



"Ok sir" ya yi parking a kusan tare Barrister da Alhassan da shima ya hango

Aafiyyah suka fito daga mota Barrister ya fito yana cewa "Come with me Amsh" ya ce

yana Wakko cute babyn yana nufar wajan Aafiyyah data dur™ushe a wajan....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login