Showing 30001 words to 33000 words out of 214217 words

Chapter 11 - Mutallab Part 1 and 2 by Nimcyluv

Nimcyluv   

05 Jun 2026

101

garin. Kallo kallo aka shiga yi tsakanin Hon MaWatai da Eng Ali wali dukkan su cikin shiga ta alfarma, ga mutane da take musu baya kowanne da tarin ´an jagaliya da ´an daba gudun kota kwana. Hon MaWatai ya yi murmushi yana mi™awa Ali wali"

hannu ya ce

"""Kwana da yawa Ali wali?"" Ali wali ya Wauke hannu sai kuma ya juya ya ce"

"""Ba yanzu ba ka jira na wani lokaci komai zai haska, za a yi tsawa wal™iya ta bayyana munafukan da suke"

"Soye cikin duhun ciyayi"" murmushi Hon MaWatai ya yi kawai yana furta ""Allah Ya nuna mana"" gaisuwa duk sukai sai dai daddy tsakaninsu kawai addu'a ya mi™ewa daga wajan. Bayan yin ta'aziyya Hon MaWatai ya ce ""Allah Ya yi wa Ashraf Rahama, ya ta™aita iya kan shi"" SharfaWi ya juya ya kalli Hon MaWatai kana ya kalli Eng Ali wali sai kuma ya ce ""Amin, yanzu ba gashi ba gwanin sha'awa a dinga siyasa bada gaba ba sai an fi samun nutsuwar zuciya data ™wa™walwa duk wanda zai samu wannan kujerar Ubangiji ya gama rubutawa kawai dai lalube ake yi cikin duhu ku haWa kai da hannu kowa ya yi kamfel nasa babban jin"

"daWin ba jam'iyyarku Waya ba"""

Cikin jinjina kai Hon MaWatai ya yi murmushi daman shi bashi da wata matsala da Eng Ali wali shi yake

"haukan shi hankalinsa na kan wanda ya yi shiru, shirun nasa kuma yana nufin babbar barazana a gare shi ""Siyasa ai ba zata haWa musulmi irina faWa da wani ba, munga jiya mun ga yau muna da tabbacin za muga gobe mai kyau, ni fatana na samu gurbin saka hannun jari a kamfaninka idan aka bani dama an yi"

"mini komai SharfaWi"" daddy na jin su can aka kira shi waya da sauri ya mi™e tsaye yana neman uzurin"

tafiya Eng Ali wali ya bisa da idanu.

"Cikin dare Fiyya ta farka da wani irin ciwon kai na Sari guda, ta kasa buWe idanunta a hankali ta saka"

"hannu ta dafe kan ta duk da halin cewa bai hanata yin addu'a ya yi tashi a baccin ba domin tabbatarwa da kanta ba a cikin kabari ta farka ba. ""Sannu Maama"" shine abin da Ummi ta iya cewa tana hamdala a ranta domin shirun ya yi yawa ta dam™e hannunta sosai"

"""Ummi kai na ciwo, ciwo nake ji a gefen kaina"" jikinta har rawa yake na tsananin ciwo Ummi ta ce"

"""Maama zai daina in sha Allah, bari a kira likita"""

"""Ummi daddy fa?"""

"""Yanzu ya fita, ki yi ta addu'a komai ya yi farko yana da ™arshe, wannan ciwon kan zai daina miki"

"watarana buWe idon ki kalle ni"" a hankali ta buWe idanun ganin yadda idanun ya yi jajir ya saka Ummi cewa ""Subuhanallahi wannan jan kuma na magani da mene?"""

"""Ummi jimawar da ta yi a kwance da ciwon kan shine ya saka idanun ja yanzu daddy zai shigo Fiyya zata"

"ji sau™i ki kwantar da hankali"" daidai nan daddy ya buWe ™ofa ya shigo J na bin shi a baya da Dr Hash, ganinsu kuma ya saka komai ya dawo tunanin Fiyya ta runtse idanunta tana jin fargaba na saukar mata. ""Da gaske Ashraf ya mutu daddy? Da gaske an binne Ashraf babu Ashraf ya mutu yanzu haka yana kwance cikin kabari mijin da zan aura ranar Waurin aurena ya mutu daddy na shiga uku"" daddy ya kama"

hannun Fiyya cikin nutsuwa ya ce

"""Laa, sam ba ki shiga uku ba tana iya yiyuwa ya shige iyakar shi ne, kuma mutuwa a hannun Ubangiji"

"take idan lokacin ya yi kota wacce siga ce dole wannan rai ya koma wajan wanda ya samar dashi, Maama da gaske mijin da za ki aura mutu ki sawa ranki ha™uri ki yi masa addu'a ki saka salama ki Wauka bashi ne zaSinki ko alheri gare ki ba, Ubangiji na yin komai a lokacin ya yi niyya babu mai tuhumarsa hujjar hakan domin shi ishasshe ne ki yi addu'a Safiyyerh Ashraf is no longer alive pray for him"" juyawa Fiyya ta yi ta zubawa daddy manyan idanunta wanda yake cike da hawaye da ™yar ta ce ""Ashraf ya mutu ya bar ni cikin zullumi daddy, inama tuntuni aka Waura mini aure da shi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wayyo ni"

"Safiyyerh"""

"""Zullumi na me kuma Safiyyerh kin ga abubuwa da yawa a rayuwa sai mutuwar Ashraf zai tsaya miki? Ba"

"za ki yi addu'a ki sawa zuciyarki sallama, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne kamar yadda aka sanar yau Waurin auren ki da Ashraf Allah bai yi ba, haka kuma al™awarin Allah gaskiya ne igiyar auren wani ta hau kan ki Maama"" ta yi shiru don ta tabbatar daddy ba zai fahimce ta ba, ba zai gane me take nufi ba, ta yi missed Ashraf tun ba'a je ko'ina ba ta ji inama ita Ubangiji ya Wauki rayuwarta ya bar Ashraf ko da bai aure ta ba, babu mamaki ta dalilinsa wani ya san abin da yake Soye gashi ta mutu ya barta da wani irin"

damuwa ba tare daya bar mata ™ofa ko Waya da zata gane ba komai ba.

"""Daddy me ya sa ka haWa aure na da Ashraf tun fari?"" Daddy ya kalli Fiyya cikin kwantar da hankali"

"""Saboda ya cancanta kuma ya dace Maama ki yi shiru da wannan maganganun duk zafin ciwo ne yake sawa kike furta su kamar saukar ruwan sama ki yi addu'a"" ta jinjina masa kai a hankali ta zare hannunta daga cikin nasa idanunta rufe sai sauke numfashi take yi ba tare da ta ce komai ba ta juya ta kwanta maganganun Ashraf na dawo ba, a ranta ta dinga masa addu'a ita bata taSa sanin bashi da lafiya ba, he"

never told her he was sick innalillahi.

Dr ne ya shigo zai yi magana daddy ya yi saurin girgiza masa kai alamar kada ya ce wani abu serious Dr

"Win ya zubawa Safiyyerh idanu ya ce ""za'a sallame ta yau kamar yadda ka bu™aci baka son kwana zan"

"mata allura amma before"""

"""Thank you Dr"""

"Dr Hash ya mi™e ya ce ""daddy zan je asibiti ina da aikin dare Awais zai yi dropping nawa bana jin daWi"""

"Ummi ta ce ""Kuma baka jin daWin zaka tafi kamar dole ka yi kwanan tsaye ba'a Waukan uzuri ne"" ya Wan yi murmushi kawai ya ce ""Ummi ai ba zai yiwu na amshi kuWi na ™i aiki ba, sai Ubangiji ya kama ni da"

"wannan hak™in ki yi addu'a zan iya"" ta ce ""To Allah ya sauwa™e ya bada sa'a ya kuma kare"""

"""Amin Ummi"""

"Dr Win ya yi wa Fiyya allura ta samu bacci mai nauyi, Ummi dai kallon daddy take jin ya kira Aliyu ya zo ya"

"Wauki Fiyya nan da 20 minutes shi zai tafi tare da Ummi har lokacin Aliyu bai san da batun auren ba kamar yadda Fiyya bata Wauki maganar daddy serious ba. Ya gyara mata kwanciya ya mi™e Ummi ta mi™e tana shafa kan Safiyyerh a haka suka fita. Har wajan ™arfe 1:30 Fiyya na kwance tana bacci lokaci zuwa lokaci wata nurse ke shigowa duba ta. Yana tsaye hannunsa biyu zube cikin aljihu ba zai ce ga abin da yake tunani ba, amma fuskarta kawai yake kallo ganin yadda a bacci ma take Sata rai ta sauke ajjiyar"

"zuciya, ™ofa aka buWe ya yi saurin yin baya yana kame fuska sosai."

"Dr ya kalli Captain ya ce ""Sai yanzu na Wauka ma ko a nan zata kwana"" Aliyu dai ya yi shiru ya zaro waya"

"ya fara dannawa ""ga maganganun nata wannan za a yi amfani da shi lokacin...,"" ""Ka kira su, sai ka musu bayani"" shi daya tsaya tunanin yadda zai tashe ta yake ga daddy sai kiran shi yake banda haka da ba zai zo bama, ya saka ™afa ya fara zungurun gadon dr ya ce ""Allurar da aka yi mata nada ™arfi sai dai ka Wauke ta"" siririn tsaki ya yi ""to Wauke ta kai"" ganin fuskar Aliyu cikin serious ya sa dr ya nufi Fiyya zai Wauke ta zuwa waje kafin ya ™arasa kawai yaga Captain ya saka hannu da drip Win da mayafin nata ya Waga sama ta zabura ta yi saurin ri™e shi Idan ba kuskuren ji ya yi ba ya ji kamar ta ce ""TAHHB"" ya sata gaban mota"

ya kwantar da kujera kamar wanda ake bi haka yake jan motar.

****

Yana dur™ushe ya tsattsare mutumin da jajayen idanunsa wanda suka shige ciki alamar a buge hannunsa

ri™e da askira gefe kuma jibgegen karan shi Tiger ne da duk a cikin karnukan ya fi son shi. Ya saka askira Win a cinyar mutumin ya nutsa jini ya fara fita sosai yana ihu da kururuwa cikin tsakiyar daren ga duhu

ko'ina ya ce

"""Wai me ya sa baka da imani ne, zaka raba mini cinya biyu"""

"Duk da cewa a buge yake amma tar ya buWe idanunsa, cikin muryarsa da kana ji ka san shi ba ma'abocin"

magana bane da wani kalar sautin mai kama da gurnanin zaki ya ce

"""Ka gane ni yanzu?"" Ya jinjina kai yana wani irin nishi da kakari kamar na mutuwa ya ce ""Na gane na"

"gane, wallahi na gane ka"""

"""Good"" ya sake nutsa askirar ya yi feshi kunama ta faWo ta shige cikin wandon birnin ya ce ""Sanda aka yi"

"mini baru ma'ana aure, da nazo kai na ganin bakin ™ofar gidana, haka ne?"" Ya sake faWa yana ™ara cilla masa wata kunamar ba™a ™irin ta sake shigewa cikin wandon mutumin, Darma da Goje sun tale shi"

kowanne ya take hannu Waya mutumin ya yi shiru hakan kuma ya sake fusata Moh ainun

"""Idan aka bani ciwon kai hauka nake yi ba zaka ka ji daWi ba, a yunwa ce nake, yi batu"" kamar zai mutu"

"cikin kakarin mutuwa ya ce ""Zan yi, zan yi magana"" suka sake shi suna kallon shi."

"""Mutane kala biyu ne suka shigo a wannan daren da aka kawo ta, na farko sun bani kuWi fuskar su a rufe"

"take na biyun ma sun sake bani kuWi suma fuskar su a rufe take amma sun bani sa™o na baka tun a wannan lokacin, bayan an kama ka na rasa wa zan bawa na dinga bulayi kawai na ha™ura, daga baya kuma aka zo aka sake cewa na bada wannan sa™on na ce a'a sai sukai mini tagoma shi da kuWi har miliyan Waya kawai na basu ai kan ™asar nan yadda muke fama da babu da yunwa ga iyalai ina dasu"

"kawai na amsa na bashi"""

"Darma ya ce ""ka ji kimini ´an yankin nan ba za ku gama da duniya lafiya ba, da ™yar kusha ruwan"

"alkausara"" Moh ya zubawa mutumin jajayen idanunsa sai kuma ya mi™e tsaye magana yake son yi amma ta ma™ale a harshen shi da ™yar ya ce ""Ku yi masa Salli-Salli"" yana cewa haka ya juya."

"""Baka ji ba, ai na haddace abin da aka rubuta harafi uku ne a jiki. A.M.A, sai wani suna nada ban kamar"

"sunan asibiti kamar sunan unguwa idan na tuna zan zo na faWa maka amma don Allah kar ku yi mini komai a tausaya mini sabuwar amarya ce dani"""

"""Ni tawa matar ko kwana ban yi Wakinta ba, duk irin gwagwarmayar dana sha, uhmmm"" ya yi shiru a"

lokacin sautin muryarta yake ji na kakarin mutuwa a kunnensa can ya mi™e kawai ya yi gaba. Goje ya ce

"""Zan dinga zuwa lokaci lokaci domin kana cikin taskar Moh"""

"Da sauri suka bi bayansa ganin har ya yi nisa sosai ""Mai dawa daman ka iya yaran nasara na ji ka ce"

"Good"""

"""Na yi kala da wanda iya turanci ko mota ko amfani da waya ne?"" Kallon tsaf sukai masa Darma ya ce"

"""Ciki ne kai yasin sai fama kake da kan ka ba wannan maganar a basar kawai ya maganar Wawan nan?"""

"Kamar zai yi shiru sai ya ce ""Bana son sabga da mace zan iya kashe ta kamar yadda itama Wayar na kashe ta"""

"Darma ya fashe da dariya sosai yana kaWa kan shi ya ce ""ba wannan ba wallahi wata figigiya da ita, suma"

"dai basu da man kai wai ita ce manja"" Goje ya ce ""matsalar kai da™i™i ne ajawo sam ciki ne kai, manager ake cewa dake mayen garau garau ne kai wai manja ai uwar manja gaja kawai"" Darma dai bai kuma Goje ba ya ce ""Maganar gaskiya wannan za a iya karya mata ™ugu a wajan Wakko ta ma sille kenan, Mai dawa ko kai baka ganta bane"" Ya yi musu shiru yana jinsu dai ""Sai godiya, ina magana baka ganta ba wata ´ar"

"shila da ita?"""

"""Ita wa?"""

"""Manja Win"""

"""Idan ka ™ara ce mana manja a wajan nan za kaga manja ganin idanunka, Wan wahalar yaro kawai"""

"Mutallab dai idanunsa a lumshe tunanin da yake yi daban, kalmomin da mutumin ya faWa masa nata yawo a cikin kan shi. A.M.A Ya kasa fahimtar kowanne harafi me yake nufi sai kawai ya taune bakinsa ™irjinsa na buWewa duk jikinsa tsami yake masa ya buWe idanunsa ya kalli sama yana ganin yadda"

gajimare ke gudu yana haWewa tare da warewa muryarsa bata wani fito sosai can ™asa ya furta kalmar.

"""her eyes look alike, tiger""."

Washegari misalin 12 na rana Safiyyerh na saman bene cikin Wakinta ta dinga kallon Kinal bata da

"nutsuwa sosai da babu abin da zai hanata yin dariya. Kinal ta share hawayenta tana Sata fuska cikin sanyin murya ta ce ""Kalli yadda sukai mini da fuska daga tambaya na Wauka za su faWa mini ashe ´an"

"wahala, ni bada wata munufar na je wajan su ba wallahi kawai su bani amsa na ™ara gaba"""

"""To ga amsar nan ai"""

"""Maama fuska ita ce kyan mace fa, yanzu idan tawa ta lalace waye zai aure ni haka? Sun kusa tsaga mini"

"baki gashi yanzu ina da aiki a ™asa sosai har Hon MaWatai zan yi wa wa™a"" Safiyyerh ta yi shiru tana tunani so take ta fice daga cikin gidan secretly amma no way ""wai ina magana kina ji ba zan shariyar nan naki damuna yake, na zo Webe miki damuwa da kewa na rashin Ashraf kamar yadda Ummi ta bu™ata duk"

"da ciwon da bakina yake mini ina da zuba ke kina ignoring nawa for God sake"""

"""Idan ba ™i auro ba sai ki auri Wan daban kawai"" Kinal ta yi tsaki ta ce ""Kuma zan iya, mene a ciki"""

"""Shi auren Wan daban?"" Fiyya ta bu™aci amsa tana kallon Kinal. Kinal ta ce ""Deal, nama yi miki al™awarin"

"in dai ina da numfashi wallahi wallahi sai na auri Waya daga cikin ´an daban nan, kamar ni mawa™iya za"

"su yi wa haka? Uhm"" Fiyya ta lumshe idanu ta buWe deep down ™irjinta na bugawa sai ta ce"

"""You most like them ma, ´an daban ai sun iya soyayya"""

"""Ke ta ya kika san sun iya?"" Shoulders kawai Fiyya ta Waga ba tare da ta ce komai can ta sauke numfashi"

tana kallon Kinal ta ce

"""Kinal Ashraf ya rasu, mijin da zan aura ya bar ni Kinal ina cikin damuwa ina jin da old Safiyyerh ce ba zan"

"ce ina cikin damuwa ba, gwara ta kashe ni haka nake ji"" Kinal ta jinjina kai ""Fiyya something is over doesn't mean your life is over, ki yi ha™uri mu Wauki ™addara ki yi wa Ashraf addu'a Please kar ki saka damuwa wani abun ya zo yana damun ki daman ke idan kika birki ce kamar mai ´ar mero a ka, ™addararmu zata zama mai kyau muna tare da addu'ar iyaye ai"" sun jima tare da Kinal har yamma kana"

ta tafi gida tana jin dole ta sake komawa wajan ´an kodin Win nan.

"Da ™yar da daddare Fiyya ta sakko ™asa bayan tayi sallar issha tana sanye da hijabi har ™asa, fuskarsa"

looking ok ba yabo ba fallasa sai dai ta faWa idanunta ya fito akwai damuwa a tattare da ita. Inda ta yangi

"su J ta nufa ta shiga tsakiyar ´an mazan ta zauna a nutse ta ce ""Sannun ku"" Awais ya Wago ya kalleta ya"

"ce ""Yawwa Manager ya ™arin ha™uri?"" Idanunta ya juya ta cije baki ta ce"

"""Allahamdulilah,thank you"" daddy dake kallon ta cike da tausayi ya ce ""tashi a nan wajan Safiyyerh"""

"""Daddy me ya sa?"""

"""Ki dai tashi na ce ko?"""

"A sanyaye ta mi™e sai kawai ta yi sama ya bita da idanu a hankali ta ce ""Sai yaushe zaka faWa mata batun"

"auren?"" Daddy ya ce ""Da sai an kammala Visa Win ta, na san wacce take da ita a baya ta yi expired, to Safiyyerh stubborn girl ce da na yi maganar visa zata kalli cikin idanuna ta fara mini turanci wayonta tsoro yake bani, kuma yanzu i feel very comfortable da Aliyu matsayin mijinta duk da basa shiri amma ba"

"zai Waga mata ™afa bana son dai ta yi rayuwa a wajan shi kamar Prisoner, za ta yi shakkar yi masa abu"""

"""Kana ganin zata amince da auren?"" Ya mi™e tsaye yana haurawa sama ya ce ""In sha Allah"" daman daga"

sallah ya dawo shine ya zauna. J dai baya uhm baya uhm'uhm abubuwa da yawa ke yawo a ™asa wanda

baya rasa nasaba da tunanin wace Safiyyerh waye Aliyu?

"Ummi ta kalli yadda ya shigo ba wanda ya kula kamar bai ga kowa ba ta ce ""Aliyu tun safe ina ka je ne?"""

"Ya buWe ido ya yi shiru ta ce ""Kuma ka ci abinci ne? Kodayake ba'a tambayar soja ko ya ci abu da za'a buWe cikin ka duk ganye ne"" kallon Ummi kawai yake kuma ya yi shiru"

"""Yaushe zaka tafi goben?"""

"""A'a, night Ummi"" ya ce yana shigewa cikin Wakin shi dake part Win mazan."

Fiyya ta ci kuka a Waki kamar rai da sauri ta buWe system Winta taga sa™o a e-mail nata tun sanda sukai

last called da Ashraf bayan hakan ta minti ashirin da wajan biyar. Maganar daya tura mata ya saka ta buWe idanu sosai.

"_Safiyyerh daddy ya zo ya fita yanzu, ko ma dai menene ki tabbatar ba ki bawa wani damar mallakar FS"

"WORLD INVESTMENT COMPANY ba Fiyya mutane biyar sune mamallakan wannan kamfanin mutane masu haWari ko ni ban san su ba, da ina da yadda zan yi a yanzu zan faWa miki komai domin sau™a™a miki,"

"ki fara nemo ma'anar FS shine key Win binciken, don't cry when you miss me i love you""_"

"Safiyyerh was shocked, thinking me ya saka Ashraf ya yi mentioned sunan daddy a lokacin, meke shirin"

"faruwa ne gabaWaya kan ta ya Wauki zafi da gaske ta yi rashin Ashraf sai yanzu ne take jin gudun zuciyarta na ruSanya aikinta a kan Ashraf Win. Ta kwanta tana rufe idanunta ™arar notification na wayarta ta saka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login