Showing 81001 words to 84000 words out of 214217 words

Chapter 28 - Mutallab Part 1 and 2 by Nimcyluv

Nimcyluv   

05 Jun 2026

321

dafe da kanta bata ganin ko gabanta duhu ne a cikin idanunta haka ta dinga sauka akan matattakalar benen. Karo ta yi da mutum cikin sauri ta kama hannunsa tana Worawa a kanta ""Yaya J kai na zai cire wani abu nake ji, ciwo yake mini kamar ana jana"" gabaWaya ta rikice ta"

™an™ame shi har zufa ke tsattsafo mata.

Kama hannunta ya yi ya jata saman kujera ta™i sakin shi ya zauna a hankali tare da zaunar da ita ta yi

saurin Wora kanta a cinyarsa ya ri™e mata kan yana murza goshinta nata very careful kar ta ji zafi. Sun

jima kana ta shiga sauke ajjiyar zuciya numfashinta na sauka ya Wan le™a fuskantarta yaga bacci take ya saka hannu ya juyo da fuskarsa yana zuba mata idanu ya ri™e hannunta har lokacin bai ce komai ba.

"""Aliyu"""

"Da sauri ya saki hannun nata yana zame ta ya mi™e tsaye Ummi ta kalli Fiyya ta kalle shi ta ce ""Ita kuma"

"lafiya take bacci a nan? Yaushe ta shigo gidan ai lokacin tashi bai ba?"" Captain dai ya yi shiru ta juya ta kalle shi sosai ta ce"

"""Lafiya take?"""

"""Ban sani ba"""

"""To ya naga kana haWe rai duka zaka kawo mini me kai komai naka babu walwala Aliyu ka dubi girman"

"Allah ka dinga murmushi shifa yin murmushi sunna ne ta ma'aiki"" ya shafa kan shi yana zuba hannu a aljihu cikin gaskiyarsa ya ce ""Ban iya ba wallahi Ummi ki koyan"""

"""Shi murmushin? Allah ya rufa asiri to wannan matarka ta shiga uku"" yana dai tsaye bai ce komai ba."

"""Maama?"""

"""Ummi"""

"""Maama ta shi yammaci za ki yi ™unci ko ciwon kai idan kikai bacci"" ta buWe fararen idanunta suka haWa"

idanu ta sha kunu sosai tana tura baki ya zabga mata uwar harara ta yi baya zata koma baccin.

"""Kee"" ya kira sunanta ta buWe idanu ""Tashi kafin na yi balle da wannan silar ™afafuwan"" mi™ewa tsaye ta"

yi ta murguWa masa baki bata ce komai ba shi kuma ya yi kamar zai juya ya dam™o hannunta ta ™walla

ihu daidai nan Daddy ya shigo parlon cikin sauri ya sake ta.

"""Da kyau Soja gwara ka nuna ™arfinka akan Wiyata, yanzu zaka tattara ka koma inda ka fito"""

Captain ya juya ya bar parlon gabaWaya yarinyar haushi take bashi har zuciyarsa. Daddy ya kalli Fiyya ya

"ce ""Maama, yaushe za ki girma ina ganin wawtar wanda ya Wauki mu™a min Manager ya ba ki wallahi"""

"""Daddy kune kuke raina ni wallahi, na girma am matured enough"" ya girgiza kai kawai kasancewar t.v. na"

"kunne aka fara karato ta™aitattun labarai. Sunan Scorpio aka fara ambata matsayin wanda jami'an tsaro na hukumar FID Federal investigation department suke nema idanu rufe. Dake t.v a hankali ta juya ta kalli mai karanto labaran matashin Wan jarida dake aiki a gidan t.v na VOA juyawa ta yi ta ce ""Daddy Wan"

"bani aron wayarka"""

"""Ki yi me da ita?"""

"""Wayata zan kira, ina son fita ne wajan Kinal"" ya mi™a mata wayar ta Wan jim tana Waga hannunta tare da"

"copy na wasu numbersa sai kuma ta mi™a masa bayan ta yi deleting tana murmushi ""La la la na tuna inda"

"na sata"""

"Ya kalli t.v ya kalleta ya kuma kalli wayarsa, ya dai amsa a ransa yana mai jin tsoro da mamakin kaifin"

"tunanin Maama. Ummi kuma ta ce ""Ayi ta neman mutum kamar kiyashi shi kuma ya rasa sunan da zai"

"sawa kan shi sai kunama?"" Daddy bai yi magana ba Ummi da abin ke ta cinta ta kalli Fiyya dake shirin"

"haurawa sama ta ce ""Maama ta shi me ya yi ne?"""

"""Ummi ina zan sani, idan kika Wauke yadda ake juya biyar ta zama goma ba abin da Fiyya ta sani"" tana"

"cewa haka ta haura cikin sauri tana nanata numbersa dake kanta cikin sauri ta yi wanka ta shirya cikin abaya ta yi rolling tare da fesa turare sauri-sauri take a haka ta sakko hannunta ri™e da waya ko jaka bata Wauka ba. Daddy ya dube ta ya kalli lokaci ""Wai zuwa wajan Kinal baya tashi sai yamma? Ita Kinal Win nan"

"ta dinga zuwa mana zai fi"""

"""Daddy ba jimawa zan yi ba, na jima ban je ba mun gaisa ba"""

"""Maama bani da nutsuwa haka kawai idan kika fita gari ya hargitse bani number Kinal Win nan na kira ta"""

"kafin ta yi magana J ya yi saurin ™wace wayar Fiyya ya ce ""Bari na kira maka ita Daddy"" babu sunan Kinal a jerin wanda ta yi waya dasu yau cikin sauri ta amsa ta ce ""Number Kinal a kashe yaje fa J wai ni yarinya ce na san yadda zan kare kai na no body can come and hit me"" Ta kalli Daddy da Ummi ta juya ta kalli J"

"ta ce ""To tsoran na mene ni Safiyya A Marafa?"""

"""Allah Ya tsare Maama jeki"" amsawa ta yi da amin ta raWawa J kunne ""J akwai gulma yau bari na je na"

"dawo"" tana fita harabar gidan mota ta shiga ta yi mata key cikin nutsuwa dake driving har ta fita ganin ta"

hau kan titi ta dubi bayan motarta ta cikin gilas wata ajjiyar ta sauke mau nauyi ta rufe idanunta ta buWe sai kuma ta Wauke hanyar ta nufi wani titin daban a zuciyarta addu'a take yi sosai.

*****

Eng Ali wali na zaune a parlo cikin wani gidansa da yake ganawa da ΄an siyasa masu mara masa baya a

"kujerar shi. Ya dubi CSP chief Superintendent of Police ya ce ""Ina son ku Wauke idanunku akan yarana, ko me kuke bu™ata zan baku idan Sarna sukai zan ji da komai"" Csp ya ce ""Hon yaushe za mu cigaba da zuba idanu ΄an dabarka suna yin yadda su kaga dama a garin nan musamman a unguwar Birget gashi lamarin na shirin haddasa faWa tsakanin ΄an cikin gari da su ΄an Birget, mu jami'ai ne mun san gaskiya muke take"

"ta"""

"""Ku cigaba da takewar su wannan yaran suna da wa'adi dana samu na ci zaSe ko inuwata babu mai gani"

"a cikin su. Don haka ku rufe idanunku a toshe kunnuwa, zuwa gaba har matsayi zan saka a ™ara maka mu yi ΄an dabaru"" CSP ya jinjina kai Eng Ali wali ya Wakko kuWi mai yawa ya mi™a masa yana cewa ""Idan kun"

kama masu dilar ™wayoyi da kayan maye na san ana mi™a su hannun NDLEA ko? Ka tabbatar ™wayoyin

"na zuwa wajan Jafar shi kuma zai bawa yarana, kar ka sake sunana ya fito daman ai ΄a΄an asara ne ko an"

"kama su ba za su taSa furta ni suke yi wa aiki ba, lastly magana akan Scorpio Win nan yana neman bani ciwon kai bana son ya zama damuwata, idan F.i.d suka riga ku kama shi akwai matsala"""

"""Karka damu hon mun zuba yaran mu ta ko'ina"""

"Eng Ali wali ya ce ""Lallai Scorpio ya zo hannu kafin zaSe"""

Cikin sauri Fiyya ta fito daga cikin motarta tana shiga cikin wajan data zo a reception ta tsaya na wasu

"mintina tana zaune ta fito tana murmushi ta ce ""Ikon Allah kamar tare kuke?"" Fiyya ta buWe idanunta sosai ta ce"

"""Wa?"""

"""Captain yayanki"""

"Gabanta ya faWi ta kasa cewa komai Kinal ta zauna ta ce ""Wallahi zuwan shi biyu fa, nima dai na yi"

mamaki amma ya ce aiki yake dubawa shi ne ya le™o mu gaisa har ma na tambaye shi ke sai bai bani

"amsa. Amarya ya kike ya sabgogi"""

"""Good. Yanzu lokacin ku ne Kinal siyasa ta matso ana ta fama da habaice-habaice"""

"""Kamarya habaici?"""

"Fiyya ta cire gilas Win idanunta ta ce ""babu abin da mawa™a suka iya sai habaici wallahi ku zagi wanda"

"kuke so kuma ku yabi wanda ku kaga dama"" Kinal ta yi murmushi ta ce ""A'a ni ba ruwana idan an kira ni"

"dai wa™a ina yi amma ai ni ta soyayya nake yi tunda a nan na fi kauri, ina nan ina shirya miki ke da"

"Ashraf"" Fiyya ta sauke numfashi ta ce"

"""Ina cikin matsala Kinal ban so faWawa kowa ba wallahi"""

"""Subuhanallahi matsala wacce kuma? A kamfanin ko gida ko wani wajan?"""

"""Kema kin san a gida ba wanda zai mini komai sai mai ba™in halin nan, tunda ya dawo ya uzzura mini ko"

"parlo bana fitowa mutum sai ba™ar zuciya Wan wahala kawai aikin kawai"" Kinal dai ta zuba mata idanu kafin ta ce ""Mene damuwar?"""

"""Kwana biyu da suka shige ana bibiyata kullum idan na fita, harta nan wajan da na zo sai da aka biyo ni,"

"ni ba damuwata kai na ina tsoron su Daddy su sani kin san abu idan ya same ni tashin hankali suke shiga. Kinal ban san su waye ba me kuma suke bu™ata saboda bani da issues akan kowa wallahi na ji kawai ina son sanin wanda ke following nawa duk inda na je gwara mu yi fito na fito da shi, da na ce ko na yi hayar ΄an daba nima suna take mini baya?"" Kinal ta buWe idanunta sosai ta ce ""Daman na fara zargin kina da taSin hankali Fiyya, ke yanzu ina kika san inda ΄an daba suke bare ki je? Bakya tsoro ko shakka ai matsalarki police ne wannan ina ganin a gayawa Captain kawai"" tsaki Fiyya ta yi tana mi™ewa tsaye ""gwara duk abin da zai same ni ya zaman da dai na faWawa Captain ni ina da abin yi"" ""³an daban za ki yi"

"haya yanzu kenan?"""

"""E"" sai kuma ta koma ta zauna cikin nutsuwa ta kalli Kinal ta ce ""Akwai abubuwan da bana ganewa"

"kwana biyu kamfaninmu ina son na yi bincike duk abin da na samu ba daidai ba wallahi sai na kaiwa hukuma Kinal yatsun hannun mutum na gani a cikin kamfanin fa?"" Kinal ta zare idanu waje ta ce ""A'a ki fara samun mai kamfanin ku yi magana dashi tunda ke ce Manager"" ""Sai yanzu na fara tunani, i wonder aka bani Manager a kamfanina bayan akwai maza da yawa sosai da na yi tunanin ko experience Wina ne"

"yanzu kawai na ji ina zargi"""

"""Zargin me?"""

"Ta Waga kafaWa ta ce ""I don't know, na fara bincike dole zan gano gaskiya"" Kinal ta ce ""To ki bi a hankali"

"Please Fiyya we care about you ni ma zani anniversary na makarantarmu FGC dana shigo Kamfanin gobe,"

"har wa™a na yi mana yanzu haka wani Eng Ali wali na yi wa wa™ar da aka saka ni"" shiru Fiyya ta yi tana"

"nanata sunan FGC a ranta ""Na ji kamar na san makarantar nan fa"""

"""Ke da ba ita kika yi ba ina za ki sami, ni a can na yi secondary school kinga"""

"""Haka ne bari na je"""

"""To ki kula Please kar ki saka kan ki cikin matsala don Allah Fiyya"" murmushi kawai Fiyya ta yi tana ficewa"

daga cikin studio Win.

*****

Kamar an cillo shi haka yaga Mai dawa ya faWo masa cikin office Win nasa da yake tare da manyan

"mutane sosai tun kafin ya yi magana ya ce ""Kowa zai iya tafiya"" duk suka fice ya Waga kai ya kalli Mai dawa ya ce"

"""Ka daina zuwa ina nake ni zan dinga neman ka"""

"""Ka yi ™arya"""

"""Ni nake maka ™arya Mai dawa?"" Ya wani haWe fuska tamau fuskarsa Wauke da sabon yankan da aka yi"

"masa jiya har yanzu ba'a gyara ba. ""Kai ai ba Malam Abdullahi bane da ba zan ce kana ™arya ba"""

"Eng Ali wali ya jinjina kai ya ce ""Me ya kawo ka yanzu? Har cikin office nawa"""

"""Ka saka ni aiki har biyu, da kamo maka Wawar can da nemo Scorpio"" ya shagiWar da baki gefe ya yi fito"

"wanda ya cika office Win sosai ""Na je gidan asawanta jiya"""

"""Kana nufin gidan Abdu Marafa?"" Ali wali ya ce yana mi™ewa tsaye cike da tsoro Mai dawa ya Waga ™afa"

"ya Wora a saman table Win gaban Ali wali ""sharaWin kawo maka ita barewar shi ne mallaka mini kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, aikin Scorpio kuma ka saka cinnakunka cire hannu daga sabgar ka bar mini ni zan nemo maka shi, bana haWa aiki da wasu"""

"Ali wali ya ce ""Mene haWina da kamfanin nan? Karka saka ni rigimar da tafi ™arfina da ka san ma'anar"

"abin da FS WORLD INVESTMENT COMPANY yake nufi ba zaka haWa kan da shi ba, wannan Kamfanin ciwon idanu ne"" Mai dawa ya ce ""Ni Mutallab Tahhb Wan babana Abdullahi da inkiya Mai dawa bana harin abu na ha™ura, wannan kamfanin shi ne burina"" Ali wali ya goge zufa ya ce ""baka san kamfanin ba shi ya sa a ba ki yake maka wahalar faWa ni Ali wali sabgar siyasa na sani na saka gaba, ka bar ni a haka"

"ba zaka saka ni a masifa ba"""

"""Waye mai kamfanin?"""

"""Sannin hakan daidai yake da tunuwar asirin manyan mutane da dama, ka bar komai yadda ka sani"""

"jinjina kai Mai dawa ya yi ya ce ""Zan maka jahilanci ne, ka ri™e amana ka bi sharuWan da na ce zan maka komai ni Wan daba ne kai mai neman iko da mu™a mi ni na sare na kashe mu bauta maka shi ne. Batun kamfanin zan yi bincike da kai na, kar ka zama butu don wallahi sai na yi maka da™i™anci"""

"""In sha Allah, daga nan har bayan zan yi maka komai"""

"""Dar zan do™a yanzu sai godiya"""

"Yana fita Eng Ali wali ya Wauki waya ya kira Csp ya ce ""Waye Mutallab yaron da ya fito daga wajan state"

"cid kwanan nan bayan ya yi shekaru uku a wajan su"" ta cikin wayar Csp ya ce ""Sunan shi dai Mutallab ya kashe matarsa aka aka kama shi, daga baya kotu ta sake shi a zama na ™arshe ba wanda ya san dalili"" Ali wali ya kashe wayar yana sauke numfashi a fili ya ce ""waye MUTALLAB?"""

For more information

08164069385

"WhatsApp only.[10/11, 9:21 PM] Nanameera: *d'=Ψ%έ MUTALLAB d'=Ψ%έ*"

Page 7

*Bright pens... 2nd batch *

The door is open... Ga masu bu™atar ayi musu tallah. Na hango wasu ™wailaye a conversation group da

Mikiya writers Maman Sayed ta ce a faWa muku akwai maganin gargajiya cikin sati guda komai zai kankama haWaWWan maganin da Fiyyar Ashraf ke amfani da su ta ce a baku numberta ba... 08063114606

"Washegari da safe Fiyya na ™o™arin buWe ™ofa ta fito da nufin zuwa office ya rigata buWe ™ofar, kallo Waya"

"ta yi masa ta Wauke kan ta zuwa gefe a hankali kuma can ta ce ""Ina kwana?"" bai amsa ba sai cewa da ya yi ""You told Abba za ki wajan wata, amma kin yi ™arya ina kika je?"" Manyan idanunta ta Wago ta kalle shi ta ce ""˜arya kuma?"" Ya rufe ™ofar ya tsaya ""Idan kina yi mini kamar ba ki gane ba, kwaWa miki mari zan yi maybe it will help you to understand it very well"" ita mamakin shi take yi ""Ni fa Manager ce business zai iya fitar dani ko'ina"" ya buWe mata manyan idanunsa sosai sai kuma ya ce ""ina kika je"" ta tura baki gaba sosai ta yi gefensa za ta shige ya saka hannu ya fisgota kafin ta yi motsi ya Wago fuskarta ya wanka mata mari ™wayar idanunsa tamkar zata fito waje yana ihu a saman kan ta ya ce ""Idan na sake maimaita miki"

"tambayar sai na tabbatar yatsun hannuna sun kwanta fuskarki"""

"""Sai dai ka kashe ni"" ta yi maganar ko gezau gefen fuskarta ya yi jajur dakakkiyar zuciyarta kuma ya saka"

"ta nuna ko a jikin ta, ™asan zuciyarta kuma wani zafi da raWaWi take ji ""ni kike cewa na kashe ki?"" Hannu ta saka zata ™wace nata hannu idanunta cikin nasa ba tsoro ta ce ""Me kake so na yi maka? Ka shigo kana tambayata abin da ban sani ba, ka saka hannu ka mari fuskar da kullum nake shafa mata mayuka masu tsada, ni ka mara ban maka komai ba, tunda ka tsane ni ka kashe ni kawai"" da ™yar ta iya ™are maganar saboda muryarta dake rawa Captain ya saka hannu ya sake Wauke fuskar Fiyya da mari yana huci ya ™ara Waga hannu zai mare ta cikin sauri ya tsayar da hannun nasa ganin hancinta na fitar da jini sosai kuma"

ya™i tsayawa.

"Ta yi masa ™uri da idanunta da ruwa ya kwanta a ciki, jinin kuma bai fasa zuba ba daidai nan aka buWe"

™ofar tare da shigowa ciki da sauri Fiyya ta nufi wajan Daddy ta ri™e shi tana fashewa da kukan dake cin

"ran ta jikinta har wani irin rawa yake yi da Sari jinin dake fita a hancinta kuma ya shiga Sata masa farar rigar jikinsa. Daddy ya juya ya kalli Captain daya haWe fuskarsa ""Aliyu me ka yi mata?"""

"""Ni kuma?"" Ya tambayi daddy irin bai ma san me ya faru ba ""To ita da waye haka ji bi yadda take kuka"

"hancinta na jini kuma kai na gani a Wakin, dole kasan mene ya faru"" cikin damuwa daddy ya yi maganar wacce sai da ta bayyana saman fuskarsa ya Wago Fiyya yana duban ta sosai ya ™ara kallon Captain"

"""Maama wannan jinin fa? Daman kina yin haSo ne wani abun Aliyu ya yi miki?"" Ita dai Fiyya ta™i cewa"

"komai sai shasshe™ar kuka take yi numfashinta na yin sama, Daddy duk ya rikice baya wasa da al'amarin daya shafi Maama ko kaWan a ™asan zuciyarsa yake jin soyayyarta ya kuma tabbatar ita ce rauninsa Fiyya kawai za a taSa a iya nakasta rayuwarsa. ""Ya isa daina kukan haka nan, Allah Ya nuna mini sati mai kamawa ki tafi gidan mijinki ni ma zan fi samun nutsuwa da hakan zan fi samu nutsuwa idan kikai auren"

"nan Safiyyerh"""

"""I love you daddy"" Fiyya ta ce a hankali tana rungume daddy ya shafa kan ta cike da soyayya ""daddy love"

"Safiyyerh"" tuni Captain ya fice daga cikin parlon. Anty Turai da zuwan ta gidan kenan ta ce ""Ikon Allah. Yaya kai ne kake Waurewar yarinyar nan gindi wallahi ka lalata da soyayya take yin abin data ga dama, ko"

"Aliyu baka tambaya abin da ta yi masa ba ta wannan figaggiyar yarinyar kake"""

"""Fita daga Wakin nan Turai"" rai Sace Anty Turai ta fice tana zabgawa Fiyya harara ranta duk a Sace."

"Daddy ya kalli Fiyya sosai kamar zai yi magana sai kuma ya ce ""jeki wanke fuskarki I'll drop you"""

"""Daddy daman i missed your drive wallahi"" murmushi ya yi mata a duk santa zai kalli Fiyya sai gabansa"

"ya faWi ya juya a hankali ya dubi picture Winta dake gaban madubi sanye da kayan graduation ta yi wani kyakkyawan murmushi ta rungume hannunta tana kallon gefe guda. Ya ™arasa ya Wauki photon ya shafa a hankali ""Maama na ni kamar na yi ba daidai ba, bani da wani zaSi ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login