Showing 60001 words to 63000 words out of 214217 words

Chapter 21 - Mutallab Part 1 and 2 by Nimcyluv

Nimcyluv   

05 Jun 2026

128

yi"

"""Na Wauka lissafin kuWi kawai kike ai? Ashe likita ce"""

"Ta yi murmushi ta ce ""Ina yini?"" Ta faWa tana kallon Moh ya yi kicin-kicin da fuska bai amsa ba."

"""Wallahi kyau kake mini idan kana haWa fuskar nan, na ji ina son ka kuma zan iya aurenka wallahi"" ya"

juya ya kalleta da sauri ta kashe masa idanu Waya ta ce

"""What if I tell you, I love you?"" Ta sake cewa"

"""Idan fa ka amince zan so ka har numfashina na ™arshe a duniya, kawai dai kar ka wula™anta ni"""

"""Ke bar nan"""

"Ya furta a kausashe kamar ya ce ya shiga uku ""Na san saboda na ce maka ina da aure ne, wasa nake yi"

"don kar ku yi mini wani abun ne na faWa fa, trust me i love you kuma na ji zan iya aurenka a yadda kake, zan baka farinciki walwala da jin daWi ka amince mini ka ji dear"" Moh ya dinga kallon ta wani irin kallo wanda bai ma san yana yi ba,sai dai ba'a tantance kallon na mene yanayin fuskarsa bai bada damar hakan ba, kaifin idanunsa ya saka Safiyyerh ™asa da nata idanun, duk da shaye-shayen da ya ke yi da Waukar wu™a matsayin abokiyar rayuwa da tarin raunukan da suke fuskar bai hana wani irin tsoro da shakkarsa ta gitta a zuciyar Safiyyerh Abdu Marafa ba, wani kwarjinin take hango wa na musamman a fuskar Mutallab Tahhb haibarsa da kwarjininsa mai ban tsoro ga namiji balle Wiya mace sai yanzu take ji ta yi tsaurin idanu wajan tunkarar shi da wannan maganar mai kama da tatsuniya a gare shi, gare shi kallon kin raina mini wayo ya kewa Safiyyerh da tunanin ko ta samu matsala da nata tunanin tunanin ne? Idan ba matsala ta samu na gushewar tunani ba abu mamaki ne gare shi da jin furucinta ya yun™ura zai"

tashi ta riga shi mi™ewa kanta a ™asa hawaye na zuba a idanunta.

"""Don darajar da Allah Ya yiwa Manzon Sallallahu alaihi Wasallama ka saurare ni, ba zan taSa juya maka"

"baya ko da nasani b a kasancewa ta da kai, kai musulmi ne nima musulma ce babu haramci idan mace ta ™aunaci namijin daya kwanta a ™asan zuciyarta, a kullum na ganka sai na ji zuciyata na kiran Safiyyerh wannan shine ™addararki zaSin da kike jira irin namijin da kike fata, idan zuciyata ta kusanci zuciyarka sai na ji tawa zuciyar ta sake buWewa da tarin tausayinka, kullum mutuwa nake da farfaWuwa da soyayyarka ta yan kwanakin nan data rutsa da zuciyar Safiyyerh Abdu Marafa, kullum mutuwa nake da son ka, wallahi...,"" kasa cigaba ta yi saboda kukan daya ™wace mata da gaske, da ace ita ΄ar wasan kwaikwayo ce irin fina finai da ake haskawa sai ta ce a yanzu acting take, duk abin da take faWa she doesn't mean it, iya laSSanta ne kawai ta yi hakanne saboda ta yi kutse cikin rayuwarsa ta san waye shi me ya sa ya zama"

"abin da ya zama, tana son jin labarai mai kama da hikaya ko almara ko na soyayya."

"""Will you love me?"" Ta ce tana marairace masa fuska tare da Wan turo masa jajayen cute lips Winta, ya bi"

lips Win da kallo ta haWe hannaye waje guda ta langwaSar da kai

"""Please, Safiyyerh loves you a nan a cikin nan Wina"""

Ta nuna masa saitin ™irjinta wajan zuciya da yatsarta manuniyya sai ™ifta idanu take. Har lokacin bai ce

mata komai ba kamar yadda ta lura yawan magana ba Wabi'arsa bane yana wanzuwa da shiru da tunanin ya fi masa. A duk maganarta Waya ™are haWe fuska yake yi ya zaro sigari ya kunna ya saka a baki da ™arfi ya zu™i haya™in yana jin saukar haya™in ™asan ™irjinsa ya hura kumatu ya matsa dab ya fesa mata a fuska ya yi gaba abin shi yana taku WaiWai irin he don't care. Safiyyerh ta bisa da idanu ta yi shiru ta ji ta damu sosai a ranta tana Astagafirulla data tuna da gaske ita matar aure ce matar Aliyu Abdu Marafa ce ita

halaliyyarsa ta jingina da jikin bango tana lumshe idanunta.

"Moh bai ™ara dawowa cikin gidan ba, har dare ya nutsa bama shi Waya ba kusan dukkan su basa nan ta"

"dinga sallah tana addu'a har girki ta yi musu ta ajjiye amma ya yi sanyi. Tana haka ta ji an buWe gidan da sauri an shigo ta buWe ™ofa ba tsoro ta fito Mangal sai nishi yake yana kallon ta, da gudu Goje shima ya shigo yana shigowa kuma ya rufe ™ofar ya zube a ™asa ta kalle su cikin sigar damuwa ta ce ""Ka rufe ™ofar"

"shi kuma fa?"""

"""Bai shigo ba?"" Ta jinjina masa kai ya mi™e tsaye ya ce ""Jagwal kenan, ai kuwa bama tare"""

"""Innalillahi kamarya like how bakwa tare?"""

"""Ke bafa wani abu saSe kawai ki je ki yi kasa ko"". ""A'a don Allah ka je ka nemo shi ka ji Wan'uwanka ne fa"

"idan wani abu ya same shi ai ba za ka ji daWi ba, shi ma ba zai bari komai ya same ku ba"" ya yi murmushi ta lura yana da fara'a ba kamar sauran ba ""Ubangiji nada kyakkyawan tanadi a rayuwar Mai dawa, ba"

"yanzu zai mutu ba kin ji ko?"""

"""Na kawo muku abinci?"""

"""Dar daidai kenan kin taimaki ΄an hanjina jagwalo shi nan a Satar da shi a rufawa ciki asiri"" abincin ta"

"Wakko ta kawo musu duk yadda taso su wanke hannu ™i sukai Kodayake haka ogan nasu shima yake. Har bacci ya Wauke ta bata saka shi a idanunta ba. Sai da asuba ta fito dafa ruwan wanka kamar jiya haka ta ganshi ya yi shiru yana kallon sama, tunanin maganganun da Abbasa ta yi masa yake da abin da Ali wali"

ya dinga nanata masa akan Safiyyerh.

"""Bai kamata gwarzona ya wanzu yana tunanin da zai iya illata masa rayuwarsa da zuciyarsa ba, haba"

"mafaraucina"" ya juya ya kalle ta, ta kashe masa idanu ta ce ""Yes, ba farautar dabbobi kawai ka iya ba ka yi dacen farautar zuciyar ΄ar Professor Abdu Marafa"" kamar a buge yake haka ta lura da shi musamman yanayin zaman da ya yi, sai a lokacin ta lura da yankan dake damtsen hannunsa ta ™arasa ta du™a ta ce ""Subuhanallahi faWa ka je ka yi haba mai sunan manya, Muhammad Mutallab fa masu sunanku salihan"

"banyi ne"""

"Ya du™ar da kan shi ™asa ta je ta Wakko kayan da Goje ya kawo ta zauna dab da shi, ta kamo hannun nasa"

"sarai ya jita amma bai kula ta ba, tunani ne ya addaba masa. Ya shiga hura masa iskar bakinsa ganin"

yankan na kumfa data saka magani ta gama yi masa treatment ta kalle shi taga ya rufe idanu mi™ewa ta

yi zata fita kamar daga sama ta ji ya ce

"""Cikakken sunanki"""

"""Safiyyerh Abdu Marafa"""

"""Cikakke"" ya sake maimaitawa ""Haka sunan yake fa Jarumi"""

"""Shi Abdu?"""

"""E, sunan daddy kenan Abdu"" ya buWe jajayen idanunsa ya watsa mata su ta yi saurin yin ™asa da nata"

"idanun ta fidda ran zai yi magana har zata juya ya ce ""˜arya, idan na tuna miki na kwaWa miki mari ko?"". ""Allah ni dai haka na sani babana ne fa"""

"""Uhmm"" ganin kamar da magana a bakinsa kuma a buge yake ta matsa ta zauna ta ce ""Jarumi, do you"

"want to say something? Say it. Ka ce wani abu Jarumi"""

"""FaWi mana Jarumi"""

"""Tiger"" ya ce a hankali ta ce ""Me ka ce? Ban ji ba"""

"""Ammm, hmm kika ce ba ki da aure?"" Ta ce ""E, bani da shi like a told you"" ya buWe ido ya zura mata"

"idanu yana ta kallon ta da ™yar ya iya cewa ""za ki so ni?"""

"""Zan aure ka na rayu da kai idan ka faWa mini labarinka waye kai?"" Ya sake yi mata shiru ""Ina ji"""

"""Zana ba ki labarina idan za ki aure ni"""

"""Ni Safiyyerh na yi maka wannan al™awarin zan rayu da kai a duk yadda rayuwa ta yi da kai Jarumi"" ya"

"mi™a mata tafin hannunsa a hankali kamar mai jin tsoro ta kalli hannun cike da rashin fahimta, jiran ba'asi take shi kuma ya yi shiru sun Wauki minti biyar da wasu da™i™o a hankali ya sake furta ""Promise"" ta dinga kallon hannun kafin ta yi Astagafirulla da tunanin Ubangiji ya yafe mata saboda igiyar auren wani ce a kanta ta Wora Wan ™aramin hannunta cikin nasa, tana sawa ya dam™e kamar abin da yake jira kenan ya yi shiru ya lumshe idanunsa muryarta na rawa ta ce ""I Promise you Jarumi"" yana ri™e da hannun bai cika ba bai kuma yi magana ba can ya sake ta, ta fara masa magana sai dai ko tari bai kuma yi ba"

tunaninta bacci yake yi ta dinga kallon shi tana son hango kyau ko ko muninsa.

A daren ranar su Goje basa nan sai shi Waya yana busa haya™i a sama yake jinsa sosai ya ji an buWe ™ofa

"an shigo, maza ne har su huWu sun rufe fuskokinsu ya dam™i wu™arsa kafin ya mi™e Waya ya cafki wajan yankan da Safiyyerh ta gyara masa ya janyo hadda naman wajan suka fara kokawa yana buga su da ™asa, cikin sauri Safiyyerh dake bacci ta farka zata fito daga cikin Wakin ya yi baya da ™arfi ya tura ta ciki ya rufe ™ofar ta taga ta le™o tana kiran shi, taga ya Waga wu™a ya sokawa Waya a gefen wuya ya ™ara soka masa a ciki ya watsar da shi can gefe yana kakari, Safiyyerh ta zaro idanu tana rufe baki saboda ihu za ta yi ganin yadda aka yi kisan kai akan idanunta, bata san mene ya faru ba taga Waya ya zaro sirinjin allura ya zirarawa Moh a damtsen shi, ya sake zaro wani ya yi masa da azama Moh ya Waga wu™ar hannunsa ya sari wanda ya yi masa hakan ya goce ganin sun yi masa allurar suka ja wanda yake kwance kamar gawa"

"suka bar gidan, a hankali ya yi baya ya zube saman kujera jini na Wiga jikinsa"

"Ilahirin jikin Safiyyerh rawa yake cikinta ya ™ulle ta shiga uku, kisan kai aka yi akan idanunta haka dabar"

"take dama? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Moh kuma minti goma ya yi yawa ya ji zufa na yanko masa jikinsa ya yi sanyi wani irin ba™on al'amarin ya fara ziyartar gangar jikinsa yana sauka a mararsa, abin da bai taSa tunani ba idanunsa ya shige ciki ya Wauki ™waya ya zura a ™asan harshen shi da tunanin zai daina ji, amma ina kan shi ya hau ciwo ya mi™e da ™yar ya nufi Waki jin tsigar jikinsa na mi™ewa da zubewa sanyi na ratsa shi komai na jikinsa ya bubbuWe al'amarin bu™atuwar wani abu. Ya kwanta ya yi shiru can ya mirgina ya yi rufda ciki ya lumshe idanunsa ya ji™e shimfiWar lokacin Waya da zufa da jinin da yake zufa a jikinsa, ya rasa ciwon ciki yake ko mara ko zazzaSi? Jijiyoyin kan shi sun mi™e raWau lallai ya ji akwai abin da yake bu™ata ya dinga juyi ya shanye sigari kwali wajan biyu amma ba abin da ya sauya ba zai ce"

tsautsayi ne ya kai shi Wakin Safiyyerh ba saboda kawai tsintar kan shi ya yi a ciki.

Safiyyerh na bacci ta ji hucin numfashin mutum a fuskarta ta buWe idanu da sauri ihu za ta yi ganin

"fuskarsa kamar zai haWe da tata ta yun™ura zata tashi ya saka hannu ya mayar da ita kwancan ""Dan Allah"

"karka mini komai ka yi ha™uri ba zan sake kula ka ba, innalillahi na shiga uku daddy ka yi na tuba don"

"Allah"" bai kulata ba yana daga dur™ushen da yake dab da ita ya mi™a hannu ya kashe wutar Wakin gabaWaya."

LAST FREE PAGES

Waye Mutallab?

Waye Scorpion?

Wace Safiyyerh?

Waye Daddy?

Mene FS WORLD INVESTMENT COMPANY?

Labarin Mutallab da tarihinsa ya fi wannan da muke ciki yanzu ai za ku zo jin wannan soyayyar ta

™uruciya ba?

Mene yake saka a fara daba da shaye-shaye?

Wanne ganganci iyaye suke yi akan yara?

Mece siyasa da cikakken tarihin dimokuraWiyya?

Za ku su sanin ya ake mulki a ™asar nan?

Har ku yi supporting yaran ku?

Soyayya na saka shaye-shaye ne ko daba? Me ya sa Mata har uku suka mutu ta sadanadin MOH me ya sa

ya kashe matarsa SAFIYYERH?

YAUSHE SAFIYYERH TA HAIFI YARO?

maza hanzarta yin payment chat with me on WhatsApp 08164069385

BRIGHT PENS... 2ND BATCH











"[10/1, 9:36 PM] Nanameera: *d'=Ψ%έ MUTALLAB d'=Ψ%έ*"

Page 1

Nimcyluv

Bright pens. second batch

*Marubuciyar. d'=Ψ%έ*

*Mijin malama*

*Munafukin miji*

*Moon*

*Idan ba ke*

..... E.t.c and now *MUTALLAB*

"* for some reasons. Akwai copywrite kar a haWa mini ducoment, banda YouTube a bar mini kayana"

ha™™ina ne*

"Jami'an tsaro ne ta ko'ina cikin kayan kaki ma bambanta, duk da cewa yammacin ranar lahadi ne a watan"

Fabrairu bai hana ta gane fuskarsa ba. Cikin tashin hankali jikinta na rawa da kyarma ta nufe shi tare da

"™o™arin cakomo wuyan babbar rigarsa tana furta cewa ""Shi ne, wallahi shi ne, daman na ce zan gano shi"""

a gigice mutumin dake ™o™arin shiga motarsa da aka buWe masa ya yi baya yana mai ™arewa matar kallo sosai sai dai ya kasa gano ko wace ita? Daga ina me kuma take bu™ata.

"""Wace ita?"" Ya furta yana tambayar zuciyarsa tare da kallon gefe. ""Wallahi shi ne, mugu azzalumi sai ka"

"yi kuka, ka wula™anta "" Jin furucinta ya saka ΄an'jarida dawowa kan ta, suka fara tambayar ""Kin san"

"shine? Mene haWinki da shi?"" Kafin ta yi magana wani ya ce ""Arrest her, ku kamata"""

"A hankali ya jingina da jikin motar can ya numfasa yana kallon yaronsa ya ce ""Wace ce? Na santa ne? To"

"me ya sa take abu kamar ta sanni?"""

"""Sir da gaske ta sanka bana jin ko mutuwa ta yi ta dawo zata manta fuskarka, kuma zamanta a raye yana"

"nufin abubuwan da yawa dole a yi wa tufkar hanci, kar a bari ΄an'jarida su samu ganawa da ita, even your securites, wannan matsalar kai da kai ce kuma zata shafi kimarka"" cike da mamaki ya yi ta kallon yaron nasa na tsayin sacanni da ™yar ya cije leSe ya ce ""To ina na santa? Me ya sa zata zama"

"damuwata?"""

"""Sir ita ce wacce ka saka aka kawo maka ita, wacce ka yi wa fyaWe a lokacin ,"""

"""Ya isa!"" Ya ce yana jin jiri na neman Wauke shi, ya dubi tarin jama'ar da suke wajan can ya yi murmushi"

"yana Wauke fuska sai kuma ya ™urawa yaron idanu ya juya ya kalli matar ya gyatsine fuska ya ce ""kuma ta"

"kasance a raye ya haka? To a yi hanzarin toshe wannan Sarnar ya zama kamar ba a yi ba"""

"""Amma me ya kamata a yi mata?"""

"""A yi mata allurar hauka, wacce ake yi duk shekara da wata wata kana a kaita gidan yari, life in prison har"

"ta mutu. Bayan haukan zata mance komai, su ΄an΄an talakawa wama ya damu da su mutu ko su yi rai bata da wani mai tsaya mata kai mutuwa ma za ta yi"" yana faWin hakan ya shige mota. Tana takure a jikin ™ofar Wakin da aka ajjiyeta idanunta ™ur a kan photonsa zuciyarta sai zafi take mata wani abu ya tsaya mata. Da sauri ta juya jin an buWe ™ofa wani mutum ne sanye da farar riga ya rufe fuskarsa hannunsa ri™e da ™aton sirinji iya ruwan allurar da ya yi ja abin tsoro ne, ta fara ja da baya amma a haka ya fincikota tare da yin cilli da ita,ta faWi saman carpet bai tsaya jiran komai ba ya caka mata allurar a ™ashin"

bayanta wajan spinal cord ihu ta fara da birgima idanunta ya shiga ™a™™afewa jikinta na sandarewa ta

dinga buga kanta da jikin bango tana buge-buge a hankali jini ya fara fitowa ta cikin hanci da bakinta

tabbacin allurar ta amshe ta za kuma ta yi aikin da ake bu™ata a jiki da ™wa™walwarta.

******

Cikin sauri suke tafiya a wani Wan dogon lungu mai duhun gaske tsarin wajan gabaWaya a ™untacce yake

kamar zunubin gidan yari. Magana suke ™asa-™asa Waya daga cikin su kuma yana duba agogon dake hannunsa tare da duba cikar lokacin fuskarsa a haWe take sosai. Sai da suka kawo ™arshen ginin suka tsaya ya Waga kai a hankali ya dubi saman da kansa ke taSowa ya Wan rusuna sai kuma ya dubi jami'in

"tsaron dake wajan ya yi masa nuni daya buWe ™ofar. ""Yes sir!"""

Bayan ya sara ya ™ame ya buWe ™aton kwaWon yana toshe hanci saboda wari da zarnin wajan. SP Gali ya

kalli team Win nasa cikin bada umarni ya ce

"""Ku jira nan, idan akwai damuwa zan muku alama na san dai he can't do anything, ba zai iya komai ba"""

"gabaWaya suka jinjina masa kai tare da zagaye ™ofar fuskar kowannen su manne da ba™in gilas. A hankali Sp Gali ya tura ™ofar ya shiga yana dur™osawa saboda rashin girman wajan. Tunda kafin su ™arasu wajan ya san da zuwan nasu har aka buWe ™ofar tare da shigowa, yana dur™ushe inda yake ya kifa kansa a ™asa hannunsa dun™ule ya dam™e abu wanda tun kafin a kawo shi gidan abu yake a hannunsa, yin duniya ya™i"

buWe abun balle a san menene shi.

"""Hey you!"" Sp Gali ya ce yana saka ™afa tare da buge ™afarsa ganin ya™i motsawa, tamkar gunki haka ya™i"

"motsi ya kuma ™i Wago kansa Sp Gali ya shiga kallon wajan ya rasa wanne irin hali ne da wannan yaron mai ba™ar zuciya da taurin kai ya sauke numfashi cikin kwantar da murya ya ce ""Ni idan na ce maka ina da tausayi na yi maka ™arya, amma ka saka zuciyata karaya kana bawa kanka wahala kana bawa jami'anmu wahala. Me zai hana ka sau™a™a mana wahalar nan ka faWa mana gaskiyar abin da ya faru a wannan rana kuma a wannan daren? Me ya sa ka aika abin da ka aikata? Ka kashe matarka, ka kashe ta har lahira kuma ka™i magana shekara uku kenan kana wajanmu ka rainawa hukuma hankali da kotu, kai baka da zuciya ne dame kake ta™ama saboda kana da tsari a jikinka ™arfe ba zai ratsa naman jikinka ba, muna da kalolin azaba nau'i-nau'i amma gaskiya muke bu™ata, ka amsa cewa ka kashe matarka a zaman"

"kotu na yau shikenan sai a yanke maka hukunci daidai da zaluncin da ka aikata"""

"Har Sp Gali ya kammala maganarsa bai motsa ba, babu alamun zai Wago kai balle ya tanka. Sp ya mi™a"

hannu zuwa hannun mutumin dake dun™ule da abu zai amsa a firgice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login