Showing 189001 words to 192000 words out of 214217 words

Chapter 64 - Mutallab Part 1 and 2 by Nimcyluv

Nimcyluv   

05 Jun 2026

63

su, daman

koyaushe kamar ta shafa jambaki haka lips Winta suke anytime.



"Me ne ba za ki iya ba?"



Ya tambaye ta, a lokacin da yake sanya tafukan hannayensa ya ri™o ™ugunta zuwa kusa

da shi, yana sauke mata numfashi a fuska tare da sanya yatsa guda ya shiga zagaye

fuskarta da shi, idanunsa ciki.



"Ba zan iya abin da kake so ba"



"Still dai, Maj bai fahimta ba"

"I can't sleep with you"



Sai ya ja numfashi ya ce "No need, ni zan iya ai, kar ki ji War"



Ta girgiza kai, tana ™o™arin yin baya, sai ya kasa bata damar yin hakan saboda wani

irin azababben shau™i dake fisgar zuciyarsa zuwa ga Maamah, shau™in da bai taSa

nutsuwa ya fahimci cewa yana da shi ko babu ba, bai Wauka yana da cikakkiyar lafiya

da kuzari mai zafin har hakan ba, yana zargin kansa a lokuta mabanbanta idan ya ga

mace bai ji yana developing any feelings a kan ta ba, bai taSa jin sha'awar wata

Wiya mace a duniya ba, abokan shi sojoji sun sha attempted haWa baki da mace ko

zata ja hankalinsa amma ba su yi nasara ba, lokaci da yawa su kan kalle shi su ce.



"Baka da cikakkiyar lafiya Maj" sai kawai ya yi gyatsine idan ya so, idan bai so

ba, ko kallon su ba yayi, har blue films sukan sawa ya ji sounds Win a kunnensa

amma bai taSa damuwa ba. A duk sanda zai dawo gida ya Wora idanunsa a kan Aafiyyah

a lokacin ya ke sanin cewa shi rayayye ne, da numfashi a jikinsa har yanzu bai gama

macewa ba, a ranar yini zai yi yana kallon picture Win Aafiyyah har ya ji nutsuwa,

irin relief Win da Aafiyyah ce kawai ke samar da shi a zuciyarsa, ya jure zaman

gida ba mace, ya jure zaman jeji babu mace, ya jure zaman barrack ba mace, tsayin

kwanaki, tsayin satuttuka, tsayin watanni, tsayin shekaru sama da talatin da biyar

ko bakwai, yana namiji kuma mai lafiya ya kasa tarayya da kowacce mace, sai ya ji

cewa ba macace baya so ba,wacce ya bawa dukkan zuciyarsa ita yake bu™ata a jikinsa,

ita yake bu™atar ya sanya girmansa cikin duniyarta wacce sunna ta bashi dama, bai

taSa mafarkin samun Aafiyyah a matsayin matarsa ba, domin ya gama amanna cewa ita

lil sis Winsa ce, amma zuciyarsa ta kasa hango masa kowacce Wiya mace sai Maamah,

wannan dalilin ya saka baya ™aunar dawowa hutu domin yana shiga tsakanin azabar da

baya iya jurewa sai ya shigo cikin bedroom Win Aafiyyah ya zuba mata idanu, ya raya

daren hannunsa sar™afe cikin nata yana kallon yadda take bacci peacefully.



Tunaninsa ya dawo gare shi lokacin da ya ji tana cewa "Yaya...,"



Sai ya dube ta, duba na tsanaki wani abu na sauka a jikinsa ya ce



"Ko dai ba ki yi na'am da auren bane?"



"Kamarya?" Ta ce cikin raunin murya.



"Look Maamah, ke ba yarinya bace kin fahimci me nake nufi ok?"



Ta jinjina kai, hawaye na cika idanunta ita bata san me ya sa take tsintar kan ta a

cikin wannan yanayin ba, ba auren ne bata so ba, ba kuma Aliyun bata so ba, ita

birninta ma a yanzu bai huce taga sun zama abu Waya ba, ta cikawa Paaahh burinsa na

ganin tsatsonta, amma ta gaza ta rasa meke going a cikin kwakwalwarta, tana da

wayewa daidai ita wacce ta isa ta san mene aure me kuma ake nufi da aure, amma

tsoro yana mata shamaki da abin da Maj yake bu™ata, dole ta ji tsoro saboda tana

yawan jin yadda dararen farko da ake yin huka dasu, amma nata tsoron na musamman

ne, bata san abin ba bata san ya ake yi ba, amma reflection Win da take tsintar kan

ta ciki shine yake ™o™arin tarwatsa tunaninta da nutsuwar da take ™o™arin sama musu

ita da Maj Win, itama tana bu™atar mijinta.



Rau-rau idanunta ta yi ta ce "Kana jin zafina a cikin zuciyarka ko? Kana jin kamar

bana ™aunarka?"



Ta girgiza kai "Ba haka bane, amma ka bani lokaci ka ji?"



Maj ya kasa magana, shi maganarta ma azaba ce a ckin zuciyarsa kamar ana yayyafin

wuta haka yake ji a jikinsa ta marairace fuska ta ce "Please Yaya, give me some

time"

"Why Yaya?" Ya tambaya.



Sai ta langwaSar da kan ta zuwa gefe, tana yarfe hannunta cike da shagwaSa wacce

daman halin Maamah ce ta ce "I am sorry Hubby"



"Uhm.... Huh..." Ya ja numfashi ya sauke sai kawai ya jata zuwa cikin jikinsa ya

rungume ta, a ™o™arin samawa kan shi nutsuwa, fat fat fat haka zuciyarsa da tata

suke bugawa at the same time, bugun zuciyar Maj dai har tsoro yake bata. Suna

rungume da junan ta ji yana yi mata wani abu, ta fara jurewa jin ya tsananta ya

saka ta yi saurin Wago kai ta kalle shi tana faWin "Washh"



"Sorry, i never hurt you"



Ta yi shiru a kunnenta ya raWa mata "I want to..... I want to" ya rufe ido da ™yar

ya ce "I want to be okay with you, ba abin da kike tunani bane, kawai mu yi sharing

warm Win jikin juna, agree?" Sai ta Waga masa kai, ya sumbaci goshinta ya sake

sakar musu ruwa. Ya rigata fita daga cikin bathroom jikinsa sanye da bathrobe yana

tsane kan shi da towel, ta bi bayansa da kallo bayan ya fita ta dawo da tunaninta

ta zubawa madubin dake banWakin idanu, ba tunani take ba, kan ta take kallo ba, ta

sauya, wanne irin sauyi? Ita dai tabbas ta san cewa ta sauya, akwai kuma abin da ta

yi missing a rayuwarta, abu mai tsananin muhimmaci a rayuwarta da duniyarta, what

is this? Mene haka daya rabu da rayuwarta? Ta yi believing cewa idan babu abin, to

babu ita, babu Safiyyerh without abin no Safiyyerh, nutsuwarta shine fahimtar me ta

rasa a rayuwarta?

Murmushi ta yi mai sanyi wanda ya haddasa lomawar dimples Winta, sai kuma ta Sata

rai wata kunya ta kamata sanda ta tuna ashe Maj ya kalle mata ™irjin da take

matukar ji dasu kamar rai, daurewa kawai take yi amma mu'amala da mutumin da take

tunanin yayanta ne, mahaifa Waya ta samar dasu It's very difficult to her, nauyi

take ji, girman abin take gani. Sai da ta shafe tsayin lokaci a banWakin kafin ta

yi wanka ta fito sanye da towel jikinta na Wigar da ruwa, da sauri ta shirya bayan

ta shafa oil Win S Bayero da haWin humura da kwalacca masu sanya nutsuwa a zuciyar

mutum, ta gyara sumar kanta ta Waure da ribbon. Sallah ta gabatar harda shafa'i da

wutiri tana idarwa ta fesa turare ta fesa mouth mint, wardrobe ta je ta Wauki rigar

bacci D&G couples iya cinyarta ta sauka ba bacci take ji ba, sai ta Wauki laptop

Winta ta Wauka da kuma wayarta ta nufi parlour ta zauna sai taga Maj baya ciki,

program Win rediyon aka fara har ta fara danne-danne a laptop ta ajjiye saboda

muryar mahafinta da ta ji wanda mutane da yawa sukewa kallon Professor Abdul-Johar

Marafa madadin Dig Abdul-Johar Marafa. Bayani yake yi sosai akan zaSen da za'a

gudanar na ™ananan hukumomin da suke jagorantar Kano/Nigeria yana kira tare da

gargaWi ga matasa akan su guji tayar da husuma a wajan zaSe kowa ya yi zaSe ya koma

gida cikin iyalansa, masu kula da harkokin zaSe suji tsoron Allah wajan kula da

hak™in al'umma na daga abin da suka zaSa, a kare musu ™uri'unsu har zuwa inec a

guji tayar da fitina kar a sake kuWi ya rijiyi mutum wajan siyar da kimar shi ta

Wan adam a kiyaye shaye-shaye ko shan abin da zai gusar mak da hankali har ka

aikata Sarna.... Haka Dig Abdul-Johar ya dinga bayani yana janyo hankalin mutane

cikin siga ta siyasa.



Aafiyyah wayarta ta Wauka ta kunna network ta shiga Facebook, sai a lokacin ta ha

followers Winta har sun je 1.m, ta jima rabon da ta yi rubutu. Sai ta shiga wajan

da aka saka what is on your mind? Photon Dr Abraham Denial David ta Wakko ta yi

posting tare da caption Win  Cikar mafarkin kowanne matashin Wan Kano



Within 2 minutes, sai comments sama da 200 a lokacin gudu. Wani kira yake who be

this? Wani ya ce shima har da shi a masu neman takarar, wani kuma ya ce bayan

ubansa Denial David ya mulki Germany matsayin shugaban ™asa, shine mu kuma zai

mulke mu? Wani ya ce, ai sun saba satar kuWin jama'a, ka sani ko karayar arzi™i ce

ta same shi? Wani ya sake replied da "An ce fa Abraham Win ba musulmi bane"



Ta dinga duba comments Win sai ta ji ta karaya, amma akwai matured people da suke

comments tare da reposting. Wani suna ta gani Alhassan Abraham Denial, ya yi liked

posting Win, ta yi saved sunan a kanta, sai taga Ibrahim Qasim ya yi like ya kuma

yi comment da "support" wani mutum ya ce "Ni dama mai kamfanin ArWos group aka bawa

mulkin nan, saboda yana da tausayin talakawa da ™o™arin taimako ga sau™a™awa mutane

wajan siyan kayansu, ni kam hundred percent zan yi supporting nasa."Who is the

owner of the company?" A new person a conversation Win ya tambaya. "Ban sani ba, ba

wanda ya san shi ai" daga nan aka dinga comments yawancin mutane ra'ayinsu akan Hon

MaWatai yake sai masu Eng Ali wali, da yawan matasa kuma ra'ayinsu goes to Dr

Abraham Denial David.



Highlighting ta shiga, sai taga just now posted Win Alhassan photon ArWos group ya

saka da caption Win



"Kuna son sanin me kamfanin?"



Mutane suna ta faWin Yes, yes sai wani me suna Ibrahim Khalil ya ce



"Don't do this Alhassan"



Ta ji ranta na Saci, sai ta nufi X nan ma ta yi posting Instagram ne da Tiktok ne

daman bata yi bata ra'ayin shi. Bayan ta gama ta ajjiye wayar ta samu kan ta da yin

addu'a sosai ita kawai tana bu™atar Dr Abraham Denial David ya samu nasara haka

kawai Hon MaWatai da Eng Ali wali ba su yi mata ba. Kashe Laptop ta yi ta mi™e ta

nufi bedroom, har lokacin Maj baya ciki sai ta damu ga lokacin ya ja, kawai ta

kwanta abin ta. Cikin dare ta juya kaWan sai ta ji wayam babu shi ta duba 3:20 na

dare, ga gidan ya yi mata girma mi™ewa ta yi ™afarta cikin bedroom slippers, a

hankali take tafiya ta zo tsakiyar parlour ta ji an rungumeta ihu za ta yi ya

saurin cewa "Shiiii"



"Hubby"



Ya yi shiru, sai ta kunna haske suka haWa ido ta dinga kallon shi from head to toe,

ba™a™en kaya ne a jikinsa hannunsa ri™e da bindiga



"Aiki cikin dare?"



Ya Waga mata gira, bai bata damar magana ba ya ja hannunta zuwa cikin makeken

bedroom Winsa ya ce "ki kwanta nan, zan duba abu ok"



Ta jinjina kai, idanunta cike da bacci tana kwanciya bacci ya Wauke ta, cikin

baccin ta jita a jikinsa da kuma abin da yake mata, ta yi saurin buWe ido tas,

™irjinta na bugawa subhi ya kusa, sunayen Allah take kira da ™o™arin ganin ta jure,

again wannan reflection Win take gani, ta yun™ura a gigice jin yana ™o™arin shigar

ta duk da bai ma Wauki layi ba. "Yaya Please, don Allah ka bari wayyo" take faWa

jikinta duka Sari yake yi. Muryarsa na breaking ya ce "Ki cire tsoro Safii, ina

bu™atar ki?" Girgiza kai ta shiga, sai yaga jikinta ya saki zufa ta ji™ata sosai ya

zare jikinsa ya mirgina ya janyo jikinsa bayan ya ™ara gudun ac, ya dinga shafa

kanta cike da kulawa yana matsa hannunta da danna ™irjinta. "Hmmmmmm"



Ta ja numfashi sai kuma ta yi saurin razana "Ban so, ban so" ta ce a gigice.



"Shhhh, na bari ok?"



Sai ta buWe ido suna haWa ido gabanta ya faWi taga idanunsa jawur jikinsa zafi zau

sai ta fashe da kuka sosai ta ce "Ka yi ha™uri don Allah, don Allah Maj" bai magana

ba sai bayanta kawai yake bubbugawa yana jin kamar ana tsaga masa mararsa, kamar

mararsa za ta yi bindiga saboda ciwon da take yi masa. Shiru ta yi saboda abin da

take tunani "Are you ok?" Ya yun™ura ya jingina da ita a frame Win gadon.

"When you are with, am completely ok" ya ce silently.



"To yaya, gobe zan bari ka yi kaWan ka ji? Ina jin tsoro ne"



"To zan jira a bani kaWan Win" ya ce yana lakace karan hancinta.



"KaWan fa?"



Ya Wage mata gira, sai ta ji tausayinsa sosai ganin kallon da take yi masa ya ce

"To ΄ar Dig Abdul-Johar"



"Are you ok?"



"Maybe..."



"How can i help you?"



Ya ce "Sleep with me"



"Zan yi, amma banda...," sai ta yi shiru sai ya kwanta kawai bai ce komai ba, domin

nauyi bakinsa yake masa daman sharrin soyayya ce da kan iya juya mutum da sauya

masa Wabi'a shi ya sa har ya iya buWe bakinsa da zuciyarsa ga Maamah. A hankali ta

bi jikinsa ta kwanta ta shige sosai, sai ta ji ya kama hannunta a kunne ya ce "And

help me with this...," ya ce yana Wora hannunta a mararsa ta runtse idanunta saboda

tsananin kunya ya ce "Common matar maj"



*

Morning/news

Kamar kodayaushe VOA sune suka fara bayyanar da harin da aka samu da aka kaiwa Hon

MaWatai again, amma ba'a yi nasarar kashe shi ba, kuma aka bada tabbacin Scorpion

ne ya kai harin saboda shaidar da yake bari a kodayaushe. Nan take sanarwa ta fita

dasa hannun gwamnati akan janyo hankalin jami'ai na ganganci da rayuwar manyan

mutane da suke yi, kuma gwamnati ta yi Allah wadai da rashin iya aiki daga jami'ai

da suke da alhakin kare rayukan ΄an siyasa da dukiyoyinsu kai tsaye kuma da Fid

ake, domin an daina batun SSS tunda daga cikin SSS aka ware team guda masu matsayin

Federal investigation department alhakin kama Scorpion ba'a kan DSS ko SSS yake ba,

ba kuma akan National security Organisation (NSO) ba kuma hak™in hukumar NSA bane

ba kuma hak™in NIA bane balle kuma DIA ba, ba kuma gabaWaya aikin akan FCID ne

wannan dalilin ya saka tun 7:00 Aafiyyah ta bar gida lokaci AA MAJ na bacci bai san

meke faruwa ba.



Aafiyyah ta zubawa Muhammad idanu wanda yake numfashi a hankali saboda wahalar da

aka gama gana masa a yanzu, fitar Dig Abdul-Johar kenan da shi da sauran team Win

ita kaWai ta yi saura. Black Win Suit ce a jikinta mai riga da wando ta yi rolling

kanta da red Win vail takalmin ™afarta ma red ne, black shade glasses ne a fuskarta

lips Winta sun yi wani yirrr dasu sai glowing suke yi. Ta harWe ™afafuwanta tana

study Win Muhammad wanda suke tunanin Scorpion ne kuma Mutallab cikin nutsuwa ta ce

"waya taimaka maka ka fita daga wannan wajan har ka kaiwa Hon MaWatai hari?"



Bai kulata ba, kan shi ™asa ™irjinsa na Wagawa a hankali. "Har yanzu jikinka bai

gama laushi ba ko?"



"Leave!"



Ya ce a ruWe duk sanda zai ji muryarta zuwan shi Lagos yake tunawa. "Scorpion" ta

ce, cikin sweetness voice Winta sai ta mi™e tsaye ta dawo kusa da shi, ta du™a dab

da shi ya yi saurin rufe idanunsa ya haWe fuska tamau "Kawai na ji ina jin tausayin

ka yau, ka bani amsa ya aka yi ka fita? Akwai munafukai ne cikin team Win mu ko

ya?"

Ya share ta.



"Me ya sa kake son kashe Hon MaWatai da Eng Ali wali?"



"Dalilin daya saka na kashe Alhaji Lawwalli da Alhaji Sadu™u" ya bata amsa.



"Me dalilin?" Ta tambaya, tana bin zagayayyiyar ba™ar fuskarsa da kallo, tana

mamakin yadda take jin muryar Kimiyya a cikin bakinsa, sai ta fara tunanin ai

Muhammad ta sani da Kimiyya's voice, me ya sa ta ji muryar yanzu a wajan Scorpion?

Bayan haka kamannin Scorpion yana mata kamar wani, ta yi shiru tana tunani. Sai ta

katse tunanin saboda kan ta daya fara ciwo "mene dalilin?"



"Ki je ki tambayi Hon MaWatai da Ali wali, ki ce musu dalilin daya saka na kashe

Alhaji Lawwalli da Alhaji Sadu™u shine dalilin daya saka nake neman rayuwarsu,

wannan dalilin daya faru a garin Rano har suka sauya mahaifa saboda wannan dalilin,

kuma suka sauya daga fulani zuwa zalla Hausawa, sun san dalilin sai su faWa miki

komai, daga nan sai ki zo wajena ki gani, akan gaskiya nake bibiyar rayuwarsu ko

akan ™arya, daga nan zan ga kalar naki adalcin za ki sake ni ki kama su ne ko za'a

ba ki cin hanci" ya ce yana fesar da numfashi sai ga jini ya fita daga cikin

hancinsa. "Ka faWa mini waya fitar da kai jiya daga cikin wajan nan"



"Hon MaWatai" ya bata amsa.



Da sauri ta mi™e tsaye jikinta na rawa ta ce "What? Hon MaWatai akan wanne dalilin,

mu da muke kare rayuwarsa shine ya fitar da kai? Akan wanne dalilin kenan kuma?"



"Gudun kar na fallasa asirin su"



Bata saurari Muhammad ba, ta mi™e da sauri tana ciro. Id card Winta, da

bindigoginta guda biyu ta soka cikin aljihu ta saka shade glasses Winta, sa™o ta

turawa Dig Johar, kana ta yi waje. Muhammad ya bi bayanta da kallo musamman hips

Winta yana lumshe idanunsa ya furta "Sophie"



Tana fita mota ta shiga bata tsaya jiran sauran team Win ba, cikin ™warewa a

driving ta shiga kwarara gudu saman kwalta, tana ta kiran number Kimiyya amma baya

Wauka. Daman duk wani waje da Hon MaWatai ke zama Fcid sun sani, a ™ofar gate wasu

securities suka tsayar da ita, id card ta nuna musu sai suka sara mata ta shiga, ko

gama daidaita parking ba ta yi ba ya fito cikin sauri-sauri tana catwalk haka ya

shiga cikin parlourn idanunta rufe bata lura da mutanen da suke wajan ba ta nufi

wajan Hon MaWatai ta ce



"You are under arrest Hon BoWejo MaWatai" ta ce tana Worawa MaWatai bindiga saman

kan shi.



"Waya ba ki permission na kama shi? Akan wanne dalilin? Ina arrest oder?" Ya ce

yana zaro bindiga.



Without looking at him ta ce



"Sp Ghali Gaddafi, shut up"



Domin sarai ta Wauki muryarsa a cikin kunnenta ta dubi Hon MaWatai ta ce "Alhaji

BoWejo ko?"



"Waye haka?" MaWatai asked.



Tana sake daidaita bindigar akan MaWatai ta ce "Kodayake a Fs world kake matsayin

Alhaji BoWejo ko? A siyasa kuma Hon MaWatai? Good nice one. Safiyyerh A Marafa bata

zo a matsayin Manager ta Fs world ba, yanzu ina matsayin Safiyyerh Abdul-Johar

Marafa staff a Federal investigation department, bana jira wajan bani permission

domin ina da hujjar kamaka akan abin da ka aikata"



"Safiyyerh cire bindigar nan"



Cewar Sp Ghali. Sai ta zaro Waya bindigar ta ce "Sp Ghali Gaddafi shut up or

else....," ta taune lips Winta ta ce "Matsayinka daban, nawa daban, kuma ina sama

da kai wallahi ka sake yi mini magana zan harbeka tabbas"



Hon MaWatai kallon Aafiyyah kawai yake yi idanunsa jajur ya mi™e tsaye ya ce "Dame

kike ta™ama? Jami'an FCID bamu suke bawa tsaro ba, yanzu kira Waya zan saka a cire

ki gabaWaya stupid girl, ke ba ki da Wa'a ko? Kina crossing limit Winki? Akan wanne

dalilin ma za ki zo mini gida?" Ta ce "Ka saka a fitar da Scorpion saboda kada ya

faWi gaskiyar abin da kuka aikata kai da sauran mutanen? Saboda kada ya fallasa

asirinku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login