Showing 210001 words to 213000 words out of 238465 words
murmushi,
zama yayi shina yana mayar mun da murmushin yace
"Ina jinki, wannan albishir din da kika ce zaki mun fadi ina jinki".
"Oh ga mahaukaci yana magana shine dukkan ku zaku mun shiru ko? Malam tashi ka fita
ke kuma Ma'u zaki san ni kike wulaqantawa akan wani can dan iska da be san
darajarki ba" Bashir ya fada a haukace kamar ze rufe mu da duka.
"Ko dai mu bari anjima na gaya maka a waya? Kaga yanzu akwai hayaniya bazata barmu
mu tattauna da kyau ba kuma maganar tana da buqatar nutsuwa sosai" na fada ba
tareda na mayar da hankali akan shirmen Bashir ba
"Aa muje waje toh ko cikin mota dangaskiya kika ga na tafi ba tareda naji dalilin
kiran nna ba toh inaga yau bazan iya bacci ba"
Dariya nayi na miqe ina cewa
"Gaskiya dai muje nasan ko ka ji din ma duk haka take be zama lallai ka iya bacci
ba yau" fizgoni da akayi baya yasa nayi shiru ina gama daidaita tsayuwata kuwa na
kwashe shida mari a mugun fusace nace
"Rashin kamun kan nawa be kai kowanne gaja ya ringa dora qazamin hannunsa a jikina
ba" na waiwaya na kalli Yusuf da yanayin fuskarsa ya chanza zuwa matuqar bacin rai
nace
"Yusuf bazan iya magana yanzu ba saboda raina ya baci, kaje kawai ka gayawa Alhaji
Qarami sati biyun daya saka sunyi yawa a mayar dashi Juma'ar nan me zuwa"
"Bangane abinda kike nufi ba Asmy? Me za'a dawo dashi wannan juma'ar ko daurin
auran mu kike nufi?" Ya shiga jero mun tambayoyin a rikice, wani mugun kallo na
jefawa Bashir daya dafe kunci yai mutuwar tsaye nayi kafin nace masa
"Haka nake nufi ko yayi maka wuri da yawa.." kafin na idar da maganata ya kife a
gurin yayi sujjada ya dago cikin wata kalar madaukakiyar murna ya riqo Bashir yana
cewa
"Nagode Nagode Bashir ka gaya mun dame zan biyaka a rayuwa? A da na dauka a
matsayin babban abokin Adawa ashe ban san banida masoyi sama dakai ba tunda gashi
kayi silar da zan mallaki muradin zuciyata.
Kai na rantse ka shirya samun double promotion, a ina kake aiki? Koda yake barshi
zan binciko da kaina" seya sake shi ya juyo ya kalleni
"Wife! Ina fatan wannan hukuncin ya zama mafi Alkahirin hukunci da kika taba
yankewa a rayuwarki bari naje zamuyi waya" ya kwasa da gudu kamar yaro ya fita,
seda naga rufe qofar sa kafin na juyo kan Bashir muka hada baki ni ina cewa
"Fitar mun daga gida kafin nayi maka tijarar da baka taba zato ba dan daman saboda
shi na daga maka qafa kar nayi abinda zan zubar da mutunchi na a gabansa"
Shi kuma yana cewa
"Aure zaki daura da wani namiji nan da sati daya Ma'u? Dagaske zaki iya rayuwa da
wani bayan ni? Nasan kinyi ne dan ki baqantamun rai na yarda amma ki janye dan
girman Allah.
Bana nufin duk abinda na fada subutar baki nayi da kishinki da yake damuna amma
kema kinsan ba abinda nake nufi ba kenan" ya fada yana durqusawa kamar ze kamo
qafafuna.
Juyawa nayi ina cewa
"Karka ja nayi abinda yayanka zasu tsaneni Bashir tunda sauran mutunchin juna a
tsakanin mu ka fita, badai ni ka kira mara kamun kai ba? Ka jira na fito daga daki
yau zan nuna maka qarshen rashin kamun kai kaji ko" na shige dakina ina tunanin me
zan aikatawa Bashir da zan nuna masa bashi kadai ne saitin kansa yake gocewa ba,
nima wani lokacin nawa notinnan suna tabuwa.
Posting se baba ta gani ππΌππΌππΌππΌ
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 61
"Ma'u, Ma'u ki tsaya kiji wallahi ba abinda nake nufi ba kenan kema kin sani
kishinki ne ya saka bansan ma mename fada ba. Dan Allah kice mun wasa kike yi ta
yaya a gabana zakice zaki auri wani? Bayan Aliyu ya mun alqawarin ze dawo mun dake
haba Ma'u dan Allah kiyi haquri ki janye maganar ki" ya fada a rude yana biyo
bayana.
A mugun fusace na waiwayo na nuna shi nace
"Wallahi Bashir ka shigo dakin nan seka raina kanka, Aliyu ko? Aliyu ubana ne daya
maka alqawarin dawo dani se ka turo shi ya dauke ni daman kai ka turo su suka zo
suna mun wasan kwaikwayo to wallahi sena ci ubansu,
ina saboda sun samu damar zuwa in da nake yasa har kake tsara musu abinda zasu zo
suyi ko to daga yau ta qare ka tattara yayanka ku barmun gida duk kuma yaran daya
sake zuwa inda nake was a sena bata masa" na qarasa ina bugo qofar har seda ta
bigeshi dandab yake da shigowa dakin.
Kan gadona na fada na fashe da kukan da ni kaina ban san na menene ba. Me nayiwa
Bashir dana kasa samun soyayyar sa a rayuwa? Meye bani dashi? Ta ina na gaza daya
kasa dubana ya mutuntani ko dan darajar soyayyar da nake masa.
Wayata ce tayi qara, nasan baze wuce Yusuf ba dan haka na janyota a fusace zan
kashe dan kowama haushin sa nakeji a yanzu sedai ganin Alhaji Qarami ya saka na
amsa ina kaiwa Kunnena na gaishe shi cikin kukan da nake.
"Ma'u ina ga tare zaku dena koke koken quruciya keda Takwarana yanzu kuma me aka
miki da kike kuka a daren nan?"
"Alhaji Bashir ne, wai yazo har cikin gidan nan yace....."
"Allah ya rufa asiri, tsakanin ki da Bashir kuma Ma'u ai babu me shiga, ke kika
bashi fuskar da ze zo ai koma menene yayi miki tunda ance Ki bashi Yayansa kinqi
kinga kuka yanzu kika fara. Ni ba wannan bama, Yusuf ya gaya mun yanda kukayi, har
na kira Baffa Isiya da Baffa Madu na gaya musu saboda a fara shirye shirye acan se
kuma nace dai bari na kiraki na sake tabbatar wa daga bakinki" Alhaji Qarami ya
katse ni alamar be damu da wani zancen Bashir dana dakko masa ba.
"Ni Yaya ba da gaske nake masa ba, kawai saboda Bashir ya fita a harkata yasa na
fada masa haka kuma ma ni kiran da nayi ma sa so nake na gaya masa yama dena bata
lokacinsa ni ba aure zanyi ba" na fada cikin sabon kuka jin abinda Alhaji Qarami ya
rikito mun, waya aike shi ya gayawa Baffa Isiya? Mutumin da ya tinga mana Tijara
nida Yaya Suwaiba ranar daurin auran su Bilal akan mu fito da mazaje muyi aure in
ba haka ba ze dubo a Kumo ya aura mana babu ruwansa sedai mu koma qauye da zama.
"Toh fa, to yanzu ya kike so ayi Ma'u tun farko waya ce miki ana wasa da zancen
aure ma? Yanzu so kike na koma nace musu wasa ake maganar auran nan bayan har Baffa
Isiyan yace iyayen Yusuf din idan a shirye suke suje Gobe akwai auran Shatu da za'a
mayar itama se a hada kawai goben a daura ba se an jira wata Juma'a ba.
Dakyar fa na lallashe shi ya bari shine zakice wasa kike to kira shi da kanki ki
gaya masa dan ni dai bazan iya ba, kuma kinsan kin zalunci Yusuf, kin saka masa rai
yana can ya rasa yaya zeyi saboda murna yanzu kice wasa kike idan bakiyi wasa ba
haqqinsa seya kamaki Ma'u" Alhaji Qarami ya fada cikin fushin da ban san shi dashi
ba.
"Ni Yaya inason auran Yusuf wallahi amma makomar yarana nake dubawa, ni bance
zankoma gidan Bashir ba dan inason zama dashi kawai Yaya saboda yarana kasan dai
bazasu samu kulawa idan bana nan ba...."
"Toh wayace karki koma kije mana Allah ya bada sa'a, amma banji dadi ba yanda kika
maidani qaramin mutum kika watsa mun qasa a ido a karo na biyu Ma'u babu komai,
Bashir dai kike so ko to sanda kuka shirya se ku maida auran Allah ya bada sa'a"
yana gama fadar haka qit ya kashe wayarsa.
Qoqarin bin bayan kiran nayi amma yaqi dagawa daga qarshe ma ya kashe wayar, yanzu
shima ya fita sabgata to ina zan kai matsala ni Ma'u idan ta same ni? Meyasa duk
suka kasa fuskantar abinda nake nufi sunqi su dubi abin ta maslahar Yayana Aa se
kawai Rashin kirkin Bashir suke dubawa.
Kiran Goggo ne ya shigo wayata, seda gabana ya fadi bansan me zatace ba, qarata aka
kai mata ko kuma chanjin labarinbe rigada ya isar mata ba haka dai na daure na amsa
na saka wayar a kunnena nayi shiru.
"Ma'u yanzu nake jin labari me dadi, ubangiji ya sanya Alkahiri yasa yin na Allah
ne. Kice ma abu ya matso jiya kika kirani da wasu tsiyatakun ki kai Ma'u dai bazaki
girma ba Allah ya qara shirya ki" Goggo ta fada ina iya jiyo murnar dake cikin
muryar ta.
Ajiyar zuciya na sauke jin bata san sabon labarin ba nace
"Uhm Amin Goggo, a dai ci gaba dayi mana Addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkahiri"
"Oh kice dai da sauran rina a kaba wane Alkahiri kuma za'a zaba bayan wannan sedai
ayi addu'ar Allah ya tabbatar da Alkahirin ko? Ko dai kinsake canza ra'ayin ne Dan
daman seda na Fadawa Bilki indai kece sedai gyaran Allah kawai, akan wannan Bashir
din ana iya zama taron daurin aurema kice kin fasa suma dena murna suna wasu tsare
tsare".
Cikin kuka nace
"Toh ni Goggo ya zanyi dan Allah? Kowa ya tsane ni se zagina suke dan kawai nace
zan koma gidan uban yayana, kuma ni wallahi saboda Yaran nan nake son komawa gidan
Bashir ba wani abu ba amma kowa se yace wani ba haka ba se kace idan sune zasu
yarda su zubar da Yayan su tafi wani gurin....."
"Allah na gode maka ni Maryam, Ina dai gidan Bashir ne ko to ki koma Ma'u Allah ya
tabbatar da Alkahiri ya baku zaman lafiya ince dai shikenan? Kiyi haquri da muke
miki katsalandan kinji bazamu sake ba"
"Ni Goggo ba haka nake nufi ba, wallahi indai danta halin Bashir ne na gama
auransa, yanzu ko yau bakiga irin wulaqancin da yazo har cikin gida yayi mana ba
dagani har Yusuf har yana cewa wai banida kamun kai ina kawo zawarawa cikin gida
zan lalata masa tarbiyyar Yaya"
Salati Goggo ta jawo ta dire kafin ta dora da cewa
"Yanzu Ma'u Rashin zuciyar taki harya kai haka? Da bakin ki kike fadar yazo har
cikin gidan ki a gaban mutane ya zageki sannan kike neman mayar da kanki gidansa
saboda Rashin sanin ciwon kai ko? Toh kije Allah ya taimaka Allah kuma yasa wannan
zazzafar soyayyar da kike wa Bashir kar ta zama Ajalinki.
Idan da ace kin san abinda kikeyi da ko hanyar da Bashir yabi bazaki sake bi ba
amma nema kike ki sake cusa kanki cikin rayuwarsa Allah ya taimaka ya bada Sa'a"
cikin fushi sosai tayi maganar, na bude baki tayi saurin katse ni da cewa
"Karkice komai ni ba hanaki nayi ba Allah kafin kice nima na tsaneki koma baqin
ciki muke miki karki koma gidan Abin qaunar ki ko Allah ya bada sa'a".
Duk yanda naso na fahimtar da ita amma Goggo ta baude, maganganu take fada mun da
suka tayar mun da hankali, ita batace kar na koma ba amma qiri qiri ta nuna
Adawarta da komen nawa to ya take so nayi?
Sanda ta saka albarka ma ya zaman ya kasance balle yanzu da take adawa da komen?
Ni yanzu duk ba wannan ba wnada ze dakatar da Baffa Isiya kadai nake nema, Alawa ce
ta fado mun a rai, Allah sarki yar uwata da ra'ayin mu yazo daya nasan zata iya
jure duk zagin da ze mata ta nema mun wannan alfarmar amma yanzu yanda take jin
Yusuf din nan yanda kasan qanin Baffan mu haka ta dauke shi.
A whatsapp na dubata dan dare yayi be kamata na kirata ba naci Sa'a kuwa tana
online nan da nan na farayi mata Voice note na tura.
Ina kallo ta kunna taji amma taqi bani amsa na ringa mata magiya ina roqonta se can
naga ta kirani whatsapp call jikina na rawa na daga ina cewa
"Dan Allah yar uwa kimun wannan taimakon, ba cewa nayi bazan aure shi ba amma kwana
hudu tayi gaggawa nima fushi ne yasaka ni fadar haka amma ki taimaka mun ki kira
Alhaji Qarami ki roqamun Arziqi a maidashi wata daya dan Allah"
"Uhm kinga kafin sannan kin San yanda kikayi kika kora shi ba ai ni Allah yasa ma
goben kawai a daura kowa ya huta dan wallahi Ma'u kyanki auran dole tunda ke baki
san abinda ya kamata dake ba" ta fada
"Naji koma menene na yarda nidai ki mun wannan, nifa bawai bana son Yusuf kema kin
sani da bana sonsa ko sauraronsa bazan tingayi ba wallahi amma ni auran ne ban
shirya ba Alawa ina buqatar lokaci har yanzu Addu'a nake Allah ya zaba mun mafi
Alkahiri" na fada cikin kwantar da murya dan fatana kawai ta amince zata kira
Yayan.
"Kina da matsala Ma'u duk wani gewaye gewaye da kike da wani neman Alkahiri wai
jira kike Alkahirin yazo gaban ki ya tsaya yace Ma'u gani nine zabin Alkahirin ki
ko menene? Shifa Allah yana bawa mutum dama ne kuma in yayi wasa da ita shine a
ruwa in ma zaki nutsu ki fuskanci gaskiya tun wuri wallahi kiyi bana miki fatan
daga baya kizo kina da kin sani da kaza kika Ma'u amma shikenan"
"Naji Alawa, idan Auran Yusuf Alkahiri ne a gareni ma Allah yasa goben idan sunje
ta bakin naki a daura kowa ya huta Amma yanzu dai ki taimaka ki kira Yayan, shi
idan ya gayawa Yusuf din idan sunje suce wata daya shikenan".
"Allah dai ba abin wasan ki bane Ma'u in ma qarya kike yana iya gwada miki ikonsa a
yanda baki zata ba, shikenan zan kira shi da safe idan Allah ya kaimu" ta fada tana
qoqarin kashe wayar nayi saurin tare ta da cewa
"Da safe kuma Alawa? Kin fa san qila da wuri zasu tafi gara dai ki kirashi yanzu
dan Allah kinji"
"Hala kinsha kwaya, Alhaji Qaramin zan kira sha biyu na dare ni dallah ki kyale ni
duk saurin su dai ai se sunyi sallar Asuba zasu fita ko su suka kawo sammako duniya
to zan kira shi da Asuba in kuma kika sake magana wallahi fasawa zanyi aikin banza
kai se kace ma wani ne zeji miki dadin da muka dage sekin auri me son ki ki koma
gidan Bashir din kawai yafi sauqi ma" ta fada a hasale.
Shiru nayi mata dan nasan hali idan na tanka tana iya cewa ta fasa din tunda daman
ba so take yi ba, mukayi sallama na ajiye wayar na hau juyi a gado ina Addu'ar
Allah yasa ta kirashi ya samu yayi musu magana kafin su tafi dan idan har sukaje
gurin Baffa to in naga ban auri Yusuf ran Juma'a ba se wani ikon Allah.
Washe gari saboda damuwar dana kwana da ita ban iya zuwa aiki ba saboda ciwon kan
daya saukar mun, ina kwance har Yara suka tafi makaranta daman Faridah da yan biyu
ne kadai suka kwana ragowar tun shigowar Bashir jiya ban sake jin duriyar su ba.
Ina kwancan Amnah ta kwankwasa qofa na bata izini ta shigo. Bayan ta gaishe ni ta
zauna daga qasa ina kallon idon ta na gane tayi kuka dan fuskarta gaba daya ta
tasa. A sanyaye ta bude baki tace
"Mami naga baki fito ba yau bazakije aiki bane?"
"Bazanje ba Amnah bana jin dadi"
"Sannu Mami, na kawo miki breakfast toh?" Ta sake tambayata. Seda na tashi zaune
tareda jingina da bangon gadon kafin nace
"ki kawo mun Baqin shayi kawai ya isa"
Ina shan shayin wayata tayi qara, Yusuf ne. Naja wani uban tsaki na ajiye dan gani
nake duk shine maqasudin matsalata a yanzu, duk da be takurawa rayuwata ba da babu
me damuna akan zancen wani aure yanzu ai bashi kadai bane yake sona amma yafi kowa
naci ko dan yana ganin shi dan gida ne kowa yana sonsa gashi yanzu ya jawo mun ni
ta ina zan fara kiran wani Baffa Isiya nace masa karya amsa maganar su?
Seda wayar ta katse ya sake kira ta kuma yankewa ban daga ba se gashi ya turo mun
da saqo cewar yanzu ze wuce Abuja kuma Wakilansa suna kan hanyar zuwa Kumo gurin
Baffa Isiya se wani tarin godiyarsa da damar dana bashi da alqawarin bazanyi dana
sanin amincewa dashi ba.
Ina gama karanta saqon na shiga kiran layinsa dan in gaya masa ya dakatar dasu
karsu je amma nayi rashin sa'a a kashe, safa da marwa na ringayi a dakin kamar
zanyi kuka, dana sani na daga kiran nasa qila abinda ze gaya mun kenan a sannan na
dakatar dashi amma yanzu qila kafin ya sauka na samu muyi magana ai sun rigada
sunje an gama duk abinda za'ayi gashi bani da tabbacin Alawiyya ta kira Alhaji
Qarami dan wayarta ma a kashe take.
Tunanin wa zan kira a yanzu na ringayi a raina, Alhaji Yasir? Kai bazan kirashi ba
dan indai yana bayan su Alhaji Qarami to fadan da zan sha a gurin sa ma sena
gwammace na haqura na auri Yusuf ko bana sonsa kuwa. Yaya Kabiru ne ya fado mun a
rai, duk mazan gidan mu yafisu sauqin kai dan shi Ustazi ne da be dauki Duniya da
nisa ba, nasan ko yana kan ra'ayinsu nasan idan yaji nawa bangaren ze saurare ni,
qila ma ya taya ni shawo kansu.
Da wannan shawara na danna kiran lambar Yaya Kabiru. Cikin muryarsa ta ustazai masu
aje gemu yace
"Assalam Alaikum Malama Asma'u barka da safiya" ya fada bayan daya daga wayar.
"Yaya ina kwana? Ya gida ya aiki?
"Lafiya lau ya kike ya yaran? Se kuma mukaji abin arziqi. Ainihin jiya da daddare
Babban Yaya ya sanar mana cewa mu tafi Kumo yau da safe ainihin za'azo neman
auranki kai nayi murna kwarai wato har alawa na fita na rabawa yaran makarantar
dare nace suyi Addu'a Allah ya tabbatar da Alkahiri ai Malama Asma'u in Allah ya
yarda kam kinyi miji a wannan karon"
Gaba daya kaina zafi ya qarayi da wannan bayani da yake faman yi mun ina qoqarin
tare shi amma ina seda ya kai qarshe.
"Daman Yaya maganar ce tasa na kiraka yanzu, kuna gida ne ko kun tafi Kumon?" Na
fada ina taraddadin amsar da ze bani, cikin rashin sa'a kuwa se ji nayi yace
"Ai tun qarfe takwas muna nan, kinsan Halin Baffa Isiya baya son wasa musamman akan
abu me muhimmanci irin wannan abu, Masha Allah ai kingansu ma sun qarso yanda
za'ayi yanzu ki bari idan mun gama ainihin sena kiraki naji menene" yana gama fada
ya katse wayarsa.
Kamar zan rusa kuka haka na zabga tagumi na zauna qirjina kuwa se dukan uku uku
yake. Na tabbatar idan har Baffa Isiya ya karbi maganar nan tofa rusata se dai ikon
Allah ko idan shi Yusuf din ne da kansa yace ya fasa wanda bana taba tunanin haka
wai ma tun farko waya aikeni aikata hakan?
Duk wannan Bashir din ne ya jawo, gashi tunda yazo ya gama shirmensa jiya ko a waya
be kirani ba balle ya bani haqurin abinda yayi kai nima fa wata wawuya ce wallahi
da har nake tunanin Bashir ya chanza daga