Showing 138001 words to 141000 words out of 238465 words
da yayi wa Ma’u y sake hasalashi, tayi qara fari tayi kyau abinta a yanda ta
fitan nan babu me mata kallo matar aure ma bare har a hasaso mata yaya shida dole
itama yaja mata kunne gaskiya tunda dai haryanzu ai da auransa akanta. Haka ya wuni
ranar a gurin aiki cikin quncin dashi kamsa be san na menene ba, sanda ya tashi ya
tsaya ya siyi fruits da kaza kafin ya wuce gida.
ASMA’U
Hankali kwance na ringa tuqina harna isa ma’aikatar mu, muka gaisa da abokanan
aikina cikin mutun taka suna yimun sannun rashin lafiyar danayi qaryarta har na
zauna ranar aka bani tukuicin saki nidai se yaqe nake ina amsa musu dan a yanzu
bana son wani abu da ze ringa tunamun da wancan Al’amari.
Se da muka fita break din rana Olivia wata abokiyar aikina ta same ni ina cin
abincin da se a sannan na samu na siya.
Cikin harshen turanci take cewa
“Asma’u Juliet tana gaya mun wata magana ranar amma ban yarda ba wai dagaske ne kun
rabu da me gidanki baku tare yanzu?”
Sak nayi ina kalllon Olivia, daman Olivia irin mutanen nan ce maso shegen gulmar
bala’i duk wani abu na ma’aikatar nan kaji shi a bakinta ka rasa ta inda ma take
samun labarai akan mutane kuma idan taji daman ka qaddara kamar anyi yekuwa ne dan
kowaanne ma’aikaci se labarin nan ya isar masa.
Dagaske yanzu dai mutane sun dena kiwon akuya sun koma mutum tabbas, Juliet din da
take magana qawarta ce ni kuma a estate dinmu take budurwar wani abokin aikin su
Bashir ce a gidan sa take da zama bama fa layin mu daya ba suna can qasan mune amma
ace har labari ya kai musu ashe dai ba a arewa kadai mata suka iya gulma da sa ido
ba harda suma a nan kudu.
Bude baki nayi da niyyar bata amsa Maman Islaha qawata ta gurin aiki ta qaraso
wurin, cikin fada fada tace da Olivia din
“Wannan wane irin rainin wayo ne zaki ajiyeta kina mata wannan tambayar ina ruwanki
da auranta da kike tambaya akai ita wadda ta baki labarin meya hana ki tsayawa kiji
inganjinsa a gurinta? Dallah malama bar gurin nan tunda baki da aiki se soka baki a
rayuwar mutane da shegiyar gulma kawai” sosai ta balbaleta da fada dan Maman Islaha
irin yarabawan nan ne da basa daga qafa.
Olivia kuwa simi simi ta bar gurin tana waiwayena, mayar da kai nayi ina juya
abincin dan gaba daya ya fita a raina Maman Islaha ta dafa ni tana cewa
“Ki manta da ita kici abincinki ni wallahi mamaki kika bani ma da baki dauke ta da
mari ba ace kina zaune tazo tana miki irin wannan maganar se kace ubanta ne ya
kashe miki auran, idan kuma mijinki take so tun wuri se ki san me ake ciki...” seta
dakata ganin ina hawayen da ni kaina bansan sanda suka fara zuba ba.
“Maman Faridah lafiya meya faru?” Ta fada a rude tana ruqoni, sena saki kukan gaba
daya ina cewa
“Yanzu dan aurena ya mutu shikenan har na zama abin gulma ana yayatani a duniya
kenan?”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un auranki ya mutu Maman Faridah dagaske? yaushe?
Kardai yarinyar nan son mijinki takeyi din da gaske kiyi mun magana” ta jero mun
tambayar daga ganinta kasan hankalin ta ya tashi da jin maganata.
Seda na tsagaita kukan dan har hankalin masu cin abinci ya fara dawowa kanmu kafin
nayi mata bayanin komai cikin sanyi tun kafin na kai qarshe ta qundumo wata ashar
me maiqo da yarbaci ta aunawa Bashir ta qara lailayo wata ta watsa mun kafin cikin
fushi tace mun
“Amma kin bani mamaki Maman Faridah yo se me shi ya tafka asara fa ba ke ba dan
wallahi harya mutu baze taba maida kamar ki ba shine har zaki tsaya kina kuka wani
ana yayata ki a duniya an dade ba’a fada ba tunda ba kanki faru ba sakin aure har a
sakeki akan kishiya kintaya kina wani zubda hawaye mtsw,
Kansa ya cuta in sha Allahu se kin samu me sonki wanda yasan darajar ki kuma akan
idonsa zega yanda za’a ringa tarairayarki sedai ya hadiyi zuciya ya mutu, Allah ya
kaimu ki gana iddah ni kaina ina da Candidates se wanda kika zaba kika darje”.
Haka Maman Islaha taci gaba da gaya mun maganganu da suka sake bani kwarin guiwar
yakice Bashir daga rayuwata, har tana ce mun se na chanza shiga tunda yanzu bani da
aure na dena zumbula wadannan Dogayen rigunan da suke boye dirina se nayi dariya
nace mata
“Maman Islaha ko da aure ko babu dole in rufe jikina in kare mutunchin kaina, bafa
yarinya ce ni ba sannan ga yara ina dasu nan da kika ganni ma babu lissafin sake
aure a gabana zan ci gaba kawai da neman kudina na kula da yarana shikenan”.
A ranar bamu tashi da wuri ba saboda mitin din gaggawa da mukayi, abin takaici ina
zuwa na kunna motata taqi tashi bayan nasan lafiya qalau take ba’a ko yi sati uku
ba da a ka kaita a dubata a sannan dinma ba abinda ya sameta shine yanzu zata mun
halin qarfen nasara.
Ina tsaye ina ta faman zabga tsaki, David daya daga cikin yaran da suke kula da
gurin pakin ya qaraso yana tambayata lafiya nagaya masa abinda ya faru shine ya
bude gaban motar yana duddubawa duk ya gama yan dabarunsa amma taqi tashi, haka na
kwashe kayana daga ciki na kulleta, ga Magriba tayi gashi duk yan arear mu sun wuce
haka dai na kira uber dukda bana son hawa da daddare.
Ina tsaye a daga can gaban get ina jiran me uber wata dalleliyar mota Marsandi
qirar shekarar da muke ciki baqa wuluk se qyalli ta wuceni, da ido na bita a raina
ina yaba motar aga quginta kadai zaka san ba qaramar mota bace a raina nace
“Allah kayi mana arziqi muci me kyau mu saka me kyau mu hau mota me kyau” ina cikin
haka se ganin motar nayi tana dawowa da baya. Matsawa nayi daga inda nake ina
waiwaya wa bayana dan naga tazarar gurij da cikin ma’aikatar mu idan ta kama da
abin gudu in fece kar inje masu satar mutane ne se gani nayi motar ta sake biyo ni
ai kuwa na daga qafa na fara sauri, sunana danaji na ciki ya ambata ya saka na juya
da sauri na kalle shi.
“Asma’u” ya sake ambata yana kallona, nima kallonsa nakeyi ina so na tuna ko na
sanshi amma banga alamar hakan ba.
Baqi ne amma ba irin wukuk din nan ba fatarsa a goge take alamar hutu da jin dadi
sun ratsata a kallo daya zaka tabbatar da kyakykyawa ne irin kyau na maza me cike
da kamala. A zaunen da yake na tabbatar da dogone irinsu Bashir sannan yana da
cikar halitta bashida qiba amma jikinsa a murde yake alamar yana daga qarfe daga
damtsen hannunsa da yake a bude ma zaka tabbatar da hakan.
Gaba daya a abinda be wuce second talatin ba na qare masa kallon, nayi guntun tsaki
dan ban gano wata alama da take nuna na taba sanin ko me kama dashi ba a rayuwa
qila irin samarin nan ne ya canki suna akayi sa’a ya fada daidai se kawai na juya
na fara tafiya a raina ina mitar abinda ya tsayar da me Uber kusan minti talatin
shiru bayan a map naga yana dab da inda nake. Maganar da saurayin ya sakeyi ce ta
sakani juyawa a sukwane ina kallonsa
“Ma’u danja wutar baya Ma’un lelen Baffanta” ya fada yana sakin wani murmushi daya
saka gabana yankewa ya fadi.
“Yusuf” na fadi sunan a rarrabe ina qare masa kallo dan ya fito daga cikin motar ya
jingina shima yana kallona. Murmushinsa me kyau ya sake yi mun kafin yace
“Har kin tuna ni kenan da yake kinji kirarin naki ko, daman na fada miki ko kin
manta fuskata a rayuwa na barmiki abinda bazaki taba mantawa ba gashi kuwa ina fada
har kin gano ni, me kikeyi a gurin nan ga duhu ya yi haka?”
Jinsa kawai nakeyi ina kuma qare masa kallo dason tabbatar da dagaske Yusuf din ne
dai ko kuwa wani ne daya san tsokanar da yakeyi mun ada, se kuma dana nutsu na gane
shidin ne amma canjin daya samu a rayuwa tabbas ya zarta ace ka gane shi a kallo
daya yanda kasan wanda aka saka a inji akayi masa qare qaren abubuwa, Babban abinda
yafi bani mamaki ma yarintar da ke tattare dashi.
A sanda nasan Yusuf ma a qallah ya haura shekara talatin kenan yanzu yana hararo
hamsin ne amma nake ganinsa kamar yanzu ne yake talatin din da yan kai.
“Ki dena kallona haka karna komawa matata a rabi ina tambayarki me kikeyi a nan
baki amsa ba” ya sake fada cikin sigar tsokana ya baro jikij motar zuwa inda nake
tsaye, se naji kunya na sunkuyar da kai ya gane kallon qurillar da nake masa.
Ma’aikatar mu na nuna masa ina cewa “Daga gurin aiki nake motata ta lalace tana
ciki shine na fito ina jiran Uber da nayi order”.
“Anan kike aiki Masha Allah Ma’u shiyasa mana seda nayi dagaske na iya gano ki,
idan ba damuwa muje sena ajiye ki shiga motar haya da daren nan babu dadi.
Ban musa masa ba, muka qarasa ya bude mun gaban motar wani sanyi da qamshi suka
bugoni har seda na lumshe ido ina shiga naji na wani lume a cikin kujera kai jama’a
kudi dai yayi a rayuwa.
“Wace unguwa mukayi” ya fada yana kallona, se na gaya masa ya kunna motar muka fara
tafiya shiru, Yusuf ne ya katse mana shiruj yana cewa
“Yaushe kuka dawo lagos da zama nasan dai a Gombe kikayi aure koh?”
“Eh Gombe nake bamufi shekara shida da dawowa nan din ba ai bayan daya samu chanjin
aiki” na fada ba tareda na kalle shi ba.
“Ban sani ba ai, ina yawan shigow Lagos dan bana sati biyu banzo ba ga qanwata a
gari ai da na tinga shigowa muna gaisawa. Ina Mijinki Bashir ne sunan sa ko wanda
ya kasamu karma muje fa yaji haushina na dakko masa mata babu izini yanzu yaranki
nawa?” Ya sake fada hankalin sa na kan titi, seda na waiwaya na kalle shi kafin
nace
“Yana nan, yanzu yaranmu shida harda twins kaifa?”
“Kai lallai rabone ya kore mu yara shida ai ba wasa ba kice dana matsa da yanzu ana
irgamun shekaru goma sha a qasa” ya fada yana yar dariya nima nayi dariyar ina cewa
“Ba wani nan kawai dai komai ka gani da yanda Allah ya shirya faruwarsa ne kawai”.
“Hakane amma dai ai Ya shammaceni da yawa ya rabani da Ma’u lokacin da na tabbatar
nafishi sonki” da sauri kuma ya buga sitiyari tareda rufe bakinsa yace
“Astagfirullah, Afuwan Ma’u wallahi na manta nake dawo da maganar baya”.
Murmushi kawai nayi se nace “wai ma ya akayi ka gane ni?”
“Ma’u kenan, wallahi ko fuskarki ban gani ba seda na dawo da baya kawai zuciyata ce
naji ta buga irin bugun da ke kadai kike sakata tayi shiyasa na tsaya dan na
tabbatar ko ba kece bace tabbas akwai abinda yake da alaqa dake a gurin shiyasa na
tsaya se kawai naci karo dake, kinsan dai ke baki chanza kama ba kyau da qiba kawai
kika qara amma kina nan a Ma’un nan dai me yawo babu dankwali”.
“Yusuf ka bari”
“Na bari Ma’u, Allah na tuba ka yafe mun kasan bada niyya nakeyi ba kawai dai kai
ka jarabceni da son baiwar nan taka har na rasa yanda zanyi a rayuwata”. Yanda yayi
maganr har fuskar ta nuna gaskiyar abinda ya fada ya sakani sunkuyar dakai na qasa,
gaba daya se naji kamar ya daure ni da igiyoyi, haka muka qarasa tafiyar kamar
kurane shine ma yake tambayata kwatance har muka qarasa bakin Eatate din.
“Ko na sauke ki anan ki qarasa?” Ya fada yana kallona se nayi murmushi kawai ya
shige da motar bayan da ya sauke glass suka kallemu ganina ya saka masu gadi bamu
hanya tunda sunsan motar bata gurin bace.
Har qofar Flat dina Yusuf ya paka motarsa, na riqe jakata a hannuna ina cewa
“Nagode sosai Yusuf, ko zamu shiga ku gaisa da yaran?”
“Tab so kike Mijinki ya harbeni kenan, ki bari dai tunda naga guri ai kuma se kun
gaji dani zanzo naga yarana sedai idan kuma mijinki ne ya hana, ina fata dai babu
matsala kawo kin da nayi ko?”
“Ba matsala, Nagode sosai ka gaida madam da yara, baka ma gayamun su nawa bane”.
“Zasu ji, guda daya ce Ma’u tana nan ta isheni da fitina yanda kika san ke kika
haifeta” yayi maganar yana miqomun wayar sa dake dauke da hoton wata kyakykyawar
yarinya fara tas kamar yar turawa amma kamanninta sak da Yusuf din bazata wuce
sa’ar Abdallah na ba.
“Kai masha Allah, ya sunanta” na fada ina sake kallon sauran hotunan nata.
“Baki ji ba nace miki Ma’u takwarar ki ce”
“Wasa kakeyi amma ko? Ina hajia baka saka sunanta ba zaka ce sunana ka saka” na
fada ina kallonsa.
“Wallahi Ma’u ke nayiwa takwara, bama ita kadai ba na qudurce a raina ko yaya mata
goma zan haifa sunanki zanyi ta maimaita musu”
Yanda yayi maganar cikin wani yanayi ya sakani kama hannun motar zan bude ina cewa
“Nagode kwarai toh ka gaida takwara, idan tare kukazo seka kawo su mu gaisa” na
danna mabudin naji qofar a rufe, daga bangarensa ya danna wani abu qofar ta bude,
mukayi sallama na wuce ina jin yanda kayan jikina suka kama qamshin da motar
takeyi.
“Tab tsautsayi ace ina gidan Bashir na shigo lift din nan da yau tsirena kawai zeyi
ya huta” na fada a fili ina kaiwa qofar gidana se ji nayi naci karo da mutun, ina
daga kai muka hada ido da Bashir da idonsa ya kada yayi jajir ga wasu jiniyoyi da
suka tashi a goshinsa alamar yakai qololuwar bacin rai.
“Wane Dan iska ne ya sauke ki a mota Ma’u” ya fada yana kallona.
Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya
da yanmata albishir gareku
BONONZA; BONONZA;BONONZA;
Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU
ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO
MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN
KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN
DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K
MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA
GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA
KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 45
"Magana nakeyi miki Ma'u nace wane dan iska ne ya saukeki a mota a cikin wannan
tsohon daren?" Bashir ya sake fada cikin hargagi.
Ban tankashi ba haka ban matsa daga inda nake tsaye ba sema waiwayawa nayi na kalli
wasu samari su uku da suka zo wucewa suka tsaya kallon mu gashi kuma ko wanne da
waya a hannunsa.
"Ka matsamun na wuce gasu can suna kallonka idan kuma so kakeyi suyi maka video
seka bada himma" na fada kafin na raba shi zan wuce cikin gidan se kuwa ya biyo ni
kamar wani kububuwa ya sake shan gabana yana cewa
"Kinsan Allah idan baki gayamun waye wancan ba ba video ba ko gidan Tv zasu dakko
su kawo gurin nan sedai duk wacce za'ayi ayi amma bazaki shiga gidaj nan ba".
Wata dariyar rainin hankali nayi kafin naja da baya ina kallonsa nace
"To wai kai a na me kake so kasan waya kawo ni, kana da matsala da hakan ne? gida
kuma kalli dakyau a qofar gidana kake ba wai gidanka naje zan shiga ba da zakace
zaka tare ni dan haka ka matsamun na wuce malam banyi sallar magriba ba ga Isha ta
tarar dani"
ina gama fadar haka na sake yin gaba da niyyar shiga gidan ba zato se ji nayi
Bashir ya fincikoni ya watsa ni baya, takalmin qafata ya gurde na tafi zan fadi
Allah ya taimakeni na durqushe ai kuwa ina dagowa banyi wata wata ba na sauke masa
wani bahagon mari da ni kaina seda na aikata sannan na gane menayi.
Wallahi a lokacin mantawa nayi da Bashir ne a gabana, gani nayi tamkar wani random
guy ne haka nan yayi mun wannan wulaqancin ni kuma zuciyata izani naga ta haka
kadai zan rama abinda yayi mun se bayan danayi marin sanan na dawo hankalina amma
se na aro dakiya na dorawa kaina na gyara tsayuwata sosai ina kallonsa nace
"Koda wasa karka sake yunqurin dora hannunka a jikina dan tuntuni ka haramtawa
kanka hakan, sannan daga yau babu ruwanka da duk abinda ya shafeni, aurene
tsakanina dakai kuma ya qare dan haka ina da yancin yin duk abinda naso ko shiga
motar wanda naso ba tareda kai ko wani ya tuhumeni ba ka kiyaye" na dauki jakata da
wayata da suka fadi na wuce shi zuciyata kuwa kamar ana kidan mandiri, seda naga na
tura qofar na shiga be janyoni ya watsa mun marin daya fi wanda na masa ba sannan
na sauke ajiyar zuciya ina share gumin dana hada a goshi.
BASHIR
Wata qara yaji "quuu" kamar gidan radio sun tashi daga aiki haka ya ringaji a
kunnensa. Ba zafin marin ne ya sakashi suman tsaye ba Aa tsabar mamaki da tsoro ne
wai shi, shindin dai ENGINEER BASHR AHAMAD yau Asma'u ta mara da yatsunta guda
biyar kuma da gaske ido biyu ba magarki ba abun ya faru?
Harta gama surunta ta wuce kallonta kawai yakeyi, ji yakeyi dama ace wani ya tashe
shi ya zaman mafarki yakeyi dan wannan abun beyi kama da wanda ze faru a gaske ba
ace yau shi Ma'u ta daga hannu ta mara akan yana tuhumar waya kawota gida a mota
sannan har take iya gaya masa aure ne ya hadasu kuma ya qare dan haka babu shi babu
sabgarta, seda ta shige gida ta rufo qofa sannan ya motsa.
Ya waiwaya inda samarin dazu suke yaga basa nan, waya sani ma ko sun nadi abinda ya
faru kafin suka wuce oho. Gaba daya kansa nema ya qulle ya rasa me ya kamata yayi,
binta zeyi ya rama marin da tayi masa ko kuwa ci gaba zeyi da bin ba'asin wanda ya
kawota? Kokuwa ya wuce gida ne ya qarasa cin uban waccen yarinyar da tayi masa
jalof din taliya da kifi me qaya a matsayin abincin daren sa wai mema zeyi a ciki
yanzu??
Harya juya kalaman ta suka sake dawo masa "karka sake yunqurin dora hannunka a
jikina dan hakan ya haramta a gareka"
Se kawai ya fasa tafiya ya bi bayanta zuwa cikin gidan, dole ya dakatar da Ma'u
daga wannan dogon mafarkin data shiga ya nuna mata cewa haryanzu igiyar auranta
tana hannunsa.
A da yayi niyyar seta zaunu ta nemi sulhu dan kanta amma yaga alamar hakan
gangancine, yau wani ya kawota gida harta daga hannu ta mareshi gobe kuma