Showing 99001 words to 102000 words out of 238465 words
Baffa yake bani kudin makaranta dan shi yake dauke da nauyin karatuna ga
kuma na man mota da ake hadamun dashi yanzu.
Ta inda matsala ta dan bullo mana rashin lafiyar da Baban su Bashir ya fara, bayan
kaishi Asibiti suka tabbatar da cewa yana da Suga da hawan jini ne suka taso masa
lokaci daya seda yaci kudi sosai kafin lafiyarsa ta samu sannan aka dorashi akan
magani abinda ya turgude dan jarin kasuwancin da yake yi kenan dan da kudin akayi
duk hidimar Asibitin sa.
Ganin da nayi rayuwa ta fara yi musu matsi, kuma Baban da yake fita ya nema musu na
cefane gashi a gida babu wadatacciyar lafiya. Bashir baya aiki a yanzu Amiru yana
shekarar qarshe a Jami’a, Afiya tana Level 1 se Fainusa da Sadiya da suke secondary
daga Sa’ad,Samirah har Naziru lokacin a primary suke.
Akwai ranar da mukaje duba Baban da da yamma, abinda ya daga mun hankali muna zuwa
na tarar da Dada tana yi musu kwadon garin kwaki harda Baban da yake fama da Siga a
sannan shi aka zuba masa yaci. Abun ya bala’in daga mun hankali.
Bayan mun koma gida washe gari banyi shawara da Bashir ba na dauki Buhun shinkafa
biyu, taliya, macaroni, semovita komai biyu ga pastar mai hatta Maggi seda na diba
na hada sannan na tsaya a hanya na siyi kayan Shayi da kayan miya na tafi gidan.
Yara na samu a qofar gidan suka shigar da kayan, motar Aliyu dana gani ya tabbatar
mun da Bashir yana gidan dan daman tun safe yau ya fita dan haka ban shiga ba kawai
na wuce gidan mu. A can na tarar da Junaidiyya wai ta zo gida haihuwa ga Yah Bilki
ma tazo da tsohon cikinta haka Yah Fati Alawiyya ce dai nata be isa haihuwa ba ni
se a sannan ma tunani na ya tafi ga rashin samun cikin da banyi ba.
Dukda ina son yara amma hakan besa na taba damun kaina da sena samu ciki dole dole
ba kuma shima Bashir ko sau daya be taba mun maganar ko nuna wani abu akan hakan ba
gaba daya mun barwa Allah shi ke bayarwa idan lokaci yayi nasan zamu samu namu
muna.
A gidan na wuni har dare dan ina son naga Baffa, se bayan Isha ya shigo gida ashe
Yola yaje daurin auren Yar Baffa Sama’ila.
“Mamana ya akayi ne har yanzu baki tafi gida ba” ya fada bayan dana gaishe shi,
sena marairaice fuska nace
“Baffa Kasan Alhajin su Bashir bashida lafiya ko”
“Na sani wallahi ai na dubashi ma sanda yana Asibiti sannan bayan sun dawo ma na
sake leqa gidan, ciwo ne babu dadi yanzu kuma abinda ake ta fama dashi kenan wannan
Siga Allah ya tsare mu dai”.
“Amin Baffa, daman wata Alfarma nake nema idan babu damuwa” na fada ina gyara
zamana. Se ya kalleni yace
“Gidan ku Ma’u ni zaki kalla kice kina neman Alfarma a gurina, idan banyi muku abu
ba wa kuke dashi a fadin duniyar nan daya fini?
Kar na sake jin haka, ki tambayeni kai tsaye abinda kike so ko menene shi a duniyar
nan zanyi miki dan duk abinda na mallaka domin na inganta rayuwar ku ne” Baffa ya
fada cikin dakewa alamar babu wasa a maganar sa. Sena saki murmushi. So da qaunar
Baffan nawa tana qara ratsani nace
“Wallahi Baffa gani nayi gaba daya rashin lafiyar nan ta saka sun shiga wani hali,
kaga yanzu baya iya fita kasuwa ga Bashir kuma aikin da yakeyi ma an siyar da
kamfanin shine nace ban sani ba ko akwai abinda zaka iya yi akai”.
“Ash sha yanzu shi Bashir din baya aiki kenan, kinga ko jiya seda mukayi maganar da
Muhammadu (Alhaji Qarami) yace mun yana iyakar qoqarinsa akan maganar aikin, kinsan
qasar tamu ne yanzu da lamarin aiki ko kana da hanya fa idan wanda yafi ka yazo se
kiga an samu tangarda.
Sannan yace daman su masu kwalin Irin nasa me martaba ta daya (first class) suna
wahalar samun aiki a ma’aikatun mu na cikin qasa saboda yawanci manyan gurin suna
ganin kamar in suka dauke su zasu fisu sedai a ma’aikatu mallakin qasashen waje su
daman sunfi buqatar irinsu din ze ci gaba da bada takaddun in Allah yaso za’a dace.
Shiyasa ni nafi ganewa kasuwanci amma ku yaran yanzu gaba daya kun ta’allaqa akan
aikin gwamnatin nan da gaba daya abinda kuke samu a wata se kiga Dan kasuwa ya same
shi a sati daya wani ma cikin yini, yanzu dai ki turomun shi, idab yana da sha’awa
yazo kasuwa idan Allah yasa yana da nasibi a ciki se ki gani.
Maganar Alhaji Amadu kuma zan duba abinda za’ayi, kama daga kan rashin lafiyar tasa
har zuwa matsalar iyalin se muga abinda Allah zeyi”.
Sosai na ringa zubawa Baffa Godiya da Addu’oin fatan Alkahiri, har na tashi zan
tafi ya tsaidani da cewa
“Yawwa na tuna kuwa Jiya Manager Bankin da nake ajiya munyi magana naji yace zasu
dauki Ma’aikata, shi bangaren nasa ze iya aiki a banki ne?”
Cikin farin ciki na koma ina cewa “Eh Baffa, shi aikin banki indai ka iya kwanfuta
da kana da lissafi a takardun ka zasu dauke ka, kuma duk yana dasu”
“Toh bari na kirashi yanzu naji idan da hali se ya fara wannan din kafin sanda
Allah ze kawo wani”.
Ina tsaye ya kira Manager ya kuma amsa tareda cewa ze turowa Baffan Email yanzu a
tura da CV din, sannan ranar Litinan yaje Bankin ya same shi da hardcopy na
takaddun.
Haka na koma gida raina qal na tarar da Bashir ya rigani komawa yana zaune yana
shan Shayi.
“Se yanzu” ya faaa yana kallona, seda na ajiye jaka da mayafina na zauna kusa dashi
tareda rungumo shi nace
“Canki”
“Kinsan ban iya cankar abu ba ko” ya fada yana kallon fuskata, sena dakko wata ta
na bude inda na rubuta Email din na miqa masa ina cewa “Gashi yanzu kaje Cafe ka
tura da Soft copy na CV dinka sannan ranar Monday zaka kai hard copy din”.
Kallona yayi da rashin fahimta, nan da nan na gaya masa yanda mukayi da Baffa na
rufe da cewa “Idan kuma kafi son kasuwar yace kaje ka same shi, ni da zaka hada
dukka ma kana aikin kana taba kasuwancin se ya fi yanda su Yaya sukeyi.
A zatona zanga farin ciki a fuskar Bashir irin wanda nake ciki amma se naga akasin
haka, cikin daure fuska ya kalleni yace
“Yanzu Ma’u har kin fara gajiya ne yasa kika tafi nemar mun taimako a gidan ku,
daman dazun ina gida an kai kaya yaran suka ce kece kika kawo yanzu kuma kinzo da
wannan”.
Tsabar mamaki ma kasa rufe baki nayi na tsaya ina kallon Bashir, a zatona abun
kirki nayi ashe shi a nasa girman kan gani yake baya yaci kenan na nema masa
taimako a gidan, se kawai na miqe na kwashi gyalena da jaka na ajiye masa Key din
motar ina cewa
“Ban shigo da ita ba tana waje naga ka datse get din da kwado” nayi shigewata daki.
Yanzu fisabilillahi da ace na samar masa aiki da kuma na zama ni nake dauke da
dawainiyar mu wanne yafi? A zatona tunda ya fadi hakan baze yi ba se gashi washe
gari yana ce mun ya tura ranar litinin din kuma yaje ya kai Takaddun cikin ikon
Allah ba’a rufa sati ba sega shi sun tura masa da takarda sun daukeshi aikin wani
satin ma ze fara zuwa.
Haka muka cigaba da tafiya zuwa yanzu duniya tayi mana daidai, Baffa ya dauke
nauyin makarantar Sa’ad, Samirah da Naziru ya saka su cikin foundation din sa da
yake biyawa Marayu da wadanda iyayensu basu da qarfi makaranta, shikansa Alhajin ya
saka Ahmad Yayan mu da yake likita ne yana aiki da Asibitin Malam Aminu Kano su
acan ana samun tallafi daga qungiyoyi dan haka ana daukar nauyin magungunan masu
lalurori ansamar wa Alhajin kyauta yanzu ake bashi magani ga ganin likita duk sanda
ya tashi har kanon yake zuwa tunda sunfi mu kwararrun likitoci se gashi a dan
lokaci ya dawo hayyacin sa ramar da yayi duk ta cike ya koma fita kasuwarsa yanzu
sannan ga Kayan Abinci da ake rabawa maqota yanzu suma duk wata se an kai musu
Albarkacin surukuta nasu rabon ma daban yake.
Dan haka yanzu dan abinda Bashir zeyi musu be wuce na neman Albarka da duk da
yakewa iyayensa ba idan yana da hali ni kaina yanzu se sambarka dan babu abinda
Bashir ya rageni dashi ya karbi ragamar gidan sa komai yana yi yanzu har kudin
makaranta yake bani daman tuni na bashi mota ta saboda zuwa aiki wanda dakyar ya
karba acewarsa Wanda ya siyamun bazeji dadi ba, be karba bama seda na kira Alhaji
Yasir din a gabansa na gaya masa Bashir ya samu aiki dan haka na bashi motata
saboda sauqin zirga zirga tunda ni ina dab da kammala karatun Jarabawa zamu fara,
“Babu komai ai taki ce kina da damar yin duk yanda kika so, daman saboda bana so
naga kina hawa motar haya ne ko ki ringa neman lift yasa tunda mijinki ne kinga ze
kaiki ko ina kuma ya dakko ki, Allah yaci gaba da baku zaman lafiya mu shine fatan
mu kawai” Alhaji Yasir din ya fada.
“Wallahi Ma’u rayuwar gidan mu tana burgeni, yayunku nada mutunchi sun kuma riqe
girmansu ba tareda nuna banbanci ba ko yau Baffan ku ya mutu bashida damuwa yasan
kanzuri’arsa a hade take ba kamar yanda yake faruwa a yawancin gidajen masu kudi ba
da zaki ga kowa yan dakinsu ya sani kuma burinsu ace sune a gaba sun fi sauran”
Bashir ya fada bayan da muka gama wayar, se nayi murmushi nace
“Idan Namiji ya zama tsayayye a gidan sa tabbas kan zuri’arsa zata hadu, amma daga
inda ka nuna banbanci tsakanin matanka shikenan kayiwa zaman lafiya gibi a gidan ka
dan yayan ko wacce zasu tashi wasu na ganin an fi son uwarsu sune yan gata sauran
kuma zaau qullace ka na ganin kana wulaqanta uwarsu ka banbantata da dayar kaga
baza’a taba samun zaman lafiya ba.
Kaima idan ka tashi qara aure kayi koyi da halin Baffan mu wallahi zakaji dadin
rayuwarka”
“Ni ai dan ke kadai aka halicceni Ma’u babu sauran gurbin da wata zata sake samu a
cikin zuciyata” ya fada yana janyo ni jikinsa.
Haka rayuwa taci gaba da shudawa. Nagama Diploma ta har sakamakon mu ya fito Bashir
ya siya mun DE form dukda ban so ba yace gara naci gaba na gama lokaci daya na huta
kawai.
Zaman gida da nake yanzu yasa Amirah ta dawo da zuwa, ba laifi yanzu ta dan saitu
tunda ta qara girma ga makaranta da take zuwa kuma nima ba kamar da ba da bana
saurara mata yanda zan tarbiyyan tar da Dan dana haka haka nake kula da ita dukda
wani sa’in in ta koma taja gayawa Addah haka zata qaraci mitar ta nidai bazan
kukata ba.
Indai har zata ci gaba da turomun ita to kuwa dole na saita ta yanda nake so. Yanzu
kusan kullum a nan take wuni dan Addah bata zama, tun safe in zata fice qantalinta
zata kawo mun Uniform din Islamiyyar Amiran da farko har Ummi ta fara Bari Bashir
ya hana kai tsaye yace mata karta sake barinta dan matarsa ba me raino bace ai kuwa
munga ruwan masifa dan har Dada seda ta karbi rabonta haka dai aka dena se Amiran
ake barmun.
Wani lokacin ma har kwana takeyi idan Addah tayi dare bata dawo ba ko Bashir yace
ta tafi ta zauna a gun Sauran Matan gidan se nace Yabarta kawai dan har ga Allah
ina son yarinyar daman rashin jin ta ne ya ke hadamu nima kuma zuwa yanzu na fara
sha’awar ajiye nawa Dan dan duk su Alawiyya sun haihu shekarar mu daya da kusan
wata takwas yanzu da aure amma ni shiru.
Akwai ranar da na taba yiwa Bashir maganar nace masa ko zamuje Asibiti yace muna Aa
“Komai lokacine kuma bamuyi dadewar a har zamu ce zamu Asibiti ba, mu qara haquri
Allah yasa jinkirin ya zama Alkahiri” ya fada dole na haqura.
Da zaman haka da nakeyi akwai wata makaranta a qasan layin mu nacewa Bashir zan
nemi koyarwa acan be hana ni ba kuwa dan da kansa ma yaje ya tambayarmun suka ce
naje ai kuwa aka sauke ni zan ringa koyarda yan JS1-3 Computer Science, qarfe 8
nake shiga 12 na gama classes dina in tafi gida kuma sosai nake jin dadin aikina
haka yaran suna ganewa dan Allah yayi mun baiwa ta iya magana, sannan yanda nake
da Sakin fuska yasa muka saba sosai da dalibaina.
Cikin hukuncin Allah se gashi na samu ciki wanda sam ban san dashi ba seda ya kai
kusan wata uku a jikina sannan naje Asibiti saboda rashin ganin Al’adata na tsahon
lokaci se gashi gwajin farko an tabbatar mun ina da ciki bayan an yi scanning aka
gayamun watanninsa.
Tun ina Asibitin na kira Bashir na gaya masa, sosai kuwa ya nuna murnar sa yace na
tafi gida na huta kafin ya dawo haka muka kwana ranar cikin farin ciki kamar mu
ciro dan haka muka ringa kallon hoton scanning din da ba ganinsa ake yi sosai bama.
Kamar kuwa cikin nan na jiran a san dashi se Laulayi ya taso ni gab, kuma wani abu
safiya nayi idan Bashir ya fita haka zan wuni da zazzabi da ciwon kai amma duk inda
La’asar tayi kafin ya shigo gida na ware dan haka ko nayi masa qorafin baya yarda
musamman idan ya dawo banyi girki ba ya ringa mita kenan in ce bani da lafiya kuma
yace shi be gani ba.
A daidai lokacin kuma Admission dina ya fito, wannan karon na samu daman Business
Administration na nema sun bani Level two haka na fara jigilar zuwa makaranta ga
ciki ga karatu dan ma farkon semester ne, randa naji ba kanta kwanciyata nakeyi a
gida naqi zuwa, haka muka ci rabin zangon, an tafi hutun Midsemeater aka tsunduma
yajin aikin da ba qaramin dadi abun ya mun ba na ringa Addua Allah yasa kar a koma
sena haihu.
Haka mukayi ta lallabawa, ina rainon cikina, Addah kullum tana tafe da kayan
kwalamar da tasan zan so amma fa idan tazo ita ma haka zata koma da niqi niqin
tsaraba dan duk abinda idonta ya kai se ta dauka ni kuma bana hanawa sedai Bashir
yayi ta fada idan ya gani ko ya tambayi abu nace babu dan yasan ita kadai ce take
zuwa ta dauka.
A lokacin su Fainusa sunyi candy dan haka suna zuwar mun sosai wata ran ma ni zan
kirasu idan naga kwana biyu basu zoba haka zasu wuni suyi warkaja min su son rai,
kayan sawata da duk suka mun kadan saboda ciki haka zan tattara in basu, kayan
kwalliya turare duk zuwa da abinda zan basu har seda ta kai ta kawo ko bikin qawaye
zasuje gurina za’ayi aron su takalmi, jaka sarqa wani lokacin in suka karba nace su
barshi.
Lokaci daya maganar auran qannen Bashir Mata su ukun ta taso. dafarko auran Afiya
aka saka, wane tudu wane gangare se ji nayi a bakin Addah wai ai gaba dayansu za’a
hada”.
“Ni nacewa Nafi a hada yaran nan dukka kawai lokaci daya a huta to me za’a jira
tunda duk da tsayayyun maneman su gasu da garin jiki ai bata jerasu a gaba su zamar
mata kamar wasu kishiyoyi ba.
Tana wani ya za’ayi hidima zatayi yawa bayan ga Bashir Allah ya rufa masa asiri
aikin Banki fa yakeyi har a tsaya ana wani zancen kudi” Addahn take gaya mun.
Niko banda “Allah ya sanya Alkahiri” ban ce mata komai ba dan mamaki take bani
yanda take ji da aikin Bankin nan na Bashir seka rantse wani babban Manaja ne a CBN
idan ba haka ba ta yaya za’a tattago auran yaya mata har uku kuma a dan qurarren
lokaci kwata kwata wata hudu fa suka saka rana. Ai ko bashi da nasa hidindumun a
bashi isashshen lokaci ya shirya balle ga hidimar haihuwa a gabansa dan kusan
lokaci daya bikin ze kama da haihuwata.
Haka Bashir ya ringa mita kullum ya zauna saurin me akeyi da za’ace su uku za’a
hada ina laifin Afiya da Sadiya dan duka duka Fainusa bata cike sha shida ba kawai
girman jikine yasa aka mata tsallake a makaranta suka gama tareda Sadiyan.
Haka naci gaba da rainon ciki na a can kuma suna ta shirin biki, Alhajin su yayi
iya qoqarin sa ya bada kudin gadajen Amaren kowa daya harda katifa dan shi kansa
ba’a san ransa aka saka auran duka ba amma bala’in nacin Addah da har ta zuge Dadan
itama ta hau ta zauna dole yasa musu ido sannan ya kira Bashir ya gaya masa karya
kuskura ya takura kansa su saka shi yin hidimar data fi qarfinsa akai kowacce da
abinda Allah ya hore tunda sun nace se anyi.
Dan haka gaba daya dan Albashin nasa da duk wani saving dinsa ya basu akayi musu
kujeru gudummawar da aka samu daga sauran yan uwa da abokan arziqi suka harhada aka
yi abunda ya samu.
Ido kawai na zubawa Bashir ganin har cikina ya kusa fita daga wata na takwas amma
ko pant din jariri be siyo ba ko ya bani kudi yace na siya se hidimar auran
qannensa yake yi. Raina ya sosu da abin har na kasa haqura wata rana nayi masa
magana se ce mun yayi
“Ma’u kenan saurin me kike yi ki bari a haihu mana ko bakiga hidimar data ke a gaba
na bane duk qoqarin da nayi kina kallo kullum da sabon abunda zasu ce akai ni gaba
daya ma na gaji Allah Allah nake ayi bikin nan kowa ya huta”.
Sosai naji zafin maganar sa a lokacin, cikin bacin rai nace masa “Amma shima wannan
abu me muhimmanci ne kuma kasan dai kaine meyi sannan ba yau kasan ina da ciki zan
haihu ba tun ma kafin maganar bikin ta taso cikin ne a gaba yanzu kake cewa a bari
a haihu tukunna cikin da ko a yanzu za a iya haife shi amma ko rigar da za’a saka
masa bamu tana da ba ai shikenan” na tashi na bar masa gurin.
Nakuma qudurce a raina bazan sake masa magana ba dan daman tuni na sissiyi wasu
wasu kaya unisex dana gani suka mun kyau se kawai na hada akwatina ta zuwa Asibiti
na jingine in yaso naga iya gudun ruwan Bashir.
Wannan Abun yasa gudummawar danayi niyyar bayarwa ma na maida abata tunda a take
takensa nasan ba abin arziqi zeyi mun idan na haihu ba nayi amfani da kudin na
toshe wata kafar, Addah tayi shaguben harta gaji akan biki nata matsowa wai matar
babban Yaya bance komai ba, ai ni ma ina da wayona ni na iya bauta musu amma abinda
yake doke ayi mun saboda tasu buqatar tafi tawa ana nema a tauye ni sannan na
kwashi gudummawa na bayar lallai ma se kawai nayi dariya nace mata
“Ai babban yayan ya wakilce ni yayi komai sedai mu jira Allah ya kaimu musha biki”.
Ana saura sati daya bikin Matan gidan nu suka aika wa Dadan da saitin Kuloli manya
guda uku, a ranar ta kirani a wata tana ta godiya wai an kawo kula masu kyau da
tsada