Showing 111001 words to 114000 words out of 238465 words

Chapter 38 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

kina maimaita wadannan maganganun a gaba na sa’arki na zama,
wallahi se na yi mugun saba miki” na qarasa ina huci bayan dana ture kayan abincin
gaba na dan gaba daya komai ya fice daga raina ita kuma sum sum ta tashi daga gurin
ta shige dakinsu.

Wannan abun kunya har ina, tabbas Bashir irin mazan da basa iya rufe bakinsu ne a
lokacin da yake mu’amalar aure amma ban dauka ihun nasa har yana karade gida da
Amirah zata iya jiyo wa ba musamman idan ka duba tazarar da ke tsakanin dakin sa da
inda nasu dakin yake dama dai a dakina ne ana jiyo duk motsin da akeyi a dakin
Bashir.

Haka na wuni cikin rashin sukunin zuciya dan Amirah tuni ta fice ta tafi gidan
Addah ina nan sukuku har yara suka taso daga makaranta su kansu seda suka gane bana
jin dadi.

Da magriba muna Kitchen da Amna ina girki tana dan tayani da wasu abubuwan, tun
tuni nake saqawa a zuciyata na tuntubeta da dabara naji ko suma suna jin wani abun
ina ta fargabar amsar da zan samu tunda dai daki daya suke kwana, me nauyin bacci
ma taji bare amma da sam bata da nauyin bacci amma kuma ya zama dole na tambayeta
kodan nasan matakin da zan dauka saboda tarbiyyar su, ina ta hiqilo akai kar naje
tufka nakeyi ta baya tana warwarewa.

Gundumbala nayi nace “Amnah, ni kuwa jiya kinji wani motsi ko maganganu a gidan nan
da daddare?”

Seta dago daga yankan Albasar da takeyi tace “motsi kuma Mami gaskiya ban ji komai
ba in banda karatun da kika kunna a Mp gurin qarfe uku ma dana tashi zanyi fitsari
shine naji ya mutu na fito na duba ashe chaji ne ya qare na jona kuma dai banji
komai ba wallahi”.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi kafin na sake cewa “Ni kuwa se na ringa jin kamar
ana hayaniya da daddare bama iya jiya ba, duk sanda Abin ku yake gari ina ji ta
windon dakinsa kuma dana tambayi Amirah ma se tace mun itama tana ji”.

“Toh Mami qila daga qidan su Faisal ne (maqotan mu ta gefen da dakin Bashir yake)
kin san suna da yawa kuma Raliya tace suna kaiwa har qarfe uku wataran basuyi bacci
ba suna kallo musamman weekend, Anty Amirah kuma daman ai a dakin ki take kwana
itama kinga zata ringa ji”.
“A dakina take kwana kuma?” Na tambayi Amna da mamaki, seta daga kai Alamar da
gaske tace

“Eh mana Mami bake kika ce ta ringa kwana a can ba duk sanda Abbi yake gari wai
kince idan ana barin daki babu kowa Aljanu suna kwana a ciki shiyasa duk sanda zaki
kwana a dakin Abbi to ita kuma a dakin ki take kwana se da Asuba take dawowa nan”.

“Lallai watan cin kutumar uban Amirah ya kama” na raya a zuciyata. Ban taba sanin
yar is kar yarinya bace mara mutunchi se yau, daman dakina take zuwa ta kwanta tayi
mana labe kenan saboda taji abinda muke tabbas kuwa a yau ba se gobe ba seta bar
gidan nan wallahi.

Muna cin abinci ta shigo gidan sadaf sadaf kamar munafuka se tayi turus da ganina a
zaune dan nasan hasashenta ina daki saboda idan na idar da sallar Isha se nayi
shafa’i da wutri na danyi lazumi na kafin nake futuwa palour yau din kuma da
magribar nan Period yazo mun.

Kallonta nayi daga sama har qasa a fili na ce “kan uban nan” ina miqewa tsaye sosai
na qare mata kallo, Kayana ne a jikinta, Wata Atamface falle biyu na siya saboda
kyan da tayi mun akayi mun fitted straight gown dikin yaqi shigata saboda ya matse,
tunda ta gani take nacin na bar mata ni kuma naqi saboda ina son Atamfar kuma na
nema tsaf an rasa samun wata se plain yadi tailor ya siya yace ze gyara mun dinkin
shine taje ta dauka ban sani ba dan da zata fita ma Hijabi ta saka har qasa ban ga
kayan jikin ta ba.

Irin kallon da nake jifan ta dashi ya sakata qarasowa tana cewa “Dan girman Allah
Mami kiyi haquri wallahi dan Allah...” tas na kwasheta da Mari kafin na nuna mata
qofar dakin su cikin kaushin murya nace

“Minti goma na baki ki shiga ki cire mun kaya ki kuma tattara yanaki ki wuce gida
yanzun nan dan bazan sake zama dake ba tunda baki da tarbiyya”.

Kuka ta saka mun tana tambayata wai me tayi dan Allah nayi haquri na sake jaddada
mata wallahi seta bar gidan nan a yau, tunda har take yi mana labe wata rana kuma
ai leqa mu zatayi idan ba’ayi sa’a ba haka ta tattara a daren ta wuce gida tana
fita muka kulle gida na kuma kashe wayata dan na tabbatar idan Addah bata biyo sahu
ba toh kuwa zata kira waya.

Washe gari kuwa qarfe bakwai da rabi A gidan tayiwa Addah, mun fito zan kai yara
makaranta naji ana dukan Get, Musbahu yaron shagona yaje ya bude se gata kamar an
wullota ta hau tijara da diban Albarka akan me zan korar mata ya ita da gidan dan
uwanta.

“Gata nan ai a gaban ki ki tambayeta me tayi mun” na fada ina kunna mota, ina ji
tana ta zuba rashin darajar ta nayi banza dasu na zuba yara a mota, dai dai zan
fita naji tana cewa

“Wallahi baki isa ba Asma’u, baki isa kice me kadai zaki mallake Bashir da
dukiyarsa ba se Amirah ta dawo cikin gidan nan kuma a lokacin baki isa ke koreta
ba” nidai nayi zooming na fice na barta a tsaye tana kumfar baki.

Dariya ma ta bani wai na mallake Bashir da dukiyarsa nayi me dasu, su kudi suka
dama da har suke ganin ya tara wata tsiya dab dai ni har yanzu ina masa Kallon
Bashir din dana sani me tun bashi da komai, idan ma ba haka ba babu wanda ya tayani
shan wahalar sa a cikin su idan ma nace zan mallake shi ni kadai ai banyi laifi ba
ko.


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 38

Se bayan dana kai yaran na dawo sannan na kunna wayata, kiran Dada ne ya fara
shigowa na daga na gaishe ta daga yanda ta amsa nasan labari ya isarmata kenan.

"Akan me zaki kori Amirah daga gidan Bashir Ma'u" ta fada bayan da muka gaisa.

Lallai wato gidan Bashir tana gaya mun ba gidana bane kenan, murmushi nayi, babu
kunya tiryan tiryan na karanta mata abinda ya faru da duk abinda Amiran ta fada mun
dama sauran abubuwan da takeyi a cikin gidantsaf seda na tsara mata.

Seda tayi jum da na tabbatar na kunya ne kafin tace "To ai koma menene be kamata ki
koreta ba haka da se kija mata kunne ko ki kawo mana qararta mu se mu tsawatar
mata, yanzu dai se kuyi haquri ta dawo kuci gaba da zama Allah ya kiyaye gaba".

"Wallahi Dada bazan sake zama da Amirah a gidan nan ba, ta koma gidansu idan
auranta ya tashi bazan fasa yi mata duk abinda idan a hannuna take zanyi ba amma fa
ba dai gidan nan ba" na fada kai tsaye dan ganin ana nema ayi mun fin qarfi, ita
bataga illar abinda tayi ba kenan har ake cewa nayi haquri ta dawo to kuwa baze
sabu ba.

Muna gama waya na kira Bashir na kora masa jawabi dan tun a jiya da daren nake ta
neman wayar sa ban samu ba se text message na bar masa. Yanzun kuwa yana amsawa na
kora masa abinda yasa nace ta tafin, zuwan Addah harma da wayar da mukayi da Dada.

"Wallahi bazan sake zama da yarinyar nan ba kama gaya musu"

"Daman ai ke kika gayyato ta gidan tun farko ai ni meye nawa a ciki?" Bashir ya
fada.

Bansan dai ya suka qarke ba a batun Amirah kwanaki kadan tsakani ya tayar da
maganar komawar mu Lagos dan ya samu gida babba da ze wadace mu. Nayi zaton za'a
samu matsala dasu Dada saboda kes din Amiraj da mukayi amma se naji shiru haka muka
fara shirye shiryen dan a lokacin ana Third term ne har yara sun fara shirin
jarabawa, daga sun gama zamu tafi se a saka su sabuwar makaranta su koma sabon
session.

Lokacin da zamu tafi gida gida nabi duk nayiwa kowa Sallama har gidan Addah naje
muka rabu faran faran tana cewa se sunzo dan tana son zuwa Lagos in muka nutsu zata
zo tayi mana sati har bakin ruwa se an kaita nace Allah ya nuna mana lokacin ta
hada mana tsarabar kayan qamshi da su daddawa harda man Shanu ga dambun nama da
tayiwa Jafar dan shine mutumin ta.

Haka muka tattara muka koma Ikko, gidan da Bashir ya samu babban gida ne me kyau
yana cikin rukunin gidajen manyan ma'aikatan su.
Flat ne me dauke da manyan dakuna guda biyu se madaidaita suma biyu ko wanne kuma
da Bandaki a cikin sa, ga qaton palour da Gurin Dining, Kitchen, store sannan ta
bayan gidan da akwai babban fili da akayiwa shuke shuke daga gefe akayi garden.

Gida dai masha Allah kuma Bashir ya saka komai na buqata a ciki. Se da nayi dagaske
kafin na iya daure kewar gida na saba da garin, dan ma nayi sa'ar maqociya wadda
take matar Ogan Bashir ce Anty Halima mutuniyar kirki, ita ta qara wayar mun kai da
zaman Lagos na gane kan kasuwa ya zaman ina sarar kaya na turo dasu ko ina kake so
a fadin Nigeria.


Kamar wasa naga tallan daukar ma'aikata na wani kamfani da suke hadahadar ma'adanan
qasa anan Lagos, a lokacin na cewa Bashir zan cike ya kuma bani goyon baya na nemi
aiki cikin ikon Allah se kuwa na samu suka daukeni matsayin meyi musu tallace
tallace.

Na kama aiki ba dadewa wata rana kwasam muka samu baquncin Addah, Dada harda
Amirah. Sosai mukaji dadin zuwan su dan baka gane dadin gida se randa kayi nesa da
yan uwanka kwanan su hudu Addah da Dada suka juya aka bar Amirah da alokacin wai an
saka ranar auranta da wani yaro Bashir shima sunansa dan Abokin babban su Bayan
sallahr Azumi da sati daya.

Dalilin kawota kuwa saboda acewarsu na koya mata yan abubuwan da ya kamata ta iya,
nayi dariya kuwa nace duk abinda bata koya ba a zaman kusan shekara goma da mukayi
tare banajin zata iyashi a watanni biyu kacal, haka dai suka tafi suka barmu na
kuwa dage tsakani na da Allah ina dora yarinyar nan akan hanya ta hanyar nusar da
ita komai.

Tunda tazo sau daya Saurayin nata Bashir yazo da yake anan Lagos shima yake zama,
nidai itin yanda naga yana ta dari dari da ita bayan ya tafi na kasa shiru seda
nayi mata magana nace

"Wai ni Amirah hada ku akayi da Bashir ne?"
"Aa Me kika gani Anty?"
"Gani nayi yanda yaqi sakewa dazu da yazo musamman tunda Baban Ali ya dawo jikinsa
fa har wani rawa ya ringayi".

Dariya tayi tace "haka fa yake Anty ni wallahi har tunanin yanda ma zamu zauna
dashi nakeyi, nida nake son na samu miji mu sha soyayya irin taku da Yaya shi yasa
fa na samo me irin sunan sa ma. Nidai ki taimaka mun Anty ki koya mun duk irin
abubuwan da kikeyi nima na zama star".

Hade rai nayi, na fuskanci Amirah dai se gyaran Allah sauqin ta dai za'a mata auran
taje ta qarata in huta, haka muka ci gaba da zama ina koya mata duk wasu abubuwa
daya kamata macen data san kanta ta iya su.

Bilhaqqi nake bata sirrika da kuma gyara tamkar yanda zanwa qanwata ciki daya kafin
cikar wata daya kuwa ta fara hawa saiti dayake ita ta saka kanta hatta girki yanzu
tana qoqari sosai dama abun nata harda qyuiya da qyashi suke hanata tayi a lokacin
baya yanzu da yake a rajin kanta ne wani lokacin kafin na taso daga aiki ma ta gama
abinci, gyaran gidane dai se a slow, zata ci kwalliya amma gurin da zata zauna be
dameta ba.

Tsakanin ta da Bashir dai bana ce komai ba dan daga gaisuwa wata magana bata qara
hadasu idan yana zaune ma bata fitowa tana daki tana chatting din daya zamar musu
dabi'a yanzu daga ita har Bashir dan shima yanzu muna zaune bini bini yana danne
dannen waya wani lokacin kuma se naga ya zauna yayi shiru kawai kamar akwai abin da
yake damun sa dan inbanyi qarya ba se nace har rama yayi amma se na ta'allaqa hakan
qila da yanayin aiki, a haka muka shiga watan Azumi wanda ya rage saura sati biyar
bikin Amirah kenan.

Ranar da aka kai Azumi na uku bayan ansha ruwa Addah ta kirani take gayamun sunje
ganin gidan Amirah.

"Gidan yar taki yayi kyau Ma'u sena kin gani daki uku mijin ya bata da palour se ku
yunquro dan kinsan gidan kishiya ne dole ki gwangwaje yar taki".

"Gidan kishiya kuma Addah dama Bashir din ya taba aure ne" na fada da mamakin
maganar tata, se ta shiga in da in da tana cewa
"Au Faccala nake so nace miki, gidan su daya da matar wansa wannan kishin ai har
yafi na kishiyoyi zafi, zan saka a turo miki da kudaden da Babanta ya bayar a siyi
gado dana gurina da za'ayi mata kayan Kitchen tunda ai kece uwarta".

"Hakane kuwa to Allah ya sanya Alkahiri ya nuna mana lokaci babu damuwa, a turo din
kinsan daman kaya anan sunfi kyau da Sauqi se mu siya a kawo kawai" daga haka
mukayi sallama Allah a raina naji dadin karamcin da akayi mun aka dorani akan har
kar bikin.

Haka na tasa Bashir da nacin se ya siya mata gado daya se a hada da na gurin
Babanta biyu kenan daki dayan in mijin yaso se ya gyara abinsa amma Bashir ya dage
akan shi bazeyi ba bashida kudi saboda a sannan gini yakeyi, ya rushe gidan mu na
Gombe ya siyi filin kusada mu an qara ana mana sabon gini kuma daga yanayin plan
din nasan dole zeci kudi.

Dana takurashi daga qashe yace dubu dari yayi niyar bada gudummawa nace sunyi kadan
gadon nan fa dole shi ze siya mata haka dai ya haqura daga qarshe ya yarda yace na
ranta masa kudin muka siya mata gado me kyau dan dubai a sannan ma dubu dari hudu
muka siye shi irin nawa dana siya na chanza na dakina na mayar da na ciki dakin su
Amna.

Hidimar da nayi ta kayan auran Amirah ko bikin Farida nake yi se haka dan wallahi
bazan iya lissafa nawa na kashe mata ba a kayan Kitchen Anty Halima har fada ta
ringa yi mun tace dangin miji nakeyiwa wannan hidimar a maimakon nayi musu gwaninta
qarshe baki zan janyowa kaina suce da kudin dan uwansu nake wadaqa amma na toshe
kunnena nayi mata.

Haka na tattara kaya rankatakaf aka kwasa a mota aka kai Gombe sannan muka ci gaba
da gyaran Amarya kuma da shirin biki dan har dinkunan ta duk nan aka kawo na bawa
sabon tailor da nayi ya yi mata dinkuna na daukar magana biki kawai muke jira.

Randa aka kai azumi na Ashirin da biyu Bashir yazo mun da Albishir din ya biya mana
Umarah nida Yara Gaba daya kuma wai a gobe zamu tashi abin ne da kamar baze yuwu ba
shiyasa be gayamun ba se yau da safe sannan komai ya kammala.

Nayi murna kuma banyi ba. Murnar da nayi ta tafiya Umarar ce da kuma yarana dukka
gaba daya abinda na dade ina mafarkin yi inda naji rashin dadi kuma ba tare da
Bashir zamu tafi ba dukda sati biyu zamuyi dakyar idan tarar da bikin Amirah qila
ranar da aka gama zamu dawo amma.

Haka muka tashi hada kaya a daren dan ma tashin namu bana safe bane, ta waya na
kira gida mukayi musu sallama washe gari tun safe Amirah ta fara tafiya Gombe,
harda kukanta wai bana nan za'ayi biki gaskiya zataje ta cewa su Addah a qara sati
se na dawo haka na rarrasheta ta tafi, mun samu delay najirgi dan haka se qarfe 7
na Magriba muma muka tashi zuwa qasa me tsarki muka bar Bashir shi kadai yana ta
daga mana hannu.

Mun sauka qasar madina lafiya, sosai na kama ibadah ta dan ko kusa ban bari hidimar
yara ta hanani ribatar goman qarshe da muka shiga ba. Kwanan mu biyar muka tafi
Makka muka dauki Haramin umarar mu, bayan mun sauke nan ma a kullum ina Masallaci
ina ibaduna, kwanan mu biyu aka sallace banyi sanya ba na duqufa sosai ina ta kaiwa
Allah kokena. Adduata duk akan Iyayena, Yarana da Mijina tareda sauran Al'umar
musulmi baki daya.

Ranar Juma'a data kama Lahadi zamu dawo Nigeria da yamma mun fita kasuwa da yara
wayata dake cikin jaka ta ringa qara, seda muka shiga shagon nacewa Amna zu zagaya
su dauki abubuwan da suke so kafin na dakko wayar na duba,

Rahma ce Amaryar Amiru da mamaki nake kallon tarin missed calls dinta gida shida se
na fara qoqarin kiran ta dan tabbas nasan ba lafiya ba irin wannan kiran nayi sa'a
kuwa ringing biyu ta amsa wayar.

"Maman Aliyu wane labari naji dan Allah kice mun ba gaskiya bane" ta fada ba tareda
ta bari ko gaisawa munyi ba. Se naji gaba na ya fadi, daman dauriya nakeyi, a
kwanakin kullum cikin faduwar gaba nake da quncin zuciya na rasa me yake damuna
shiyasa ko da yaushe ina cikin Harami ina sallah ko karatun qur'ani su kadai suke
sanyayamun zuciya na kuma fawwalawa Allah ya iya mun koma menene yake tun karo ni
dan a duk sanda naji irin wannan yanayin to tabbas wani mummunan abu ne yake shirin
samuna.

"Maman Aliyu bakya jina ne kin yi shiru k baki samu labarin abinda yake faruwa
bane" Rahma ta sake fada abinda ya fito dani daga duniyar tunanin dana luluqa.
"Wani abun ne ya faru Rahma ban sani ba wallahi Allah dai yasa lafiya" na fada a
sanyaye, se tayi shiru kafin cikin wani yanayi tace

"Tunda baki sani ba bazakiji a bakina ba Maman Aliyu amma ki kira Yaya Bashir yanzu
base anjimaba kiji komai" kafin nace wani abu ta yanke wayar.

Seda na kira Bashir sau uku amma be daga ba, ganin magriba ta kusa sena haqura muka
qarasa siyayyar mu muka koma masauki akan zuwa bayan Isha se na sake kiransa idan
na dawo daga masallaci amma sam na kasa samun nutsuwar zuciya.

Kira na ringa doka masa abinda ya bani mamaki ko ince ya fara bani tsoro ganin na
kira yafi sau Ashirin wayar tana qara amma ba'a daga ba sena mayar da akalar kiran
nawa kan Amiru dan na sake kiran Rahman itama bata amsa ba.

Kira biyu ana ukun Amiru ya daga. Cikin sanyinsa muka gaisa se mukayi shiru gaba
daya ni ina jira naji yace wani abu ne ya samu Bashir shima yana jiran jin dalilin
kiran, ni na katse shirun da cewa

"Baba Amiru Bashir kunyi waya da Bashir kuwa yau"

"Eh mun yi waya bamu dade da rabuwa bama na barshi a gida yanzu na fita"

"Oh yana Gombe ashe, nayita kiran wayarsa ne amma ban samu ba shine nace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login