Showing 78001 words to 81000 words out of 238465 words

Chapter 27 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

ba
batun aure babu tsayayye”.

“Shidai malamin Primary da kika qi shine mijin idan kuma kika daga za’ayi dayan
biyu ko ki mutu ayi ko kuma a haife miki shege a gida” ya fada ba tareda ya kalle
ta ba, se Addah ta dage qirji tace “na shiga uku Malam na mutu fa kace?”

“Hajia Da wani abu ne ko shikenan” ya sake fada yana kallon Hajia Maliya, seta miqe
tana cewa “Aa babu komai malam daman yau rakiya nayo ni ai al’amura se godiya
kawai, Fatu bada abin sadaka mu tafi”.

Kallonta Addah tayi da niyyar Magana Malamin ya rigata da cewa “Kuje tayi mun
sadaka da kudin Allah ya yafe mun zunubaina” daga haka sukayi masa sallama suka
tafi.
Seda masu babur suka sauke su a Tashar Dukku har sun shiga mota Hajia Maliya ta
kalli Addah tace “Fatu bakiyi sadakar bafa ko se munje cikin gari?”

“Ke dallah rabani da dan rainin wayo, aikin me yayi mun da zanyi masa sadaka wani
Allah ya yafe masa ashe yasan abinda yake babu kyau kenan” Addah ta fada a fusace
dan sam ita ba abinda taso ba kenan, dukda wani sashe na ranta yayi fari da aka ce
Ma’u zata fita amma ita so tayi ayi mata abinda idan ta fitan bazata dawo ba.

“Ai aikin gama ya gama tunda har kika taka kikaje gurinsa kema kin debo naki kason
zunubin kuma dole ki bada kudin nan kinsan dai ba’acin kudin malamai a zauna
lafiya” itama Hajia Maliya ta hayayyaqo mata.

“Gashinan nidai Allah ya saka mun” Addah ta gada tana cilla mata yan dubu dubu guda
biyar, se Hajia Maliya ta cafe ta fita daga motar tana cewa “Ya saka mun dai nida
na kawo ki ke da ba’a miki abun arziqi, Yara Almajirai ta samu ta bawa kudin kafin
ta koma motar mintina kadan ta cika suka dauko hanya.


Da suka sauka a tasha ma sama sama sukayi sallama kowa ta kama gabanta, suna zuwa
gida kuwa Amirah ta tafasa saiwar nan ta fara sha dan tafi mata magungunan da Addah
ta karbo kwana ki tana ji Addan nata bala’i waya sani ko shima hadin bakine da
Maliya irin nasu Wizy ita dai bata kula ba harta gaji tayi shiru dan kanta.

Suna dan yin waya da Bashir lokaci zuwa lokaci badai kamar da ba kuma yawanci da
rana ne idan yana gurin aiki da ya shiga gida kota kira baya dagawa ta rasa abinda
yasa. Randa ta yi masa qorafi ma seda suka samu sabani har yayi mata yaji kusan
kwana hudu be kirata ba toh da yake neman shir takeyi tana so ta karbi kudi a
hannunsa ta danyi wasu abubuwan shi yasa ta kira ta bashi haquri.

Kwananta uku da dawowa sukayi baquwa, Amaryace da aka kawo gidan da yake kallon
nasu daman matar gidan ta rasu tun tuni se yanzu mijin ya sake aure.

Amarya Sa’ada da kadan ta girmi Amirah amma bazawarace auranta daya tana da yaya
biyu ma suka rabu da mijinta cikin dan lokaci sabo sosai ya shiga tsakaninsu da
Amiran da yake mijinta ba mazauni bane kusan kullum in ta gama ayyukanta se ta
shiga gidansu Amirah kota kira ta ita taje suyi hira a haka har ta karanci Amiran
ta gane irin zaman da sukeyi da Bashir har ma da kishiyarta.

“Amma kedai anyi mara wayo wallahi, yarinyar ki dake kin maida kanki baya ita me
haihuwa biyar itace star a gurin miji kina zaune. Inda kinsan kanki wallahi da tuni
sanda ze tattarota ya dawo da ita nan ke ki bishi bama ze sani ba” Sa’ada ta fada
ranar da Amiran take mata qorafin Bashir yaqi kaita inda yake aiki.

Kwananta Arba’in da biyar da Haihuwa Sosai kuma taji dadin maganin da Malamin nan
ya bata dan duk sauran kunburin nan bata fi sati tana sha ba ta neme su ta rasa
jikinta ya dawo dai dai rashin kwarin da takeji ma duk ya ragu daman kuma aikinta
tuni ya kame yayi kyau dan haka ta fara shirye shiryen tarbar Bashir.

Tunda ya tafin nan be sake ce mata ze zo ba itama kuma ganin bata gama shirya wa ba
ya saka bata ce masa yau she zezo dinba amma yanzu da take jinta garau dole ta nemo
shi dan haka ta chanza salon hirar su yanzu, babu ruwanta ko yana offfice ta
kirashi seta san yanda tayi ta rikitashi da salo kala kala da ta koya a gurin
sabuwar qawarta Sa’ada.

Wayar da sukayi ta qarshe ma wani Text Sa’ada ta rubuta mata tace ta tura masa, duk
bala’in taurin kansa se ya sauke ya taho gurinta idan kuwa taga bezo ba to ta
sallama kawai Asma’u tasha gabanta har gaban abada Bashir baya Sha’awar wata Mace
idanba ita ba ilai kuwa tana tura masan ta kirashi ta sake gigitashi da kalamai
masu kashe jiki se ji tayi yace gobe zezo Gombe,

da tayi masa qorafin ba,a share gida bama cewa yayi babu komai ta shirya daya zo se
suje Hotel kawai ai kuwa kamar tayi me dan murna tun a Daren ta fara shirya kaya da
abubuwan da zatayi amfani dasu ji takeyi kamar ta janyo safiyar tayi.

Bashir ya sauka Gombe lafiya kamar yanda suka tsara da Amirah yana sauka ya kirata
dan da Naziru ya dakko shima a hanya ya sauke Nazirun ya karbi motar ya wuce gidan
Addah yana zuwa ta fito suka tafi.

Babban Daki me kyau ya kama musu, su Amirah se rawar kai ake itama yau an fita
yawan shanawa da miji, dan hoton nan da akeyi mata da miji anje chilling ita sedai
ta gani a gurin qawayenta saboda duk sanda zezo gurinta a Gomben seta jangwalo
tsiyar da zasuyi in ma an shirya fitar ta rushe shiyasa take shaqar takaici idan
taga hotonsu da Ma’u Fitar Asabar da Lahadin nan da sukeyi toh itama wannan karon
in sha Allahu zata dage babu abinda ze bata mata wannan lokacin hotuna kuwa sedai
zuciyar wasu ta buga dan haushi.

Sosai sukaji dadin zama a hotel din nan an murji Amraci an more, washe gari Asbar
da safe yaje gidan su Ya gaida su Dada be dade ba ya koma, sun sha yawon su kuwa
Joint joint ta dinga janshi ansha hotuna sosai ya kuma yi mata shopping sosai. A
yar Keypad dinta ta tura hotunan saboda me memory ce, ta daure ta cije batayi masa
zancen waya ba ta bari ta gani zuwa ya tafi tukunna karta ballo wata tsiyar.

Seta tuna maganar malamin nan daya ce idan ta kwantar da hankali zata ji dadin
Bashir Asiri ba wani tasiri zeyi akan sa ba gashi kuwa ta gani dan cikin lumana ya
amince ze chanza mata Tv da Set din Tv stand da Centre table harya bada kudin Tv da
deposite din su Centre table din duk da dai Tv ba irin ta Asma’u bace amma itama
babba aka siya mata 53’ ina laifi?

Randa ze tafi kuwa harda ita suka kaishi Airport tana narke masa kamar karsu rabu
suna dawowa gida Naziru ya ajiye ta ba’a rufa awa biyu ba se gashi da sabuwar
IPhone 11 pro inji Bashir a kawo mata harda layi me Data.

Murna kamar Amirah tayi me ta ringa kwasar Shoki tana tsalle nan da nan ta kirashi
tayi masa godiya

“Indai zaki chanza ki dawo irin haka babu abinda bazanyi miki ba Meerah” Bashir ya
fada. Cike da sabon jin dadi sukayi sallama ta kashe wayar nan da nan ta hada ta ta
dora layi ta shiga downloading WhatsApp, a wayar Ummi ta saka Memoryn ta ta tura
hotunan zuwa sabuwar wayar ta tana cewa “yau akwai fafatawa kenan, dole nawatsa
hotuna a Internet kowa ya gani” (An kuma ashe tuban muzuru kikayi toh Allah sa a
wanye qalau dai 😂😂)


Biki mukeyi se Monday In Sha Allah zaku ji ni 🙏🙏🙏🙏



🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 30

ASMA’U

Cikin kwanaki biyar muka gama abinda ya kaimu, ada naso na yi weekend na huta ne
har nadan zaga dangi amma saboda yanayin rabuwar mu da Bashir yasa na fasa daga
gidan Alhaji qarami ko gidan Yayata Junaidiyya da mijinta yayi Accident, naso naje
na dubashi amma gudun kar sauran suce banje musu ba yasa kawai na haqura.
A ranar Juma’ar da muka gama na bi jirgin dare zuwa Lagos.

Kadaran kadahan Bashir ya karbe ni, ban damu ba na shiga sabgogina ina dai ta
qoqarin ganin komai ya daidaita a tsakanin mu amma yaqi bada hadin kai sam.

Ranar Talata da daddare bayan mun gama cin abinci Bashir da Aliyu suka fita siyo
Biredi sauran yaran kuma duk suka koma cikin palour ni kuma na zauna a Gurin Dining
din ina danna waya, kiran Muslim Yaya nane ya shigo wayata, mun dan jima muna
magana kafin mukayi sallama yana kashewa Khadija qanwata ta kirani.

Abdallah ne ya taso ya kawo mun littafinsa na quantitative reasoning ya kakare a
wani guri daman ina jinsu da yayyan yanata su koya masa kowa yaqi dan haka na saka
wayar a speaker muna hirar ina nuna masa.

Hirar wata faccalarta takeyi mun, babansu yana da kudi kamar su kashe shi amma irin
matsolon nan ne ba’a cin kudin sa se akayi dace data tashi aure ta auri me kwadayi
dan shi dalilin auranta ma saboda kudin baban nata ne.

Tofa tunda akayi aure yaga babu lashi se rashin mutunchin yau daban na gobe daban
qarshe ya yiwo mata kishiya ma shine yanzu ba’a dade ba baban nasu ya rasu anyi
musu rabon Gado ta samu kudi sosai se kuma ya dawo kamar yaron ta se yanda take so
yakeyi har Kishiyar ma yanzu ya mayar mata da ita kamar me aiki kome take so shi
za’ayi a gidan nan.

“Wallahi Anty se kin ganshi jiya da mukaje sabon gidan da tayi yana tsaye yanda
kika san dan aiki daga tayi motsi ze zaburo yace Hajia me kike so Hajia me za’ayi,
ni ban taba ganin meson zuciya irin Rabi’u ba wallahi” Khadija ta fada.

Dariya nayi ina cewa “kudi ake gaya miki huce takaici kenan, ai idan mace ta
gawurta zakiga har mijin ma wani shakkar ta yakeyi balle kuma kishiya. Shiyasa kika
ga mun dage muna neman su maganin wulaqanci” na fada dai dai sanda Bashir da Aliyu
suka shigo, wani kallo dana kasa fassara ma’anarsa ya yimun kafin yasa kai ya shige
dakin sa.

Hirar mu muka ci gaba sannan mukayi sallama lokacin na gamawa Abdallah Homework din
se na tashi daga gurin nima na shiga dakin Bashir.
Qarar ruwa da naji yasa na gane yana Toilet, sena zauna a gefen gado ina jiransa ya
fito.

Kudi nake so na ara a gurinsa ina so na qarasa mana siyayyar kayan sallah dan haka
nakeyi kafin lokacin yazo na siyi komai idan ya bani kudin se nayi wasu hidimar
dasu yanzu kudaden hannuna duk na tattara na bada kudin Umarar Goggo daman Kudin
Hayar da zan karba na saka rai dasu to su kuma tun kafin suzo ma na bada Aron su.

Seda na barshi ya gama shiryawa ya zauna sannan nace “Baban Ali Aron kudi nake so
dan Allah”.
Shiru yamun ban damu ba na cigaba da cewa
“Kasan na gaya maka zancen tafiyar Goggo to na bada kudin, wadanda kuma nake saka
rai na hayar gidajen nan wallahi Yaya Abubakar ya rance wai ya cikawa su Bilal sun
tada ginin gidajen su bayan Babbar Sallah nan muke saka ran bikinsu”.

A maimakon ya amsa ze bani ko baze bayar ba se ji nayi yace “Lallai Ma’u karanki ya
isa tsaiko.
Wato ban isa ki tambayeni kudi ba sedai kice na ara miki ko? To bari kiji ni ba
sakaran namiji bane da har kike tunanin dan kina riqe wasu yan kudade zaki fi
qarfina, inaji har fada kikeyi kudi maganin wulaqanci idan mace ta gawurta miji
zeyi shakkarta to bari kiji ko kin fi Dangwote kudi ina nan a matsayin mijin ki
kuma baki isa na biki ba.

Daman tunda kika fara aikin nan naga halayenki da yawa sun chanza, saboda zan fita
nema kema ki fita kina ganin kanmu daya ba? to ya zama dole zan dauki mataki, ki
fara shirin ajiye aikin nan”.

Kamar sokuwa haka na ringa binsa da kallo har ya gama magana. Dan Allah meye
laifina anan? Daga neman rancen kudi shine ze tado wadannan maganganun haka.

Sena sake matsawa kusa dashi ina cewa

“Yanzu saboda Allah Baban Ali rashin tambayar ka kudi da nakeyi ashe nan ma laifi
nake ada da nake tambayar ka kuma cewa kayi ai na ishe ka da bani bani kai bakaga
amfanin Kasuwancin da nake yi ba wai dan Allah me yasa ba’a maka gwaninta ne??

Kuma ni a yaushe kaji nace nafi qarfin ka ko ina so ka bini idan dai ba neman tada
zaune tsaye ba daga ji mutum yana waya se kace dakai ake baka san hawa ba baka san
sauka ba.

Maganar aiki ko kuma wani kudin daban da nake samu kasan idan da tarawa nakeyi da
yanzu na kai inda nakai wallahi amma ko na samu jikinka suke komawa tunda kafin na
amfani kaina da biyar na amfana wa yaranka da dari. Yaushe rabon da ka dauki
sisinka ka bani da sunan wata hidima tawa kota yaran nan?

Siyowar da kakeyi da kanka ma tunda kaga idan ya qare inayi ka sakar mun se sanda
ta raya maka sannan zaka siyo ko ka bada kudi a siyayyar.

Idan ba sallah ba na manta rabonda yau Baban Ali ka kawo dankunne kace gashi wannan
naki ne kuma kullum kana ganina da sabon abu amma baka taba tambayata a ina na samu
ba duk ba sauqin ka bane, idan da bani da abinyi ai duk nauyin a kanka suke”.

“Oh gori zakiyi mun kenan daman ni nace ki ringayi ko ke kika dorawa kanki?
To ki dena, daga yau karki sake saka silenki a hidimar gidana kota yayana ki gani
idan bazan iya ba” Ya fada a fusace.

Haka kawai naji zuciyata ta karye wani kuka yana neman taho mun, wai me zanyi na
burge Bashir a rayuwa ne? Duk abinda nayi aje a dawo wata rana se ya zama abin
fitina, seda na dauke hawayen daya zubo mun akan fuskata kafin nace

“Ko baka fada ba nima bazan sakeyi ba idan yaso seka gani in abin kirki nake maka
ko akasin haka” daga haka naja bakina nayi shiru ina goge hawayen da suke zuba daga
ido na dan na kasa hana su fitowa.

Meyasa maza ba’a iya musu a rayuwa ne? Idan kika zauna baki nemi na kanki ba a
goranta miki idan kin tashi kin nema shima baki tsira ba to ya ake so kayi?

Wayar sa ce ta katse mana shirun da mukayi se ya daga yace “zan kiraki” kafin ya
kashe.
Ina lura da yanda yake satar kallona yana zuba tsaki se na dena goge hawayen na
barsu kawai suna shata se ya miqe gaba daya ya bar mun dakin yana fita kuwa na
fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa.

Bashir
Gaba daya jikinsa yai sanyi da ganin hawayen nata, shi da kansa yasan be kyauta sam
Asma’u bata cancanci wani abu a gurinsa ba bayan kulawa da tattali amma dole tasa
kashi yin koma menene dan a nasa ganin an fara dakko sare sarin da zata fi qarfin
nasa saboda sam ada ai ba haka take ba.

Idan ya gaya mata magana tana ji amma yanzu abinda tasa a gaban ta kawai shi
takeyi. Bata yij shawara dashi sedai kawai ta gaya masa zatayi abu kaza in aka ci
gaba da haka ai wataran ma se tayi sannan ze sani dan haka ya quduri niyyar kawai
ta aje aikin nan tunda shi yake sake bude mata ido tana hulda da manyab mutabe tana
ganin rayuwa kala kala.

Kwana biyu a tsakanin gaba daya na dauke masa wuta na fita a sabgarsa na kuma
qudurce a raina yar biyar dita Bashir baze sake ci ba. Dakansa ya sakko ya ringa
neman shiri dayaga yanda na watsar dashi seda na gara shi kuwa sannan na haqura
amma fa ba wai na chanza ra’ayi ba jira kawai nake wata yayi na fara tatike Aljihun
Bashir.

Sati biyu tsakani wata ya qare kuma a satin nasan zeje Gombe, ina sane na zauna na
rubuta uban list kai harda abinda muke dasu seda na rubuta na hada total dina kusan
dubu dari da Ashirin, ana gobe ze tafi ina jinsa yana mitar an qara kudin jirgi
seda ya gama na miqa masa takardar ina cewa

“Ga wannan karna manta ka tafi, na manta Gas din mu ya qare shima qaramar cylinder
da tayi saura ita aka saka jiya sannan lemon yan makaranta da Biscuits suma babu na
manta ban rubuta”.

Takardar ya karba ya duba se ya dago ya kalleni yace “Wannan kudin duk na menene
haka kusan dubu dari da Ashirin?”

“Shi yasa fa na rubuta maka komai dalla dalla da kudinsa karma kace qari nayi maka
ko wani abu” na fada ba tareda na kalle shi ba, seda yaja wata qwafa kafin naji
yace

“Yanzu kudin zan baki kenan?”
“Ka siyo da kanka ma duk daya ne ai” nayi saurin katse shi. Beyi magana ba mintina
kadan naji wayata tayi qara alamar shigowar message na jawo na duba Alert ne na
dubu dari da Hamsin daga Bashir nayi murmushi nace
“Sun shigo harda qari ma muka samu toh mungode Allah ya qara budi”.
Washe gari ya tafi Gombe.

Weekend din a daddafe nayi shi dan gaba daya bana jin dadi, zazzabin dare ne yake
damuna safiya nayi kuma naji garau na bari akan Monday idan be dena ba zanje
Asibiti.

GOMBE

Wato wata Irin ladabi da biyyaya Amirah ta ara ta yafawa kanta wanda duk hudubar
Sa’ada ce. Jikinta na bari Daman yanzu da yace zezo zataje ta qalqale gida a gyara
ko ina dukda dai da taimakon Ummi harda Sa’adan ma suke zuwa wani lokacin sannan
idan yazo tana iya qoqari tayi tsafta harya tafi a bangaren girki ne dai har yanzu
da saura yana ci yana qorafi dan baya masa kamar na Ma’u.

Wannan zuwan da yayi sosai yaji dadinsa ga tarairaya yana samu da kula kamar wani
jariri babu aikin office babu hayaniyar yara.

Butulci irin na dan Adam a yanzu se yake ganin Yafi samun yanda yake so a gurin
Amirah musamman da yanzu ta dena masa qorafin da tambaye tambayen kudin da takeyi
gashi a karan kanta ta canza sosai komai tana yi yanda yake so.

Suna zauna ana gobe ze tafi tana bare masa Ayaba yana ci ya kalleta yace “kina son
zuwa Lagos?”

Sam Amirah bata kawo da ita yake ba dan a bazata maganar tazo mata har seda ya sake
maimaitawa kafin tace “Meze hana mana Yaya ai kowacce mace zata so ta zauna kusada
mijinta daman, wani gidan zaka samar min kenan”ta fada tana danne zumudin ta,
lallai ta yarda kissa tafi Asiri tunda gashi yanzu hankali kwance tana samun
abubuwan da suka wahala suka kashe kudinsu a banza akansu.

“Aa ina ganin zaku ringa karba karba ne dan baze yuwu na ajiye ku gaba daya acan
ba”.

“Toh Anty fa ya zatayi da aikinta” ta fada tana gyara zama a ranta tana Addu’ar
Allah yasa matsala suka samu daman ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login