Showing 216001 words to 219000 words out of 238465 words

Chapter 73 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

fita daga Get din Estate dinsu Ma'u ya rangadawa Alhaji Qarami waya
baya so ya bata lokaci ballantana ta dawo ta chanja magana dan yasan koda Ace
abinda tayi niyyar gaya masa kenan to Juma'ar data yanke harda tagomashin bacin ran
Bashir ya saka.

Sanda ya gayawa Ahaji Qarami maganar se ya zamana tsakaninsa da Yusuf din har an
rasa ma wanene yafi wani murna nan take yace masa ba matsala ya gayawa mutanensa
idan sun shirya gobe suje yanzu ze kira Baffan su ya sanar masa.

lafewa yayi a cikin kujerar motar yana sakin murmushi ransa fes jinsa kawai yake
kamar wanda akayiwa Bushara da Aljanna tabbas ya yarda mahaqurci mawadaci kuma
Allah shine meyi a sanda yaso ba'a saka shi ba kuma a hana shi.

Hajiyar ya dannawa kira dan da ita ya kamata ya fara raba wannan abin Farin cikin
ringin biyu ta daga ckin kamilalliyar muryarta ta dattijai ta yi masa sallama.

"Hajiya barka da dare, Albishirinki Hajiya" Ya fada a jere
"Barka dai Babangida wane abin farin ciki ne haka ya faru da har muryarka ta gaza
boyewa ko taqaddamar tikitin takarar taku ce ta qare kayi nasara?" Ta fada a sake
daga jinta irin mutanen nan ne masu sakewa sosai da yaransu
Wani murmushi ya saki kamar yanagabanta kafin yace
"Wannan ai ba komai bane akan wannan albishir din Hajiya ki canka da kanki wane abu
ne kike zaton ze sakani farin ciki haka?"

Shiru tayi se can tace "Asma'u, nasan dai a yanzu idan ba zancen takara ba toh
sedai ita din nasan dai wadannan sune manyan burikan ka a rayuwa"

"Kin canka Hajiya yau Ma'u ta amsa da kanta ta bani damar na tura magabata na a
daura mana aure wannan Juma'ar me zuwa dan haka Hajiya ki gayawa su Baba Sale idan
ze yuwu gobe idan Allah ya kaimu suje, zan tura miki da Lambar Babban Yayansu se ki
bashi suyi magana suji ina ne zasuje neman auran".

"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah, Babangida kaga abinda nake gayamaka ko?
Ita rayuwa kabi ta a sannu. Duk yanda kaso da faruwar abu idan Allah be kawo shi ba
haka zaka haqura. Yanzu kaga ribar haquri ko? Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa
yin na Allah ne, nayi murna nayi murna Babangida Allah yasa za'ayi damu bari na
kira Kawun naka yanzu kuwa na sanar masa na tabbatar shima zeyi farin ciki da
wannan Al'amari dan ko shekaran jiya dayazo seda yayi mun ciwon baki akan zancen
auranka yace wasu da yawa ma basu yarda kana da aure ba ko wannan ze iya kawo maka
tangarda a cikin tafiyar siyasarka" Hajiya ta fada cikin tsananin murna.

"Toh ai yanzu ciwon baki ya qare Hajiya in sha Allahu ki dai kirashi yanzun dan
Allah kuyi magana a samu goben aje"

"Toh sarkin zumudi gobe ai yayi wuri ina lefinzuwa jibi haka?" Ta fada cikin
tsokana, da sauri ya tare ta da cewa

"Haba Hajiya wane irin jibi kuma? Juma'a fa tace a daura aure kuma yau litinin
nidai gara suje goben ayi komai. Mansur yana nan duk abinda ake da buqata a karba a
hannunsa kafin na shigo"

"Toh Allah ya tabbatar mana da Alkahiri, bari na tura ayi mun magana da kawun naku
nasan yanzu yana waje tunda ba'a dade da idar da sallah ba beci ace ya tafi gida
ba" da haka sukayi sallama shi murna ita murna.

Ranar qaryar bacci duk iya satar sa hakayaga Yusuf ya qyale dan kwana yayi yana
sallahda tasbihi na nuna godiyarsa ga Allah bisa cika masa wannan babban buri na
rayuwarsa, gani yake ko Yanzu ya mutu ya samu farin cikin da ya dade yana kwadayi.
Ma'u ta amsa soyayarsa ta yarda dashi a matsayin Mijin da zata aura.

Qarfe Sha biyu na washe garin ranar ta kafa tarihin da ko a hasase be taba hasko
faruwarsa a rayuwarsa ba. Suna zaune gaban shugaban qasa a lokacin, tattaunawa ce
me matuqar muhimmanci sukeyi saboda yana cikin kwamitin tsaro na qasa gaba daya
hankalin sa rabi ne akan tattaunawar da sukeyi inda ya kasa rabin a jiran tsammanin
sakamakoj neman auran da aka tafi masa.

Kunnensa maqale da Bluetooth yana sauraran duk abinda yake faruwa acan Kumo gidan
Baffa Isiya saboda seda ya jaddadawa Qaninsa da aka tafi dashi akan suna zuwa ya
kirashi a waya yana so yaji duk abinda akayi karma suje suce a qara lokaci akan
abinda ya gaya musu.

Sanda yaji an fara karanto Siga tsakanin Baba Sale Wakilinsa da Baffa Isiya wakilin
Ma'u miqewa tsaye yayi cikin tsananin mamaki haka mutanen da suke zaune tare dashi
gaba daya suka saka ido suna kallonsa dan dama tuni sun lura da hankalin sa baya
kan abinda sukeyi.

Besan lokacin daya sulale yayi sujjada a inda yake ba ta godiya ga Allah lokacin
dayaji wani da be shaida muryarsa ba yana jaddada dauruwar aure tsakanin Yusuf
Sulaiman Wunti da Asma'u Abdullahi Tukur se gani akayi hawaye suna tsere akan
fuskar sa, abin dariya abin takaici fuskarsa shabe shabe yana haqaye kuma yana
dariya yake gaya musu abinda ya faru, nan da nan suka hau taya shi murna dan duk
wanda yasan Yusuf yasan Asma'u, kai ko mace me sunanta ya hadu da ita se taci
wannan darajar ya karramata.

Dole ya datse mitin ya fice suna ta tsokanarsa, ya ringa neman Layin Asma'u ya
gagara samunta se ya mayar da Akalar kiran kan Alhaji Qarami suka hadu suna ta
jimamai dan tuni Malam Kabiru ya kira ya zayyana masa dan shine ma Ummul aba'isin
da suka sake fanfa Baffa Isiya akan a daura kawai to me za'a jira.

"Wato Yaya nasan halin Asma'u sarai shaqiyyar yarinya ce, wato ainihin dazu da safe
ta kirani. Daga muryarta na fahimci ta kira tayi mun shaqiyancin nata ne se na yi
kamar ban gane ba, tana ta wani hanya hanya ainihin danaga zata batamun lokaci
kawai nace mata muna Kumo ai gashi ma har baqin sun iso ainihin idan sun tafi zan
kirata alhalin a lukacin ma ina shan Shayi ne da Kubza ko shiryawa banyi ba"
Bayanin da Yaya Kabiru yayi wa Alhaji Qarami kenan.

Duk yanda Yusuf yaso ya daure kasawa yayi dole ya yanki tikitin komawa Lagos na
qarfe shidan yamma. baze iya ba yana buqatar ganin Ma'u a yau, ya rungumeta a
jikinsa ya kirata da matarsa halalinsa aure ya bashi ita yanzu yana da dukkan wata
cikakkiyar dama da iko a kanta wai dadi kashe shi shi Yusuf yau ya zama Angon Asmy.

Yana hanyar zuwa Airport Intee ta fado masa a rai, dafe kansa yayi, tun a daren
jiya yaso ya shaida mata maganar auran da zeyi se gashi abubuwan sunzo a yanda babu
wanda yayi zaton faruwarsu.

Lambarta ta America ya daddanna ya kira amma akace masa a kashe take, seda ya
hadiye wani abu daya taso masa na bacin rai akan wannan dabi'ar ta Intee da sam
bata dauke shi da qima ko mutunchi na Miji ba. Ya tabbatar da tafiya tayi wata
qasar ba tareda ta nemi izininsa ba ko da yake abinda aka sabane ai, idan har ta
gaya masa zataje wani guri to kudi ne bata dashi tana da buqatar ya bata.

Lambar mahaifiyarta ya nemo har ze danna ya tuna da a cikin watan nan da aka shiga
akwai bikin qanwarta da suke uba daya da za'ayi a nan Nigeria zata iya yuwuwa sun
taho bikin ma shine bashi da qimar da zata sanar masa seya canza akalar kiran zuwa
lambarta ta Nigeria cikin Sa'a kuwa ta shiga.

Seda ta qaraci ringin ta katse ya sake kira dana dab da yankewa ta daga cikin
muryar bacci tace
"Hello Sweet"
"Intee zaki taho Nigeria amma baki sanar dani ba me yasa kike..."
"Ai kaga halinka sweet qorafi qorafi baka da aikinyi kai se anyi maka laifi toh
idan na gaya maka zanzo me zaka mun? Bana son takura ne nasan ina gaya maka zakazo
ka fara damun mutum da jarabarka shiyasa ma ban neme kaba" Intee tayi saurin katse
shi.

Shiru kawai yayi yana jinta, to meye ma baqo a cikin halinta ne wai shekara bakwai
ai sun zama jiki sedai ya mata fatan shiriya idan tana da rabo, tunowa da abinda
yasa ya kirata ya saka shi sakin wani murmushi a idonsa yana hango Asmynsa yana
ayyana irin Albarkatun da ze diba a jikinta dan ko ba'a fada ba daga kallo kasan
Asmy irin matan da Allah ya wadata su da komai ne ma'ana kyau na zahiri dana badini
wanda ya same su sedai yai ta sujjada yana godewa Allah.

"Se mutum yayi magana ka fara fushi kuma, to jiya fa nazo ban taho da Asmy bane shi
yasa ban kiraka ba kuma kaga hidimar biki zamu fara saura sati daya ina da buqatar
na samu hutu saboda kwalliyata tayi kyau" Intee ta fada cikin shagwaba.

"Ba fushi nayi ba ai bakya laifi Yammata ya kamata kam ki huta kiyi kyau sosai
kinji, dama ina so na gaya miki ne kin tuna maganar da mukayi kwanaki ko?"
"Wacce magana kasan nifa ban fita riqe abubuwa marasa muhimmanci da basu shafe ni
ba"

"Hakane, toh maganar aure na da nayi miki" ya fada bayan daya ja numfashi yana
jinjina halin matarsa a ransa

"Oh wai wannan maganar to ai tun lokacin ni na gaya maka bani da matsala da wannan
kawai dai ka tabbata idan ka tashi auran ka samu classy mace wadda idan aka nunata
aka ce mijin mu daya da ita bazan ji kunya ba kuma zata kulamu dakai dakayu sosai
shine kawai ni damuwata"

"Intee kina sona kuwa?" Ya fada cikin tsananin mamakinta saboda be yarda ba duk
sanda take gaya masa gashi yanzu ta sake maimaita wa anya yarinyar nan tasan abinda
take yi ma kuwa

"Ina sonka mana Sweet me yasa kake tambaya?" Ta fada ba tareda damuwar komai ba.

"Babu komai, kin tuna Asma'u? Takwarar Asmy wadda kika kaita gurinta a Lagos?"

"Uhm bazan iya tunata ba saboda bata da ajin da zan tsaya na kalleta har na gane
kamanninta" ta fada a yatsine. Murmushi yayi me sauti kafin yace

"Koh? Toh ita zan aura ko nace miki ita na aura dan yau akaje tambayar mun auranta
se kawai aka daura auran gaba daya"

"Haka iyayenta suka gaji da ita lalai me yasa Nigerians kwata kwata basu da lissafi
ne se kace ana neman kai da ita da kyanta da komai daga zuwa tambayar auranta kamar
wata tsohuwa za'a bada ita babu jan aji gaskiya an cuceta wallahi" Intee ta fada
ranta a sake babu alamar wai Mijinta ne yace mata ya qara aure balle abin ya dadata
da qasa.

Dariya Ya fashe da ita jin wai babu jan aji babu komai aka bada ita cikin sigar
tsokana yace mata

"Toh ai abin daga ni ne, idan kin manta na tuna miki kema fa kina ganina kika
rikice kika cewa Dady idan bani ba se kin fada rijiya haka babu jan ajin babu komai
aka bani ke toh itama yanzu kin gani aka bani ita"

"Koma dai mene ne zan koma bacci na, da kasan wannan maganar cema da text kayi mun
kawai, Allah ya sanya Alkahiri ka gayawa Amarya ta kulamun dakai sosai, Ina sonka
se anjima" tana hama fadar haka ta kashe wayar.

Murmushi ya ringa saki wato ta kowanne bangaren Intee babu abinda ya shafeta ita
kanta kawai ta sani, tayi wanka tayi kwalliya yau tana wannN qasa gobe tana waccen
shikenan abinda ta saka a gaba babu zancen wasu haqqoqin aure ballantana har ta
zauna tana kishinsa to Allah ya kyauta.

Harya shiga jirgi yana ci gaba da gwada Layin Ma'u yanzu ko yana shiga dagawa ne
batayi, jikinsa yaji yayi sanyi duk karsashin da ya taho dashi yayi qasa besan wace
tarba ze samu a gurinta ba. Da amincewarta aka daura auran nan ko kuwa itama
shammatarta akayi irin yanda abun yazo masa?

To koma dai yaya ne aure ya dauru ba saki ba yaji duk abinda zatayi sedai tayi amma
ko duniya zata taru bega ubanda ze iya kashe auran nan ba.

Yana sauka a Lagos kai tsaye gidanta ya wuce dan daman Driver sa na Aiport yana
jiransa. Tundaga qofar gidan yana iya jiyo hayaniya daga ciki sedai baya gane
abinda ake cewa, kwankwasawa ya shigayi amma shiru ba'a bude ba se ya koma mota da
sauri ya dakko wayarsa daya bari ya shiga kiran layinta cikin sa'a Yanzu ta daga.

BASHIR
Farkawa yayi ya ganshi akan gadon Asibiti ga ledar qarin ruwa da aka saka masa
harta qare Jini ya fara tafiya, da sauri ya zareta dan shi kadai ne a dakin babu
kowa, ya jura qafafunsa qasa da niyyar tashi yana yunqurawa Kansa ya sara yayi
saurin komawa kan gadon yana dafe kan da hannu biyu.

"Sannu ka tashi kenan?" Wata siririyar nurse data shiga dakin ta fada cikin harshen
turanci tana qarasawa kusa dashi, hannun sa ta kama ta duba taga ya cire ruwan seta
mayar da hannunta kansa inda ya dafe tana cewa

"Kan yana ciwo ne? Ka kwanta tukunna na dubaka be kamata ka tashi zaune ba daman se
jikinka ya qara daidaita".

Seda taje ta yaye labulen window haske ya ratso dakin abinda ya tabbatar masa da
cewar safiya tayi kenan kafin ta dawo ta hau auna Bp dinsa dasu pulse duk tana yi
tana rubutawa bayan ta gama ta kalle shi tace

"Har yanzu jininka be sauka ba Mr, ka kwanta bari baje na kira likita ina zuwa" ta
juya zata fita. Dakyar ya bude bakinsa da yake jin kamar muryarsa ma ta tafi gaba
daya yace mata

"Ina so nayi sallah"
"Kayi haquri yanzu likita zezo" taja qofa tayi waje abinta.
Kwanciya yayi kansa yana bala'in sara masa zuciyarsa kanta wani bugu take fat fat
kamar zata fasa qirjinsa ta fito kai shi gaba daya ma dubiyar juya masa take, me
yasa tunda ya rasa Ma'u ya rasa kwanciyar hankali a rayuwar sa ne shi.

Yana nan kwance har Nurse suka dawo tare da likita, Dattijone ya manyanta nan da
nan ya rufe Bashir da fada dan sanda suka shigo ma gaba daya yayi zurfi a tunani
Likitan nata yi masa magana sam be ji ba seda ya taba shi kafin yayi firgigit ya
farka.

"Da girmanka da komai kake abu kamar wani qaramin yaro, ta yaya kake tunanin zaka
samu lafiya bayan ana qoqarin ganin jininka ya sauka kuma kana qara saka kanka a
tunani? Koma me yake damunka yanzu ai ajiye shi zakayi ka ji da lafiyar ka amma
kana neman ka kashe kanka a banza da tunane tunane haha mutane ku ringa yiwa kanku
fada mana".

Shidai Bashir yayi shiru har ya gama dube duben sa yacewa Nurse din ta kama shi ta
kaishi qofar bandakin da yace ze shiga. A cukule yace musu ze iya, haka ya daure da
bin bango ya shiga dan duk takun da yayi ji yake kamar ana kwada masa guduma a kai.

Seda yayi sallar Asubar da ta kufce masa dan lokacin kusan tara na safe kenan, yana
zaune yana lazumi rabi kuma tunanin Ma'u yake da yanda zebi ya gyara kwabarsa.
Amirah ce ta fado masa a rai da jaririnta yayi saurin shafa Addu'a ya miqe dakyar
dan se yanzu ya tuna da batun suturar jaririn ma.

Da karfin hali da komai ya gama cike duk takaddu aka bashi gawar Babyn a Ambulance
suka tafi gida dan ya rigada ya kira Limamin masallacin da suke sallah na cikin
Estate dinsu.

Yanzu da a gida yake cikin yan uwansa da komai anyi shi a tsanake amma yanzu bashi
me yi masa dole ya daure duk wani ciwo ya tafi yayi.

Se bayan da aka gama Jana'izar Babyn daya sakawa Muhammad Bashir kafin ya shiga
gida dukda Asibiti ya kamata ya koma dan shi kadai yasan abinda yakeji a jikinsa
bayan ciwon kai yanzu harda zazzabi ne yake neman kama shi.
Addah na zaune zuru a palour ya tura qofar ya shiga, da bala'in sauri ta tare shi
tana cewa
"Yanzu Bashir daga fita tun jiya se yanzu zaka dawo ina Amirar? Tun jiya nake kiran
wayoyinku a kashe gaba daya hankali na ya tashi har su Nafi na kira na gaya musu da
tace Naziru ma ze taho a jiyan amma Babanku ya hana wai ai da babu Lafiya za'a sani
Na ganka kai kadai ina ita Amiran? Qila ma gantalinku kuka tafi kuka barni a gida
kwal kamar mayya bayan kasan baqin halin yayanka ba kulani suke ba".

Kujera ya samu ya zauna dan baze iya tsayuwa ba kafin yace mata

"Tana Asibiti"
"Na shiga uku meya sameta? Badai wata matsalar bace kuma?" addah ta fada tana dafe
qirji, se yai jim kafin yace mata

"Ki shirya, bari na watsa ruwa muje" ya daddafa ya qarasa dakinsa.

Da sauri Addah ta shige dakin da take ta dauko wayarta da mayafi ta dawo falo ta
rafka tagumi jikinta har tsuma yakeyi. Tana nan zaune ta jiyo horn daga waje, har
zata leqa sega Bashir ya fito daga dakinsa ita se sannan ma ta fahimci layi yake
idan yana tafiya haka tabi bayansa suka fita bayan da yace ta kulle gidan suka hau
motar sa da ya saka Samuel ya dauko suka koma Asibitin.

Sun tarar da Amirah na zaune suna yar hira da matar da take dayaj gadon da yake
dakin da take. Tana ganin su ta takwarkwashe fuska ta saka kuka Addah tayi kanta da
saurin gaske taba tambayar lafiya musamman da bataga cikin Amiran ba se wara ido
take gefe da gefe tana neman jinjiri.

Bashir kuwa yana ganin ta fara kukan ya juya ya fice, bashi da buqatar qarin damuwa
a yanzu. Dakin da aka kwantar dashi dazu ya koma, yana shiga suka ci karo da
Likitan nan ya kuwa rufeshi da fada kamar ze kai masa bugu akan ina ya tafi? Wama
ya bashi izinin tashi daga gadon da har ze kama hanya ya tafi wani guri.

Shidai haka ya koma ya kwanta, seda ya karya da Abincin Asibitin da sam babu
dandano ko kadan kafin aka masa Allurai harda me saka bacci nan da nan kuwa yayi
awon gaba dashi.

Qarfe Biyar na yamma aka basu sallama daga shi har Amiran dan babu abinda yake
damunta sedai ta koma gida kuma ta cigaba da jego Allah ya bada rayayye a gaba.

Musa abokinsa daya biya duba shi bayan sun tashi daga aiki ne ya roqa daya kaishi
gida saboda gujewa surutuan Addah da suka hau motar sa Samuel ya kaisu gida

tun data samu labarin mutuwar Jaririn fa take kuka da hawaye yanda kasan itace ma
Amiran, Gombe kuwa babu lokon da labari be isa ba acewarta dukda an saki Ma'u baqin
Asirin da tayiwa Amirah na karta haihu a gidan be karye ba ai kuwa duk inda zata
shiga se taje ta nemo makarinsa sedai baqin ciki ya kashe ta amma Amirah seta haifi
Yaya a gidan Bashir.

Suna shiga gidan ya wuce dakinsa, wayarsa da ya saka a Silent ya ciro daga
Aljihunsa jin tanaVibrating. Ya gane Lambar da ta kira dukda babu suna, Bala ne, da
mamaki ya ringa kallon wayar rabon da suyi magana tun waccen ranar kusan wata nawa
yanzu, lokaci daya wani bacin rai ya taso masa na tunawa da furucin Balan akan Ma'u
se kawai ya ajiye wayar ya shiga cire rigar sa yana ayyana dalilin da ze sa Bala ya
kirashi a yanzu bayan abinda ya faru har yana tunanin ze sake hada wata hulda dashi
ne?

Alwala ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login