Showing 84001 words to 87000 words out of 238465 words
hannu biyu a qirji yana bina da kallo, daga inda
nake ina iya jin yanda yake sauke numfashi kamar wanda ya hadiyi kunama.
Qara jinjina qarfin hali da rainin wayon Bashir nayi a raina, wato ni nice rumfa
sha shirgi ko ga Uwar garke wai na tattara yara mu koma Gombe, to kuwa yau na
shirya ganin qarshen rainin hankali da duk abinda Bashir yake taqama dashi dan haka
nace
"Idan har saboda MATAR KA kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR".
"Haka kika ce"
"Eh Haka na fada”.
Seda ya hadiye wasu qulalai da suka tokare masa maqogaro, kaso tamanin na zuciyarsa
yana kwabarsa amma kashi Ashirin ya rinjayi harshen sa
"Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki".
Wani irin dummm naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi munin ji a
rayuwata gaba daya, wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir kasan me ka fada kuwa? dagaske kake" na
fada cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba
"Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA, badan babu kyau ba Asma’u da sena
cike miki ukun ki kinga se kiji dadin yin aikin ki dakyau ba tareda nayi miki
rashin Adalci ba" ya fada daidai sanda yake ficewa daga dakin.
Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan dake, Allah ne ya rufa min asiri na fada kan
gadon da yake baya na. A yanda nake na tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze
hana barin jikina shanyewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan
minha" cikin ikon Allah kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan jikina yana
wani irin rawa tamkar wadda aka jona mun shocking.
Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa dan ji nayi tamkar an saka super
glue an liqeta, se zufa ce take ketomun ta ko ina kaina yai dum kafin kace meye
numfashina ya fara sama sama ba shiri na fara laluben inda Inhaler ta take wadda
sabuwa ce daman dazu dana fita na siyo, dakyar na samota bayan dana zazzage jakar
dana fita da ita a qasa saboda yanda nake a rikice jikina yana rawa.
Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na
nan a toshe. Kai ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin
me ma zeyi mun?
Ni? ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan
shedan ne amma gashi kamar a zahiri hakan ta faru.
Ina cikin wannan yanayin aka sake turo qofar dakin, nasan yarana dukka suna
makaranta kuma lokacin tashinsu beyi ba.
Nima dai rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya
wai dan na huta na zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan
tsakanin nan ashe ashe....
"Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa
AMIRAH sabon kaya Zuwa Weekend ita dana isa da ita zata dawo dan haka na baki
grace of today ki hada ya naki ya naki kinga yanzu komawa Gombe dole"
kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juyawa yabarni ni
bame rai ba ni ba sumammiya ba.
Dakyar na iya miqewa na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin
qarewar yau nida yarana. To tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani
akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi a waje sa.
Kofar gidan na fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya
fada, idan ban manta ba Abokin aikin Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa
a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan tunda dama Office ne suke basu dan haka
yanzu babu kowa a ciki.
Gidan Baba na shiga dan nasan yana gida kaman yanda Bashir yake nan tunda Office
dinsu daya, haka na ringa danna door bell ba saurarawa.
Banyi zaton nayi sallama ba lokacin da Anty ta budemun qofa na nausa kai ciki kawai
dan fa bazan iya cewa wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa na tarar
da Baban na zaune a palour yana Kallon News, se kawai na isa gabansa na durqusa.
"Hajia Ma'un Bashir" ya fada yana murmushi. haka suke tsokanata kai kowa na Estate
din ma haka yake kirana kadan suka sanni da Maman Aliyu wasu kuma suce Maman twins.
"Meya faru" Baban ya sake fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka
ba amma kallo daya zakamun ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki, se kawai
na tsinci kaina da cewa
"Baba Flat din Maman Boda zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah".
"Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan
tambayoyi da daya kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace
masa
"Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kaya na a yau nabar masa
gida kafin ya dawo" na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa.
Kuka nake tamkar raina ze fita inda Baba da Anty keta faman zabga salati suna
qarwa.
"Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka?” Baba Ya fada bayan daya
tashi tsaye ya goya hannunsa a baya, sena dago cikin matsanan cin kukan da nake dan
har kamar zan shide nace
“Wallahi Baba banyi masa komai ba, kawai saboda yace na ajiye aiki na saboda Amirah
nace bazanyi ba shikenan yace se naje na zauna da aikin nawa”.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, meya ke damun Bashir da ze yanke wannan danyan
hukuncin ba tare da shawara ba? Wacece ma Amiran?” Baban ya fada yana kallon Anty
da tayi mutuwar tsaye jin musabbabin sakin, cikin tsananin bacin rai tace
“Amma Wallahi Bashir ya isa Asararre yanzu akan wannan tanbadaddiyar yarinyar me
zubin Aljanu ya sake ki lallai Namiji se a barshi”.
“Wai wace yarinya ce ina tambayarki” Cewar Baba, se Anty ta kalle shi tace
“Wacece kuwa idan banda wannan yar iskar maci Amanar yarinyar da yayi mata kishiya
da ita, shine cin Amanar be ishe su ba yanzu seda suka raba ta da auranta. In sha
Allahu se Allah ya saka miki kima dena kuka Alfarmar Annabi se yayi nadamar da
bazata amfane shi ba a rayuwa tunda dai shi wawa ne”.
“Ya isa haka Halima wannan wace irin magana ce, ka mata kuje ciki bari naje na ga
Bashir din ni” Baba ya katse ta, se ya dauki Glass dinsa na qara qarfin gani da
wayar sa ya fita Anty ta zauna akan kujera tana sake tsinewa Bashir da Amirah nidai
in banda aikin kuka babu abinda nakeyi.
Sanda Baba ya fita rashin ganin motar Badhir ya tabbatar masa yafita dan haka ya
kirashi a waya itama seda ta kusa katsewa sannan ya daga.
“Bashir kana ina ne nazo gida baka nan” Baba ya fada bayan da Badhir ya daga wayar.
“Na dan fita ne” Bashir ya fada murya a cunkushe kamar wanda aka yiwa duren dusa.
“Idan ka dawo kazo ina son ganinka” Baban ya sake fada kafin ya kashe wayar ya koma
cikin gida. A inda ya bar mu nan ya tarar damu ina ci gaba da rusa kuka Anty na
faman debewa Bashir Albarka.
“Yanzu Halima a maimakon ki tausheta shine zaki zauna kina fadar maganganu kina
sake daga mata hankali ko kin kyauta, ki samo mata ruwa tasha, Asma’u kiyi shiru
haka, na kira Bashir din yanzu ze zo”. Baba ya fada bayan daya zauna akan kujera.
Sassauta kukan nayi na shiga jan rai ina ajiyar numfashi kamar zan shide, dakyar na
dan zuqi ruwan da Anty ta bani dan jinsu nayi sun min daci a baki, na hade kai da
guiwa ina ci gaba da hawayen da na kasa tsaida su, wai ni yau aka saka? Ni Bashir
ya saka saboda Amirah.
Kusan mintina 30 aka buga gidan, Anty Baban ya kalla kafin ma yayi magana tace
“wallahi yallabai bazan bude masa ba, ni gara ka fita can ka same shi a waje dan
idan ya shigo zan iya duddura masa Ashar ma”. Se Baban ya girgiza kai kafin ya miqe
yaje ya bude qofar da kansa.
Tare suka shigo da Bashir da kallo daya zaka masa kasan ba’a cikakken hayyacinaa
yake ba. Idanunsa sunyi jajir sun koma ciki ga jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu.
Guri ya samu ya zauna ba tareda ya kalli ko gefen da nake ba, nima sau daya na
kalle shi na mayar dakai ina ci gaba da share hawaye na dukkan mu munyi shiru se
Baba ya katse shirun da cewa
“Bashir me ya hada ka da Asma’u har ta kai ga yanke irin wannan hukunci mara dadi,
koda yake abinda ya faru ya faru dawo dashi bashida amfani dan haka koma menene
haquri shine maganinsa dakai da ita duk kuyi haquri ka maida ita dakinta tunda da
sauran zama bama se wani ya san Abinda ya faru ba”
Luguden duka qirjina ya shigayi na dago na kalli Bashir ina jiran naji amsar da ze
bawa Baban, ina ma ace yace daman wasa yake yimun ba dagaske bane ba. “Daman ana
saki da wasa ne” zuciyata ta raya mun, sena sun kuyar da kaina qasa ina jin wani
abu me tauri ya taso ya tokaremun maqogaro daidai sanda Bashir yake cewa
“Ayi haquri kawai Baba amma ko zan maida ita ba yanzu ba, taje kawai lokacin data
san muhimmanci na idan da rabo se mu koma”.
“Kai dai za’a gayawa haka Bashir kaine zaka san Muhimmancin Asma’u a lokacin da ta
rigada tayi maka nisa, se kayi kuka da idon ka kayi nadamar da bazata amfane ka ba
wallahi tunda baka godewa Ni’imar ubangiji ba ka shirya godewa Azabar sa” Anty ta
fada cikin Masifa kamar zata rufe Bashir da duka kafin ta juyo kaina inda nake
durqushe ina kuka tace
“Ke kuma kukan me zakiyi kanki aka fara sakin mace ko yaya idan wani yaqi ka da
yini wani da shekara ma ze soka har zaki damu dan wani Bashir da dama can ba ajin
auranki bane ya sake ki, in sha Allahu akan idonsa zakiyi auran da se ya gigita shi
tashi muje” ta fincikeni muka shige dakin ta.
Bansan me suka tattauna da Baba ba ya shigo ransa a matuqar bace yana cewa “Lallai
yaron nan bashida mutunchi Halima, yanzu ka saki mace da yaya shida har kana
iqirarin ta bar maka gida a yau zaka kawo wata se yanzu na fuskanci kan abun daman
akan ze dawo da kishiyarta nan ya saketa kenan, babu komai duk wanda ya cuci wani a
cikinsu Allah ya saka mas.
kuje ki tayata ta hada kayanta zanje Management office yanzu naji yanda za’ayi su
bada gidan”.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 32
Tareda Anty muka koma, Bashir na zaune a palour muka wuce dakina. Wayata dana gani
ta tunamun da gida, wazan kira na gayawa wannan mummunan labarin??
“Alhaji Qarami” zuciyata ta raya mun, nan da nan na danna masa kira cikin sa’a
ringing biyu ya daga yana cewa “wato a kwanakin nan dai Ma’u tana yi dani irin
wannan kira akai akai haka”.
Kuka na fashe masa dashi sosai ya shiga tambayata ya akayi, dakyar na iya
tsagaitawa na gaya masa cewa Bashir ya sake ni. Seda yayi salati ya sanar da
ubangiji kafin yayi shiru na wani lokaci yace
“Ma’u kowa da kalar qaddarar sa a rayuwa kiyi haquri ki dauka jarabawa ce daga
ubangiji idan kika jure se ki samu saka mako me kyau. Yanzu kina ina?” Alhaji
Qarami ya fada cikin jimami, seda Naja sheshsheqa kafin nace
“Yace ya bani iya yau na kwashe kayana na bar masa gidan sa Yaya yanzu ina gidan
kayan nake hadawa”.
“Shike nan, ki hada iya abinda ya samu, bari na kira Abubakar dan yace mun yau ze
shigo nan din idan yaso ko hotel ne se ku zauna kafin gobe a duba miki gida zuwa
muga yanda hali ze yi, ki dena kuka sannan karki kira kowa a gida ki gaya masa
kinji ko”.
“Toh Yaya Nagode Allah ya saka da Alkahiri “ na fada kafin mukayi Sallama naci gaba
da taya Anty hada kayan dan tuni ta sauke kayan wardrobe dina tsaf tana ta durasu
a akwatuna. Seda muka kwashe komai dan seda muka Hada da manyan Jakunkunan Bakko da
muke zubo abubuwa daga Gombe daman in na cire kayan ciki sena ninkesu na ajiye da
rabon zasu min rana ashe. Har kayana na dakin Bashir seda ta kwaso komai bayan da
tayi masa watsa watsa da nasa a qasa.
Da muka gama da nawa kayan dakin yaran muka koma, lokacin Bashir ya bar gidan suma
muka shiga hada musu kaya kowa a akwati kafin wani lokaci mun gama Anty ta fita ta
samo samari suka ringa dauka suna kaiwa gidanta.
Mun fito da akwatin qarshe kenan Yaya Abubakar ya tsaya da motarsa a qofar gidan,
rabon da yazo tunda Bashir ya auri Amirah suka samu sabani sedai mu hadu dashi a
gida idan naje Gombe ko muyi waya.
Kai tsaye na fada jikinsa na fashe da kukan dana samu dakyar ya tsaya mun dazu yana
bubbuga baya na yace “kiyi shiru Ma’ulle abinda yake so kenan yaga gazawarki bayan
shi yayi asara bake ba”.
Tare dashi muka shiga gidan Antyn muka tarar da Baba ya dawo, cikin mutun taka suka
gaisa Baba ya shiga bashi haquri akan abinda ya faru kamar shi yayi laifin sannan
ya gaya mana ya samu approval an bani gidan kuma harda 50% discount akan kudin
hayar ma suka bayar kuma ya biya yanzu ze kira kamfani masu wankin gida suzo su
gyara yanzu se muje mu ga gurin ga Key nan an bashi.
A tare muka fita gaba daya, gidan lafiyar sa qalau dan daman ba’a dade da
renovating nasa ba qura kawai yayi se yana saboda babu mutane a ciki, muna tsaye ma
sega kamfanin daya kira sunzo da kayan aiki cikin qasa da awa daya suka wanke gidan
tas har bangwaye seda suka wanke ko ina ya dauki kyalli.
Bansani ba Ashe tunda muka shiga Yaya Abubakar ya kira Alhaji Qarami ya gaya masa
maganar gidan, se ganin motar kayan furnitures nayi sunzo da saitin gado da kujera
harda labulaye da carpet kamar wasu kayan Amarya nan da nan suka shiga daurawa.
Muna fito wajen gidan motar makaranta ta sauke su Aliyu, da mamaki suka tsaya suna
kallon gidan Farida tace “Mami gida zamu chanza naga ana saka sabon kaya a nan”
Gaba daya kasa kallonsu nayi dan ji nayi wata sabuwar karaya tana zuwar mun, yaya
zasu ji idan suka gane mun rabu da mahaifinsu? Fitowar da Yaya Abubakar yayi daga
cikin gidan ta ceceni daga tambayoyinsu suka nufeshi da murna nan take na sulale na
shige gidan Anty ban san Aliyu yana baya na ba seda naji ya ruqo hannuna yana cewa
“Mami meya faru, kukan me kikeyi?”
Aliyu ya wuce shekarun da zance zanyi masa wayo, kai tsaye ina hawaye nace masa
“Aliyu mun rabu da Abbinku, kuje ku duba idan akwai sauran abinda ban dauko muku ba
a dakin ku wan can gidan zamu koma”.
Gaba daya se yaron ya kasa magana ya tsaya yana kallona, a sanyaye ya saki hannuna
ya juya ya fita daidai sanda Itama Aman ta shigo ina jinsa yace mata suje waje na
raka su da ido har suka fice daga gidan.
Rayuwa kenan, dan Adam yana tafe besan abinda ze same shi a mintunan da suke
gabansa ba, dazu da safe na tashi da yaqinin gyaruwar Al’amura a tsakanina da
Bashir, ga labarin abin farin cikin daya same mu bansan mummunar qaddara na tafe
tana shirin shafe duk wani farin ciki da nake shiryawa ba.
Shafa cikina nayi, Allah sarki shi kuma tasa qaddarar kenan baze tashi a tsakanin
iyayensa ba.
Da taimakon yaran kafin sallar Magriba mun shirya gidan nan tsaf yayin da muka yiwa
gidan Bashir qat dan kaida fata Anty ta kafe sena dauke duk abinda yake nawa ne a
cikin gidan nan haka kuwa akayi yara suka ringa jidar kaya qananan se murna suke
wai mun chanza gida.
kayan Kitchen dina tsaf Gas da qaramar Freezer da muke zuba nama kadai aka bari
dan sune nasa babbar me qofa Biyu Yaya Muslim ne ya bani ita da suka tashi daga
gidan su na Lagos ya koma Rivers, haka kayan amfani ko ko cokaci Anty bata bari ba
harda su spices seda ta tattare.
Haka palour Kujeru da Da Tv se Dining kadai ya tsira dasu sefa gadon dakinsa dan na
dakina ma da kudina na siya, wanda ya saka mun shi na cire na sakawa Farida da Amna
a dakinsu dan haka masu daurin Gado na gama hada sabon Anty tasa suka hau kwanto
nawa tace ko baze hadu a yau ha su kwance a ajiye gobe su dawo su hada.
Har bayan Isha muna jigilar kaya daga tsohon gida zuwa sabo, mungama tattaro komai
wanda ze saku a lokacin muka saka ragowar muka barwa gobe idan Allah ya kaimu se a
qarasa.
Na fito raka Yaya Abubakar ze tafi masaukinsa daidai lokacin Bashir ya dawo,
tundaga waje ya fahimci aika aikar da akayiwa gidan dan ga winduna nan hanhai babu
labule ana hango ciki, a sukwane ya shiga gidan, kai tsaye dakin yaran ya leqa ya
kuwa yi sa’a se katakwayen gadajen su ya tarar dan mun kwashe katifun saboda bacci
a zuwan gobe suma se a dakko su.
Cikin tsananin Bala’i kamar zeyi aman wuta ya tunkaro inda muke
“Ke kadai nace ki tafi bance ki daukar mun yaro ko daya ba” ya fada yana kallona.
Seda na watsa masa wani banzan kallo kafin nace
“Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi Bashir, saki dai na saku kuma kamar yanda kace
na barmaka gida kafin gobe gashi nan ka gani Allah be hanani inda zan zauna ba amma
maganar yara baka isa in bar maka yarana a hannunka ba”.
Sosai rigima ta barke tsakanin mu shi yana rantsuwar sena bashi yaransa ni ma ina
ta bazan bayar ba, Yaya Abubakar ne ya katse mu da cewa “Ya ishe ku haka, wane irin
shirme ne zaku zo kuna neman tarawa kanku mutane a titi ga yara duk suna kallon ku
akan abinda be wuce ku zauna ku sasanta ba.
Ki shiga Gida Ma’u zamuyi magana”
Sena juya ina cewa “ka gaya masa bazan bayar ba idan ya takura kuma seadi kotu ta
raba mu” nayi shige wata gida.
A waje kuwa Asma’u na wuce kafin ma Abubakar ya fara magana Bashir din ya katse shi
da cewa “Ka gani cikin lallama ka gaya mata ta bani yarana dan wallahi bazan bar
mata su ba ballantana ta koya musu dabi’ar raini da kafiya irin tata”.
Seda Abubakar ya qare masa kallo kafin yaja qwafa, ba qaramin danne zuciyarsa yayi
ba yace “Naji, zata baka amma kayi haquri kabarsu yau. Nayi maka Alqawari gobe za’a
baka yayan ka”.
Shiru Bashir yayi kamar me tunani se yace “Shikenan, Amma wallahi goben idan ba’a
bani ba se anyi tashin hankali”
“Babu da wanda zakayi tashin hankali Bashir dan babu wanda yake da lokacin ka, kuma
kayi a hankali idan ba haka ba seka rufta kanka a