Showing 171001 words to 174000 words out of 238465 words
ya mayar da kansa ya hade da guiwa yana
jan numfashi.
"Lafiya Engineer kake zaune a qasa meya faru?"yaji muryar da be tantance ko ta waye
akan sa ba, dakyar ya dago yana nuna masa kansa da qirjinsa daga nan be sake sanin
abinda ya faru ba se farkawa yayi ya ganshi kwance a gadon Asibiti.
Dafe kansa da yayi masa nauyi yayi ya tashi zaune yana qarewa dakin kallo, "me ya
same shi? Waya kawo shi Asibiti?" Qoqarin cire qarin ruwan da aka saka masa ya
shigayi, Shigowar da likita yayi tareda wata Nurse a bayansa ya dakatar shi.
"Kai kai Engineer ya zaka cire bayan be qare ba" likita ya fada fuskarsa dauke da
murmushi ya shiga gyara masa ruwan. Dakansa ya saka masa abin duba Blood pressure
ya gama karantawa yana fadawa Nurse din ta rubuta ya sake saka abin gwada zafin
jiki nan ma ta rubuta kafin ya kalleshi yana ci gaba da murmushin yace
"Mun gode Allah jininka ya sauka zafin jikin ma babu yanzu akwai inda yake maka
ciwo ne?"
Kansa ya nuna masa, da alama dai likitan akwai Fara'a dan murmushinsa ya qara
fadadawa yana cewa
"Ze dena amma sekayi qoqari kaima ka cire duk wata damuwa daga ranka, a shekarunka
dai baka buqatar na tsaya ina gaya maka abinda ya kamata kayi ko karkayi, abu daya
dai shine lafiya tana gaba da komai.
Bansan menene damuwarka ba amma koma yayane ka daure ka rageta dan jininka ya hau
sosai, sannan akwai Yunwa a tattare dakai abinda yake qara maka qarfin ciwon kan
kenan da kuma rashin bacci, indai zaka kiayaye yawan tunani ka kuma ringa cin
abinci me kyau in sha Allah komai ze daidaita".
Kallonsa kawai Bashir yakeyi harya gama bayaninsa yana murmushin dai yacewa Nurse
ta hada masa shayi yasha se ta bashi magani. Ruwan ya cire masa saboda ya samu ya
shiga bandaki ko yana da uzuri, jiki ba kwari Bashir ya wuce Bandakin, tunanin da
aka hanashi ya shigayi lokacin da Asma'u ta hadu da Hawan jini sanadiyyar auran
Amirah da yayi ashe shima nasa rabon yana tafe sanadin rabuwa da ita.
Brush yayi ya dauro Alwala dan besan awa nawa yayi a kwance ba. Nurse din ya
tambaya waya kawo shi kuma tun yaushe tace bata san wanene ba amma tun jiya da rana
ne yanzu kuma qarfe goma na safe harya gota.
Buda ido yayi sosai yana kallonta, kwana yayi a sume kenan?
Sallah ya tayar harya fara a tsaye yaji baze iya ba seya koma ya zauna. Seda ya
biya duka bashin sallolin da suke kansa kafin Nurse ta miqa masa shayin data
saisaita ta shiga bude wasu kuloli daya gani a ajiye ta shiga zuba masa soyayyan
dankali da kwai se farfesun kayan ciki da shaqa daya yayi wa qamshin su ya gane
daga ina suka fito.
"Waya kawo abincin nan?" Ya tambayi Nurse din. Seda ta ajiye masa kafin tace
"Yaranka ne suka kawo, jiya da dare ma sun kawo abinci baka farka ba aka bayar
dashi wannan da zasu tafi makaranta suka kawo".
"Su kadai suka zo ban da mamansu?" Ya sake tambayar ta.
Tana tattara kayan aikinta tace
"Bansani ba gaskiya su kadai dai suka shigo nan Maza biyu da mata biyu" tana gama
fada ta yi gaba se ya dakatar da ita akan ta dauke ragowar abincin ta fita dasu
tana masa godiya.
Kamar wasa se gashi ya tashi da abincin tas har yana jin dama bece ta fita da
sauran ba, bayan shayin data hada masa seda ya sake hada kofi daya ya qara nan da
nan yaji ya farfado se ya shiga neman wayarsa yayi sa'a kuwa ya ganta an ajiye masa
akan durowa so yake ya kira office dinsu ya bada uzuri yana dannawa hotonsu tareda
Ma'u da yake kan screen din yayi masa sallama nan take zuciyarsa ta buga dum
"Saurayin Mami ne" maganar ta shiga yi masa yawo a kwakwalwa.
Jifa yayi da wayar ta daki bango ta tarwatse, ya dafe kansa da hannu biyu yana
jijjigawa saboda yanda ya taso masa da ciwo lokaci daya cikin sauri aka turo qofar
dakin, likitan ne tareda Nurse din dazu dan dukka dakunan Asibitin da akwai CCTV a
ciki suna lura da halin da halin da mara lafiya yake ciki.
Allura Likitan yayi masa nan da nan bacci ya dauke shi, ya kalli Nurse din da
damuwa yace
"Har na fara tunanin bashi sallama saboda yanda Komai nasa yayi normal kinga kuma
lokaci daya komai ya birkice, ina tunanin akwai wani abu da yake tunawa da yake
tayar masa da hankali kunyi magana dashi ne dazu?"
"Bamuyi magana ba, kawai ya tambayeni waya kawo shi Asibiti nace ban sani ba, se ya
tambayi abinci fa na gaya masa yaransa ne suka kawo amma banda mamansu shi kenan".
"Kuma kinsan abin da mamaki, wanda ya kawo shi makwafcinsa ne, sannan yaransa sunzo
amma babu matarsa amma dazu da safe Maceceta kawo su sedai baya shigo ba, a mota ta
jirasu suka wuce.
Ki zauna ki kula dashi, zanje zagaye duk abinda yake da akwai ki sanar dani" daga
haka ya fita yabar Nurse tana gadin Bashir.
ASMA'U
Ina kwance a dakina gama wayarmu kenan da Yusuf daya kira yana tayi mun santin
abinci ina masa dariya se ga Aliyu ya shigo gaba dayansa a birkice dan ko Knocking
beyi ba ya fado dakin.
"Meye haka Aliyu, wane irin iskanci ne zaka shigo mun daki babu sallama" na fada
ina tashi zaune.
"Mami, Abbi ne bashi da lafiya" ya fada kamar zeyi kuka. Sena yatsina fuska nace
"Allah ya bashi lafiya, ko kuwa ni likita ce da zaka zo ka gaya mun? Idan jikin
yayi zafi da yawa ku tafi Asibiti mana ai zaka iya tuqashi ko ya kira Samuel ya
kaishi".
"Mami Faduwa fa yayi a qofar gidan, Dadyn su Sa'id ne ya tafi kaishi Asibiti shida
Mr Uche" Aliyun ya sake fada se na waiwaya na kalleshi,
"Faduwa kuma? A garin yaya?"
"Nima ban sani ba, a qofar gidan nan na barshi na shiga can gidan se kawai Malam
Sani ya leqo ya gaya mun wai ya fadi yanzu an tafi kaishi Asibiti".
"Allah ya bashi lafiya" na fada a sanyaye.
"Mami zanje na ganshi"
"To seka dawo, kayi masa sannu" na fada ba tareda na kalle shi ba.
"Mami ke bazaki je ba?" Aliyun ya sake fada yana kallon qasa, harara na banka masa
nace
"Fitar mun a daki, sannan idan zaka je ka nemi motar haya dan idan ka dauki mota ka
tafi VIO suka kama ka karka ce ka sanni".
Ina jinsa yana qunquni ya fita, ban iya yin baccin da nayi niyya ba na shiga
tunanin to me ya janyowa Bashir faduwa tuntube yayi kome tunda bema shigo mana nan
ba dai dan da zanji yara sun fada kuma yaushe rabon Bashir da gidan nan ma tun
zuwan sa na qarshe wanda har na mareshi.
Da zasu dora abincin dare Amnah tace mun zasu dafa harda Abbi su kai masa nace musu
toh, ganin dare yayi kuma babu me kai su yasa muka tafi tare, a waje na tsaya suka
shiga da abincin basu jima ba suka dawo wai bacci yakeyi, muka kamo hanyar gida duk
jikinsu a sanyaye se naji nima na damu dukda banganshi ba amma yanayin da fuskarsu
ta nuna ya tabbatar mun bashi da lafiya dagaske kai ni tunda nake da Bashir ma zan
iya irga sau nawa ciwo ya kaishi Asibiti.
Muna shiga gida Yusuf ya kirani, ban daga ba seda na gama sallamar yaran muka rage
aikin gobe da safe tunda Monday ce duk zamu fita kuma dukkan su a gidan suka ce
zasu kwana. Seda nayi wanka na shirya kafin na dauki wayar.
Agogo na kalla naga har sha daya saura dare yayi, sena mayar da ita na ajiye kawai
idan Allah ya kaimu da safe na kirashi kawai ina ajiyeta kuwa ta fara qara alamar
kira, sena dauka Yusuf din ne nayi murmushi na daga na saka a kunnena.
"Ina fatan ban katse miki abinda kike yi ha dan nasan dai yanzu bakiyi bacci ba"
Yusuf ya fada.
"Aa yanzu naga missed call dinka ma se kuma naga dare yayi nace da safe na kira se
kuma ga kirankabya shigo" na fada ina kashe fitila me haske na koma kan gadon na
zauna.
"To ai ke zaki iya bacci bakiyi magana dani ba, ni kuwa kinga ko bazan iya ba,
shiyasa na baki isashshen lokaci kafin na sake kira".
"Uhm" na fada ina kaiwa kwance amma maganar sa ta dakar dani na tashi zaune dakyau
ina zare ido
"Na kasa daure wa Asmy, jan rai da jan ajin naki yayi yawa. Tun tuni nake jira ki
gaya mun da bakinki auranki ya mutu amma kinqi, nayi haquri a lissafina yanzu kin
gama iddah na kasa jurewa dan naga alamar baki da tausayi idan na biye miki haka
zakiyi ta gara zuciyata.
Yanzu dai nasan na riga kowa saka Number wallahi dan haka karka kice zaki kawo mun
uzuri, nidai gani na sake dawowa a karo na biyu da qoqon barar soyayyarki Asmy, ina
roqon ki amince dani ki bani dama na shiga rayuwarki mu rayu a qarqashin inuwa daya
a matsayin ma'aurata".
Miyau kawai nake hadiyewa qut qut ina zate ido ni kadai a daki har ya gama maganar
sa ban iya cewa komai ba. Seda muka kwashi kusan minti goma ba magana kafin ya
yanke shirun da cewa
"Kinyi shiru Asmy kice wani abu dan Allah, bance ki soni dole ba dan kin dade da
gaya mun bakya sona ba kuma zaki taba sona ba na yarda, ni ina sonki kuma na
tabbata qarfin son da nake miki ya isa ya riqe auran mu base kin taimaka da komai
ta bangarenki ba.
Nidai kawai ki bani dama na shiga rayuwar ki, idan Allah ya yarda bazakiyi dana
sani ba.
Zan baki abinda ya dace dake, zan shayar dake madarar soyayyar da ko a mafarki baki
tafa hasaso irinta ba nidai kawai ki amsa mun ki bani dama" ya qarasa da qaramin
sauti kamar me shirin yin kuka.
Se gani harda jan bargo na rufe qafata da sukayi sanyi, inda yasan yanda kalamansa
suka qulle mun baki da jijiyoyi gaba daya da yayi shiru amma ina sema qara wuta da
yayi yana zayyano mun kalaman da suke kassaramun jiki.
Irin Kalaman da a kullum nake mafarkin jinsu daga Bakin Bashir se gashi har na
qaraci zamana dashi be taba ko kwatanta gaya mun irinsu ba.
Yusuf be kyaleni ba seda yayi mun lilis da kalaman da suke bayyanar da tarin qaunar
sa gareni dan wannan ya wuce a kirashi da so. Haka mukayi sallama ba tareda na iya
bashi amsar komai ba dan zama nayi kamar wata farin shiga a lamarin.
Wai kuka zuciya da jaye jaye seta ringa rayamun dama ace Bashir ne yake gayamun
maganganun nan da lashakka sena narke a gurin nan sedai a sakani a ruwan qanqara na
hade.
Haka nayi baccina cikin nishadi cike da mafarkai masu dadi wai gani nida wani da
ban gane fuskarsa ba muna tsinkar furan soyayaa wani lambu me cike da Ni'ima harda
yan dagwai dagwai din yara mata guda biyu masu kyau da gani ma yan biyu ne.
Washe gari haka na tashi cikin nishadi muka hada abin kari harda Bashir aka zubawa
muka biya suka sake shiga su kadai suka ajiye kafin muka wuce na kaisu makaranta. A
hanya suke gaya mun har sannan bacci yakeyi se abin ya fara bani tsoro na qudure
idan mun dawo da daddare se mu sake zuw amu duba shi tunda abin na gaske ne ko babu
komai Uban yayana ne ba kuma shida wasu dangi a garin bayan mu, to wai ina matar sa
ma take? Na tambayi kaina daidai sanda nake ajiye mota ta a inda aka tanada danyin
fakin.
Sanda na shiga office na tarar da wasu clients guda uku masu son zuba hannun Jari,
nan da nan na shiga hidima dasu nan da nan kuwa muka qulla yarjejeniyar.
Da kaina na hada musu coffee muka sha kafin kafij suka saka hannu a takardu muka
basu wanda zasu tafi dasu na ajiye namu, na rakosu bakij office na juya ciki kenana
daya daga cikinsu wanda kana ganinsa kasan Bahaushe ne ya dawo da baya da murmushi
Nima murmushin nayi nace "yaya dai?"
"Mantuwa nayi" ya bani Amsa yana zaro wayarsa daga Aljihu ya miqa mun
"Na manta ban karbi numbar Hajiya ba saboda ko akwai wani abu se na kiraki".
"Ai da akwai Number a jikin Letter headed dinmu, idan kana da wani enquiry seka
kira" na fada ina zama akan kujerata, se ya ja kujera shima yana cewa
"Ki dai bani da kanki bata kamfani ba lambar wayarki nake so tunda dake muka qulla
kasuwanci".
Irin masu tsinannen nacin nan ne, daya tasani gaba seda na bashi lamba sannan ya
sarara mun, sema daya gwada kira yaga ta shiga wayata dake ajiye tayi qara sannan
ya haqura ya tafi yace mun sunansa Hayatuddin.
Mamaki na ringayi me yasa yanzu Maza suke tunkarata suce na basu lambar waya wai
tayaya suke gane banida aure yanzu tunda nidai babu abinda na chanza daga yanayin
shigata ko mu'amala amma yanzu ranaku daddaya ne zan fita ba tareda wani ya tare ni
ba, baga masu aure ba saboda tsaurin ido harda samari dan akwai ranar da na shiga
Shoprite seda nayiwa wani dan banza tatas a gurin wai yazo ze biya mun kudin kayan
dana siya.
Kafin na koma gida har Amnah ta shirya abincin da zasu kaiwa Bashir sanda na isa
har sunyi wanka suna zaman jirana. Ina shiga suka fara sintirin zuwa tambayar
yaushe zamu tafi yaushe zamu tafi dana ga zasu dame ni nace inaka sake tambayata an
fasa zuwa shine na samu sa'idah, seda mukayi sallar Isha, ina cikin yafa mayafin
Abayar dana saka kalar Maroon data karbi fatata kamar ka sace ni ka gudu Kiraj
Yusuf ya shigo wayata.
Haka kawai naji murmushi ya kwace mun, wayar mu ta jiya da daddare na tuna dan duk
yau bamuyi magana ba ya dai yi mun wani mugun text da safe dan seda muka fita break
din rana ma na gani ina karantawa kuwa na goge dan ji nayi yana neman ya tsaga mun
zuciya biyu bayan na rigada na saka zaran kirtani na dinketa tsaf ta yanda babu
abinda ze sake hudata ya shiga.
"Ran gimbiya ya dade" ya fada cikin sakakkiyar muryar sa.
"Tareda naka" na bashi amsa ina fesa turare.
"Ki saka kadan dan Allah, bana so wasu su ringa jiye mub qamshin ki baki san irin
yanda nake kishinki ba ko?" Ya fada daga cikin wayar,
Seda na janye na duba naga ko video call ne amma naga normal kirane, mamaki ya
kamani ya akayi yasan me nakeyi se ji nayi yace
"Mamaki kikeyi ya akayi na sani ko, ruhina da naki a hade suke, duk abinda kike yi
ina ji a jikina"
"Hakane" na bashi Amsa se ya fashe da dariya yace
"Gani a qofar gida nazo zance"
"Se dai ka daki gurbi dan bana nan"
"Kina ciki, shiryawa kikeyi zakuje duba Babansu Farida a Asibiti ya fadi jiya
bashida lafiya" Yusuf ya fada.
Ko be fada mun ba nasan Ya gamu da Jafar dan shine me shegen surutu kamar ya qone
akai.
"Ku fito se mu je tare na duba shi" ya sake fada kafin ya kashe wayar.
Tareda Driver sa yazo, dan hakaMota biyu mukayi tashi da tawa muka tafi.
Su Aliyu ne a motar da Driver yake ja, nida yammatan a motar Yusuf muna tafe se
jansu yake da hira ni kuwa duk nabi na takura kaina sedai ya kalleni yayi murmushi
har muka qarasa bayan da ya tsaya a wani guri ya siyi fruits harda kaza da ruwa da
Lemo kafin muka wuce.
Tundaga qofar dakin kana iya jiyo karadin Amirah, Yaran ne suka farayin gaba nida
Yusuf muka shiga a qarshe mun jera kamar wasu Mata da Miji yana rada mun yanda muka
dace wai se kallon mu akeyi da murmushi a kan fuskata nayi sallama muka shiga dakin
idona akan Bashir daya zabga uban tagumi kamar wanda aka cewa Dada ta mutu.
BASHIR
Please disregard the previous page 52 it was a technical error ππ
*SODA COMMUNICATIONπ±π»π±
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*ππ½ππ½ with the validity of 30days at affordable
price we are available 24/7 08137145294
*MTN DATA*
1GB@280β
2GB@550β
3GB@850β
4GB@1150β
5GB@ *1400* β
10GB@2800β
*AIRTEL DATA*
1gb@320β
2gb@640β
3gb@950β
5gb@1600β
*Pay throughππ½ππ½*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*π₯°π₯°π₯°we are always there at ur service. WhatsApp/Callπ08137145294
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 53
BASHIR
Se gurin Azahar ya tashi daga baccin dolen da Likita ya saka shi. Jikinsa a matuqar
mace yayi wanka ya saka uniform din marasa lafiya da aka bashi kafin yayi sallah ya
sake komawa kan gadon ya kwanta.
Abinci Nurse din dazu ta kawo masa, loma daya yayi ya ajiye dan yanda yaji shi
salam babu dandano haka yayi ta zare ido ga yunwa yana ji se Fruits ya iya sha da
Yoghurt kawai har kusan qarfe uku tun yana tsammanin zuwan wani harya fitar da rai
se a sannan ma ya tuna da yau Litinin ashe, be je aiki ba kuma be kira ya bada
uzuri ba.
Wayarsa ya dauka ya shiga kiran Engineer Musa abokinsa, bayan sun gaisa musan yaje
masa ya jiki yace masa idan sun tashi aiki zasu zo su dubashi dan Oga Abdallah ya
sanar cewa yana Asibiti.
Mamaki ya ringayi da har gashi ya kwana ya hantse ana neman awa 24 da barin sa gida
amma babu Amirah babu alamarta.
Yanzu ace da lissafi kuwa a Gurin nan mijinki ya fita ya kwana be dawo ba ai ko a
waya ta neme shi taji lafiyarsa tunda be saba hakan ba amma ze saka ido ya gani
daga nan zuwa anjima ya koma gidan se yaji abinda zata ce masa.
Yana cikin yin sallar la'asar se gata kamar an jefota dakin yana sallamewa kuwa ta
dira masa mitar ya za'ayi bashida lafiya har a dauko shi a kawo ahi Asibiti sannan
ne za'a gaya mata daga baya saboda bata da muhimmanci a gurinsa.
"Saboda ba'a gaya miki bane ya hanaki zuwa tun jiya kiga halin da nake ciki?" Ya
fada yana tsareta da ido, seda ta zumbura baki gaba kafin tace
"To ai gani nayi ba'a buqata ta shiyasa nayi zamana nasan dai duk tsiya in ma
mutuwa kayi dole a sanar mun tunda ni ce dai matarka ba wata ba" ta qarasa tana
juya ido, se kawai ya girgiza kai ya koma kan gadon ya kwanta tareda rufe ido kamar
me bacci.
Yana jin ta tana tambayarsa jikinsa yayi banza da ita, tayi maganar harta gaji amma
kamar meyi da dutse ko motsi daga qarshe dan kanta ta miqe tana cewa
"Qila bacci yayi, bari naje waje na wasa qafata kafin ya tash" ta fice abinta.
Tana fita ya bude ido ya raka ta da harara tareda dogon tsaki, haka ya zauna rabi
da rabi ido biyu da bacci saboda Allurar har sannan bata gama sakinsa ba dagoya
kawai yake ya saka wa qofa idon yana dakon zuwan yaran idanze fadi gaskiya ma
harda jiran Abinci yake dan na safen da yaci ya taso masa da tsohon kwadayin girkin
Asma'u.
Har akayi sallar Isha Amirah na zaune tana zuba masa surutun da sam ba fahimtar ta
yakeyi ba, ya hade girar sama da qasa qarin haushinsa da likita yace baze sallame
shi yau ba se ya sake kwana kuma shi