Showing 186001 words to 189000 words out of 238465 words

Chapter 63 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

suka dawo masa gida.

Hajia Addah kuwa abinda ya faru Bayan ta dawo daga gidan Ma’u ranta a jagule da
irin tarbar da Ma’un tayi mata. Sam bata taba tsammatar haka daga gareta ba saboda
yanda tasan Ma’u da haba haba da lamarinsu ada idan suka je gidanta kamar zata
goyasu saboda kirki amma yau ita tayiwa wannan korar kai tsaye ba tareda wata
shakka ko shayi ba koda yake ada Suruka take a wajenta a yanzu kuwa babu sauran
alaqa sedai ta kara kawai ai.

Babu abinda ya qara tayar mata da hankali irin nutsuwa da kyan da taga Ma’un ta
qara ga uwar daula data zuba a gidan ta dan yafi na Bashir din sau biyar wallahi
jifa wasu kujeru tana zama akai taji ta ta lume qa qamshi ta ko ina duk se taji ta
raina gidan Bashir yanzu data dawo ba kamar zuwanta dazu ba da ta ga gidan kamar
wadda taje wata Villa yanzu kuwa se taga duk ya zamar mata wani qauye dama ga
rashin gyara gaba daya dai abin ya zama se a hankali.
Tana zaune ta zabga tagumi Aliyu nata buga Game dinsa dan be nuna alamar ma yaji
shigowar mutum ba sega sallamar Jafar da kwandon Abinci. Bata jira ya qaraso ba ta
taro shi dan dagaske yunwa takeji, badan bazata gane ta inda suka shigo unguwar
bama da fita zatayi tunda da yan kudinta a jaka ta nemi abinci to Lagos kuma abinci
ai se kalar wanda ta zaba zataci.

Haka ta zauna tana ci tana zubawa Ma’u Albarka seda ta cinye kwan nan tas da sinqin
biredi ga qaton kofin data zuba shayi tayi gyatsa kafin ta dakko wayarta tana
kallon Jafar tace

“Kai Allah dai yawa uwarku Albarka yasa kuma kuji qanta, ungo nan ka duba zakaga
wata lamba da aka kira qarshe ta wani qedari ce da ubanku yace ze zo ya kaini
Asibiti na duba Antyn ku kirashi maza kace na shirya idan kuma zaka rakani to se mu
tafi tare”.

Lambar Samuel Jafar ya nemo ya kira ya gaya masa saqon Addah, yana qunquni ya amsa
gashi nan zuwa dan dazu daya dakkota har suka Zo tana zabga masa masifa dukda bajin
abinda take fada yake ba amma yasan zaginsa takeyi.

“Kai nima dai Jafaru zaka fara koyamun turancin nan tunda naga garin gaba daya kowa
shi yakeyi karna fita wata rana na manta hanyar gida na rasa waze dawo dani” Ta
fada tana dariya bayan daya miqa mata wayar yace Samuel din yana zuwa.

“Allah yasa na ki fitan ki bata daman yan yankan kai na garin nan sunfi son irin ki
masifaffun tsofaffi ai” Aliyu dake gaban Tv ya fada ba tareda ya juyo ya kalle ta
ba, nan kuwa ta hau sababi tana fadar sedai a sace uban sa badai ita ba shege me
baqin hali. Dake dangado ne kuwa ya manna mata hauka tayi tayi ba ita ta haqura ba
seda Jafar ya gaya mata ga Samuel ya dawo sannan ta fita, tayi tayi su tafi tare
yaqi dan yana Tsoron Maminsa haka ta kama hanya tana ci gaba da mitar ta.

Har bakin dakin da Amirah take Samuel ya rakata ta tura qofar tareda doka uwar
sallama kamar me magana da yan sama dai dai nan abokiyar zaman Amiran da aka kawo
jiya da daddare tana fama da matsanan cin ciwon kai dakyar aka samu tayi bacci a
sannan Mahaifiyarta dake jinyarta na zaune suna hira jefi jefi da Amirah cikin
harshen turanci sega sallamar Addah.

Cikin sauri tayiwa Addah data shigo tana sake jaddada sallama da qarin ko bacci
sukeyi ne alamar tayi shiru da hannu tana nuna mata yarinyar da har ta fara mutsu
mutsu alamar tana son farkawa.

“Ji wata masifa Allah ya tsaga mun baki a ringa mun alama wai nayi shiru in ke
bakya amsa sallama ai ita Amiran yar musulmai ce balle kice duk kune aikin banza
kai” Addah ta fada cikin daga murya tana kaiwa zaune kan kujrar dake gaban gadon
Amirah kafin taci gaba da cewa

“Haka kika qanjale Amirah sannu ko da yake iya jarabar Bashir kadai ta isa ta ramar
dake kai wannan Bashir dai ko azababbe daga zuwana fa harya...”

“Dan Allah Addah kiyi shiru dakyar aka samu tayi bacci wallahi kanta ne yake ciwo
sosai” Amirah ta katse ta kamar zatayi kuka ganin yarinyar ta fara riqe kanta da
alamar ta farka daga baccin kenan. Cikin masifa Addah ta waiwaya ta kalleta tace

“To ni ina ruwana? Ni na dora mata ciwon da za’a hanani magana ko yaya ina da akwai
dakin masu kudi da mutum ze zauna shi kadai me yasa basu kama can ba se kuma ni a
takurani ke dallah karki qaramun bacin rai akan wanda nake ciki”

Kuka yarinyar ta fara dan ba ita da take ciwon kai ba ko me lafiya dole kansa ya
buga irin yanda Addah take taqarqarewa yana daga murya kamar me magana da yan sama.
Masifa ta shigayi ita dai matar tana ta qoqarin kama yarta dake fizge fizge ganin
abin ya fara yawa yasa ta fita da gudu se gata ta dawo da Nurses guda biyu suka
rufu akan yarinyar qarshe se fita da ita dga dakin sukayi saboda yanda Addah ta
qiyin shiru gashi anyi anyi ta fita daga dakin taqi se zabga salallami take wai
wannan wane kalar sharri ne daga zuwanta se kace wata mayya yarinya zata fara fizge
fizge to Allah ya isanta.

Tana cikin sababin matar data bi bayan yarta ta tabbatar da lafiyarta ta dawo dakin
ba tareda Addah ta ankare ba tayi kanta tana zazzaga mata masifa cikin yarbanci
bakinta ne mutu ba itama ta shiga zaginta da Hausa Amirah dai ka tsakiya tana basu
haquri amma babu meji data ga suna neman bawa hammata iska seta koma kan gado ta
zabga tagumi kawai tana kallonsu da abin yayi tsamari shine matar ta jefawa Addah
flask dai dai sanda Bashir ya shigo tsautsayin ya fada akan sa.

Shiru sukayi gaba daya suna kallon Bashir din daya juya ya fice daga dakin, matar
ta dora hannu tana yan tsalle tsalle irin nasu tana kiran Jesus Addah ko harara ta
maka mata tace

“Ai wallahi se mun daure ki, badai kin qona mun Da ba wato da kasheni kikayi niyya
ko? To ki shirya yanzu za’a turo miki sammaci wallahi” A fusace ta juya kan Amirah
da duk ta rikice tace

“Ke kuma kukan uwar me kikeyi dallah taso muje mu ga halin da qafar take ciki idan
ta sale Aradu sena qonata itama haka kawai zata nakasa mun dan Yar uwa bazan
kyaleta ba.

Suna fitowa daga dakin Nurse ta taresu ta miqawa Amiran Farar takadda ta sallama
dole suka koma suka hau tattare kaya.

Haka suka fito harabar Asibiti neman duniya babu motar da Aka kawo Addah balle kuma
ta Bashir da daman basu saka ran ganinsa ba. A wayar Addah Amirah ta shiga kiransa
dan ta gaya masa an sallame su ya turo Samuel ya kaisu gida, kiran Farko harta
qaraci ringin be daga ba ana biyu kuwa aka ce mata wayar ma a kashe take.

Lambar Samuel din da Addah ta nuna mata ta kira ya daga suka gaisa kafin ma tace
sake magana ya gaya mata Oga ya aikeshi Abeokuta ze kai wani saqo kamar zata rusa
kuka haka ta kashe wayar suka samu qasan wata bishiya suka zauna gashiba wani gama
jin qwarin jikinta tayi ba dan cikin nata bana me zafin laulayi ne ga Addah da taqi
yin shiru se masifa take wai an musu wulaqanci yanzu ta ina zasu koma gida.

Dabarar sake kiran Samuel tayi akan ya gaya mata kwatancen unguwar tasu idan yaso
ko Taxi ne se su hau ta kaisu, hakan akayi sukayi shahada suka hau Taxi dan Addah
tana shiga ta tuna da fatan da Aliyu yayi mata dazu nan da nan ta jawo jarbi ta hau
ja baki ya mutu basu suka saki ransu ba seda suka gansu a qofar Estate din kafin
kowacce ta saki ajiyar zuciya.

Har qofar gida ya ajiye su, suka sauke kaya Addah ta zuge jaka ta ciro dari biyar
ta bawo me Taxi ta qyafe tana jiran ya miqo mata chanji. Kallonta yayi ya kalli
kudin kafin ya juya kan Amirah ya fara tambayarta kudinsa tunda ita ce mejin
Turanci.

Tambayarsa tayi nawa yace mata dubu goma zasu bayar tunda Drop suka dauka ta
waiwaya ta kalli Addah tace

“Addah dubu goma ne kudin motar, ki bashi dan Allah idan mun shiga ciki se mu
warware na gaji ni jiri nake ji” ta juya zata shige cikin gida Addah ta fizgota
tana cewa

“Dan fashi ne ya dakko mu ko yaya? Wannan tafiyar Asibitin da bata fi nayita a qafa
ba inda nasan hanya ita ce zakice a bashi dubu goma saboda ubanki ne ya bani ajiyar
kudin?

To banda su, dari uku nayi niyyar bayarwa shima saboda an shigo damu ciki ne amma
da a bakin get ya ajiye mu dari dari zan bayar seki nemi dubu taran ki cika masa”
ta mayar da dari biyar din cikin jaka ta harhado yan hamsin da dari na dari uku ta
watsa masa tayi gaba abinta.

Kamar Amirah zatayi kuka ta shiga roqon ta data bayar zata biyata dan ita sisi bata
magani a hannunta ko a cikin gidan gashi babu motar Bashir ballantana tace yana
gida zata shiga karbo ita kuwa Addah fafur taqi qara ko sile sema masifa da take
zazzagawa me Taxi daya juya P cap baya yana jira yaga zasu bashi kudinsa ne ko se
ya dauki mataki.

Ganin suna neman bata masa lokaci gashi wadda yaga kamar kudin a hannunta suke na
neman shigewa gida yasa ya fizge jakar Addah, babu bata lokaci ya zazzage komai a
qasa sega kudi kuwa suka zubo ya irigi dubu gomansa cif ya shige mota ko kula ihun
barawa da Addah take zundumaqa beyi ba ya qara wuta abinsa to masu wucewa ma babu
wanda ya kulasu dakyar Amirah ta turata suka shige gida se dafe kanta take daya
dauki ciwo saboda bala’in Addah.

A cikin gidan ma Sabon tashin hankali ta dasa mata akan kudinta ganin babu sarki se
Allah yasa ta shige daki ta kullo kanta, wayarta ta shiga dubawa dan ta kira Bashir
ko ze zo ya kashe wannan wutar ta ganta amma babu chaji seta jona ta shiga wanka
saboda jikinta sam babu dadi.

Lokacin data fito wayar tadan caju, lambarsa ta shiga kira yanzu a kunne take amma
kiran na shiga za’a katse shi ta kira yafi sau biyar qarshe dan kanta ta haqura ga
yunwa tana ji amma tsoron karonsu da Addah idan ta fita palour yasa ta gwammace ta
sha ruwa da wani Biscuit da yake a dakin ta kwanta ledar magungunanta kansu suna
palour haka ta haqura bata sha ba.

BASHIR
Daga Asibiti kai tsaye gidan Musa ya wuce dan yanzu can kadai yake iya zuwa ya rage
zafi tunda Musan shi kadai ne bashi da mata.

Cikin jimamin abinda ya sami qafarsa ya tare shi, ya ringa masa sannu kuwa qasan
ransa kuwa dariya ce fal musamman dayaji wai da surukarsa ake fada tsautsayi ya
fada kansa suka qonashi shi kuwa Bashir wace irin sirika yake da ita me fada da
mutane a Asibiti?

A gidan ya wuni zir, duk dai hirar da sukayi akan yanda ze gyarota da Ma’u ne dan
ya gayawa Musan yanda sukayi da Abubakar, shi ya qara bashi kwarin guiwa akan ya ci
gaba da binsa yana bashi haquri wata rana ze dace sannan kar ya daga qafa a Gurin
Ma’u duk irin wulaqanci da cin kashin da zata masa ya daure daman ance ai ramuwar
gayya tafi ta gayya zafi amma idan yayi haqurin buqata ta biya shikenan shi yaci
riba.

Shi ya sake bashi shawara ya ringa tura mata text na ban haquri akai akai. Gyara
zama Musa yayi yaci gaba da ce masa

“Kaifa matsalar ka Bashir na fuskanci gaba dayanka se a hankali yar soyayyar nan
naga alamar baka iyata ba se tsare gida da hade fuska kawai. Sufa mata da ka gani
suna son tattali da kulawa ko baka da sisi indai mace na samun nutsuwa da Farin
ciki a gurinka zata Yi haquri ta zauna dakai amma ko kafi qaruna kudi indai ta rasa
wannan ba ko wacce bace dukiya take a gabanta zata iya rabuwa dakai ta tafi inda
aka san darajarta ne ko kuma tana tare da kai ta ringa kula wasu cana waje da suke
bata kulawa suna yabonta.

Da yawa maza mu muke bada qofar da matan mu suke aikata wasu abubuwa da basu kamata
ba a bayan idon mu. Yanzu misali kaine kullum cikin hade rai a gidanka, kaida
matarka idan taga haqoranka to magana kakeyi babu dariya babu lafazi me dadi balle
ace tayi kwalliya ka yaba ko ka zauna kayi wasa da raha da ita tsakanin ku se bada
umarni kamar wata yar aiki da ubangidanta dan Allah ta yaya kake tunanin idan ta
hadu da wanda ze bata duk irin wadannan kulawar data rasa a gurinka ba bazata
kulashi ba?

Ba kowacce mace ce take da qarfin zuciyar daure wasu abubuwan ba, wata koda ba ta
sigar fasiqanci ba, wata da sunan aboki zakaga ta hadu da wani namiji da zasu zama
kamar wasu Qawaye ko Aminai duk wani sirri nata daya kamata ta yi shi tare dakai
shi ze maye mata gurbi ya zama abokin shawararta se kaga matar aure wai tana da
wani Besty duk waya ja Mijinta kuma ka tabbatar duk dakon zunubin da zatayo tare
za’a kasafta muku dan kai ka yanka mata tikitin da har zata kula wani banza can da
auranka.

Ka duba yanzu ko a gurin aikin mu yanda mata suka lalace matan aure kaga suna
qazamar rayuwa suna mu’amala da wasu mazan a waje da bana auransu ba a kaso goma
idan ka tarasu bakwai wallahi mazansu nada sa hannu cikin fadawarsu wannan halakar
saboda basu da ma lokacin su ballantana su san damuwarsu har su maganta musu ita da
yawan maza muna dauka kudi shine maganin ko wacce matsala idan ka wadata mace
shikenan ka gama mata komai wanda sam abin ba haka yake ba dole ka kula da matarka
ta kowanne bangare ka tabbatar da cewa ka toshe mata duk wata buqata idan kayi haka
kuma kaga wata matsala ta faru seka qaddara cewa jarabawa ce kuma daga ubangiji
amma ba wai dan kai ka bayar da qofar faruwar hakan ba.

Dan haka nidai shawarata Bashir ka canja takunka, ba Asma’u ba ko wacce mace zaka
zauna da ita dole ne kasan qima da martabarta. Ka sani cewar ba Alfarma kayi musu
daka auresu ba ballantana ka dauka dole suyi haqurin zama dakai da halinka Aa
zamane na ibadah da Allah ya hadaku kowa yana da haqqi akan dan uwansa”

“Haka ne kuma zanyi qoqari na gyara kuskurena Musa dan ina buqatar Ma’u a rayuwa ta
wallahi” Bashir ya fada bayan daya sauke tagumin da yayi.

“Au saboda ka dawo da Asma’u zaka chanja hili kenan? Bashir bari fa na gaya maka
gaskiya Halinka cikin goma bakwai basu da kyau ta fannin zaman takewa. Kai bafa
matanka ba kadai mu kanmu haquri muke dakai wani lokacin saboda shi hali zanen
dutseaka ce ba’a chanza wa mutum shi amma a wannan karon in har kana so lamuranka
su daidaita dole fa seka daidaita sahu a to.

Kai in banda ma halinka Bashir a zamanin nan ka samu mace kamar Asma’u bafa ajinka
bace wallahi in ma gaya maka gaskiya Allah ne kawai ya kashe ya baka ka samu tana
sonka take hidimta maka da jikinta da Aljihunta, matar nan fa ko daure fuska kayi
se hankalinta ya tashi. Ka tashi ka tafka mata kishiya ta wulaqanci koni Namiji
naji zafin abinda kayi ballantana ita sannan ka qara mata da tukwuicin saki kai ni
idan ta haqura da wuri ta dawo maka gaskiya bata mun daidai ba”.

Daure fuska Bashir yayi tamau yana kallonsa yace
“Karka kuskura kace mun kaima kana son matata dan shine mafi girman kuskuren da
zaka aikata, mu kadai ne a gidan nan yanzu zan murqusheka ka mutu Ba wanda yasan
meya faru”.

Dariya Musa yayi harda fadowa daga kan kujera kafin yace

“Maida wuqar Malam ashe daba ka fara ban sani ba. Ai ni idan zan so Ma’u bazaka
sani ba, qila se kaji nayi aure kawai kazo gidana ka ganta a matsayin matata amma
ni sam ba haka nake ba, babu kuma haka a tsakanin mu kawai dai ina nuna maka irin
girman asarar daka tafka ne a rayuwarka kuma idan baka hanzarta ba kana ji kana
kallo sedai ka mutu kana cizon yatsa da daka sani ka mayar da yayanka marayun dole
ka rabasu da uwar su haka kawai”.
Ganin da yayi daga shawara kuma abin na Musa na neman ya koma wulaqanci yasa yayi
masa sallama ya kamo hanyar gida, a hanya ya tsaya wani guri da suke siyan Shawarma
da wani Gas meat da Ma’u take bala’in so ya siya da yawa ya hado da Madarar ruwa da
kwali itama kalar wadda take sha kafin ya kamo hanyar gida.

A qofar gidanta ya ci burki, a waya ya kira Amnah yace tazo ba tareda ya fito ba ya
ce ta bude bayan motar ta kwashe ledojin ciki.

Ya dade a mota kafin ya fito qafa daya da takalmi daya babu ya dauki tasa ledar
Naman da Madarar ya shige gida, Hajia Addah na zaune a palour ta tasa Amirah data
gama zaman dakin ta fito a gaba har sannan dai zancen dubu goma yaqi ci yaqi
qarewa.

Kallo daya ya musu sanda Amirah ta masa sannu da zuwa ya wuce daki tabi bayansa,
tun dazu take jira ya dawo ita dai ya taimaketa ya biya Addah kudinta kota samu ta
shaqi iska a gidan yana shiga dakin kan ya rufo tayi wuf itama ta fada ya kuwa
balla mata harara ta sunkuyar da kai se ya wuce ya ajiye ledar hannunsa ya shiga
bandaki.

Tana zaune se hadiyar yawu take saboda qamshin naman da duk ya cika dakin ya fito,
kamar munafuka tayi qasa dakai tana gaishe shi ya amsa a taqaice yana cire rigar
jikinsa ganin taqi fita yace mata

“Lafiya?”
“Am daman Yaya an sallamo mune na kiraka da wayar Addah lokacin baka dauka ba na
kira Samuel shima yace mun...”

“Na sani na aike shi ba gashi kun dawo ba se akayi yaya to?” Ya katseta murya a
cunkushe, qasan ransa har yana tunanin wane hankali ne yazo mata da har tayi
tunanin zuwa ta duba shi kodai Addah ce ta sakata dan yasan a kalar nata tunanin
dai bazatayi ba, maganar tace ta katse shi da take cewa

“Daman Taxi muka hawo ta dawo damu, shine seda muka zo yace wai kudin motar dubu
Ashirin tunda drop muka dauka to Addah ce ta biya tun safen take ta mun masifa akan
na biyata kudinta kuma ni ko sisi bani dashi nayi ta kiranka ma dazun kana
rejecting gata can wallahi ko abincin kirki ta hanani naci da masifarta”

Wani mugun kallo me nuna zallar bacin rai yake aika mata, wato kudi take da buqata
tun dazun dalilin kiran da ta ringa masa kenan, qonewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login