Showing 237001 words to 238465 words out of 238465 words

Chapter 80 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

kuma
naja su a jiki ina tafiyar da kowa a yanda ya kamata.

Hajiya Intee kuwa lokaci da yawa ma ni mantawa nake ina da kishiya dan a rayuwa
idan kuna jin ace mutum Zero tension to Intee kenan, ita dai barta da kallon
wulaqanci wanda na lura da cewar dabi'arta ce idan aka zo batun Miji ita auro ni da
akayi ma qara mata wani Yanci yayi dan ta sakar mun ragamar komai ban fi shakara ba
ta tattaro Ma'u qarama aka dawo da ita Nigeria, shi kansa Mijin se ya shekara beje
mata ba se randa ta bushi iska ta kirashi ko ita tazo sannan fa badan ma Allah
yasaka Adali bane dana tabbata zuwa yanzu idanbe rabu da ita ba toh tabbas ita da
babu zasu zama basu da banbanci a gurinsa.

Bazan gaji da buga misali da Rayuwar Yayana ba wadda a koda yaushe na daga hannu na
bana sauke shi ba tareda na roqa musu kariya da shiriya a gurin Allah ba wanda
Alhamdulillahi dan ubangiji ya dafamun, ya shirya mun su da shiriyar sa da kuma
jajircewa irin ta mahaifinsu dan dole na Jinjinawa Bashir ta yanda abubuwan da suka
faru suka zamar masa darasi babba da yayi sanadiyyar daidaituwar rayuwar sa.
Amnah tayi aure ta Auri Naziru qanin Bashir tun taba shekara ta uku a karatun ta
yanzu haka suna Can American inda shima ya samu aiki harda qaruwar dansu guda daya
Ahmad.


Aliyu ya gama karatunsa ya dawo dukda seda ya hada harda Masters yanzu yana ayyukan
kwangila wanda Yusuf yake sakar masa sosai yake nemo masa kwangila daga ko ina dan
yanzu sun dinke baka jin kansu, wani lokacin ma zezo Bauchi bazan sani ba sedai
kawai Na ganshi yace Dady ne ya kirashi zeyi wani aiki.

Jafar nedai na hannun damana kuma sirikina dan fa hadin nan dagaske zamuyi shi da
takwarata data zama budurwa itama yanzu saboda tana da girman jiki, shekaru sha
shida idan ka ganta zaka dauka tayi Ashirin dan haka ma Babanta yace da Faridah ta
qarasa karatunta ze hadasu yayi musu aure idan yaso ita Ma'u ta cigaba a gidanta.

Yan biyu na dai da Babana sun zama yayan Amarya sedai lokaci lokaci idan sun samu
hutu suzo mana, Bashir ya qara aure tun banfi shekara uku da yin aure ba auri
Sa'idah Bayerabiya ce yar wani babban Malami a garin Lagos macen kirki data rungumi
yayana ta riqe da amana tamkar ita ta haife su.

Fadar irin tashin da sukayi da Amirah ma bata lokaci ne dan har seda tayi
sanadiyyar mutuwar auranta tayi zaman shekara daya a gida dan daman akayi sa'a ta
dawo Nigeria lokacin haihuwar Yarinyar da Bashir yayi mun takwara da ita wadda daga
kanta har yanzu bata qara ba, dan haka koda aka fara dauki ba dadi akan zancen
auran nasa a yanda na samu labari har cikin gidan su taje ta ambaci sunan uwarsa da
ubansa tace idan ya haifu a cikinsu ya sake ta babu bata lokaci kuwa Dada ta
kirashi a waya tace ya saketa Alhaji yace a ta fau baza'ayi haka ba.

Qarshe gidansa na Gombe ta cinnawa wuta ya qone qurmus ko tsinke ba'a fitar ba babu
Arziqi ya aiko mata da saki biyu ya kuma saka aka kwace yarinyar bayan daura
auransa da Amaryar sa ta wuce da ita Faransa suka ci gaba da rayuwarsu.

Seda taji jiki zawarci shekara shida kafin ya mayar da ita ya barta anan Nigeria
cikin gidan su ya gyara mata bangaren Alhajinsu bayan ya rasu take zaune ana gara
rayuwa babu dadi babu wahala dan taji jiki shiyasa ta yarda da duk yanda yace dan
ko banza bazata taba hada zaman da irin zawarcinda tayi a gidan su ba bata da
maraba da boyi boyi, kudin da zata siyi omon wanki ma gagarar ta ya ringa yi gashi
ita ba wata sana'a ta iya ba babu kuma wanda yazo koda wasan yace yana sonta saboda
yanda labarin abinda ta aikata ya karade ko ina harya gama zawarcin.

Addah kanta da take tsaya mata tayi duk abinda taga dama ta kanta take yi dan ta
gamu da wanda ya fita iskanci, malamin daya ce tayi auran kisan wuta zeyi mata
aikin da Ahaji Murtala ze mayar da ita dashi sukayi auran akan sati biyu zatayi ya
saketa se gashi yanzu ana lissafin shekara kusan Tara kenan harma ta haqura rayuwa
ta bida ita tana can wani surquqin qauye ya kafeta ga kishiyoyi uku shegun qauye
sun tasata a gaba rayuwar ta kam yanzu ta zama abin tausayi mutum dai kawai ya
tsoraci Allah a rayuwa.

Ummi qanwar Amirah tana zaune lafiya a gidan mijinta cikin rufin asirin Allah sun
rungumi junansu sun zauna tamkar babu wani abu daya taba faruwa a baya. Hatta da
mutanen gari tamkar an shafe musu tarihin abin a zuciyar su babu wanda yake tunawa
harta haifi yayanta guda uku yanzu.

Ban manta da Maqociya Aminiyar kwarai Anty Halima ba, itama tuni sun bar Lagos
bayan da Baba yayi ritaya sun koma Zamfara da yayanta hufu yanzu dan a jere a jere
tayi su tunda Allah ya bude mata hanya, hakan be saka mun yanke zumunchi ba kullum
muna cikin waya ko chatting tana sake bani sirrika tana aiko mun da makaman yaqi
nima kuma Alkahiri na be taba yanke mata ba, duk wani abu daya tashi na romon
damakaradiyya sena sakata a ciki, ga connection da nayi mata da matan abokanan
siyasar Yusuf suna siyan kayan Arziqi a gurinta duk wadda ta siya kuwa seta koma
sanna ta qara kawo mata wasu shi yasa takance dani

"Ma'u haduwa ta dake ta zame min Alkahiri", na kance d ita
"Anty duk abotar da aka qullata domin Allah daman tana zama Alkahiri me girma
fatana zumunchin mu ya dore har gidan Aljanna".

MURFI

Ina cikin Sujjada naji an bude qofar dakina an shigo, nasan Yusuf ne, Dan duk daren
duniya ko qarfe nawa ze kai suna Meeting idan sun gama a gida ze kwana, akansa na
qaryata cewar da ake yan siyasa basu da lokacin iyalansu dan nidai nawa Mijin yasha
banban da sauran.

Kafin yara su fara makaranta ko wata qasar ze tafi qafata qafarsa, har kuma Yanzu
indai tafiya bata wuce sati ba sedai na barsu a gida mu tafi balle kuma ace yana
gida Nigeria ya kwana a wani guri da ba cikin gida ba gaskiya da wuya.

Seda na sallame na Shafa addu'a kafin na kalle shi ina murmushi nace
"Sannu Excellency se yanzu"
"Kinganni fa Asmy, mutanen nan sun huramun wuta da yawa, ni kuma ina kan bakana
bazan yarda da duk wani sharadi mara tushe ba sedai idan zasu kwace tikitin takarar
su su karba amma bazanyi abinda zanje gaban Allah na kasa kare kainaba, wai har
party chairman ne yake munbarazana, nace masa duk aikin banza ne babu abinda zasu
iya wanda Allah beyi ba".

Kusada shi na koma na kama hannunsa nace
"Babu komai ka tsaya akan gaskiyarka, ba abinda ze same ka da izinin Allah kuma
seka cika burinka tunda dai kaine akan gaskiya su kuma qarya kuma a koda Yaushe
Gaskiya ita take Nasara akan qarya".

"Shiyasa nake qara sonki Asmy ta saboda a duk sanda na rasa qarfin guiwa kina dawo
mun dashi, Allah ya gafartawa Hajiya, maraicina kadan ne tunda ina da mace ta gari
da bata mantawa dani a cikin Addu'ar ta"

"Amin yah rabbi, ni yaushe za'a bude mun ofishin First Lady ne na qaddamar da
campaign dan dai kasan wannan karon baza'a barni a baya ba, First Lady lamba daya
ba wasa ba kai wayaga Ma'u a Villa" na fada cikin wasa ian wani buda kafada irin
yanda zan ringa tafiya a Villa.

"Ga babban office dinki nan, ai kici gaba da Sallah kina taya mu da Addu'oi dan ina
ganin hasken su amma darajarki ai tafi qarfin ki fita yawan campaign dan zan iya
zagewa mu daku da duk wanda yace ze daga miki yatsa, yanzu dai kawo mun Baqin
Lipton kizo kiji wani abu, ni naga wani qyallin go shi ma kike kodai mun samu
qaruwane?" Ya fad yana shafa goshi na, sena miqe ina dariya nace

"Rufa ni ka sayani, meya rage ban haifa ba ni kuwa da zan haifo shi Yanzu?"

"Bashir, ba kiyiwa Bashir takwara ba" ya fada har yanadaga murya dan na kusa fita
daga dakin. Se nayi turusna wai wayo, wani abu naji ya motsamun a zuciya kai Allah
karya kawo abinda baze wuce ba sena kalle shi ina murmushi nace

"Ai ka rigada kayi jana'izar Bashir a zuciyata dan haka bani da sauran qwan da zan
haifa na saka masa sunansa, idan kuma jinjiri kake so to sedai mu haifi Yusuf
Junior a Villah idan Allah ya kaimu".


TAMMAT BI HAMDILLAH
SAQON GAISUWA GA DAUKACIN MASOYAN LITTAFIN WATA KISHIYAR A DUK INDA KUKE A FADIN
DUNIYA ALKAHIRIN ALLAH YA KAI MUKU 🙏🙏🙏
NA GODE DA JUMURIN BIBIYA DAGA FARKO HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN ALLAH YA HADAMU
A LADAN ABINDA MUKA KARANTA NA QARUWA YA YAFE MANA KURAKUREN DA MUKA AIKATA A CIKI
MASU KIRANA A WAYA DA MASU TUROMUN SAQO NAGODE, MASU NEMANA A DUK SANDA SUKA JINI
SHIRU KWANA BIYU DAN TABBATAR DA LAFIYATA INA GODIYA SUNAYEN KU BAZASU RUBUTU BA
AMMA DUK WADDA TA GANI TASAN DA ITA NAKE KUMA NA GODE KWARAI ALLAHYA SAKA DA
MAFIFICIN ALKAHIRI
NAGODE ONE LOVE 🥰🥰😍😍

SE MUN SAKE HADUWA A LITTAFINA ME ZUWA 🙏🙏🙏

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login