Showing 183001 words to 186000 words out of 238465 words
ya kawo ki ze zo seya kaiki ki dubata ku
dawo" yana gama fada yayi ficewarsa dan gara yayita yawo a gari yana qona mai daya
zauna a gidan nan wannan birkitacciyar tsohuwar ta chaza masa kai.
Rasa abinyi Addah tayi, ta shiga Kitchen ta duba gadai kayan abinci amma bata san
ya zata yi amfani da kayan wutar ba dan Gas cooker dinsu ma soft touch ne. Palourta
dawo ta tsaya tayi sa'a sega Aliyu ya fito daga daki da Kofin shayi da farantin
daya soya dankali da kwai ga ragowar nan be cinye ba seta nufeshi tana washe baki
tace
"Yawwa Dan Albarka taimaka nima ko shayi da kwan ne ka bani wallahi Yunwa nake ji
ban karya ba na fito, bani wannan na fara dashi kafin ka hadomun wani" ta fada tana
qoqarin riqe farantin hannunsa.
Kallon daga ina ya mata kafin yayi kwana ya fasa shiga Kitchen din da yayi niyya,
akan idon Addah ba tareda ya kalata ba ya fita qofar gida ya zazzage abincin a inda
suke zubawa karnukan da suke gadi abinci ya sake dawowa ya wuceta ba tareda ya
kulata ba.
Haka ta ringa masifa kamar zata ari baki amma dan gaske yayi banza da ita qarshema
Tv ya kunna ya hada Game dinsa ya fara bugawa daidai Nan Jafar ya shigo, shine me
farat farat nan da nan ya gaishe ta. Shi ya rakata har qofar gidan Ma'u be shiga ba
dan yasan qila tayi masa fada se ya koma gidansu yana shiga kuwa Aliyu yayi kansa
da fada kamar ze dakeshi shi dai yayi shiru be amsa masa ba.
ASMA'U
Cikin filo na cusa kaina dana dafe da hannaye bibbiyu, na kasa yarda Bashir ne ya
durqusa a gabana yana bani haquri sannan waini Asma'u na iya gaya masa maganganu
haka ba tareda wani dar ba.
"Kar fa ace na dena son Bashir da gaske" na fada a fili ina tashi zaune. Tagumi na
rafka hannu biyu gaba daya na rasa me ma yake damuna. Ina jin wayata dake gefen
gado tana ta qara amma naqi dubawa dan nasan dayan uku ne ko dai Bashir ko Yusuf ko
kuma dayan Mayen Hayatuddeen.
Gaba daya daren haka na qarar dashi ina juyi da tunane tunanen da ni kaina bansan
me nake tunawa ba. Saboda rashin samun wadatacce bacci da ciwon kai na tashi idona
yayi ja kamar wadda tayi kuka.
Da yake Asabar cema abin yazo mun da sauqi nayi wanka na saka riga mara nauyi kafin
na fito palour na tarar da Amnah da Farida suna cin abinci.
Bayan mun gaisa Amnah ta tafi kawo mun abin kari se Farida ta dawo kusada ni tana
cewa
"Mami kin san me?"
"Meya faru sarkin labari?"
"Mami, Addah ce fa tazo yau, gasu can se fada suke da Abbi yace seta tafi shi bece
a turota ba ita kuma tace ba inda zataje. Nidai Mami na dawo nan gidan da kwana dan
Kinsan halin Addah fada ne da ita har da dadddare nasan hana mu bacci zata
ringayi".
"Ikon Allah" na fada ina karbar Kofin shayin da Amnah ta hadamun, hankali kwance na
shiga cin abincina har na gama ba tareda na bawa Farida amsa ba can qasan raina ina
mamakin dalilin zuwan Addah.
Ina shirin tashi daga gurin naji an doko sallama bana buqatar qarin bayani nasan
wacece lokaci daya na hade fuskata tsaf yanda kasan ban taba dariya ba a duniya ina
kallon qofa daidai sanda ta shigo cikin palour fuskar ta dauke da wannan dariyar
tata dana kira data qeta tana cewa
"Ga baqin Asuba ko da yake rana ta daga ai. Se kuka ganmu babu sanarwa ko?"
Ban amsa ba sema harde hannu da nayi a qirji ina qare mata kallo har ta zauna akan
kujera. Idan ba ido na ba se naga ta zabge babu wannan qibar kuma tayi baqiqqirin
kana ganinta kasan tajin qari matuqa.
"Asma'u ina kwana?" Maganar ta ta katse ni, daga tsayen na amsa mata da
"Lafiya" na qara daure fuska. Ina kallon yanda ta bini da ido alamar mamaki qarara
akan fuskarta kafin kuma ta waske tana cewa
"Uhm daga dayan gidan naku nake, kinsan qanwar taki bata da lafiya an kwantar da
ita a Asibiti ciki ne da ita shine fa nazo zaman jinya ashe u Asibitin naku ba'a
kai musu me jinya.
Jirgin Asubanci muka biyo ko karyawa banyi ba, ga Bashir da baqin hali wallahi ko
ruwa be bani ba in gaya miki ya ma fice ya barni a gida ni kwal kamar mayya ni ba
iya amfani da kicin din ku na zamani nayi ba shi kuma wancan me kama da uban nasa
ko kallon arziqi be mun ba shima daya.
Shine fa na fito waje sena ci karo da dan kirki Jafaru yace na shigo nan na samu na
sakawa abakin salati".
Tsam nayi ta gama rattabo jawabin ta kafin na juya dakina ina cewa
"Ayya gashi kinyi rashin sa'a fita zamuyi muma. Koma ba haka ba baki sanar mana da
zuwanki ba dan haka ba'a dafa dake ba".
Sena waiwaya na kalli yaran da sukayi tsuru suna kallon mu nace
"Ku tashi ku shirya fita zamuyi"
"Mami ina?" Abdallah ya tambayeni, sena harare shi nace
"Inda ka aikeni ubana".
Ina shiga dakin na kwalawa Amnah kira ta biyo ni da sauri.
"Ko ruwan fanfo ku ka bata senaci uban mutum wallahi ku wuce ki shirya Yan biyu ku
jirani a waje" na fada cikin sigar umarni.
Harna fara qoqarin chanza kaya wata zuciyar tace mun to akan me zan fita ma ta koma
inda tazo meye hadina da ita toh? Se kawai na kwanta akan gado na sake kwalawa
Amnah kira nace mata
"Kije ki ce mata ta fita zaku rufe gida ne" jim naga tayi alamar bazata iya ba, na
ja tsaki ina miqewa nace "matsa mun daga nan"
Na bi bayanta muka fito har sannan Addah na zaune ta rafka tagumi kamar wadda akawa
mutuwa.
Fuska a daure ba tareda na kalleta ba nace
"Ki koma can gidan ina so mu rufe qofa saboda baqi masu shigo maka ba tareda iso
ba".
Allah sarki se kuwa ta miqe tsam da natacviyar qatuwar pos dinta dana rasa uwar
datake durawa a ciki tana kallona tace
"Toh bari naje, amma dan Allah ko gayan biredi idan kuna dashi ki bani sena hada
shayi koda ruwan sanyi ne nasha tunda naga madara a can din".
"Kije za'a kawo miki" tayi mana sallama kuwa ta fice.
Kwai na saka Amnah ta soya mata guda shida nace su hada mata da biredi sinqi daya
me yanka yanka ta bawa Jafar idan yaje ya jona mata ruwa a kettle seta sha shayin
na sake komawa dakina ina shiga wayata dake kan mudubi ta fara qara.
Yusuf ne, na daga da sallama ya amsa yana cewa
"Amaryata barka da safiya" Yusuf ya fada daga daya bangaren
"Wacece Amaryar ka?" Na tambayeshi ina gyara zama se ya bani amsa da cewa
"Wata ce, yau zan shigo Lagos nayi kewar ki da yawa da naso na bari se sati na sama
amma naga bazan iya ba ke din kawai nake so na gani dai"
"Wancan satin fa kazo" na fada se yayi saurin katse ni da cewa
"Idan kika ce na zauna sena haqura ya zanyi girmanki ne amma wallahi dagaske nayi
kewarki ni kadai nasan yanda nake azabtuwa da rashin ganinki din nan. Ki taimaka
mun ki zama mallakina dan Allah ko hankalina ya tattaru a guri daya na dena raba
shi".
"Uhm" na fada kawai dan ban san me zance masa ba.
Sosai ya kwantar da murya yana cewa
"Asma'u bana so na sake yin saken da zaki kufce mun, ki amince dani na miki
Alqawarin bazakiyi dana sanin bani amanar kanki ba. Na yarda ko bakya sona wallahi
zan zauna dake qaunar da nake miki kadai ta isa ta riqe auran mu nidai kawai ki
amince mun dan yardar ki kadai nake nema.
Tunda na rasa ki ban sare ba, a kullum cikin Addu'a nake idan harda Alkahiri a
tsakanin mu Allah ya tabbatar dashi gashi yanzu bayan tsahon shekaru da har na sare
na cire raina akan ki Allah ya karbi Addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata dan
Allah Karki sake jefa zuciyata a cikin quncin da ta rayu dashi tsahon shekaru".
"Yusuf wai ka manta da da yanzu ba daya ba, waccen fa Asma'un daka so budurwace me
qarancin shekaru yanzu kuwa kana magana ne da Asma'u da ta zama uwa haihuwa biyar
fa Yusuf yaya shida a hakan kake sona?"
"Wallahi ke nake so Asma'u kedin nake so ba wata suffa taki ba. Ba aure daya ba ko
haihuwa biyar ba idan mazan duniya dukka kika aura kika haifa musu Yaya zan zauna
dake saboda ke nake so ba wani abu naki ba.
Yayanki kuma yayana ne Asma'u ko ban aureki ba ni zan iya riqe miki su idan har
buqatar hakan ta taso ballantana ace ina auranki ai basu da wani uba kuma sama da
ni. Dan girman Allah ki tausaya mun naci darajar tarin qaunar da nake miki ki bani
dama na shiga rayuwarki in Allah ya yarda bazakiyi dana sani ba".
Gaba daya yabi ya daureni da jijiyoyin jikina, magiya yake mun akan na amsa zan
aure shi ni kuwa na rasa me zan ce masa a lokacin.
Idan na Amsa Yusuf anya banyi gaggawa ba? Meye tabbacin da nake dashi akan zan samu
banbancin rayuwa a gidansa sama da irin wadda nayi tareda Bashir?
Idan na auri wani daban yaya makomar Yayana zata kasance tunda nasan ko dama da
qasa zasu hade Bashir baze taba bari dan sa yayi agolanci a wani guri ba sannan na
tabbatar shika mijin da zan aura baze yarda da zama na a kusada Bashir ba idan na
bar nan to yaya makoma da tarbiyyar yarana zata zama?
Kamar ya shiga zuciyata se ji nayi yace
"Nasan me kike tunanin Idan kika aureni zan dauke ki daga kusada Yaranki da aikin
ki tabbas zanso hakan saboda zan buqace ki a kusa dani amma in har kinfi son zama
anan din zan iya haqura na lamunce miki in har hakan ze faranta miki rainya baki
nutsuwar zuciya".
Sosai ya bude mun wuta, na rasa dalilin daya sakashi ma taso mun da wannan maganar
a yanzu, duk yanda naso na zille yaqi bani dama gashi ita kanta zuciyata a yau taqi
bani hadin kai gurin furta kalaman da zasu saka Yusuf din ya haqura da qudurinsa
akaina daga qarshe a dole muka rabu akan ya bani sati daya nayi tunani na yanke
shawara akan makomar tarayyar mu.
Acewarsa mu ba yara bane da zamu zauna muna jan lokaci idan har na yarda na aminta
dashi a matsayin abokin rayuwata a shirye yake daya zamemin bangon jingina.
Wannan maganar ta mantar dani batun Bashir na shiga Sabon lissafi da komonton
hukuncin da zan yanke akan Maganar Yusuf.
Harga Allah idan har son zuciyata ne zan zabi na koma dakina na zauna da Bashir
amma ina tuna cin zarafi da wulaqancin da yayi mun ya sake ni akan yar uwata mace
se naji sam koda na koma gidan sa bani da sauran wata qima ko mutunchi a idanunsa.
Idan har ze iya tsinka igiyoyi biyu na auran shekara goma sha bakwai akan macen
daya aura shekara uku bayana to tabbas qarasa dayar bazata yi masa wahala ba.
Amma zan miqa komai ga Allah zan nemi zabinsa duk kuma abinda yafi kwanta mun a rai
zan karbe shi a matsayin zabin da Allah yayi mun wannan na qudurce a raina babu
kuma bata lokaci na tashi da kaina na shiga Kitchen, ina da tukunya babba da nake
girkin Sadaka a ciki nan da nan na dora Jalof din shinkafa me kyau ban dauki lokaci
ba na gama na zuba a robobin take away masu murfi.
A qatuwar roba muka jera su, dakaina na dauka a mota muka fita can kan wata hanya
inda daman muke kai abincin na ringa rabawa mutane Musulmao harda wadanda ba
musulman ba duk wanda na bawa zance kayi mun Addu'a Allah yayi mun zabin Alkahiri a
cikin rayuwata nayi hakan kuma da kyakykyawan yaqinin amsuwar Addu'ata.
BASHIR
A wani gidan abinci ya karya, rashintakamaiman gurin zuwa ya saka yayi zamansa a
gurin kawai yana kallon masu shigowa suna fita.
Kusan awa daya yana zaune shidai baze ma iya cewa ga abinda yakeyi ba can dai ya
miqe ya fita yana qoqarin bude motarsa yaji anyi masa sallama daga bayansa.
Waiwayawa yayi, Macece budurwa a qallah zatayi shekara Ashirin da biyar zuwa sama
ba fara bace amma fatarta bata da duhu kuma ba wata shahararriyar kyakykyawa bace
sedai yawan Fara'arta ya taimaka gurin fito mata da kyau me sanyi.
Sallama ta sake maimaita masa fuskar ta dauke da murmushi seya dakata daga bude
motar yana qare daure tasa fuskar ya amsa ciki ciki yana kallonta.
"Sunana Zulaiha, kayi haquri fa na tsayar dakai, tun dazu naga shigowarka. Alamun
ka sun nuna kana tareda damuwa qarara. Idan kana da maganin damuwarka kayiwa kanka
idan kuma baka da shi to koma menene yake damunka ka fawwalawa Allah yin tagumi da
zama shiru bazeyi maka magani ba" ta fada cikin murmushi tana kaiwa qarshe kuwa ta
juya ta barshi a tsaye kamar ta dasa shi.
Jiki a sabule ya shiga motar, harya kunna ta kuma seya kashe cikin dakiya da
jarumta ya danna kiran lambar Abubakar dan har seda ya kulle ido kafin ya kira
ringin daya biyu uku aka daga Abubakar yayi sallama daga bangarensa.
Cikin faduwar gaba Bashir ya amsa sukayi shiru gaba dayansu kafin can Abubakar yace
"Wayake magana ban gane lambar ba"
"AB goge lambata kayi? Bashir ne fa" Bashir ya bashi amsa a sanyaye dan jij ko
lambarsa ma bashi da ita.
"Ayya Yi haquri kasan mutanen da yawa wanne Bashir kenan? Kayi mun bayani yanda zan
gane".
Seda yaja fasali a ransa ya maimaita La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu
minazzalimin kafin yace
"Nasan ko baka da lambata ai muryata bazata bace maka ba, Bashir ne dai naka kuma
Mijin qanwar ka Ma'u".
"Eh to nawa Bashir din dai ko banga lambarsa ba na haddaceta akai (sunada qani
Bashir) sannan cikin qannena babu wadda take auran Miji me suna Bashir gaskiya.
Ok kace Ma'u ko? To Ma'un dana sani a gidan mu ma bazawara ce bata da miji sedai
ko idan tsohon mijinta kake nufi sunansa Bashir" Abubakar ya fada cikin irin
lafazin nan na ko a jikina.
Shi kuwa Bashir har wata zufa ce ta shiga keto masa. Toh ta ina ma ze fara masa
magana jin irin wannan amso shi da yake bashi yana nuna masa cewar babu sauran wani
abu tsakanin su kenan yama manta dashi a babin rayuwarsa.
Daurewa yayi muryarsa har tana rawa rawa yace
"Am Abubakar na sani abubuwa da yawa sun faru a baya da sedai nace kayi haquri
laifi na ne kuma na karbi kuskurena in sha Allahu zan gyara dalilin ma daya saka na
kiraka yanzu kenan na baka haquri akan komai aya faru sannan na nemi shawarar ka
akan yanda ya kamata na gyara sauran kura kuraina".
"Toh a taqaice dai ni abinda zan iya ce maka shine kasan hausawa sun ce yanda aka
dama haka za'a sha, to nima sedai na maimaita maka hakan nace maka ka koma gefe
kawai ka nade hannu ka karbi duk wani sakamako a yanda yazo maka Malam Bashir,
batun laifi kuma ni bakayi mun komai ba.
Idan zan tuna ka gaya mun babu ruwana da sabgar gidanka ko dan kana auran qanwata
bashi ya bani damar gaya maka abinda zakayi da wanda zaka bari ba, tundaga sannan
na sake tsoka bakina a cikin sabgar gidan ka?
To na menene yabzu zaka sako ni kuma?
Ita abotar ka yanke ta tuntuni, auratayyar ma ka sakar mun qanwa to me yayi saura a
tsakanin mu yanzu babu dan haka dan Allah karka sake kirana akan wani shirme naka
can idan ba haka ba kaga yau na amsa ka a mutunce ko, ka tabbata idan ka sake a
ranar zaka gane kuskuren ka zan sauke maka fushin shekara da shekaru dana shanye
ban nuna maka ba" yana gama fadar haka ya kashe wayar sa.
Ajiyar zuciya Bashir ya sauke dan ya tsammaci fiye da hakan ai to tunda ma aka
tsaya anan ai ya gode Allah har ya samu kwarin guiwar sake tun karar sa kuwa idan
aka kwana biyu.
Hanyar Asibiti ya dauka ko ba komai Ya kamata ya je ya duba yanda ta kwana gashi
har rana ta kwale yanzu. Yana isa tun daga farkon ward din yake jiyo tashin muryar
Addah cikin masifa ga wata muryar da be tantance ta waye baita kuma ana yarbanci da
alama itama masifar takeyi, kansa ya sara masa yaji kamar ma yayi kwana ya fasa
shiga.
Ya akayi tazo da wuri bayan ya gayawa Samuel se yamma zeje ya daukota sannan ita
dawa take fada a Asibiti kuma? Badan kar taje ta jajibo masa wata fitinar ba da
juyawa zeyi ya barsu su qarata amma dole ya qarasa cikin dakin daidai sanda matar
da suke fadan ta jefowa Addah irin qaramin flask din shayi na silver akayi rashin
sa'a ta goce ya fadi tim akan qafar Bashir daya shiga dakin tsautsayi ashe be rufu
da kyau ba kuwa ruwan zafin ya kele masa a qafa ga zafin buguwar da yayi ga azabar
ruwan zafi besan sanda ya fasa qara yana sakin wayarsa da muqullin da suke hannunsa
ba suka fadi qasa.
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 56
βInnalillahi Addah ta qona shiβ Amirah dake zaune akan gado ta dora hannaye biyu
akai tana fada.
βKan balaβi kika qona shi To wallahi kin taro ruwan dafa kanki daman ni kika so ki
laβanta kenanAllah ya kareni tsiyarki ta fada akan Dana ai kuwa bazamu yarda ba
daganan har kotun qoliβ Addah ta sake hayayyaqowa matar dake tsaye tana
numfarfashi.
Irin shinqimemiyar nance ta gaske, itama cikin masifa da yarbanci ta hayayyaqowa
Addahn, wato da gani fadan a duhu akeyinsa dan babu me gane yaran wani a cikin su
gefe kuma ga Nurses biyu da suna ta faman bada baki amma ko wacce ta kafe taqi
haqura.
Cikin radadin Azaba Bashir ya juya ya fita daga dakin dan har seda ya cire takalmin
qafar da ruwan ya zuba. Kai tsaye dakin likitan da yake duba Amirah ya nufa yana
dingisa qafa suka ci karo dashi a hanya
βYawwa Engineer wannan wace irin mata ce ka kawo mana gaba daya tazo ta tayar wa da
mutane hankali kamar ta manta Asibiti tazo? Muji ka fita da ita kuma karta sake
dawo mana. Kai itama matar taka bari kawai a rubuta muku sallama idan yaso ta ringa
zuwa daga gida ana dubata kawaiβ Likita ya tare Bashir tun kafin shi yayi masa
magana.
βKa taimaka ka fara dubamun qafata farko ruwan zafi suka watsa munβ Bashir ya fada
yana zama a kan kujerar dake gaban Office din likita, se likitan yayi saurin
durqusawa ya kama qafar yana haskawa, Dakin wanke ciwo suka tafi Allah ya so shi
qunar iya sama ce dan haka magani kawai aka saka mishi ya rubuta masa wanda ze siya
yasha sannan ya gaya masa ya dan dakata da saka takalmi saboda karya takura fatar
ta kwaye.
Saboda baqin ciki ko dakin be sake komawa ba yayi tafiyarsa gida a ransa yana
ayyana irin abinda zeyi musu daga Addan har Amiran idan