Showing 192001 words to 195000 words out of 238465 words
qaro karatu”.
“Sanda Mahaifinku ya mutu Allah ya jiqansa watan mu biyu da fita takaba na daura
aure da Modibbo dukda shekaruna ba kuma nayi aure dan wata buqata ko jin dadi bane
Aa nayi ne dan samun lada da cika wasiyyar mahaifinku seke yanzu da quruciyarki
zakice bazakiyi aure ba.
Me kika dauki kanki ne Asma’u? Gaba daya fa shekarunki Talatin da shida ne a duniya
dan kinyi aure da wuri kin tara Yaya ne yasa kike daukar kanki kamar wata uwar mata
kome? A yanzu fa da akwai yammata Sa’anninki dama wanda suka girme miki da ko auran
fari basuyi ba ballantana kice kin kai shekarun da maza bazasu so ki ba.
Ina da duk labarin wadanda suke sonki ai, ba’a rufa sati ba har nan Yayanku ya rako
wannan yaron Yusuf ya gaishe ni sannan a nan ma Himu dan gurin Addah Sadiya (Yayar
Goggo ce) yayiwa Yayanki Muslim magana shi ya dakatar dashi shi yasa ma bakiga yazo
ko ya kiraki ba.
To ki tsayar da hankalinki wallahi daganan zuwa a sallace ko ki fitar da miji ko ki
tattara ki koma can gidan ku ki zauna dan bazan lamunci zamanki a bariki ke kadai
ba aure babu wani Muharrami, ke ko kunya ma bakyaji yanzu a fara sallama da Amina
ke gaki uwarta babu aure wa ze dauke ku da muhimmanci ma”.
Baki na tura jin daga maganar arziqi ta koma fada kuma. Jifa kuma inda ta juya wace
Amnan za’ayi sallama da ita yanzu fisabilillahi? Ni dana san ma wannan maganar zata
tayar da tunda ta kira na bata uzurin ina waje idan naje gida na kirata.
Fadan ta taci gaba dayi dan itama fa Goggo akwai Mita in ta kama zance daya, daga
qarshe ta rufe da zancen kwashe kayana na gidan Bashir na Gombe
“Ko da Bashir din kuka daidaita ne naga babu wanda yayi maganar kwashe kaya ko kuma
kin bar masa ne ban sani ba? Daman cikin satin daya wuce ya kirani yana wasu soki
burutsun banzansa nidai ban bashi fuska ba” ta fada.
Se a sannan ma tuna ma da inada wasu kaya a gidan Bashir na Gombe , cikin qaguwar
karta kuka daddago wata maganar nace
“Za’a kwashe Goggo, kinga ai bamu zo gari ba muqullin kuma yana nan tare dani
shiyasa, amma da munzo hutun sallah in Allah ya yarda za’a kwashe”
“To yadai fi dan karma naji wani zancen kome ko wani Abu indai ba kuma haka Allah
ya qaddaro ba gara ayi addu’a Allah ya hada kowa da rabonsa na Alkahiri”.
Wani iri naji, wato duk yanda take son Bashir yau da kanta take cewa babu zancen
kome gidan sa lallai Bashir ya bata rawar sa da tsalle.
Sallama mukayi, jafar ya dauki qatuwar Trolly muka fara zuba kayan da muka zo siya.
Can gurin da ake ajiye su nama muka ci karo da Bashir da Aliyu daga uban har dan
kowa ya kalli gefe ya tura baki sama kome suke jira oho ga dai trollyn da suka fara
zuba kaya nan a gabansu.
Kallo daya nayi musu na mayar da hankali na kan Freezer na fara ciro abinda nake da
buqata ina sakawa a cikin Trolly, gaba daya hankali na ya tafi a abinda nakeyi se
jin magana nayi daidai kunnena har seda na tsorata na dago da sauri muka hada ido
da Bashir dake tsaye dab dani.
“Meye haka zaka tsoratani” na fada ina harararaa qasa qasa, se ya marairaice kamar
wani yaro yace
“Ma’u me yasa bakya amsa kirana? Idan na turo miki saqo ma bakya bani amsa me nayi
miki dan Allah?”
Kallonsa nayi tareda jan gajeran tsaki se kawai na juya ina cewa Jafar
“Muje, in suka bar gurin se mu dawo”
“Kiyi hauwa dan Allah ki tsaya, kinga muma shopping muka zo gaba daya na manta
abubuwan da kike siyo wa na taho da Aliyu yace shima be sani ba” Bashir ya fada
yana shan gaba na.
Se na tsaya ina kallonsa a raina nace
“Tunda ba kai kake siyowa ba ai daman bazaka sani ba”
“Dan Allah Ma’u” ya katse mun tunani kamar ze durqusa mun tsabar yanda yake kwantar
da murya. Ni mamaki ma yake bani wai Bashir dai me kamar Boss shine yake karya
murya haka yana roqona ashe daman ya iya ikon Allah.
Ba tareda na kalle shi ba nace
“Me dame zaku siya”
“Duk abinda ya kamata na girki saboda Azumi banda kayan abinci da mai” yayi saurin
bani amsa.
Tare muka ringa zagayawa, ina da list dina a kai dan haka komai na dauka se Aliyu
ya daukar musu ina kallonsa se bata rai yake haka tunda ya gaishe ni be sake magana
ba kamar wanda akayiwa dolen zuwa.
Siyayya mukayi da yawan gaske dan daman ni abinda ya kawoni kenan cefanen mu yayi
qasa sosai, da mukaje gurin biyan kudi na zaro ATM dina zan bayar yayi saurin
tarewa ya miqa nasa ban ja ba na maida abuna Aljihu ai daman tare zamu ci da
Yayansa.
Seda aka loda mana kayan mu tsaf a mota na kalleshi fuska a sake nace
“Baban Ali se da safe toh a gaida Iyali mun gode” na kama murfin motata zan shiga
ya riqe yana cewa
“Dan Allah ki unblocking dina, kuma koda wani layin na kira bata shiga ki taimaka
ina so muyi magana ne tunda kin ce bakya so nazo gida”
“To shikenan zanyi” na fada bawai dan zanyi da gasken ba Aa dan kawai ya qyale ni
na tafi. A tare muka jera ina gaba yana bayan mu har gida.
Ina shiga na tarar da an kawo mana kayan dinkinmu na sallah. Seda muka gama jera
siyayyar da mukayi kafin na fito da kayayyakin nawa ne dana Amnah da Farida ina
dubawa nace
“Yaushe aka kawo kayan?”
“Kuna fita yazo, yace nasu Aliyu se wani satin za’a kawo wai Be gama wadanda aka
kai daga baya ba”.
Wani shegen Lace na daga ina dubawa da mamaki dan dai nasan babu shi a kayan dana
bayar dinkin sena kalli Amnah nace
“Wannan kamar ba namu ba inaga Hassan ya rikice ya sako mana kayan wasu, miqo mun
wayata na kirashi naji”
Wayar ta bani na shiga kiran Hassan Tailor, seda muka gaisa yake cemun nayi haquri
fa be hado dana mazan ba ya bari ne a gama dukka saboda na baya da Alhaji ya kai
sune ba’a qarasa ba.
“Wane kaya aka sake kawowa kuma Hassan? Sanan naga qari akan namu ma inaga na wasu
ne ka hado dasu fa”
“Aa Hajia dukka Alhaji ne ya kawo su wancan satin ai” ya bani amsa.
Sallama mukayi ina ta mamakin wai Bashir ne ya kai, ashe yasan shagon Telan kai
abubuwan mamakin nasa dai suna da yawa.
An kama Azumi Ramadana, yanda nake fita aiki na dawo a nutse har na kama wasu
ayyukan gida yana bani mamaki. Sena tuna Azumin da suka wuce tun bayan dana fara
aiki haka nake fita hayyacina kafin sallah kuwa sena zabga uwar rama saboda aikin
gida dana office ga Bashir da tsurfa kala kala haka zan dawo nayita dora tukwane
ina saukewa wannan karon kuwa Allah ya hutar dani, ga Amnah a gida ga Baba Harira.
Ita take zuwa duk azumi take tayamu da aikin kunu da qosan sadaka yar uwar mijin
Anty ce anan Lagos suke ta hadani da ita. Wannan karon ma tun ana saura sati daya
na kirata randa za’a dauki azumi kuwa se gata tazo, daman haka take zuwa se zamu
tafi Gombe sallah kafin ta tafi shiyasa nake samun hutu dan kafin na tashi aiki na
koma gida ma sun gama hada mana komai na shan ruwa.
Ranar Talata an kai azumi na goma sha daya, an shiga goma ta wuya in ji hausawa
aikuwa dai ranar naji wuyar gashi akayi sa’a ranar naci uban aiki a office se kusan
qarfe biyar da rabi na kama hanyar gida qarshe ina shiga ana kwada kiran sallar
magriba.
Na samu har an fitar da abincin sadaka can masallacin da ake kaiwa ga kayan shan
ruwa nan da suka hada sun shimfida babbar ledar cin abinci a qasa dukka yaran suna
gidan harda Aliyu yau dan shima wani baqin rai yake ji dashi idan yazo sau dayan
nan muka gaisa bana sake ganinsa yana can gidan su yana neman fitinar kakarsu.
Muna shan ruwa Yusuf ya kirani, bamu jima muna magana ba mukayi sallama yana
jaddada mun cewar duk buda bakin da zeyi seya kai sunana gurin Allah ina dariya.
Mun je sallar Asham muna dawowa na hadu da Bashir daya coge a qofar gidan mu da
gani gudowa yayi daga masallaci dan ana idarwa muka taho kafin maza su fara fitowa.
“Ma’u dan Allah ki saurara zamuyi magana” ya fada yana matsowa inda nake.
“Baban Ali an sha ruwa lafiya?” Na fada fuska a sake ina harde hannu a qirji, seya
shafa kansa yana cewa
“Ba lafiya ba, a taqaice ma ni ban sha ruwa ba. Amirah bata da lafiya sosai jikinta
ya sake tashi, Addah kuma kinsan bata iya irin abincin da nake ci ba, ni duk ba
wannan bama Ma’u dan girman Allah, dan darajar watan nan da muke ciki kiyi haquri
mu komawa auran mu.
Wallahi nayi madamar duk abinda na aikata kiyi haquri kuskurene kuma bazan sake ba.
Gaba daya rayuwata da sukurkuce babu abinda nake ganewa Ma’u.
Tunda kika tafi rabon da nayi bacci me dadi, a kullum cikin Yunwa nake wuni daidai
da dakina sedai idan na gaji da kaina na gyara gaba daya gidan ma ya hargitse babu
gyara babu qamshin ki Ma’u.
Gaba daya Azumin nan da akayi dore nakeyi kuma idan an sha ruwa ma dakyar nake
samun abinda zan iyaci wani lokacin ma se yara sun tafi da abinci daga wurinki nake
samun wanda zan karya Azumi na Ma’u, amma ki dubi Allah ki duba yaran mu kiga irin
rayuwar da suke tsakanin gidaje biyu bayan muna da damar da zamu zauna taredasu a
inuwa daya, na gaji da watangaliliya Ma’u ina buqatarki a kusa dani ki dawo ki
tallafi rayuwata”.
Baki na bude kawai ina kallonsa, shifa Bashir bama shi da kunya wallahi wai na
tallafi rayuwarsa.
“Wai ni Baban Ali me kake nema dani dan Allah? Saki na fa kayi akan matarka saboda
naqi nabar aiki na koma gida ita ta dawo kusa da kai kace naje na zauna da aikin ko
ba haka mukayi ba?
Me yasa baka duba yayan ba a lokacin da ka bani kwana daya rak akan in bar maka
gida zaka zubawa Amaryarka sababbin kaya?
Meyasa baka duba makomar su ba lokacin daka zo har cikin gidana kaci mun mutunchi
nida Yan uwana ka kwace yayanka duk a sannan baka san zasu ringa yawo tsakanin
gidaje ba se yanzu da ka sheqa kaga babu riba sannan zaka zo kace mun wai kayi
nadama inyi haquri na koma gidanka?
Bari kaji nasan me kake nufi, ba wai kana bani haquri bane saboda ka yarda kayi
kuskure Aa kanayi me saboda ka gaza samun yanda kake so a gidanka. Dama kai ai
babbar matsalarka a rayuwa cikinka ne koda iya wannan aka barka dole ka shiga
garari wato ga Asma’u girkau ko in dawo in ci gaba da dafa maka kana ci tunda
matarka bata yi.
Ba rashin gyara ba Allah yasa bola gidan ka ya zama wannan ku ta shafa bani ba kuma
daga yau zan ja wa masu kawo maka abincin kunne wallahi ko yunwa zata kashe ka
sedai ka mutu amma badai ni in dawo gidan ka in dafa maka abinci ba.
Kai bari kaji Bashir daga rana irin tayau kar na sake ganin qafarka a qofar gidan
nan idan ba haka ba na rantse da Allah sena maka rashin mutunchin da ko a hanya
muka hadu bazaka mun kallo biyu ba.
“Ma’u fata kike mun na mutu? Ke da kanki yau kike kira mun mutuwa?” ya fada cikin
mamaki har yana kama baki, na galla masa harara dan da gaske na harzuqa da wannan
rainin hankali na Bashir nace
“To ka mutu mana ina ruwan wani ni ina da Asara ne? Meye hadina da kai Ina Yaya ne
to Allah baze hana ni yanda zan riqe su ba in ka mutu matar ka da yan uwan ka ne
sukayi Asara bani ba.
Ka fita a harkata aure ne dakai na gama bazan koma ba ka fita a rayuwata malam idan
kuma dan kana ganina a kusada gidanka yasa ka samu damar uzzurawa rayuwata toh se
in tashi dan kasan gurin zama a Lagos ba wahala ze mun ba” ina gama fadar haka na
wuce ciki na barshi a tsaye kamar an dasa shi.
Ina shiga na hau kan yaran da fada.
“Wallahi duk wanda ya sake diban abinci ya kai gidansu sena ci ubansa kuma sedai ya
koma can ya ringa ci” na fada ina nuna su gaba daya.
“Toh Mami na sahur fa muke tafiya dashi” Jafar ya fada, daman nasan shi yake diba
ai kuwa na hayayyaqo masa ina cewa
“Tunda ubanka ne ya siyo ya ajiye mun dole ka ringa guzuri kana kai masa ai, to
bari kuji na shan ruwan ya isa can kuci na sahur a gidan ku idan ba haka ba wannan
din ma wallahi zaku jawo in hana kai gaba daya ma se ku tattara ku koma gidan ku
kar wanda ya sake zuwa ya takura mun anan”
“Yanzu Mami saboda kawai an kaiwa Babanmu abinci shine kike fada naga wasu can ma
zuwa suke ki dafa musu su tafi dashi shine mu Babanmu zaki hana mu bashi” Aliyu ya
fada yana ture kwanan gabansa.
Sena juya kansa a fusace nace
“Na hana idan kuma ka isa ka diba ka kai masa kaga yanda zanyi maganin duk wata
fitsara da kakeji a ita, saboda kaga na qyaleka kwana biyu kana iskancin dakaga
dama ko shi yasa to mu zuba ni dakai ai ka sanni ba kuma chanzawa nayi ba”
Miqewa yayi fuskar nan kamar ze fashe tsabar fushi ya nufi qofa
“In na sake ganin qafarka ma a gidan nan ma sena bata maka rai uban yan baqin
zuciya kawai, baza’a bawa uban naka abincin ba idan kunyi zuciya ku auro masa wadda
zata zo ta ringa dafa masa” na fada ina wucewa dakina.
Duk sukayi tsuru suna bina da kallo ganin yanda na horance musu. Ina ciki aka
qwanqwasa na bada izini aka shiga.
Baba Harira ce ta samu kan kujerar dake dakin ta zauna tana cewa
“Kiyi haquri Uwardakina shi yaro ba’a masa haka. Be kamata ki ringa musu haka akan
ubansu ba se su qullace ki bayan su bazasu gane abinda yake tsakanin ku ba.
Kinga ban tsawaita da son jin dalilin mutuwar auranku ba duk da nayi jimami kwarai
amma shi aure ana zaune lafiya ma in Allah ya kawo se kinga an rabu amma dan Allah
koma menene ki dena nunawa a gaban su. Zancen abinci kuma uwata ai sadaka ce idan
an bashi ba’a fadi ba”.
“Baba Harira ki qyale wannan mutumin kawai ai bashi kadai bane da matarsa a gidan
da surukarsa me yasa baza su dafa su bashi acan ba shine dan bashi da kunya har ze
tareni yana gaya mun se an kai daga nan yake ci to wallahi kar ki sake bari su fita
da abinci, in dole se sunyi sahur din su fito da Asubar suzo suci anan”.
Ganin da tayi dagaske raina a bace yake yasa ta tashi ta tafi tana qara nanatamun
da nayi haquri. Tsaki na ringa saki ni kadai, nama rasa takamaiman bacin ran nawa
na menene? Cewar da yayi na koma gidansa ne ko kuwa wani abu daban?
Anci sati biyu cikin Azumi yara suka fara jarabawar term, randa aka kai azumi na
Ashirin da shida suka gama daman tun ana saura kwana biyu su qare na turawa da
Bashir saqon cewar zamu tafi Gombe da yaran dan qila shi ba zuwa zasuyi ba idan ma
zasuje ina so ni na tafi tareda yaran saboda akwai bikin qanne na maza biyu da
za’ayi sati daya da sallah.
Ina tura saqon ya maido mun da amsar ya yarda daman ta ina ze hana shida yake neman
hanyar shiri dani yanzu kam shishshigigi da cusa kai ba irin wanda baya yi mun.
Ana ibi zamu tafi sega Hotunan tikiti ya turamun ta whatsapp, na budesu na duba na
zuwa ne kawai yana tambayar yaushe zamu dawo ban amsa ba na kashe Datar na sauka a
raina nace
“Kudina sun huta tunda ba roqar ka mukayi ba”. Kiran Yusuf ne ya shigo mun na daga
muka gaisa yana mun qorafin qarin kwanakin da suka samu dan tun satindaya wuce ya
kamata su dawo amma yanzu se ranar sallah.
“Yaushe ne tafiyar taku zan saka ayi muku booking jirgi yanzu” ya fada
“Ai an hutashsheka ma, kaga babansu ya rigada ya siya yanzu naga ya turo mun dasu”
na bashi amsa.
“Bazaku hau ba, qarfe daya gobe za azo a kai ku Airport” ya fada ta sigar bada
umarni kana ji kasan kishi ne cunkushe a qasan ransa.
“Ranka ya dade ya rigada ya siya, a daga mana qafa daman iya na zuwa ne idan zamu
dawo se mu hau naka”.
Shiru ya mun be amsa ba seda na sake magana kafin ciki ciki yace mun
“Shikenan, Amma Asmy bana son wata alaqa tsakanin ki dashi dan Allah, nasan ze
ringa fakewa da Yaransa idan na abinda ya zama dole ba babu ke babu shiga sabgarsa
kinji?”
“Naji baza’a kuma ba, to ka saki ran mana se wani magana kake kamar Boss” na fada
cikin sigar tsokana a qasan raina kuwa nace
“Ji mutum se kace ka aure ni irin wannan doka haka”.
“Baki san yanda nake kishin ki ba ko? Ki bari se randa Allah ya mallaka mun ke,
ranar zaki san yanda ake tattala abinda ake qauna daga lokacin duk wani namiji da
zeyi magana dake to ina tsakani” ya fada
Dariya nayi ina cewa “Allah ko to sannu sarkin kishi”
“Asmy se ana sonka ake kishin ka ai ko baki san haka ba? Ke daida bakya sona daman
bazakiyi kishi na ba in kuma kin sona to ki fada yanzu naji
“Shikenan dai, yanzu zan kwanta saboda mu tashi da wuri dan bamu gama hada kayan mu
ba” na fada ba tareda na bashi amsar tambayarsa ba.
“Yawwa gara dana tuna, idan kun isa Gombe za’a kawo kayan sallar su Abdallah. A
Kano na bada dinkin da suka gama kuma kaitsaye Abuja suka tura se kawai nace a
kaiwa Alhaji Tukur qilan ma ya riga ku isa yanzu”
“Kayan sallah kuma kaida kake da hidimomi da yawa ina kai ina qarawa kanka wasu?”
“Bana jin dadin abinda kike mun duk sanda nayiwa yaran nan abu. Qiri qiri kike nuna
bakya sona Asmy da ina da zuciya nima da tuni na haqura dake amma na kasa, tunda
dai bake nayiwa ba se ki barsu su karba in kuma bazasu saka ba to ki zubar kawai”
ya fada a dan fusace.
“Ni fa sam ba haka nake nufi ba gani nayi kwata kwata yaushe ka kawo musu waccan
tsarabar duk basu saka bama suna nan daman sallah muka barwa amma kayi haquri bazan
sake ba, sun gode Allah ya qara budi” na fada cikin sigar lallashi.
“Da nayi niyar yi miki tsarabar Dogayen riguna tunda naga kina son su, yanzu nake
so na fita na siya muku keda Intee amma kin jawowa kanki na fasa nata kadai zan
siya”
“Haba mana na fa ce