Showing 174001 words to 177000 words out of 238465 words

Chapter 59 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

bega amfanin zaman nasa ba dan bazasu iya yi
masa maganin abinda yake damunsa a yanzu ba.

Suna haka yaji an turo qofar yaran suka shiga, a jikinsa yaji Asma'u tana kusa
dashi be gama tunanin ba kuwa ya daga kai kenan yayi kyakykyawan gani daya saka
zuciyarsa ta tsallake bugu.

Har suka shigo cikin dakin idanunsa akansu, yanda take zabga murmushi shi kuma yana
mata rada seka rantse da Allah su kadai ne a cikin dakin dan babu alamar wai suyi
tunanin wasu na kallonsu.

"Qut" ya hadiye wani abu me tauri, lokaci daya idanun yan maza yayi jajir kaman
wanda yasha duka, Fuska a washe Yusuf ya miqa masa hannu yana cewa

"Barka da dare Engineer, ya jiki kuma? Allah yasa kaffara ne"
Kallon Yusuf din yayi ya kalli fuskarsa, gaba daya ma se ya kasa bude baki dan ji
yayi kamar an saka masa tsumma a a bakin, Yusuf da ya ga bashida niyyar bashi hannu
ya janye yana murmushi ya waiwaya kan Amirah da itama tayi kinini da fuska yace

"Madam yame jiki? Allah ya qara sauqi toh".
"Amin" ta amsa can qasa dan gani tayi ya mata kwarjini kafin ta wurga ido gefen da
Ma'u take tsaye kaman anyi mata dole tace

"Anty Ina wuni?"
"Lafiya lau, ya me jiki?" Asma'u ta amsata ba tareda ta kalle ta ba.

"Baban Ali ya qarfin jiki? Allah ya qara afuwa" Ma'u ta fada tana kallon Bashir
daya zubawa Yusuf ido ganin yanda shi Yusuf din ya kafe Ma'u da wani mayan kallo
kamar ze cinyeta.

Ji yakeyi kamar ya tashi ya shaqe Yusuf din kowa ma ya huta, yanzu da wannan
kwalliyar ya dakko ta suka taho yana shaqar qamshin turaren? Abinda yake mallakinsa
yanzu suke rabawa tareda Yusuf din.

"Asmy muje ko? Dare yana yi kuma kinga ko zama bamuyi ba muka taho" Yusuf ya fada
cikin kwantar da murya kamar me magana da yaro, murmushi Ma'u tayi masa ta fara
tafiya tana cewa

"Allah ya qara sauqi, Aliyu ku debo kwanukan safe ku taho dasu" tayi gaba abinta ba
tareda ta sake kallonsa ba se yaran suka miqe suna yi masa seda safe suka fice gaba
daya banda Aliyu.

"Zoka kwashe wannan abin daya shigo dasu" ya fada yana nuna masa ledar Fruit da
kajin da Yusuf ya siyo ko yaya akayi ya gane shi ya siya se Allah.

Juyawa Aliyun yayi ya kalli Uban kafin ya bankawa Amirah harara ya juya ya fice
abunaa ba tareda ya dauke ledojin ba.

"Kana kallonsa yana hararata ko? Wallahi sena ci uhan yaron nan zamu koma gida ne.
Daman jiya ni kadai suka bari na kwana a gidan ka kirasu ma ka gaya musu..."

"Tashi ki fita" ya fada a tsawace har seda ta zabura ta miqe, har tayi gaba ta koma
ta dauki ledar kazar tana cewa
"Idan bazaka ci ba ni na dauka dan daman banyi girki ba dazan fito" tayi gaba
abinta tana ci gaba da qunquni.

Samuel da tuntuni yake jiranta a reception ya miqe rai bace ya fita tana binsa a
baya, a kusan tare suka isa gida dasu Ma'u, saboda bala'in sa ido a qofar gidan ta
tsaya.

Tana hangen Ma'u da Yusuf suna magana kafin sukayi sallama ya shiga motarsa Driver
yaja suka wuce.

A kan kujera ta jefar da dankwali da jakarta ta zauna, gaskiya bazata sabu ba, ta
yaya za'ayi ace daga rabuwar Ma'u da Bashir har ta samu madadinsa kuma dan gayu me
kudi da take ganin kamar yafi Bashir din komai da komai wai me yasa a duk sanda
take ganin ta taddo Ma'un seta sake tsere mata ne?

Dole ta tashi tsaye, bazata zuba ido tana kallo Asma'u tayi gaba ba, tunda har ta
rabu da Bashir tana fatan ta qare rayuwarta a haka tana kallonta a matsayin da da
ita take kai(Fata na gari lamiri Amirah )

ASMA'U
A qofar gida muka tsaya bayan da yara duk suka shige ciki, Kallona kawai Yusuf yake
yana murmushi har seda na gaji nace

"Ni zan tafi dare yayi kuma gobe ina da aiki"

"Toh agogo, ni ban gaji da kallonki ba ai" ya fada yana gyara tsayuwa.

"Ai kuwa an kusa rufe gate kaga kwanan mota ya kamaka yau a cikin Estate" na fada
ina juyawa kamar zan tafi yayi saurin shan gaba na yana cewa
"Haba hajjaju ki barni mana na kalleki, gobe fa zan tafi se nayi sati daya ban sake
ganin fuskar nan taki ba".

Kamar yarinya haka na tura baki ina hararar sa qasa qasa, se ya faramun dariya yana
cewa

"Kinga Asmy ta tana dawowa yanda na santa a hankali, shikenan ki shiga ki kwanta
kiyi bacci amma fa kiyi mafarki na".

Murmushi nayi masa na kauce ina cewa "seda safe mun gode da zuwar mana dubiya kuma"

"Dole na dubashi dan kinsan yanzu banida masoyi sama dashi, tunda ya iya sako mun
ke ai ni ya gama mun komai a rayuwa. Ina ga gobe ma zan koma na sake dubashi kafin
na tafi"

"Allah ya yafe maka" na fada ina bude qofa se yayi saurin dakatar dani ya koma
gurin motar sa, wata yar qaramar leda ya miqo mun na karba ina mamakin meye wannan
a ciki dan qanqantar ta tayi yawa".

Godiya nayi masa na wuce, ina jin yanda yake bina da kallo har na shiga gida na
kullo qofar kafin ya shiga motarsa suka tafi.

Ban tsaya ba na wuce dakina dan yaran da alama sun kwanta ma, ian shiga na zare
rigar jikina ya rage Doguwar riga ta roba me siririn hannu da na saka a ciki na
fada kam gado na zazzage ledar da Yusuf ya bani.

Yan qananan akwatuna ne suka fado guda biyu, na dauki na Farko na bude, wani
hadadden zobe ne a ciki tsabar handa ya burgeni ban san sanda na ciro shi na zura a
hannuna ba yanda ya zauna seka rantse an gwada ni kafin aka qera shi, juya hannun
na ringayi ni kadai ina murmushi.

Kamar ya sani ina son zobe musamman wannan ya tafi dani, dutseb da yake ka sa ma se
na ga kamar Diamond wallahi amma ya za'ayi Yusuf ya siya mun Diamond ring.

Dayan akwatin na bude shi kuma yan kunnene qanana sosai maqale dan kamar zallar
dutseb nema akayisu dashi, ban bata lokaci ba na cire na kunnena na saka su.

Qanana ne sosai amma idan kaga yanda suka yi kyau a kunnena seka dauka wani babban
dankunne na saka. A daren nan na ringa daukar hoton kunnena da zoben, na rasa wa
zan nunawa ina shiga whatsapp naga Alawiyya a online ban bata lokaci na kuwa na
tura mata da hotunan se gashi ta kirani ina dagawa ta fasamun ihu a kunne tana cewa

"Ma'u Allah ya bamu ya taki, kin shiga zawarci da qafar dama. Ashe ina da rabon
ganin Diamond ido da ido a duniya ai kuwa zanzo kallo a cikin satin nan".

Dariya sosai na ringayi, indai tsokana ce ka samu Alawiyya ka gama, ban gama
dariyar ba ta sake cewa

"Gobe idan zaki aiki ki saka hannun nan a gaba yanda kowa zega menene a jiki su san
fa Yar uwata ta faso gari wallahi"
"Aa cire hannun zanyi nakai Museum kawai kinga afi zuwa kallo dakyau" na fada mata.
"Ke tsaya ma wai waya baki ni inata murna ban tambayeki ba, ko da yake qila nasan
Yarabawan Lagos din nan ne ko kin san daman ance sun iya kashewa Mata kudi kamar
hauka, nidai dan Allah ina daga gefe ki ringa tunawa da yar uwarki kinji"

"Allah ya yafe miki Alawiyya, ni seda safe wai ina Baban Dija kiketa wannan ihun a
daren nan?"

"Ni ki gaya mun dan Allah wa kika samo mana" ta fada tana marairaicewa, kamar an
fizgo maganar daga bakina se ji nayi nace mata

"Yusuf Wunti ne"

Ta buga ihu har seda nayi saurin cire wayar daga kunnena ina jiyo yarinyar da take
goyo Afifa ta fasa kuka da alama itama ta tsorata.

"Wallahi a satin nan se nazo Lagos wannan maganar bata waya bace kai Allah na gode
maka Allah na gode maka, kwanta kiyi bacci yar uwa qila gobe ki ganni kawai dan
bazan iya jira ba" Ta fada cikin tsananin murna kamar wadda akayiwa kyauta kafin ma
nayi magana ta kashe wayarta, murmushi nayi a fili nace

"Allah ya shirya ki Alawa"
Har na ajiye wayar se kuna na janyota na shiga rubutawa Yusuf saqo

"Nagode kwarai amma da baka wahalar da kanka ba"

"Zan iya kira?" ya dawo mun da amsa, kamar nace Aa se kuma zuciyata ta ce mun baze
ji dadi ba dan haka na mayar masa da amsa
"Eh" se gashi kuwa ya kira din.

"Bana so na kira ki fara mun qorafin bacci zakiyi amma da bamuyi magana ba nasan ni
yau sedai nayi kwanan zaune kawai" ya fada a hankali.

"To ai yanzu seka kwanta tunda munyi magana"

"Yanzu kuwa ranki ya dade, karki manta kiyi mafarkina zan kiraki da safe ki bani
labari".

Haka mukayi sallama na kwanta rigingine ina tunani, yanda Yusuf yake yi mun tamkar
wasu saurayi da budurwar da suke kan ganiyar soyayya ganai nakeyi kamar ma ya manta
da na taba aure harda tarin Yaya.

Ian daga kwance ina ta faman saqa da warwara, idan naji kamar zuciyata zata karbi
tayin Yusuf se kuma dayar ta bijiro mun da Bashir, ganin kaina na neman yayi ciwo
yasa na tattara su duka na watsa gefe na gayyato baccin dole ina ta kallon zoben
hannuna da yake qyalli a cikin duhuj dakin.

Zumbur na tashi na zauna na kunna fitilar wayata na haska cikinzoben sosai, tunawa
nayi a jikin akwatin naga wani Rubutu kamar Letter A da Y anyi musu wani irin
design daya ta shiga cikin daya kuma kamar na hango hakan a cikin dutsen ma ina
haskawa kuwa sega wasu qanann rubutu da seka nutsu sosai zaga gansu cikin dutsen
'Yusuf loves Asma'u' aka rubata, kamar yarinya haka na qanqame hannun nan nayi
bacci dashi.

BASHIR
Wani irin zafi da ciwo zuciyarsa ta ringayi masa, a da tuna kalmar saurayi da Aliyu
ya gaya masa kadai take tayar masa da hankali a yanzu daya Gansu a tare bashi da
buqatar qarin bayani fuskokinsu kadai sun isa shaidar alaqar da take a tsakaninsu,
yanzu daman Asma'u zata iya son wani namiji a rayuwarta bayan shi??
Yanzu harta manta da rayuwar da suka gina tsahon shekaru a yan kwanaki ta iya
mantawa dashi ta karbi tayin wani Namiji bayan shi abinda ko a mafarki be taba
tunanin faruwarsa sannan har ta iya zuwa gabansa dan ta nuna masa cewar a yanzu fa
baya gabanta ta tigada ta gama da shafin rayuwarsa gaba daya.

Dafe qirjinsa yayi saboda azabar ciwon da yake masa, tun yana zaune har seda ya
kwnata saboda yanda wani ciwo ya masa rubdugu lokaci daya ya shiga numfarfashi
kamar me shirin mutuwa, hankali tashe Likita da Nurses suka rufu akansa domin ceto
rayuwarsa.

Seda sukayi dagaske kafin bacci ya dauke shi dan fizge ruwan da aka daura masa ya
ringayi seda Likitan ya sake gayyato wani suka hadu suka danne shi Akayi masa
allurar baccin a jiki kafin ya kwanta lakwas yana kiran
"Asma'u karki rabu dani, wallahi ina sonki Ma'u karki zabi wani a kaina"

Cikin dare ya farka cikin ikon Allah jikin ya masa sauqi nauyin da qirjinsa yayi
masa dazu ya sauka, kulolin daya gani suka tuna masa da yunwar da yake ji nan da
nan ya janyo kwanukan ya bude.

Tuwon shinkafane da Miyar danyar kubewa dataji naman rago da manshanu.
Ba maganar wanke baki ya zuba ya fara ci loma biyu yayi kamar qaramin yaro ya fashe
da wnai irin kuka irin wanda yake bayyanar da quncin da zuciya take ciki ya kifa
kansa a qasa ya ringayi.

Likita ne ya shiga dakin dan yayi hasashen yanzu ya farka dan yaga jininsa nada
qarfi Allurar bata dadewa take sakinsa yana shiga ya tarar dashi yana kuka ya isa
gurinsa da sauri ya dagoshi yana cewa

"Subhanallahi meya faru badai jikin bane? Wane guri yana maka ciwo ne?"

Saitin zuciyar sa ya nuna masa, likita ya kamashi ya koma kan gadon kafin ya shiga
hada na'urar dake jikin gadon ze sakawa Bashir din sw ya dakata jin Bashir din yana
cewa

"Ina sonta Dr, bana so na rasata na rasa yanda zanyi ni na bata komai yanzu kuma
bansan ya zan gyara ba".

Zama Likita yayi a kusa da shi ya zare farin gilashin idonsa yana kallon Bashir
yace
"Daman Mace ce damuwarka, Wacece ita?"

"Asma'u, mata ta ta farko kuma uwar yayana. Likita banaan ya akayi shedan yayi mun
kururuwa ba nabi rudinsa na rabu da ita wallahi ina son matata amma duk duniya kowa
ya kasa fahimtata".

Shiru Likita yayi yana kallon Bashir na wani lokaci kafin ya dakko kwanon da ya
saka abinci ya miqa masa yana cewa

"Kaci se muyi magana, ina zuwa" ya tashi ya fita ya barshi.

Tura abincin kawai yakeyi, wani bangare kuma yana jin kamar ya sauke nauyi daya
furtawa wani cewar yana Son Asma'u. Amma me yasa likita ya tafi ko dai shina be
yarda yana son nata ba kamar yanda kowa yaqi yarda dashi?

Haka ya ringa tura abincin har ya gama yasha ruwa sega Likitan ya sake shigowa
hannunsa riqe da wata farar roba da gani ta magani ce.

Robar ya bude ya debo kwayoyi qanana guda biyu ya miqawa Bashir yana cewa
"Kasha, ze taimaka maka ka samu sauqin ciwon qirjin".

"Likita kaima baka yarda ina sonta ba ko? Kaima kana ganin bada gaske nakeyi ba"
Bashir ya fada ganin Likita na qoqarin sake fita bece masa komai ba, se ya waiwayo
yana murmushi yace

"Bani zaka gayawa ba Malam Bashir, shawara daya zan baka In dai kana so kaci gaba
da rayuwa me dadi ka sauke duk wani girman kai ka nemi abinda kake so. Ita mace
ba'ayi mata gadara ka hanzarta kafin lokaci ya qure maka, gobe da safe zamu sallame
ka in Allah ya kaimu tunda na fuskanci ciwon so ne yake damunka mu kuma bamu da
maganinsa sedai mu baka shawarar yanda zaka sauqaqawa kanka indai ba kana so ka
saka kanka a hatsarin kamuwa da ciwon zuciya ba".

Haka ya kwana yana juya maganganun Likita a ransa, qarfe goma na safe aka bashi
sallama, kamar mara galihu haka ya tattara Samuel yazo ya dauke shi ya kaishi gida
sanda ya isa yar gasken da alama ko tashi daga bacci ma batayi ba se ya wuce dakin
sa shima ya kwanta akan gado yana ci gaba da saqe saqe.

Kiran Bala ne ya shigo wayarsa, kamar ya share sedai ya daga dan haushinsa yakeji
tun ranar daya katse masa kira be biyo baya ba se yau.

"Allah ya taimaki Engineer Allahh sa ban katse maka aiki ba" Bala ya fada yana yar
dariya.

Shiru ya masa be damu ba yaci gaba da cewa
"Gani a Lagos na shigo yanzu, idan anjima ka tashi aiki se na shigo nan ta gurin
ku"

"Banje aiki ba ina gida yau" ya fada a cunkushe

"Oh dan Allah? Ta bari yanzu naje na kama daki idan na ajiye kayana se na shigo
gidan, a sanarwa Madam dam ko Karyawa banyi ba na taho" Bala ya fada daga daya
bangaren, se Bashir ya ajiye wayar yana cewa

"Seka iso toh".

Wa ze gayawa tayiwa wani girki ko ya manta da wacce take a gidan sa ne yanzu yake
wannan maganar. Wanka ya shiga yayi, yaji dadin zuwan Balan dan yana da buqatar
wanda zasu tattauna akan lamarin Ma'u, baya so ya sake yanke hukunci ba tareda
shawara ba.

Se daya Bala ya iso gidan yaciyo uwar kwalloya kamar me zuwa daurin aure. A palour
suka zauna Amirah ta kawo masa ruwa da lemo daga nan ta shige daki basu sake jin
duriyarta ba.

"Mutumin wai Ina Ma'u ne banji labarinta a Gombe ba ko kun daidaita ban sani ba?"
Bala ya tambaya yana shan Lemo.
Bashir yaja tsaki yace
"Tana gidanda yake kusa da namu, kasan wai har Ma'u ta manta dani ta fara sabuwar
rayuwa tareda wani mutum daban bani ba" ya qarasa cikin jin zafin abinda ya ke
fadar.

"Dagaske kai amma naji dadi" Bala ya fada cike da murna se kuma daga baya ya gano
shirmen da yayi saboda yanda yaga Bashir ya zuba masa ido yana kallonsa se yayi
saurin wayancewa yana cewa

"Ina nufin naji dadi da kace tana kusa daku kaga yanda zaku fi samun daidaito da
wuri kenan"
"Bazata saurare ni ba Bala, idan ta ganni nunawa take kamar bamu taba hada komai a
rayuwa ba Ka bani shawara ya zanyi na dawo da Ma'u rayuwata Bala kai kafi kowa
sanin ina son Matata"

"Na sani Bashir amma yanzu yayi wuri da ka nuna karayarka, kafi kowa sanin irin son
da Ma'u takeyi maka na tabbata bazata taba iya rayuwa da wani namiji idan ba kai
ba. Ko kaganta da wani is sedai tayi dan ka gani rabka ya baci amma na tabbatar
badan wai tana son sa ko akwai wani abu a tsakanin su ba.

Ka qara haquri mutumina karka manta fa laifi tayi maka ka hukuntata idan ka karaya
yanzu ka bata qofar da a gaba zata taka ka yanda take so".

"Laifin me tayi mun Bala? Nifa nayi mata laifi na tirsasata yin abinda yake son
raina saboda taqiyi na yanke hukunci ba tareda tunanin abinda hakan ze jawo mana
ba.

Da bakina na saketa nace ta barmun gidana kana zaton zata manta wannan ta sake
dawowa gareni? Bafa abinda tayi mun son zuciyata ne kawai ya kaini da dana sani"
Bashir ya fada a matuqar karye.

Bala da yake faman antaya masa harara yayi saurin tareshi yana cewa

"A wata hudun shine har ka karaya haka kake nema ka zubarwa da kanka mutunchi haba
Bashir, kai kana zaton Asma'u zata iya zaman aure da wani ba kai ba wallahi ko
bayan shekara dari nasan kai zata zaba.

Kai duk duniya fa babu wanda besab irin son da take yi maka ba dan haka ka kwantar
da hankalin ka mutumina, in banda kai ma yanzu ga yammata nan a gari birjik basu
auruba se bazawara me yaya shida kake zaton daga rabuwarta dakai zata samu miji?

Ka saki jiki mutumina ka ci gaba da harkokin ka muna nan wallahi zata zo har cikin
gidan nan ta nemi ka mayar da ita".

Kallonsa Bashir yake har ya gama magana. Ko kusa bega alamar abinda Bala ya fada a
wannan karon me yuwu ba bane amma idan ya tuno tarin qaunar da takeyi masa a baya
fa se yaga kamar hakan zata yuwu.

Amma ze gwada koda na wata dayane ya gani amma fa daga haka baze iya qara haquri
ba, in har bata sakko ba to shi ze ajiye girman kanya nemi sulhu da ita kamar yanda
likita ya bashi shawara.

A gidan Bala ya wuni har dare, abinci kuwa se siyowa sukayi dukda har sannan ba wai
ya ji garau bane.

Haka ya qarasa cinye satin kafin ya koma aiki yayi iya qoqari gurin rage damuwarsa
amma abin ya faskara akullum cikin tsoro da fargaba yake kwana da tunanin rasa
Asma'u. Sam ya kasa samun kwarin guiwar da Bala yake ta nanata masa yana ganin
lokaci yayi da zeje ya zube guiwoyinsa a gabanta ya roqesta koda kuwa zata sake
koda masa marine indai hakan ze sakko da ita daga fushin da take dashi ya amince ta
tsinko darbejiya ma ta dake shi son ranta.




Ayi manaji da wannan please

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login