Showing 168001 words to 171000 words out of 238465 words
kwado na qulle
babin sa a zuciyata na kuma dage da kaiwa Allah kukana akan in har Rabuwata dashi
Alkahiri ya kawo mun dangana gata kuwa na gani dan yanzu babu wani abu nasa da yayi
saura da nake ji a tattare dani.
Saurin kawar da tunanin nayi daga raina daidai lokacin da yaran suka shigo daga
sabuwar Islamiyyar da aka sake bude a cikin Estate din Asabar da Lahadi da safe
sauran ranakun sati bayan sallar Magriba zuwa Isha.
daman anayi daga baya suka dakatar da ita shine yanzu aka sake ginin sabuwa harda
bangaren matan aure dan nima ina shirye shiryen shiga.
Ina ganin sun bar baje a palour na qara sa ina cewa
“Aa ku tashi karku bata mun guri, kodai ku shiga can qaramin palour ko ku fita da
kujeru waje dan baqi zanyi bana so gurin ya baci”.
Daya daga cikin daku nan dana mayar musu qaramin palour suka shige Jafar Acici ya
shiga Kitchen ya hau bude bude yana cewa
“Mami tun daga farkon Layi fa nake jin qamshin abincinki yawuna duk ya tsinke kuma
nasan da kanki kikayi yau ba Yah Amnah bace”.
“To su Acici ai seka shanye yawun naka tunda ya tsinke dan bazan sammaka abincina
ba” na fada ina janye Babar kukar dana zuba musu nasu abincin a ciki, magiya ya
shiga yi mun da farantinsa a hannu ina dariya wayata tayi qara se na ajiye masa
kular ganin Yusuf ne yake kirana na fice daga Kitchen din.
“Badai har ka iso ba” na fada bayan dana amsa wayar,
“Na iso mana gani a qofar gida” ya fada cikin zolaya se nayi dariya nace
“Toh shigo mana, ka tsaya kuma daga waje?”
“Lallai yau dan gata nake har cikin gida aka gayyace ni? To me aka shirya mana ina
fatan dai Wannan mutumin baze fasa mun kai ba”
“Kana ina yanzu?” Na tambaye shi ba tareda na amsa masa maganar sa ba dan na rasa
dalilin da yasa yake son sako zancen Bashir idan muna magana.
“Yanzu zan fito daga Airport kuma kai tsaye gurinki zan wuto dan ba qaramin kewar
Wannan kyakykyawar fuskar taki nayi ba”
“Allah ya kawo ka lafiya” na fada kafin na kashe wayar. Wanka nayi saurin Fadawa, a
gurguje na shirya.
Riga da skirt na saka na Atamfa da ya zauna a jikina sosai nayi daurin daya dace da
fuskata kafin na bi jikina da sanyayyan turare, ina cikin daura Agogo kiransa ya
sake shigowa ban daga ba saboda naji dirar mota alamar ya iso kenan se kawai na
dauki gyalen daya dace da kayana na yafa har saman kaina na fito.
Seda nazo tsakiyar palour nayi turus ni kadai, yanzu fa Bazawari na ne yazo kenan
zan fita na taro shi ko ikon Allah rayuwa kenan kana taka Allah yana tsara maka
yanda yaso.
Fitowa Aliyu yayi daga palour da suke na waiwaya na kalle shi,
“Mami fita zakiyi?” Ya fada yana kallona.
Gaba daya Aliyu ya rikide ya koma Bashir, tsahonsa, tafiyarsa kamanni sa haske
kawia ya dara Bashir dan dukda gaba dayansu ba farare bane tas amma suna da haske
Farida ce kadai Fara a cikin su kuma ita kadai ce take kama dani amma hatta da
muryar su gaba daya iri daya ce haline akullum nake Addu’ar Allah ya banbanta musu.
“Mami” ya sake kirana se nayi firgigit na kalle shi nace “Eh baqo nayi yana waje”
“Baqo kuma Mami? Wane irin Baqo?” Ya tambayeni yana tsatstsare ni da ido.
Sena hada rai ina kallon sa nima nace
“Kaje ka shigo dashi, Uncle Yusuf ne” se na juya na shige dakina ina jin yanda ya
bini da kallo.
Ban dade da shiga ba naji an buga qofa, Aliyun ne ya leqo fuskarsa ba yabo ba falla
sa yace
“Ya shigo gashi a palour” ya juya abinsa.
Seda na dan ja lokaci kafin na fito, suna zaune gaba daya yaran Banda Aliyu, yanda
suke hira ana dariya seka zata sun shaqu ne ko sun dade da sanin sa.
Tunda na fito Yusuf ya zuba mun ido yana kallona har na qarasa kujerar da take
kallon wadda ya kai Ahmad ya tashi na zauna kaina a qasa ba tareda na bari mun hada
ido ba.
“Mami wai bezo da Little ba” Jafar ya fada kamar zeyi kuka, Dariya Yusuf ya saka
masa yana cewa
“Tana can har a bacci kiran Yah Jafar takeyi, sun koma makaranta amma da da ita zan
taho daman dan itama tana so tazo gurinka, amma na maka alqawarin da kunyi hutu
indai Abban ku ya yarda zan tafi da kai gurin ta idan zan koma”
Murna Jafar ya shigayi yaja qannensa suka nar gurin. Ni mamaki ma ya bani, se kace
wanda be taba zuwa Bauchi ba ko kuma duk murnar ganin Little din ne oho.
“Gimbiya Asma’u” Yusuf ya katse mun tunanina, ban san sanda na saki wani lallausan
murmushi ba kamar Gimbiyar kuwa ina qara sunkuyar da kai.
“Kinsan irin haka kike fitowa idan nazo zance shekarun baya, banbancin kawai waccen
Ma’u kwaila ce kuma tazo tana tunzura mun baki tana hararata wannan kuma babbar
macece tanayi mun murmushin da ze qarasa kassara zuciyata” Yusuf ya fada cikin wani
irin sauti, se nayi saurin rufe fuskata da tafukan hannayena inajin yanda zuciyata
take bugawa kamar zata fito.
“Ya zaki rufe dan Allah ki bude mun naci gaba da kallon kyakykyawar fuskarki kin
san kuwa yanda nayi kewarta” Yusuf ya sake fada ya ilahi ji nayi kamar kawai nayi
tsuntsuwa na bace a gurin saboda yanda kalamansa suke rugurguza mun jiki da zuciya.
Dariya yayi yana kallona yace
“Wai daman ke raguwa ce ban sani ba? To kuwa ki shirya, magana ta kadai tana
firgitaki ranar da kika zama mallakina kuma se yaya karfa ki bani kunya Ma’u”.
Wannan karon ban san sanda na miqe ba se gani na nayi na kusa kaiwa daki Yusuf kuwa
yace me zeyi idan ba dariya ba ya samu guri ya ringa kyalkyalata son ransa nidai na
shige daki na zauna bakin gado ina sauke numfashi kamar wadda tayi tsere.
Wasu Butterflies nake ji kamar suna mun yawo a kwakwalwa, Allah ya sani ina son
soyayya, ina son a tarairayeni a nuna mun duniya babu yani koda kuwa qarya mutum
yakeyi amma abinda na rasa kenan a rayuwar aurena da Bashir.
Bansan Miji yana gayawa matarsa kalaman soyayya ba, bansan me ake kira da tarairaya
ba ko kalmar I love you se na shekara ban jita a bakin Bashir ba, ba qaramin
gigicewa bace ta ke sakashi yayi magana idan muna mu’amala a sannan ne kadai
bakinsa yake bin qarfin zuciyarsa ya furta abinda beyi niyya ba qila shi yasa yanzu
yan wadan nan kalaman na Yusuf suke neman au rikita mun yar kwakwlawata.
Qarar da wayat tayi ne ya mayar dani hayyacina,
“Ki dawo nayi alqawari bazan sake cewa komai ba gaisawa kawai zamuyi na tafi dan a
gajiye nake sosai wallahi” Yusuf ya fada bayan dana amsa wayar.
Kamar me zuwa gaban suruki haka na tafi idona a qasa na sake samun can gefen kujera
na rabe ina jinsa yana mun dariya qasa qasa amma naqi dagowa balle na bashi damar
da zamu hada ido.
“Bari na tafi Asmy, na gaji sosai wata irin tafiya daga Washington amma se kace
wanda ya taho daga China”
Se na daga kai na kalle shi nace
“Wai ba daga Bauchi kake ba daman? Na zata ai kace kaje ganin su takwara ne”
“Suna America ai, ke dai kiyi ta tayani da Addu’a nima a wannan karon Allah ya
datar da ni na samu mace ta gari, na gaji da wannan gantalallen auran wanda dashi
kusan gara babu ni ina wata duniya matata tana can wani guri itama” ya fada
fuskarsa na nuna rashin jin dadin abinda yake fada din.
“Ikon Allah kaji wata gantalewa kuma” na fada ba tareda nasan a fili nayi maganar
ba seda naji yace
“Kinsan sunan da Hajiya ta sakawa auran kenan wai auran Gantali” ya qarasa yana
dariya. Murmushi nima nayi nace
“Allah to ya rufa Asiri” ya miqe yana cewa
“Amin”.
“Har zaka tafi ko ruwa baka sha ba sannan ga abinci kuma na yi maka fa” na fada
nima ina miqewa tsayen, se ya waiwayo muka hada ido yace
“Dagaske? Kai amma na gode yau nima zanci girkin Asmy daman tunda na shigo nake jin
qamshi shiru kawai nayi kar kice na fiya kwadayi, amma sedai na tafi dashi dan so
nakeyi naje na yi wanka na chanza kayan nan”.
A manyan Aluminum take away na juye masa hadin potato salad wani kuma Pepper
chicken, na hada masa da Flask din da na zuba hadaddiyar party Jallop rice dan dai
nasan babu wanda baya cin shinkafa indai dan Arewa ne dayan kuma Stit fry Egg
noodles da taji shrimp.
Harda Lemo da Ruwan duk na tarkada yara suka ringa fit dasu se gani nayi suna
shigowa da wasu irin qananan Akwatuna masu Kyau irin na yan gayu kowa da guda daya
Jafar ne ya shigo janye da guda biyu shi kuma.
“Mami tsaraba UncleYusuf ya kawo mana, ga wannan na Yaya Aliyu ne” ya fada yana
miqo mun guda daya.
“Bana so kudai da kuke kwadayayyu se kuyita karba ai” Aliyu da bansan yana gidan ba
ya fito daga dakin su Amnah yana maganar, hararar sa nayi ya kalleni ya dauke kai,
kamar ze zauna se kawai ma ya kada kansa ya fice daga gidan gaba daya ni kuwa na
bishi da ido kafin na mayar da hankali na kan sauran da suke faman bude bude
akwatunan su.
Kaya ne kowa kala biyu da takalmi harda Agogo da turare, bana buqatar a gaya mun
masu tsada ne dab Designers ne nagaske da kana kallonsu kasan sunci kudi.
Wayata na dauka na wuce daki ina kiran lambar Yusuf din
“Wannan kayan fa hidimar tayi yawa ai kuma ace ko wanne se da aka siya masa gaskiya
sunyi yawa” na fada bayan daya daga wayar.
“Akwai wani abu naki a ciki ne?” Ya tambayeni, sena girgiza kai kamar yana gabana
nace
“Aa” na bashi amsa
“To qorafin me kikeyi? Yarana na siyowa bake ba, idan ma kishi kike saboda ban yi
miki tsaraba ba toh sedai kiyi haquri bandake” ya bani amsa yana murmushi.
Murmushi nima nayi nace
“Mungode, Allah ya qara budi”
“Karki sake gode mun dan kinfi qarfin duk wani abu a gurina. Zan iyayin komai
saboda Farin cikin ki Asmy, zamuyi magana idan na qarasa masauki in naci abinci
sannan se nayi tunanin idan kin cancanci tukuici”
Da haka mukayi sallama ni kadai na ringa murmushi ina kallon wayar hannuna bayan da
na kashe, wato soyaya tayi a rayuwa malam.
ENGINEER BASHIR
*SODA COMMUNICATION📱💻📱
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*💃🏽💃🏽 with the validity of 30days at affordable
price we are available 24/7 08137145294
*MTN DATA*
1GB@280✅
2GB@550✅
3GB@850✅
4GB@1150✅
5GB@ *1400* ✅
10GB@2800✅
*AIRTEL DATA*
1gb@320✅
2gb@640✅
3gb@950✅
5gb@1600✅
*Pay through👇🏽👇🏽*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*🥰🥰🥰we are always there at ur service. WhatsApp/Call📞08137145294
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 52
ENGINEER BASHIR
Watanni ukun da suka shude Bashir yayi su ne cikin wata rayuwa me cike da qunci da
rashin sukunin zuciya. Ya sake zama shiru shiru duk da daman shi ba me yawan magana
bane amma a yanzu kana kallonsa zaka san shirun sa yana da nasa ba da tarin damuwa
da yake ciki.
Abun ne ya hadar masa goma da Ashirin, kewar Ma'unsa tana neman zauta shi ga rashin
kula da rashin abinci me kyau da baya samu a gidansa kullum se tashin hankali da
hayaniya idan ya fita har baya so lokacin tashi aiki ya dawo gida.
Gaba daya a yanzu idan ka ganshi se ya baka tausayi yanda gaba daya ya fige ya fita
hayyacinsa, hidimomi sun sako shi a gaba, wata daya da rabuwarsa da Asma'u gaba
daya ya kasa gane kan cefanen gidansa.
Be taba sanin cewa Neman da Asma'u takeyi rufin asirinsa bane se ranar daya dawo
daga aiki ya tarar da Amirah ta dafa masa farar shinkafa ta soya manja da yaji ta
ajiye masa a ranar Azumi yayi, kuma kafin ya fita da safe ya gaya mata azumin
yakeyi be shigo gida ba seda yayi sallar magriba dan haka yana shiga kan Dining ya
wuce kai tsaye dan ya ci abinci.
Yana budewa yayi arba da abinda ta ajiye masa gaba daya se ya gagara bude baki ma
yayi mata magana, mai da yaji a gidansa abinda rabon dako a ido ya ganta tun
zamanin da yana Jami'a shine yau aka dafa masa a matsayin abin shan ruwa.
Yar gasken kuwa daya tambayeta dalili kai tsaye ta gaya masa cewar kayan miya sun
qare kuma ita bata da kati a wayarta bare ta kirashi ta sanar masa shiyasa taga
daya dawo bata girka komai ba tunda tana da yaji gara ko fara da mai dince tayi
masa.
Yanzu shine ajiye buhun huna, shine cefane, dai da Maggi se ya siyo ya ajiye mata
sannan in dai bashi ya duba ya sake siyowa ba babu ruwanta abinda yake da akwai shi
zata sarrafa tayi abincin da kusan kullum Asarar sa akeyi dan yaran basa ci shi
kuma bashida nutsuwa da kwnaciyar hankalin da zeci da yawa, da ya zauna cin abinci
in sha Allahu seta qirqiro abinda zata bata masa rai ya tashi daga gurin.
Ya rasa wace irin macece Amirah da bata taba tashi kawo qorafi da mita se a lokacin
da za'aci abinci ko lokacin kwanciya wadannan abubuwa suka taru suka sake dagula
masa lissafi.
Be qara shiga uku ba seda Amirah ta fara laulayi. A iya saninsa bayan haihuwar da
tayi an saka mata Implant a Asibiti saboda ta huta jikinta ya dawo daidai amma se
gashi ba'a rufa shekara ba ta samu wani cikin.
Lokacin da yayi mata magana akan ya haka ta faru kai tsaye tace masa cirewa tayi
sanda zata taho saboda itama tana so ta tara Yaya a dena mata gadara dasu, be ja ba
ya barta tunda ai jikinta ne ta sani idan dadi taji idan ma wuya ce duk tafi kowa
sani shidai tunda ta fara Amaye Amaye da wasu abubuwa ya tattarata ta koma dakinta
dan wata muguwar qazanta ta farayi abin dai ba'a cewa komai.
A bangaren matsalar Ma'u kuwa yankewa kansa shawara yayi akan ze saka mata ido ne
yaga iya gudun ruwanta, ze jira daga nan har shekara har zuwa sanda zata huce ta
saurare shi a sannan baze sha wahalar shawo kanta ba su komawa auransu amma babu
qarya yayi kewar Asma'u koma yace yana kan kewarta, fuskarta, muryarta, qamshin ta
da gayunta daddadan girkinta ga murmushinta me saka shi manta kowa da komai kai
wallahi dole ya maido da Asma'u rayuwarsa dan kuwa tabbas rasata babbar Asarace a
gareshi.
Yanzu haka tun daya rabi da ita baya iya bacci saboda tunanin ta, idan kuwa har
bacci yayi nasarar sace shi me nauyi to cike yake da mafarkin Asma'un.
Abu dayane yake dan kwnatar masa da hankali yanzu da be sake ganin wannan mutumin
yazo gurinta ba, tun waccen ranar ma babu wani Namiji da ya sake gani tare da ita
idan ba Yemi ba wanda ya bincika ya tabbatar abokin aikinta ne kawai babu wata
alaqa a tsakaninau bayan ta aiki.
Sedai kuma guiwar sa tana yin sanyi irin yanda yaga gaba daya ta ci gaba da
rayuwarta babu wata alama da take nuna tana da damuwa ko tunawa da shi dan yanzu ko
sun hadu a hanya gaisawa sukeyi kamar wasu maqota, yanda zata gaisa da sauran
mutanen da suke cikin layinsu shima irin wannan gaisuwar take yi masa babu wani abu
da yake nuna sun taba hada wata alaqa ta soyayya bare har aje ga batun aure amma
kuma baze sare ba, zeyi ta binta a hankali har zuwa sanda ita da kanta zata sakko
ta neme shi.
A ranar Lahadin yana kwance a dakinsa kamar yanda yanzu ya mayar da hakan dabi'arsa
zaman daki kamar wata sabuwar Amarya. Amirah ce ta shiga dakin fuskar nan qozai
qozai da ita kana ganinta kaga me yaron ciki duk ta firgice ta saka doguwar rigar
bacci cotton ta daura zani akai kanta ko dankwali babu ga gashinta me laushi duk ya
tashi.
Kan gadon ta nufa ta zauna daidai kansa se yayi saurin miqewa zaune ya matsa can
gefe yana hade fuska, Amirah da abin ya mugun bata mata rai, bakinta cike da yawun
da yake yawan taruwan mata tace
"Wai wane irin wulaqanci ne haka se kace wata kashi daga nazo kusada kai zaka tashi
sannan ka dena cin abincina gaba daya mun zama kaman wasu yan haya a gidan nan kowa
sabgar gabansa yake yi"
"Malama ki wuce kije kiyi wanka kuma karki sake zuwa kina mun magana da yawu a
bakinki. Sannan na miki magana akan ki ringa suturta jikinki kin qi ko? Shikenan"
Bashir ya fada yana miqewa ya shige bandaki ya barta tana banbamin fadab bazatayi
wankan ba ai jikinta ne ba nasa ba.
Sanda ya fito bata dakin, shiryawa ya shigayi, yasan tunda ta fara wannan neman
rigimar to idan ya zauna gidan dole se ta saka shi yayi hayagaga shi kuwa yanzu
ciwon kan da yake fama dashi kullum ma ya ishe shi ba se ya qara wani ba.
Yana tsaye yana warming mota kamar ance ya kalli qofar gidan Ma'u yaga wasu
lafiyayyun motoci guda biyu a ajiye ga Bouncers hudu majiya qarfi se fareti suke a
qofar gidan.
A farko tunaninsa Alkasim ne yazo, yayan au Ma'u ne babban dan sandan farin kaya ne
yasha shine me yawo da wadan nan mutanen ko a Gombe idan yana gida haka Zasuyita
zagaye unguwar.
Harya shiga motarsa ze tafi ta mudubi ya hango ana fito da kwanukan abinci, cike da
mamaki ya dakata ai kuwa idonsa sukayi mummunan gani da mutumin daya fi tsana a
Yanzu ya fito daga gidan yana zuba murmushi kamar wanda akayiwa Albishir da
Aljanna.
Be gama cika da mamaki ba seda yaga Ana ta fitowa da yara akwatuna suna dauka, yana
nan tsaye suka wuce shi kamar da gayya ma har wani quuu suka taka motar suka fice
da gidu Bashir ya bisu da ido zuciyarsa na tafasa saboda bacin rai.
Kashe motarsa yayi ya nufi gidan, a bakin qofa suka hadu da Aliyu daya fito fuskar
nan kinini kamar wanda aka daka sukayi wa juna kallon kallo kamar wasu zakaru kafin
Aliyun ya rabe shi ze wuce se yayi saurin ruqoshi yana cewa
"Waye ya fita daga gidan nan yanzu?"
"Saurayin Mami ne, Uncle Yusuf" Aliyun ya bashi amsa kai tsaye kafin ya janye
hannunsa ya yayi gaba.
Seda Bashir ya dage bango kafin ya iya tsayawa da qafarsa. "Saurayin Ma'u?" Ya
maimaita maganar a fili yana bin bayan Aliyu da ya tafi ya barshi da kallo.
Dagaske Ma'u ta bawa wani damar shiga rayuwarta bayan shi? Wannan irin kata'i ne
yake taso masa daga qirji yana shaqe masa wuya kalamar saurayi da Aliyu ya gaya
masa tayi masa zafin da gara ace wuta ya fi masa sauqi akan jin wannan mummunar
maganar.
Fasa shiga gidan yayi ya juya dan tsoro yakeji, idan ya shiga ya samu tabbacin
maganar da Aliyu ya gaya masa daga bakin Ma'u ya tabbatar zuciyarsa kawai bugawa
zatayi a take ya mutu dan baze iya dauka.
Yana dafe da qirjinsa dakyar ya iya kwasar qafarsa ya koma jikin motarsa yana sauke
numfashi kamar wanda yayi gudun 10KM. Gaba daya jinsa yake shi ba a sama ba ba a
qasa ba, qafafunsa kansu rawa sukeyi beyi aune ba se ganinsa yayi dirshen ya zauna
akan kwaltar da take qofar gidan kawai se