Showing 117001 words to 120000 words out of 238465 words

Chapter 40 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

amma ban dago ba ban kuma matsa daga inda nake ba ya tsallakeni ya
fice daga palour, be san jira kawai nakeyi ma na samu wata dama na fice na bar musu
gurin dan bazan iya musa masa ba tun farko dalilin da ya sa na zauna ma kenan.

“Gamu munzo guiwoyin mu a qasa Asma’u munsan ba’a kyauta miki ba ni kaina wallahi
bansan abinda ya faru ba kenan se daga baya amma ki dubi girman Allah kiyi haquri,
kuskure dai an rigada anyi shi sedai muyi fatan Allah ya kiyaye na gama amma yanzu
kiyi haquri ku karbi qaddara a yanda tazo muku” Abdulkari ya fada, se na daga kai
na kallesu ina shirin buda baki nayi magana Bala ya rigani da cewa

“Allah ya huci ran uwar gida sarautar mata, kinsan fa kinsha kan mutumin bala’in
tsoronki yakeyi shiyasa ya kasa gaya miki zancen auran nan. Kuma ma ni gani nayi ai
ba wani abu a ciki tunda qanwarki ce daman da aje a dakko miki Bare wadda baki san
halin ta ba Uwargida ai gara ta gida ko, easy kawai ki shanye a koma a ci gaba da
gashi”

“Sedai a koma a ci gaba da gasa ubanka Bala” na fada a fusace ina miqewa tsaye
kafin na nuna Bashir da yai tsamo tsamo kamar kazar data sha dukan ruwa ya zate ido
yana aikawa Bala da mugun kallon katobarar dayayi nace

“Kai kuma tun da sauran burbudin mutunta juna a tsakanin mu ka rubuta takaddata ka
aiko mun da ita dan wallahi Bashir kayi kadan ka wulaqanta ni kayi mun kishiya ta
rashin mutunchi, idan kuma kaqi tabbas kotu ce zata raba auran mu da kai” ina fadar
haka na juya amma kafin na kai waje Bashir da bansan tasowarsa ya riqe ni kamar
dansanda da Barawo yana cewa

“Bazan iya ba Ma’u, na sani nayi kuskure amma wallahi rashin sanin ta inda zan fara
gaya miki maganar yasa na aikata haka. Basan a ya zaki kalleni ba Ma’u idan nace
miki zan qara aure. Ni kaina na rasa ta yanda Al’amura suka juya har na fara son
Amirah na yarda kiyi mun duk irin hukuncin da kikaga ya dace komai tsananinsa zan
dauka amma bazan taba iya rabuwa da ke ba Ma’u”

Wani tuquqi ne ya taso mun, yanzu har Bashir ya iya kallon tsabar idona yace dani
wai yana son Amirah lallai na yarda In da ranka zaka sha kallo. Hannayensa daya
riqeni na banbare daga jikina ina cewa

“Tunda kana sonta seka je ka zauna da ita amma ni dai wallahi na gama zaman aure
dakai ko kaine autan maza Bashir kaje ka zauna da matar so tunda na gamayi maka
rana”

“Kiyi haquri dan girman Allah Ma’u ki yafe mun ki bani dama na wanke kaina nayi
miki Alqawarin babu abinda ze chanza a tsakanina dake saboda wannan auran, Ina
sonki ina qaunar ki ki dauka wannan abun yana cikin qaddadarar mu daga ni har ke”
ya fada yana qoqarin sake kama hannuna nayi baya ina cewa

“Qaddarar ka dai kai kadai kuma ka matsa karka sake rabar jikina idan ba haka ba
Bashir sena kwada maka mari wallahi”. Sosai na birkice nayi masa tijara yanda ne
taba tsammani ba a rayuwar sa, na hada da Balan da Abdulkarimun nayi musu zagi na
tsamar nama kafin na jadda da masa akan ya kawo mun takaddata dan wallahi na gama
zama da Bashir na yarda su Addahn suci galaba a kaina. Dana hada miji da Amirah
gara na fita na bar mata gidan ta zauna dashi ita kadai.

Bangaren Hajia Umma na wuce gurin Alhaji Qarami, banko bashi dama yayi magana ba na
fashe masa da kuka ina rantsuwar bazan komawa Bashir ba ya saka shi ya kawo mun
takaddata na tsane shi na tsani zama dashi. Haka yayita bani haquri ya kuma
tabbatar mun da cewa tilas Bashir ya sake ni tunda har na nemi hakan amma yanzu na
kwantar da hankalina kodan jinina da akace ya hau a samu ya sauka kar kuma na sake
janyo wa kaina wata matsalar.

Haka na kwashe sati biyu cif a gida muna kan wannan danbaruwar, kullum Bashir se ya
zo kamar maye haka ze durqusa yana bani haquri nima kuma ban fasa ci masa mutunchi
da jaddada masa cewa ya bani takaddata ba tunda ba’a aure dole nace na gama.

Gashi makarantar yara kullum se kiran waya sukeyi an koma tuni lafiya basu dawo ba
nace musu mun bar gari ne za’a zo a fada officially a cire su haka gurin aikina ma
da suka tuntubeni tunda hutun sati uku na dauka gashi na haura kawai se nanemi
takaddar hutu ba tareda biyan Albashi ba, dan bazan bar aiki na ba saboda a yanzu
ne nafi buqatar sa Idan Bashir ya sake ina da buqatar neman hanyoyin da zan ruqe
kaina da Yayana dasu.

Bazan manta ranar da Dada da Addah suka wanko qafarsu wai sunzo biko na ba, na yaba
da tsantsar rashin kunya irinta mutanen nan. A ranar nayi musu abunda Bahaushw yake
cewa idan Malam beji kunyar hawa Jaki ba to shima Jakin baze ji kunyar kada shi ba.

Na fito musu a yar zamani na wanke su tas da soso da sabulu na kuma sake jaddada
musu da idan sunji haushi su saka Dan su ya sake ni su gani tsakanij ni dashi waya
rasa na raka su da Allah ya isar abinda sukayi mun kuma in sha Allahu nan kusa zasu
ga sakayyar yaudarata da sukayi haka suka kwashi kafafu a sanyaye dan ba Dada ba
Addah kanta da bata raina abin kunya tayi mamakin yanda na sakawa idona toka nayi
musu tas.

Daukata sukeyi a duk yanda suka takani zan biyune shiyasa ma yanzun suka zo saboda
horon da Bashir yaje yayi musu akan kodai suje su bani haquri na koma dakina ko
kuma ya saki Amirah tunda ita ce duk musabbabin tashin hankalin da akeyi.

Wai mutane saboda qin Allah se kaga sun kirani da sunan wai ban kyauta ba abinda
nayi wa iyayen Bashir tunda auren daya qara ai ba haramci bane da zance ni bazan
zauna da kishiya ba.

Har da wadda take cemun ilimina be amfana mun komai ba ina Karatun islamiyyar da
nayi ina Bokon nawa zan zauna ina ja ina jayayya da abinda Allah ya halasta, ban
dagawa ko wace yar iska qafa ba na kuma roqi Allah duk wadda tace nayi Haquri Allah
yasa ayi mata abinda yafi nawa muni idan yaso se taji in ma rashin tawakkalin me ya
sakani yin haka ko yaya.

A cikin wannan yana yi wata rana muka samu baquncin Goggo da tunda aka fara wannan
abun sau daya mukayi magana da ita shima ni na kirata kuma tace mun nayi haquri
daga haka bata qara komai ba.

Ina kwance a daki aka kirani a lokacin idan ka ganni se na baka tausayi, na rame na
fige fuskata babu komai daga ido se dogon hanci ina shiga palour idona ya sauka
akan Bashir daje zaune a qasa, ban lura da sauran mutanen da suke ciki ba na hau
kansa da masifa ina cewa

“Wallahi ko maye ne kai Bashir haka zaka ganni ka kyale tunda nace banayi banga
wanda ya isa ya tilastani ci gaba da zama da kai ba, ka tashi ka tafi tun kafin
nasa azo a fitar dakai mara zuciya kawai”

“Idan baki saka an fita dashi ba baki isa fitsararriya mara mutunchi ba Asma’u”
muryar Goggo da ban san da zuwan ta ba ta katse ni kafin ta ci gaba da cewa

“Ashe duk rashin mutunchi da diban Albarkar da akace kinayi dagaske ne kuma a gaban
ku Hajiya kuna kallo aka rasa wanda ze tsawatar mata. Saboda bakida mutunchi Mijin
naki kike sakawa a gaba kina fada masa irin wadannan maganganun ku to bari kiji shi
Allah babu ruwansa ze hukuntaki ne akan laifin ki na sabawa miji da ci masa mutunci
babu ruwan Allah da cewar Bashir ya auro miki wadda bakya so anyi miki ba daidai ba
dan haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki kafin ki kanki wuta da qafafunki.

Sannan saboda kin zama yar kanki se abinda kika tsarawa ranki zakiyi shine kike
iqirarin zaki kashe auranki saboda kanki farau kishiya ko kuma kece ta qarshe da
za’ayiwa ko?

Ki idan kina da hankali ma ya kamata ki tashi jiniyoyij wuya akan za’a miki
kishiya, gidan mu mata nawa Ubanki ya aura gamu nan mu Hudu ya mutu ya bari kin
taba gabin wata tayi tashin hankali da yar uwarta a cikin gidan nan?”

“Amma Goggon su bazaki hada mu dasu ba, ko bayan haka hanyar da Bashir yabi tayin
qarin auransa ce bata dace ba kuma ko wacce mace akayiwa irin haka dole ranta ya
baci ai” Hajia Anjin ta tare Goggo jin yanda take ta surfa fada, se Goggon ta
kalleta tace

“Saboda ya auri yar uwarsa ne take tashin hankali dan ba’a gaya mata ba, ai ba
kansa aka fara ba tunda ubanta ma a sanda ya auro ni ai baku sani ba tafiya yayi
bikin abokinsa ya dawo muku da ni a matsayin kishiya me yasa a sannan ku baku yi
tashin hankali kunce bazaku yarda ba?”

“Aa Maryam Allah ya jiqan Alhaji bazaki taba hadashi da wannan yaron ba domin
Alhaji Adali ne gamu nan dukka bari kiji kafin A daura auran ku da Alhaji seda ya
kira mu a wayar landilayin da daddaya ko waccen mu seda ya gaya mana abinda ya faru
ya kuma sanar mana da cewa ze aureki bisa wasiyyar Sama’ila dan haka da yardar mu
da Amincewar mu Alhaji ya auro ki, sannan tunda tace bazata koma ba ai Asma’u ta
wuce yarinta bare ace za’a zabar mata abinda zatayi”
Hajia Babba ta fada sauran suka amsa da “kwarai haka aka yi.

“To shikenan tunda kun daure mata gindin tayi duk rashin mutunchin da take so kun
bata goyon baya ni baza’a hada kai dani ba, Ke Asma’u idan na isa dake ki tattara
ya naki ya naki yanzu ki bi mijinki, kuma diban Albarkar da kikayiwa uwarsa da
yayarta kije ki basu haquri, dan cikin matan yayyen ki kaf babu wadda ta taba duban
idon mu ta gaya mana maganar banza balle mu yayanmu suje suyiwa na wasu”.

Tunda suka fara mahawarar na durqushe a gurin ina Kuka, wato qarata Bashir ya kai
gurin Goggo ita kuma ta goya masa baya. Da sauri na daga kai na kalleta hankali
tashe jin irin umarnin data bani, se nayi saurin matsawa kusada ita ina cewa

“Amma Goggo...”
“Karki ce mun komai sedai kuman idan kin shirya nuna mun ban isa dake din ba
shikenan” ta yi saurin katse ni, se na mayar da kaina qasa na ci gaba da kuka me
ciwo, ya zalunce ni kuma ha hadani da mahaifiyata Bashir wane irin mugun mutum ne a
rayuwa.

Haka naja qaqafuna na koma daki na shiga tattara kayana ina kuka yarana da suka
biyoni suna tayani. Ina cikin hada kayan Hajia Babba ta shigo dakin,

“Ki bar shirin yanzu Asma’u tace ku bari zuwa jibi se ki koma. Kiyi haquri ita
rayuwar Ya mace daman haka da qalubale wata rana komai ze zama tarihi in sha
Allahu” haka tayi ta bani baki har seda naji zuciyata tayi sanyi na kwanta a kan
Gado ina saka da cin alwashin irin gashin qumar da zanyiwa Bashir idan har na koma
gidan sa. Shi da sake jin dadin zama dani har abada.

Washe gari Goggo ta koma bayan ta sake yi mun kakkausan gargadi akan idan na sake
ta sake jin wani abu se tayi mummunan saba mun, na koma gidana na zauna kuma duk
abinda zan gani naje nayi haquri karna kuskura na dauki dabi’ar kai qara ko na ce
zan sake yin yaji.

“Asma’u badan bana sonki yasa nayi miki haka ba, nasan ba’a kyauta miki ba amma
hakan baze zama silar da zaki bar uban yayanki ba idan kin rabu da Bashir saboda
kishiya qarshe dai wata zaki je ki tarar a duk inda zaki fada to menene amfanin
haka” Goggo ta fada cikin lallama bayan da ta gama yimun fadan kuma, sena share
hawayena tunda yanzu ta sakko se muyi magana ta fahimta nace

“Wallahi Goggo ni ba qarin auran sa ko rashin gayamun da beyi bane ya dame ni amma
me yasa ze auri Amirah?”

“Saboda yana sonta kuma ita Allah ya zaba masa kin san dai duk yanda mutum yaso da
son kasancewar abu idan Allah be hukunta hakan ba baze faru ba ko, haka duk yanda
ka kai ga qin abu idan Allah ya qaddara faruwar sa babu abinda ya isa ya tsayar da
hakan to kar kiyi jayayya da hukuncin Allah Asma’u, ki dauka daman tun kafin
wanzuwar duniya yanda Ubangiji ya qaddara ke matar Bashir ce haka itama aka rubuto
matar sa ce dan haka dole se ya aure ku.

Maganar munafunci ko yaudarar ki da sukayi wannan ki barwa Allah komai kina zaune
se kiga ya saka miki a ruwan sanyi kinji ko kiyi haquri kar kuma wannan dalilin
yasa kice zaki quntata zamanki da mijinki, a yanzu ne ya kamata kija shi a jiki
dakyau ki bashi dukkan kulawa da soyayyar data kamata saboda ba ke kadai bace, duk
abinda ya rasa a gurinki ze same shi a wani gurin daga nan kuma se hankalin sa ya
fi karkata can saboda zuciya ai tana son me kyautata mata ke kuma daga qarshe se
kiga kamar dan ya samu wata ne ya watsar dake bayan ke kika bada damar hakan.

Dan haka bani da damuwa akan ki Ma’uta nasan zaki riqe kanbun nan naki na Uwargida
sarautar mata dakyau ina so ki nuna musu cewa ke din fa badai mutum ba se Allah,
Allah yayi miki Albarka ya ci gaba da kareki a duk inda kike”.

Kalaman Goggo sunyi tasiri sosai a zuciyata dan gaskiya ta fada da ace wata daban
aka auro mun davkuwa tabbas na nuna mata cewa kishi da MA’U ba wasa bane se ta
shirya amma a duk sanda na tuna wa Bashir ya aura se naji bazan iya amfani da ko
daya daga cikin abinda ta fada din ba.

Haka ta koma Yola washe garin ranar nima yan uwana suka raka ni gidan mu na Gombe
bayan da suka hadu suka sake yi mun nasiha da rarrashi, banje na bawa su Dada
haquri ba itama kuma Goggon bata tsananta ba tunda na yarda zan koma din ta rabu
dani.

Gini yayi kyau sosai kuma an saka komai na amfani sabo daga yanayin kyau da
tsaruwar kayan na tabbatar da aikin Yan gidan mu ne sunyi zumunchi sosai suka hada
mun gida kamar na wata sabuwar Amarya ko tsohon lokaci nada ba’a saka a gidan ba.

Yanda kowa ya ringa yabawa ni kuwa baqin sa nake gani dan da gidan da mamallakinsa
a yanzu basa gabana ko kadan biyayyar iyaye ce ta dawo dani cikinsa.

Bayan kowa ya watse Bashir ya shigo yanda kasan wasu Baqin da basu taba haduwa ba
haka muka zama, shi yana kaffa kaffa dani karya yi abinda ze zama laifi ni kuma na
baiwa Banza ajiyarsa ina ta sabgogina se shi da yaransa yake ta magana yana
tambayarsu abubuwan da suke buqata wanda sarai nasan dani yake naji dadi da suka ce
masa babu.

Su kansu yaran daga kan Amna zuwa Farida ba wani sakewa sukayi dashi ba Abdallah da
yan biyu ne babu abinda ya sha musu kai suke ta murna sunyi kewar Abbi. Aliyu daman
yafi kowa daukar zafi, kuka ya ringayi da gaske lokacin da yaji maganar auran ya
kuma dauki fushi da uban ko yau din da muka dawo ina kallon yanda yake cika yana
batsewa.

Da daddare gurin qarfe tara muna zaune a palourn qasa muna hira muka ga an bude
qofa, da yake irin wadda bata buduwa ta wajen nan ce nasan Bashir ne shine yake da
key dan haka ban ko kalli qofar ba na sake hada rai na zubawa TV ido.

Da sallama a bakinsa ya shigo, takun qarar takalmin da naji bayan muryarsa ya saka
na waiwaya da mamakin naga shi da waye haka karaf idona ya sauka cikin na Amirah
data sha Kwalliya da wani Material Cotton baqi me Pink din flowers dinkin riga da
skirt sun kamata dam se wani dan yalolon gyale data yafo a kafada.

Cikin abinda be wuce second biyar ba na qare mata kallo na mayar da kaina zuwa ga
TV ina nanata “La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minzzalimin” a zuciyata
saboda jin wani abu yana tasomun kamar zanyi aman zuciyata har wata zufa naji tana
tsatstsafo mun.

Ta gefen ido nake kallon sanda suka zauna akan kujera, ina jin qamshin turaren data
saka ya baza gurin irin turaren da nake amfani dasu ne na Maryam collection ta
zauna a kusa da Bashir sosai kamar zata shige jikinsa shi kuma se turata yake yi
abin ma se ya bani dariya na dan yi murmushi a raina nace “yaro yaro ne” amma ban
ko juya na kalle su ba.

Ina jin yaran suka hada baki suka gaishe shi ya amsa a zatona zasu gaida Amirah se
naji dif sun ma mayar da hankali akan film din da muke kallo Bashir da qarfin hali
naji yana cewa wai

“Baku ga Antyn ku ba baku gaisheta ba”

“Wacece tana ina ai mu kai kadai muka gani Abbi se Amirah” Aliyu ya fada yana kafe
uban da kallo wanda mamaki ne nasan ya hana Bashir din magana. Yanda kasan bana
gurin haka nayi musu dayake film din yazo qarshe ana gamawa yaran suka miqe dan
daman abinda ya zaunar da mu kenan nima se na shiga qoqarin miqewa Bashir ya
dakatar da ni da cewa

“Ma’u ina kuma zaki je gurinki fa muka zo” sena koma na zauna na waiwaya ina kallon
sa da murmushi akan fuskata wanda a badini kuka nakeyi cikin zuciyata amma nayi
Alqawarin wannan yarinyar bata isa taga gazawata ba, se a yanzu nima na dawo
hayyacina tabbas idan na bar mata gidan ta ci galaba akaina dan haka zan zauna kuma
ba zaman dadi ba kowa se yaji a jikinsa.

“Amirah baki gaida Antyn ki ba “ ya fada bayan dana zauna, Amirah da ta hada fuska
bakin nan kamar ze tabo POP tace “Nima ai yayanta basu gaishe ni ba, kana ji fa
wannan marakunyar Aliyun cewa yayi ma be ganni ba kuma baka ce komai ba”.

Dukda qasa qasa tayi maganar amma tsaf naji ta a raina nace “zanci uwarki ne
yarinya mu dai ke zuwa”.

Kamar me jira kuwa l Bashir ya hau masifa yana fada mata maganganu, abin haushi
abin dariya dramar tasu ganin abin bana qare bane na miqe nace masa
“Ka rufe mana qofar idan kun fita” ban ko saurara ba na haye sama na barsu a gurin.
Har na kwanta Bashir ya shigo dakin, da saurin gaske ya nufoni kafin ya qaraso na
dire daga gadon ban yi wata wata ba na izge Fitilar gefeb gadona daga soket na daga
ta na nuna masa ina cewa

“Wallahi ka kuskura hannunka ya tabani sena yi maka rotse da wannan, badai ka
hadani da Goggo ta tilastani dawowa gidan ka ba, ka tabbatar da ka kaiwa tashin
hankali katin gayyata da hannunka”.

Yanda nayin ya tabbatar masa dagaske idan ya matsa zan iya kwada masan, daga nesa
ya ringa yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login