Showing 45001 words to 48000 words out of 238465 words

Chapter 16 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

qaqqafewa kamar me suma ga
qirjinta na sama da qasa da sauri har wani wahalallen tari take saki a shaqe ba’a
maji sosai Amirah na gefenta tuni Goggoro yayi ta kansa kwalliya ta jagale tana
rusar kuka hannu aka.

Habiba Kishiyar Addah ce tayi qarfin halin cewa a dauki yarinyar a kai Asibiti mana
se a sannan ma tunanin su ya kawo nan da nan Ummi ta shiga kiran wayar Naziru tunda
shine wakilin Bashir din amma se aka ce mata call waiting, bata haqura ba taci gaba
da kiran wayar amma be daga ba.

LAGOS Nigeria
Wato ranar bayan Bashir ya tashi daga aiki se yabi wani abokinsa gidan sa saboda
koya dawo gidan baya masa dadi. Suna zaune suna cin abincin da sukayiwo take away a
hanya dan shi abokin bashi da Aure suna yan hirarrakinsu. Bayan sun gama Bashir ya
dauki remote yana chanza tasha kafin lokacin sallar Magriba yayi su fita shikuma
abokin wayarsa ya dauka ya shiga Tiktok dan shi ma’abocin duba Tiktok ne.

Bashir na daga gefe lokaci lokaci ya daga kai ya kalleshi jin yanda yake dariya
shikadai, sedai ya girgiza kai kawai yana mamaki besan me mutane suke ji ko gani a
wannan Tiktok dinba. Yana yawan ganin Abokanan sa suna shiga suyi kallace
kallacensu har Ma’u ma yana ganin tana shiga ta kalli video Girke Girke amma shi a
shirme yake daukansa. Dukda sunce akwai abubuwan amfani amma gani yake rashin
Amfanin yafi amfanin yawa ai.

“Mata da bidi’a abarsu kawai yanzu suna ma ya zama biki kenan ji wannan ai wallahi
bama ko wanne biki ba” Abokin Bashir din Musa ya fada yana nunawa Bashir video
bayan yayi joining Live din da wata friend dinsa takeyi. Kallo daya Bashir yayi
musu “yace Allah ya sawwaqa” ganin mata nata tiqar rawa abinsu.

“Masha Allah amma mejegon tayi kyau nima fa mutumina Gomben nan zanzo ka bani wata
yar fara haka na aura wallahi” Musa ya sake fada. Haka kawai se ya samu kansa da
juyawa ya sake kallon wayar karaf idonsa ya sauka kan mejego Amirah tana kwaso
shoki.

Murza idonsa ya sakeyi dan ya tabbatar ita dince ko kama ce ya miqa hannu ya karbi
wayar daga hannun musan daidai Live Video ya katse.

“Musa bude mun page din yarinyar nan na gani” Bashir din ya fada. Se Musa ya saka
dariya yana cewa
“Kai mutumina biyu ne fa dakai tsalatsala ka barmu dai mu zero mu nema amma banda
kai” ya qarasa yana miqa masa bayan ya budo masa page din Nabila Dikko qawar
Amirah.

Videon farko da tayi uploading kadai ya kalla ransa yai qololuwar baci, videon da
aka mata ne bayan an gama mata makeup da Baby Iman a hannunta. Wayar ya miqawa
Musan kawai ya zaro tasa Musa kuma ya bishi da ido ganin yanda fuskarsa ta nuna
bacin rai qarara.

Number Naziru ya kira ringing biyu ya daga.
“Naziru me yake faruwa a gidan nan?” Ya tambayeshi. Naziru da daman yake shirin
kiran Yayan nasa dan dawowarsa daga makaranta kenan Dada take gaya masa ana can ana
taron sunan, ze kira Bashir din kuma ta hana dan haka ya karkace ya fara jero masa
yanda akayi

“Wallahi yaya taron suna sukeyi gida ya cika da mata harda me kida suka dakko tun
daga Kano wai Feli sunansa kowa nadai manta sunacan dai sunayi wallahi ga sanyi ya
kankama a Gombe kuma.....”

“Kanaji ko, kaje gidan ka kulle qofar ta waje kayi tafiyarka kawai kabarsu” Bashir
din ya katse Naziru jin zancen nasa yaqi qarewa.
“Yes” Nazirun ya fada ransa qal dan dama yasan Indai Bashir ne ya san takan Tsiya
aikuwa Kwado ze siyo qundumeme ya garqame su kuma baze bude ba se irin sha biyun
daren nan gobe ma su sake zuwa suna.

Be fadawa Dada yanda sukayi ba haka be bi takan Kiran da Ummi takeyi masa ba dan
daidai lokacin ne suna waya Bashir. Machine ya hau dan yafi sauri bayan ya siyi
garqamemen kwadonsa kamar me kulle kurkuku ya nufi gidan.

A gidan suna kuwa bangaren su Ma’u sun sha hirarsu sosai har Magrib sannan driver
Zahra yazo, sallama sukayi kamar karsu rabu Sannan Ma’u da Rahma suka rakota kallon
matan da sukayi cirko cirko a tsakar gidan sukayi dan duk budirin nan basu san me
yake faruwa ba suna sama abinsu kuma da yake sun rufe windows yasa basa jin qarar
kidan sosai koda aka kashe ma abun be dame su ba.

Rabawa sukayi suka nufi Get dan bama wanda hankalin yakai kansu Asma’u ta saka key
din hannunta ta budewa Zahra a ranta tana mamakin ganin an garqame qofa harda kwado
Zahra na saka qafarta waje Naziru na dira ai harda gudu ya hado har yana tsorata su
Zahra tayi Waje Ma’u tai ciki da sauri ganin yana neman datse mata hannu abinda ya
ankarar da matan dake tsaye kenan suka yo Get din da gudu amma ina kafin suzo tuni
ya danna Kwado ya bame.

Baki bude Rahma da Ma’u suke kallonsu,
“Kiyiwa Allah Hajia ki bude mana mu tafi dare yanayi haka kawai an kullemu kamar
wasu barayi” wata mata ta fada. Kiran sunan Naziru Ma’u ta shigayi gaba daya kanta
ya kulle se ya amsa mata yana cewa

“Anty kije kawai zan kiraki a waya in miki bayani”. Seta juya ita da Rahma sunajin
matan wasu na magiyar a bude wasu na zage zage.

A palourn qasan suka zauna ta dannawa Naziru kira.

“Baba Naziru wai ya akayi ne meya faru aka garqame mana gida” ta tambayeshi bayan
ya daga wayar. Seda yai dariya san ransa dannan yace

“Wallahi Anty ina zaune Yaya ya kirani yace na siyi kwado nazo na kulle gidan nan
da duk jama’ar ciki inyi tafiyata ze kirani sanda ya kamata nazo na bude”.

“Ikon Allah, me akayi toh” ta tambayeshi.
“Oho inaga dai daman besan da zasuyi taron nan ba shine dalili qilan” cewar
Nazirun.

“Toh Allah ya rufa asiri nidai yayana suna waje daman yanzu nake shirin naje na
dakko su tunda gaka taimaka ai kasan gidan Su Qawar Amna Amina ka debo munsu”

“Ba case Anty Bari naje” sukayi sallama ta ajiye wayar.

“Kinji me gidan ne yace a kulle masa gidansa” Ma’u ta gayawa Rahma.

“Amma naji dadi dan fa sanda Abban Ilham ya kawoni yaga taron nan tambayata yakeyi
meya faru nace nima ban sani ba nadai yi hasashen suna ake, yace aikuwa dakyar idan
yaya bashir ya sani toh Allah dai yasa atashi lafiya nace Amin
Yanzu kuwa naga alamar kamar ba lafiya ba dan banga iyayen bikin ba a gurin”.

“Koma meye susuka sani dai, muje muyi Isha naji an fara kira” Asma’u ta fada suka
miqe suka shiga dakinta na qasa dan yin sallar.


Dakin Mejego kuwa kiran duniya Naziru be dauki waya ba haka suka tasa ya a gaba
suna kuka ita se qaqqafewa take Su kuma suna aukij kuka Amirah kamar itama zata
shide babu wanda fasahar kaita wani Asibitin tazo masa a cikinsu.

“Ina Fatun, wallahi tun da sauran mutunta juna tsakaninmu kizo ki bude mu mu fita
idan ba haka ba wallahi bazaki so abinda zan aikata a gidan nan ba” Hajia Mariya
datafi kowa shiga tashin hankali dan kamar Mijin na jira ta gane an sace mota se
gashi ya kirata akan yana Airport za’azo a karbi key din motar a dakko shi, seda
wanda ya tura yaje aka ce masa bata nan ya kirashi gashi yanzu se kiranta yake yana
Zazzage mata kwandon rashin mutunchi yace ta kuma tattaro dik inda take karya
rigata zuwa gida in ma ita bata dawo ba to motarsa ta rigashi isa.

Qaqawara qaqa 🤔🤔🤔🤔🤔🤔


Ayi qara haquri dai yanayin se a hankali 🙏🙏🙏

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 19

Tunda Bashir ya qulla tsiya ya kuma tabbatar Naziru ya kulle gidan dan sun sake yin
waya ya gaya masa ya je dakko su Amna a gidan qawarsu a sannan ce masa yayi ya wuce
ya kaisu gidan Bilkisu yayar Asma’u kawai dan idan yace gidan Dada zata zargi wani
abu kuma baya so labarin ya isar mata da wuri.

kashe wayarsa yayi dan karma wani dayake ganin mutunchi ya kirashi ya roqeshi. Beko
qara minti goma a gidan Musa ba ya tafi yana tuqi a ransa yana wassafa irin
hukuncin da ze dauka akan Amirah tunda har ta take dokarsa ta nuna bata jin
maganarsa tabbas ze nuna mata shima ba kanwar lasa bane.

Daya isa gida shikadai ya ringa safa da marwa a cikin palour yana kwafa tabbas se
ya hukunta yarinyar nan hukunci me tsanani, tunanin halinda Baby Iman take ciki
yake yana fatan Allah yasa yarinyar tana lafiya wani abu be sameta ba hakan ze dan
rangwanta wa Amirah hukuncin da zeyi mata amma ya rantse tabbas wani abu ya sami
yarinyar nan se kansa besan me ze mata ba. Yana so ya kira Ma’u amma bayaso ya
kunna wayar wani kiran ya shiga qarshe haka ya haqura ya zauna jiran lokacin daya
diba kafin ya sake kiran Naziru.

Gidan suna kuwa gagarumin ruguntsumi ne ya sake tashi. Ana tsaka da dambaruwar
yanda za’ayi a bude qofa, dangi da qawayen Addah sun taru suna mata tijara sun cika
palour Amirah taf kaman an sakko daga Idi daidai da iska me kyau babu ta shaqa se
kaya kaya akeyi.

Amirah na durqushe se rasgar kuka take har sannan akan yarinyar da harta gaji da
komawa da numfashinta ta kwanta laqwas kamar mara rai ita duk wannan hayaniyar ba
ganewa take ba, buqatarta a samu me kai mata ya Asibiti dan ta dade da saddaqarwa
yau kashi ta ya gama bushewa.

Addah data gaji da tijara da cin mutunchin da Jama’a suke mata ta zaro Key ta
cillawa Hajia Mariya datafi kowa hasala a cikin matan dan ita aka dira daka, so
take kawai ta fita ta san nayi dan ko karan hauka ya cijeta bazata doshi gidan
mijinta yanzu ba se da wannan mota da bata san uban da ya sace ba dan haka ta yanke
shawarar daga nan office din Yan sanda zata ta bada report daga can kuma tayi
gidansu dan tasan waye mijinta sarai haka kawai ma yayi bala’i bare yau da aka
taboshi da lasisi.

Cafkar key din tayi tana watsawa Addah kallon wulaqanci tace “da karki bayar
wallahi da sena tubeki na dauki muqullin nan yau” ta fara kutsawa da niyyar zuwa
bude qofa Hajia Hassana ta katseta tana cewa
“Mariya wannan muqulli fa aikin banza ne dan ta waje wani hatsabibin yaro ya kullo
mu wallahi. Kuna tsaka da hayaniya dazun nan Uwargidanta ta raka baquwa ta bude
kofar tana fita yaron nan ya danno daga waje ya rufe jeki duba ma ki gani babu
kwadon nan ta ciki”.

Kafin ma ta qarasa dayawa sun dauki sabon kukan tashin hankalin rashin sanin wane
kalar bala’in ne kuma yake tunkaro su, To bala’i mana in ba haka ba ta yaya za’a ce
an kullo su ta waje ma bata ciki ba yanzu suyi yaya su fita dan dai wannan katangar
gidan basu isa su tsallakata ba.

Ummi ce da tuni itama ido sukayi mici mici saboda kuka ta sunkuci Iman tana ceda
Amirah “nidai matsa ki gani wannan hayaniyar da hucin numfashin kadai sun isa su
qarasata muje ko a Napep ne mu tare mu kaita Asibiti” ta nadeta a cikin shawl din
ta kyau ta juya da niyyar fita kamar ana jiran ta kuwa dif wutar palour ta dauke
duhu ya mamaye ko ina bame ganin wani a ciki.

Gaba daya guri ya sake rikicewa da ihu dan kina tsaye sedai kiji an wafce miki jaka
nan aka shiga turereniyar fita ana faduwa duk wadda kuwa ta fadi sunanta sorry dan
taketa za’ayi ana neman hanyar tsira a garin haka aka dungure mata Tv ta fado qas
tim Centre table kuwa daman tuni ya karbi rabonsa se fatan kar wani ya taka kwalba
a garin gudu.

Wata qara me kama da rugugin tsawa a ka fasa kafin sukaji faduwar abu tim a qasa,
sabon gudu ne ya falle ga duhu ba wanda yasan takamaiman ina yake dosa aka ringa
gwabza karo ana faduwa kuwa kafin kace me anyi wada wada da kayan palour Amirah,
Seda aka kwashi a qallah minti goma se ga haske ya dawo ai kan kace kwabo wayam sun
fice daga palour an dawo tsakar gida kowa tayi cirko cirko fuskokin mata jagejage
da hawaye wannan Suna ko jaraba?

Addah data ja qafa da niyyar gudu itama caraf aka riqeta cikin abinda befi sakan
uku ba ta saki fitsarin tsoro ganin sunyi ido hudu da Hajia Mariya dake yashe a
qasa da ko ba’a gaya mata ba tasan riqaqqun iskokanta ne suka tashi. Tun da tace an
sace motar nan abinda take taraddadi kenan dan indai ranta ya baci se sunzo kuma
Al’amarin bazeyiwa kowa kyau ba dan Aljanunta basu da mutunchi yanzu basuqi suyiwa
kowa na gidan sunan nan bulala dari dari ba.

Sake yunqurawa tayi da niyyar gudu Mariya ta miqe cikin muryar yara tace mata
“Addah fatu muje washan goyo ja’ayi yau kowa seya goya ni in ba haka ba nayi masha
buyayay goma ke zaki faya kuma”

“Quuuu” cikin Addah ya bada qara, yo ai badanba gara bulalar akan tace a goyata.
Ita kadai ma Hajia Mariya ba kadan bace qaruwar mace ce ta gaske bare idan wannan
yar Aljanar tata tazo me son goyo seta Allah in kuma bakayi ba kaci na jaki. Addah
naji tana gani ta tasata a gaba suka fito inda Jama’a sukayi cirko cirko ta dane
bayanta kuwa.

Zanso kuga idon Addah haka ta goya hajia Mariya tana nishi kamar zata mutu ta kaita
ta dawo da ita amma taqi sauka tace se an sake haka ta kuma sahu daya da ita sukaje
suka dawo sannan ta sauka. Zaba ta ringayi wanda ze goyata in ka tsaya gardama
sedai kaji dundu kamar an buga maka guduma kuma in ta hau marasa qarfi suka fadi
nan ma ta hau tamola da mutum aifa gida ya sakw zama kamar gidan Allura se kuka ake
wannan jaraba har ina.

Aliyu dake cikin dan dakin da Change over da Solar su ta gidan yake ya kwashe da
dariya har yana kaiwa qasa. A kan idonsa komai yake gudana dama jira yake gari ya
qara duhu ya kashe haske ya qara musu tension akan wanda suke ciki gashi kuwa yayi
ga kuma sabon show an samu kai amma fa abu yayi kyau kuma yaji dadi, fitowa yayi ya
wuce part dinsu, knocking biyu Jafar ya bude masa ya shiga yana Dariya.

Asma’u dake zaune akan kujerar Dining suna waya da Yaya Bilkisu ta gayavmata su
Farida suna can Naziru ya kaisu ta dago ta kalleshi, tun ma kafin tayi magana yace
“Mami kinga yan suna kuwa ga wata can tana Aljanu tace se sun goyata kowa
takalminta a hannu lipstick duk ya goge”.

Duk yanda taso dakewa tayi masa fada kasawa tayi ta fashe da dariya dan tana hango
harabar gidan dan tarwai yake da hasken fitulun da aka zagaye shi dasu, saboda ma
taga komai dakyau yasa ta dage labulaye suka rage hasken fitulun palour duk drama
da akeyi akan idonta ne tana ganin haske ya dauke kuwa jikinta ya bata Aliyu ne dan
ta san aikinsa ne kashe wutakuma dazu ta ganshi a zaune a qofar power room din
magana ce kawai bata masa ba ta wuce.

“Allah ya shiryeka, kar naga ka sake fita in ba haka ba ranka ze baci” ta fada tana
miqewa.
“Sunan wani film waishi daga murna” ta fada tana shiga kitchen dariya fal ranta,
Yogurt ta dauka da cups biyu ta koma dakinta inda ta bar Rahma tana sallar Isha
tunda yaranta sun samu mafaka ai shikenan ita kam.

Abuubuwa sun sake rikicewa Addah ido ya raina fata, data san haka ce zata faru kuma
da bata kulle qofar ba gara tabar kowa ta tafi gidan ta idan yaso tayi Allah ya isa
amma gashi yanzu an bata goma daya bata gyaru ba. Dakyar ta samu ta zillewa yar
zulai Aljanar Hajia Mariya tayi bayan gidan gashi ta Rasa wanda ze kira mata Dada
dan ita kadaice kuma madafarta a yanzu idan ma ba’a san wandaya kullo su ba ita
zata iya nemo wanda ze zo ya buge kwadon amma wannan garqamewa da akayi musu idan
wuta ta tashi fa Allah ya kiyaye subi ina su fita?

To kuma kiran Dadar ma ba hali dan an sace waya kuma tasan babu me bata aron tasa
idan ma an bata ita ba haddace Number ta tayi ba, dabara ce ta fado mata arai, bari
taje gurin Ma’u ta kira mata Bashir ai shine me gida dukma tsiyar da za’ayi sudai a
bude su tukunna jama’ar data tara su tafi wannan bala’in ya ragu dan dai kam taga
suna yau ganin idonta bakuma ta fata Allah ya sake maimaita mata irin wannan taron.
Sadadawa tayi ta faki ido ta zagaya ta kofar kitchen din Ma’u.

Kamar zata balla qofa haka ta ringa doka musu bugu tanayi tana wai waye gudun kar
wani ya ganita Har Jafar ze bude Aliyu ya riqo shi yana cewa “kai baka da hankali
ko to jeka bude musu baka san me yake faruwa a gidan nan bane” se Jafar din ya fasa
amma be zauna ba ya tafi ya gayawa Ma’u.

Ta yar hudar jikin qofar ta hango Addah fuska tayi qozai qozai abunka da fara
daurin da aka dandasa mata dazu yayi ta kansa ga kunnenta daya da dan kunne daya
babu ta tabbatar bata ma lura da hakan ba. Bude mata qofar tayi tana shigowa kuwa
takai qasa tana rushewa da kuka kamar qaramar yarinya.

Kiyiwa Allah Asama’u ki kira Bashir azo a budewa mutanen nan qofa su fita kafin su
kashe ni nidai nayi dana sanin wannan qaddararren taron suna ashe rabon wahala ne
yasa muka nace se munyi” ta sake rushewa da kuka harda sheshsheqa.

Ba qaramin dauriya Ma’u tayi ta riqe dariyarta ba amma dukda haka da Addah a
hayyacinta take seta gane dariya take mata tace “toh Addah meya faru kuma ni da
naji shiru an dena kida ma na zata kun tashi ne.
Wayar Baban Aliyu kuwa a kashe take fa dan na kirashi tun dasu naji amma bari na
same kira ko yanzu ya kunnata” ta fada tana danna wayar ta lalubi Number sa ta
danna kira, kai kodan ta sake kunno musu shi idan be sani ba ai yasa ta kirashi
sedai kamar dazu data kira ce mata akayi a kashe take.

“Wallahi Addah a kashe take” ta fada tana janye wayar a kunnenta
“Kiramun Nafi dan Allah ita ta samo mana wanda ze bude mu” Addah ta katseta seta
maida akalar kiranta kan Dada itama seda ta mata kira biyu sannan ta daga ba tareda
ta yi magana ba ta miqawa da Addah wayar ta karba tana rushewa da Dadan da kuka.

“Nafi na shiga uku na hada taron masifa da Bala’i yau ki taimake ni yar uwata ki
kawomun dauki” Addah ta fada cikin matsanancin kuka. Dada da harta kwanta dan cikin
ikon babu wand aya kirata ya gaya mata wannan Al’amari dan yayanta da sukaje suna
bayanda Asma’u da Amirah suka gwanya musu rashin M fushi sukayi suka bar gidan,
ragowan dangin da suke can kuwa tunanin su kirata be zo musu ba koda yake rabi da
kwatan yan suna an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login