Showing 60001 words to 63000 words out of 238465 words

Chapter 21 - Wata Kishiyar by Maryamah Mrs AM

suka shiga da kayan shida me Uber daya kawo shi.

Dole na fasa kwanciyar na shiga ware komai ina saka shi gurinsa kafin na gama har
uku tayi dan ban nemo yan tayi ba ganin sun gaji yasa na barsu su huta. Bayan na
gama na shiga dakina, zama nayi akan gadon ina miqa Kafin na dan kishingida ina
duba waya ganin da sauran kusan 30 mins kafin ayi la’asar yasa na kwanta wai in dan
matse ban tashi farkawa ba kuwa se qarfe biyar harda rabi na yamma na miqe ina
salati ganin irin baccin da nayi, anyi la’asar tun tuni ga Bashir nasan yana dab da
gida yanzu kuma Azumi yake.

Alwala na farayi nayi sallar bayan na idar na shiga wanka. Ban wani jima ba ina
fitowa na shafa mai sama sama na goga yar hoda da kwalli se lip balm kafin na fesa
turare, doguwar riga na saka ta wani plain material Silk Dark green an masa dinkin
kamar Jallabiyar qirar Turkey babu adon komai a jiki se maballai da aka jera a
jikin wuta zuwa qirji guda uku da kuma bakin hannu. Mayafin ta na yafa a kaina
wanda be kai kalar rigar duhu ba na zura flat shoe baqi na fito da wayata a hannu
ina tunanin me zan dora masa mara wahala da zan gama da wuri.

“Mamina” Ahmad ya fada yana rungumeni, se na janye shi gefe ina cewa “Ina zuwa
Ahmad Abbi ya kusa dawowa gashi ban masa abin buda baki ba” ai ban qarasa rufe
bakina ba naji tsayuwar motar da nake da tabbacin tasa ce a qofar gida. Kitchen din
na fada da sauri a rainaina cewa “shikenan yau an bani”dan Bashir baya wasa da
abinci. Idan yayi azumi yafison kafin asha ruwa an gama jere masa komai a gabansa
yanda bama ze jira komai ba.

Da niyyar dafa masa tea in soya kwai na shiga in yaso kafin yaje sallah ya dawo ko
couscous ne na turara masa, nasan dakyar idan yaran nan sun ci farfesun kayan cikin
da Anty ta kawo dazun ba tunda ba son shi suke ba se in hada masa ya qarata, mita
ce dai nasan sena sha ta yau dan babu ruwansa baze duba irin aikin da muka sha a
gidan ko gajia ba tunda kawai nasan yana azumi dole na tanadar masa abincin.

Amna da Farida na tarar Amna na kwashe dankali daga mai Ita kuma Faridan na yanka
Fruits a bowl, suka kalleni a tare suna murmushi “Mami kinsha bacci, naga yamma
tayi nace bari mu hadawa Abbi kayan shan ruwa” Amna ta fada tana kashe Gas din
bayan ta qarasa kwashe dankalin.

“Allah dai yayi muku albarka, na manta shaf ma kuna gida ai” na fada ina qarasawa
kan Island inda suka ajiye kwanukan da aka zuzzuba abincin na bude na farkon.

Farar shinkafa ce se ganyen parsley da aka yi garnishing na maida murfin ina cewa
“Aa su Chef Amna harda wani ganye ganye aka zubawa Umfafar. Farida ta miqomun spoon
tana cewa “Mami ci sauce din kiji ni nayi ko Yah Amna”.

Na karba na bude kwanon miyar, sauce din hanta da qoda sukayi se qamshi take na kai
baki dadin ya ratsani, se na ajiye spoon din, “dagaske ita tayi Amna”
“Ita tayi Mami kawai gaya mata yanda zatayi nake se kuma na bata measurement na
komai” Amnan ta fada.

Lallai ashe mun samu sabuwar chef, Yayi dadi sosai amma karki fadawa Abbi ki bari
se ya gama ci tukunna”. Ina rufe baki Bashir ya shigo kitchen din, Farida ta ajiye
wuqar hannunta ta nufeshi tana masa oyoyo.

“Me kike a Kitchen Farida da wuqa a hannunki bana hana ba” ya fada yana kallon
fuskarta, ssannu da zuwa nayi masa ba tareda na amsa tambayar tasa ba dan dani yake
ba Farida ba. Ledar hannunsa ya miqo Amna ta karba yace “ki sake warming nasa” ya
juya suka fita yaja riqe da hannun Farida.

Fruit Salad din na qara sa hadawa, muka fito da kayan dukka muka jera a Dining
lokacin har an fara kiran sallah. Dabino na koma na dakko masa da ruwa mara sanyi
na ajiye akan stool din gefen kujera sannan na zubo fruits din a dan qaramin bowl
na ajiye daidai sanda ya fito daga dakinsa da alama alwala yayi.

Ina kitchen ina hada kayan da zan soya masa kwai suka fita masallaci dan shi bazaki
soya kwai ki ajiye masa ba ya fiso daga kasko se farantinsa. Kayan cikin na dumama
na fito da Balangun da Amna ta saka a Oven shima na juye masa a bowl a raina ina
jinjina qaunar Bashir da nama. Seda na soya kwan bayan sun dawo na ajiye masa komai
sannan na shiga dakina na barshi da yaran suna tayashi shan ruwa.
Dana idar da sallah ma ban fito ba, miqewa nayi ina chat da yan uwa da abokan
arziqi har aka yi Isha. Ji nayi ana kwankwasa qofa. Aliyune, bayan ya shigo yace
“Abbi yana kiranki”
Da “toh” na amsa na miqe ya qara powder da turare na yafa mayafi na na fita.

Suna zaune a kan kujerun Palour sun cika ko ina, “ikon Allah wai duk bataliyar nan
yayan Ma’une” na raya a raina kawai na tuntsyre da dariya se suka juyo dukka suna
kallona.

“Lafiya kike dariya” Bashir ya tambayeni, seda na zauna a kusada shi kafin nace
“ganin yaran nan nayi da yawa nake mamakin wai duk nawa ne”.

“Da sauran wasu ma a gaba ai” ya fada yana kallona da wani kalar expression,
kallonsa nayi nima har sannan fuskarsa bata koma daidai ba da sauran alamun damuwa
da bacin rai akanta nace “Aa ni ai na gama, na barwa yan baya gashinan sun fara ai”
harya bude baki zeyi magana wayarsa tayi qara, Dr Hadi ne pediatrist din da yake
kula da Iman. Daga wayar yayi bayan ya miqe ya shige dakinsa nima sena tashi na
qarasa kan Dining na debi abinci.

Ina ci muna yar hira da yara, ina kammalawa suka kwashe komai aka kai Kitchen muka
tattare palour qal dan kusan komai da dare mukeyinsa daman saboda fitar safiya muna
gamawa nace suje su kwanta gobe akwai school.

Dakina na koma na sake wanka na shirya tsaf na tafi dakin Bashir, yana kwance rabin
jikinsa akan Gadon qafafunsa kuma a qasa ya harde hannu a qirji yana kallon sama da
alama tunani yake. Banajin yaji shigata har seda na ajiye wayata da Zoben dana zare
daga hannuna akan Bedside sukayi qara sannan ya dago a dan zabure.

“Yadai?” Na tambayeshi se ya girgiza mun kai alamar babu komai kafin ya miqe ya
shiga toilet. Ina shafa addua ta ya fito daga toilet din daure da towel a qugunsa,
kallonsa nayi sam bazakace Bashir ya fara jiyo qamshin Hamsin ba saboda kyan
jikinsa, a tsarin halitta befi ka bashi shekaru 35 zuwa 37 ba amma a zahiri
shekarunsa 45 ne.

Har ya shafa mai ya saka kayan bacci riga da wando light blue ina zaune ina kallon
sa, yanda yake abubuwa a sabule kamar mara laka harya gama ya kashe fitilar tareda
hawa kan Gadon ya janyoni jikinsa ya dora kansa akan qirjina mukayi shiru bakajin
komai se qarar Ac a dakin, kusan minti goma a zatona ma bacci yayi naji ya riqo
hannuna sosai yana cewa “bana so na rasa ta”.

“Qum” naji kaman an jefeni da dutse dan a sukwane zuciyata Amirah ta kawo mun sedai
kafin nayi magana naji ya sake cewa “bana son na rasa Iman Ma’u, ina son yarinyar
kwatankwacin yanda nake son Farida, na dade inawa Farida fatan ta samu yar uwa se
yanzu Allah ya bata gashi ina neman rasata”.

Wato wani sanyi naji a raina, sena gyara kwanciya ta ina cewa “ba abinda ze faru da
izinin Allah zata tashi, naga jikin ai da sauqi jiya da muka je koh?”

“Eh da sauqi sosai, yanzu ma kiran da Dr yamun su naso su sallameta ne” ya fada
yana tashi zaune sosai.

“Kai masha Allah, Allah ya qara lafiya” na fada ina gyara kwanciya harda jan bargo
a zatona maganar ta qare sejin Bashir nayi yana wani soki burutsu

“Idan an sallamota ina so zan kawo ta nan” ya fada. Naji ba wai banji shi ba amma
son na tabbatar da ma’anar maganar tasa yasa na dago na kalleshi kafin nace
“Ban gane me kake nufi ba zaka kawo ta nan, Amiran nan zasu dawo ne ban sani ba?”
“Aa ba Amirah ce zata dawo ba Iman nake nufi zan kawo miki ki riqeta na bar miki
ita”.

“Ikon Allah” na fada a fili kafin na tashi zaune sosai na ina kallonsa,
“Ka kawota nan fa kace Baban Ali jaririyar da ko wata bata cika a duniya ba, me ya
samu ita Amiran da bazata iya riqe yarta ba. To ai ko mutuwa tayi tunda tana da uwa
a raye zata karbeta bare da ranta ace za’a raba ta da yar data sha wahala kafin ta
sameta ah gaskiya kaima baka zo da maslaha ba”.

Kallona yake har na kai qarshen maganar, nayi zaton ze balbaleni da masifa ne yace
seya kawo yarinyar amma aka sin haka sema wani marairaicewa daya sakeyi ya kamo
hannuna yana cewa

“Kin fita cancanta daki tarbiyyantar mun da yaya, sam waccen yarinyar bata da
tunanin da zata iya kula da kanta ma bare wani. Kina gani bataji tausayin yarinyar
ba suka jaza mata wahala bana tunanin zata iya rainon yarinyar”.

Sakato nayi ina ji da ganin ikon Allah rainin hankali da tsakar dare, ace ta haifi
amma bazata iya kula da ita ba ni ga jakar Ÿaÿa shine za’a dakko wata bakwaini a
kawo mun lallai zanga uban da ya isa kuwa. Fizge hannuna nayi na kwanta tareda juya
masa baya nace

“Ai Kowa ma be iya ba daga baya ya koya itama a hankali zata iya tunda babu wanda
baya son dan sa” naja bargo na rufe har kaina. Shiru naji har kusan minti goma beyi
magana ba be kwanta ba nima ban sake motsawa ba tun ina mita a raina har bacci yai
gaba dani amma ahu daya na qudurce wallahi ko sama da qasa zata hade bazan zamar
masa yar raino ba.
Ban kuka ga uban daya isa ya saka na karbi yarinyar ba.

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 24


Gombe
Bayan Naziru ya kaimu Airport kai tsaye kasuwa ya wuce ya siyi duk abinda Bashir ya
gaya masa ya kaiwa Amirah. Tana zaune a palour bayan ta gama kukan ta yai sallama
ta amsa fuska a kumbure be kulata ba ya shiga kwaso kayan da taimakon Almajiran
daya kira suka shigar mata da su Kitchen.

Har ya gama bata ko sake kallonsa ba dan haushin sa takeji tasan shi yake qara zuga
Bashir din ma akan komai, seda ya kai qofa ta tuna da zancen waya seta miqe da
sauri tabi bayansa tana kwalla masa kira ya kuwa shareta kamar beji ba seda yaje
gurin mota tana biye dashi.

“Meye kike bina kamar naci miki Bashi” ya fada yana harararta, inda haka kawai ne
seta rama amma tunda abu take nema seta karyar da kai tana cewa “Dan Allah Yaya
Naziru waya zaka siyo mun da layi”.
Seda ya harareta kafin yace “waya? Me zakiyi da waya ina taki?”

“An sace” ta bashi amsa kai tsaye.
“Toh ai shikenan gara da aka sace, kuma ni sa’an kine ko dan aikenki da zan siyo
miki waya ke baki da qafa ko baki san inda ake siyarwa ba” Nazirun ya fada. Seta
marairai ce tana cewa

“Dan Allah ka taimaka mun Yaya”. Kwafa yayi kafin yace

“Kawo kudin toh badan halin ki ba”

“Nagode” ta fada kafin ta qirgo dubu biyar da dari biyar ta bashi, ya karba ya irga
ya kalleta yace

“Saboda a gidan ku ake qera wa ko waye ze siyar miki da wayar dubu biyar”

“Yaya Tecno fa me keypad ai bata wuce haka ba”

“To se kije ki siyo kin tsaya kina batamun lokaci” ya fada yana miqa mata kudin,
setayi saurin dakatar dashi tana cewa “yi haquri dan Allah nawa ce se na ciki”

“Dubu goma ce sannan ki bada dubu biyu kudin mai tunda babu siyo miki waya a
lissafin da aka mun. Ba yanda ta iya tana ji tana gani ta zare dubu goma sha biyu
da dari biyar ta bashi ya tafi, idan da abun nata da mutunchi tasan a kyauta ma
siyo mata zeyi amma yanda tasan yana jin haushinta ma tayi mamakin da yayi saurin
karbar aiken.

Ciki ta koma ta tafasa ruwan zafi ta dakko kayan Tea a siyayyar da ya yo mata harda
bread ta zauna ta karya, tana zaune a gurin ya dawo ya miqa mata leda da kwalin
wayar a ciki da layi harda katin dubu daya ta karba tayi godiya harya juya ta kuma
tsaida shi tana cewa

“Dan girman Allah yaya ka roqar mun Yaya Bashir ya bari naje na ga Iman kaga fa tun
da aka kaita Asibiti banje ba”.

Wani banzan kallo ya mata kafin yace “karki rainamun hankali dan kin ga na biye
miki malama, dacan baki san tana Asibitin ba se yau? To bari kiji ya gayamun
sharadin daya gindaya miki kuma wallahi na baza CIDs a layin nan ki sake ki fita
dan nasan ba tunani ne dake ba tsaf za’a iya zugaki ace ki fita ai be sani ba kinga
kuwa auranki ya mutu” yana gama fada ya juya ya fice yabar Amirah da baqin ciki ya
cika mata ciki kamar tayi bindiga.

Dakinta ta shiga tana duba wani littafi da ta kwafe numbobinta a lokacin Ummi nata
mata iskanci wai rashin aikin yi me sa hauka gashi yanzu ze mata rana. A garin
neman littafin ta samo tsohon layin ta da ba sosai take amfani dashi ba, da murna
ta saka tana Addu’a Allah yasa basu kulle shi ba ai kuwa tana gwada kira ya tafi
amma babu kati seta loda katindaya siyo mata ranta fes ta samu numbobin harma da
wasu masu amfani da bata dasu a wancan layin.

Ummi ta kira ta hadata da Addah, tiryantiryan Addah ta bata labarin yanda akayi
anje an siyar da gida miliyan uku da dubu dari shida, an biya me Gwal kudinta
Miliyan Daya da dubu dari tawkas da Arba’in dan seda ta kawo resit din sarqar aka
je da warin dan kunne gurin masu gwal suka fadi nawa gram din sa yake sannan aka
buga lissafi a gurin aka siyar da warin ma aka bawa Addah kudin.

Ragowar masu bashi ma tas seda Alhaji ya cire wa kowa aka biya dan abinda yai saura
kuma ya riqe a hannun sa yace ze saka mata a kasuwa, ta qarasa tana cewa “Nayi
baqin ciki amma dai hankali na ya kwanta da yanzu qila ina firzin, yanzu idan an
kwana biyu kuma se muga yanda za’ayi ki maida abubuwan da aka lalata miki yanzu dai
ki kwantar da kai ku shirya da Bashir dan a jikinsa zaki samu ni kuma zan nemo mana
hanyar da zamu bi ta qarqashin qasa a samu komai daidai ba matsala”.

Sallama sukayi Addah na gaya mata kartazo gida yanzu ta bari se an kwana biyu
tukunna se a sannan ta gaya mata yanda sukayi da Bashir.

“Ki rabu dashi, lambo zamu musu dagashi har uban naki zan nemo mana inda za’a tasar
mana kansu dan shi kansa Alhajin shi ya siyi gidan sena san yanda na dawo da abuna
amma yanzu muyi luf tukunna, zan turo miki Ummi seta taya ki zama. Waccen Magen yar
kuma gara ki barta a Asibitin ma in aka dawo miki da ita qarin wahala ne” .
Da haka sukayi sallama ta dan ji dama dama tunda an kashe waccen babbar wutar.

LAGOS

Kusan kwanan zaune Bashir yayi dan farkawata biyu ina ganinsa ido biyu yana faman
tunanin da ban san koh na menene ba, yo ina dalili haka kawai ze saka kansa a
damuwa akan abinda yasan bame yuwuwa bane ba ma. Ko masallaci basu fita ba a gida
sukayi sallah yana idarwa kuma ya koma ya kwanta, ganin haka yasa na fita na fara
hadawa yara abin kari su kuma suna shirin makaranta.

Indomie na soya musu dan har na dakko doya Abdallah yace bazasu ci ba sauran ma
suka amsa Aliyu daya baya cin soyayyar Indomin na soya masa kwai ya hada da Bread
suka karya. Har suka gama ba Bashir ba labarin sa, se na miqe na shiga dakin dan in
gaya masa sun shirya fa.

Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu biyu na shiga.
“Baban Ali lafiya dai baka shirya ba ga yara can suna jiranka” na fada ina zama a
gefensa. Beyi magana ba ya tashi ya shiga Toilet minti kadan ya fito yana goge
hannunsa da qaramin Towel, Rigar jikinsa ya cire ya dora Jallabiyya akan dogon
wandon sannan ya dauki key da wayar sa ya fita yana cewa “kiyimun kunun gyada da
kosai” ya sa kai ya fice.

“Ko ba kunun gyada da qosai” na fada a fili ina hararar qofar daya fita, gadon na
shiga gyarawa, babu dattin komai a dakin dan haka na dauke robobin ruwan da muka
sha da dare na fita dasu. Seda na jiqa wake wanda daman bayarwa nake da yawa a
gyara a surfa mun se a shanya shi ya bushe idan na tashi amfani kawai jiqawa nake
na markada. Na debi gyada da farar shinkafa suma na jiqa.

Palour na koma na gyara palour da Dining din tsaf na kunna turaren sannan na shiga
wanka. Riga da Zani na saka na Atamfa na kashe dauri jelar kitson da aka mun two
step sun zubo kan bayana. Juyi nayi a gaba mudubin nida kaina na burge kaina bare
kuma Bashir ya ganni dukda ba cewa zeyi nayi kyau ba amma nasan har ransa ze yaba
ai.

Seda na markada gyada da shinkafar na saka danyar citta da kanumfari dan kadan dan
kar yayi baqi sannan sake wanke blander na zuba waken na markada shi da attaruhu da
Albasa se yar tafarnuwa. Kunun na fara damawa bayan yayi kauri na zuba ruwan lemon
tsami yayi fari tas gwanin sha’awa na juye a Flask ragowar kuma na zuba a Wani
qaramin flask din da niyyar na kaiwa Anty idan na gama.

Ina ajiye Flask din kunun akan Dining Bashir ya shigo da sallama ciki ciki na amsa
ina kallonsa tareda yi masa sannu da zuwa.
“Yanzu zakaci na siya qosan?” Na tambaye shi, se ya girgiza mun kai yana cewa bari
nayi wanka tukunna ya shiga daki na bi bayansa.

Seda ya fara shafa mai bayan yayi wankan na fita na dora ma suya na yanka Albasa
sannan na shiga buga qullina sosai bayan na saka kwai guda daya saboda ya qarawa
qosan laushi, gishiri na saka da daskomiya dan kadan se Albasa dana yanka qanana na
shiga suyar qosan, gaba daya kasko biyu da dan kadan nayi dan bashi da yawa, ina
kwashe na qarshen na jiyo shi yana kira na sena kashe wutar na juye a Bowl na dakko
na fita palour.

Yana zaune a Dining din ya saka Jeans blue da Farar Short sleeve a gabanta an
rubuta “HANDSOME” na kalleshi da murmushi nace “handsome indeed”. Murmushin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login