Showing 153001 words to 156000 words out of 238465 words
fuskata tsaf kafin na kulle motar na fito ina gyara zaman
gyalena a kafada daya, cikin takun yauqi da yanga na qarasa inda su Bashir suke ina
jin yanda idon mutane yayi mun caa a raina na shiga karanta 'A'uthubikalimatillahi
tammat min kulli shaydanin wa hammatin wa min kulli aynin lammati' saboda mugun ido
haka na qarasa inda suke kallo daya nayiwa Bashir daya watso mun idanunsa da suka
fara rinewa da bacin rai nan take na dauke kaina ina murmushin qeta.
A saitinsa na tsaya fuskata dauke da murmushi na gaishe shi, be amsa ba se matsowa
da yayi bayan ya saki hannun Amirah da tunda ta ganni ta shaqa tayi fam se wani
harare harare takeyi kuma dai baze wuce tsabar hassada da baqin cikin gani na bane
ya saka. A daidai kunnena ya tsaya idonsa akan fuskata yace
"Meye kike yi haka Ma'u baki kalli kanki a mudubi ba da zaki fito a haka cikin
wannan kwalliyar? Jifa yanda maza suke kallonki dan Allah ki koma nasan bazaki rasa
Hijab ko Abaya a mota ba ki saka".
Wata siririyar dariya nayi kafin nayi qasa nima da murya yanda shi kadai ze ji
abinda na fada nace masa
"Ai daman saboda mazan su kalleni nayi, ko ka manta a kasuwa nake yanzu ne?"
Ina fadar haka na janye daga kusa dashi ina ji ya na kira sunana amma nayi kamar ma
banji ba, katinan hannuna na fara bawa yaran da akwai table Number dan haka sukayi
gaba, na miqawa Anty nata na miqawa Bashir daya sannan na juya ina cewa Anty
"Muje toh, Baban Ali seka shigo koh" nayi gaba abuna dan ban nuna nasan da wanzuwar
wata halitta ma a kusa dashi ba, hannuna ya riqo da sauri na waiwaya na watsa masa
wani mugun kallo da ni kaina bansan na iya shi ba, se yayi saurin sakina yana cewa
"Yi haquri amma dan Allah kije ki.."
"Karka sake mun haka, da mutunchi na kazo kana kamani a gaban mutane bana so,
sannan baka da hurumin da zaka gaya mun abinda zanyi yanzu ko wanda zan bari ka
gane" na fada ina qara daure fuska.
Ina kallo ya hadiye wani abu qut kafin ya marairaice fuska ya sake cewa
"Nace kiyi haquri ai, naga kati daya kika bani ina na Amirah?"
Juyawa nayi na kalli Amiran da ya ce se numfarfashi takeyi kamar wadda zata haihu
na maida idona kansa nace masa
"Na iya wadanda aka gayyata kenan, bama buqatar qarin gayyar sodi" ina gama fada na
bi bayan Anty da ta dade dayin gaba daman.
Bansan yanda suka qare ba, munfi kusan minti sha biyar da shiga kafin na hango su
sun shigo Amirah na bayansa fuskar nan kamar ka tsira mata Tsinke ta fashe tsabar
yanda ta kumbura, acan kejerun yan regular naga ya sama mata sit ta zauna, ya dan
duqa da alama magana yake gaya mata kafin a fusace naga ya taho inda muke zaune.
Na zata masifa ze zo yayi na qara tamke fuska ta tsaf se naga yana zuwa yaja
kujerar da tayi saura ya zauna ya gaida Anty ta amsa masa sama sama nidai na mayar
da hankali kan cultural dance da akeyi ina jin yanda idon Bashir yake kaina amma
naqi kallon barin da yake.
Wayata dake ajiye akan teburin ce ta dauki qara, yanda kasan shi aka kira ya bi
wayar da kallo na kai hannu na dauka, Yusuf ne da nayiwa saving da Abban Takwara,
saboda qarar kida banajinsa dan haka na tashi nayi tacan baya gurin inda kujerun su
Amirah yake, ta kusa da ita na wuce ina giftawa naji ta saki tsaki ban kulata ba na
wuce na amsa wayata.
Gaya mun yayi yana waje nace ya jirani gani nan zuwa, na sake zuwa na wuceta dan
banida lokacin da zan tsaya ina kula wannan yarinyar. Seda na koma sit dina, jakata
na bude na ciro ragowar kati daya dan Ma'u Jafar ne ya dagata da yake ta sangarta
ta lankwashe a jikinsa yanda kasan wata yar Yaye dan haka basu karbi katin taba
muna shiga ya bani na saka a jaka.
Ina kallon yanda Bashir ya bini da kallo ganin na ciro wani katin daga jaka, se na
juya na cewa Anty ina zuwa na wuce ta saitin Bashir ya shaqi qamshij da nakeyi kuwa
kafin ya ajiye numfashi na wuce shi ina juya mazaunan da Allah ya hore mun shi kuwa
Ya bini da kallo da baki a sake har na qulewa ganinsa.
A qofar gurin naci karo da Yusuf, wani dace shaddar jikinsa yanda kasan tare muka
siya da kayan jikina sunyi bala'in dacewa.
Cikin mutuntaka muka gaisa da wani dana gansu tare babban mutum ne sosai wai shima
Sanata ne akwai yaransa biyu a yan Graduation din, ba'a ma karbi katinan mu ba muka
shiga tareda Yusuf din kai tsaye teburin da muke zaune na wuce gaba yana bina a
baya.
BASHIR
Tunda yaga Asma'u a gurin gaba daya ta sake kwance masa notin kai. Kwalliyar ta
tayi bala'in tafiya da imaninsa ga wani kishinta daya taso masa Ganin yanda maza
suke binta da kallo.
Tana bashi katin nan da ta juya haka ya rakata da ido gani yake kamar qara mata
quruciya akayi dirin jikinta ya sake fitowa, yana can aikin kallonta tsakin da
Amirah tayi ne ya dawo dashi hayyacinsa se ya kalleta sanda take cewa
"Yanzu kana kallo ta tafi bayan kaji abinda tace wato nice ma gayyar sodi ko kuma
kayi shiru baka ce komai ba"
"To so kikeyi na kamata da kokawa nace seta baki ko kuma nawa zan baki? Daman ai ba
gayyatarki ki akayi ba gayyar sodin kika zo.
Kinga ki kama kanki wallahi karki sake kice zakiyi mun shirme a gurin nan zan bata
miki rai" Bashir ya fada cikin bacin rai, wallahi da a Gombe nema tafiyarsa zeyi ya
barta idan yaso ta koma gida dan dai kawai nan bata san hanya bane.
Amirah data shaqa iya wuya, dakyar ta danne bacin ranta tace
"To yanzu a waje zaka barni ka shiga ciki kenan" ta fada kamar zatayi kuka
"Seki koma mota ki zauna dan dai ni ban san a inda zan samo miki kati ba kuma nan
ba irin taron da kika saba zuwa bane ko ba'a gayyace kuba ku shiga su komai a tsare
sukeyinsa" Bashir ya fada yana hararar ta, se kawai ta saka masa kuka tana cewa
"Da kasan wulaqanci zaka mun idan nazo tun a gida se kace bazaka dani ba amma yanzu
kace na tafi mota bayan ga katuna can a hannunta harda wasu daban ta gayyato se
nice baza'a bani ba"
Tsaki Bashir yayi ganin tana neman tara masa Jama'a dan har an fara kallon su yace
mata yana zuwa ya tafi Gurin securities din bakin gate.
Seda yaci wuya dakyar ya samo mata regular card shi kansa dubu goma aka siyar masa,
daya bata a maimakon ta gode seta hau sabon qorafi wai ba irin nasu bane dan ko a
kala katin ya banbanta.
Banza ya mata suka shiga ya rakata kujerarta se raba ido take ganin Jama'a kala
kala yanzu da wannan shagalin za'a mata buqulun zuwa tab, Allah ya kaimu Na Aliyu
wannan ai dan mijinta ne itama dole tana teburin gaba tunda yanzu ance mata gayyar
sodi.
Hakata zauna wani mugun kishi ga kyashi da hassadar Ma'u na dukanta. Duk abinda ta
gani a jikinta ji takeyi dama itace, simple lace me Azabar kyau ga zobuna da
awarwaron gwal suma qira mara hayaniya sun qara fito da kwalliyar ta sosai qarin
baqin cikinta yanda Bashir ya kasa dena kallon Ma'un ba daban ba da se tace su tafi
kawai amma ina setaga kwal uwar daka sannan idan sun koma gida se ayi uwar da
za'ayi.
BASHIR
Kwarewa yayi da ruwan da yake sha a daidai sanda Ma'u da Yusuf suka ratso dakin
taron kamar wasu shaqiqan masoya fuskokinsu dauke da murmushi. Ba Bashir kadai ba,
da yawa mutane seda suka bisu da kallo haka suka qarasa har teburin Yusuf ya daga
Ma'u qarama data fasa ihun murnar ganinsa ya zauna a gurin suna fuskantar juna da
Bashir.
Fuska a sake ya miqawa Bashir da yayi suman zaune hannu dukda can qasan zuciyarsa
bazeyi qarya ba daurewa kawai yayi amma sosai yake Adawa da Bashir din daya rabashi
da macen da yake so sama da kowace mace a rayuwarsa.
Ya wargaza masa mafarkin shimfida rayuwar aure me ciki da aminci da qauna qarshe ya
barshi da gantalewa da zama macen da bata dauki aure a bakin komai ba.
Malam Bashir kuwa bin hannun Yusuf yayi dake daure da wani shegen Agogon diamond a
tsintiyar hannunsa, kai Cufflinks dinsa kadai abin kallo ne wani irin tuquqin baqij
ciki da kishi suka taso suka shaqe masa wuya kawai ya mayar da kai gefe ba tareda
ya karbi musabahar ba, ko a jikin Yusuf ya maida hannun gurin su Aliyu duk suka
gaisa yana tambayar su sunayensu dan ko shine Bashir din akan Mace kamar Ma'u zeyi
abinda yafi haka shi yama ga qoqarin sa daya zauna teburi daya dashi ai
Gaisuwa me kyau sukayi da Anty Halima nan da nan suka shiga hira kamar sun san juna
dan shima akwai faran faran da mutane halinsu yazo daya dukda da ita da gayya ta
qara sakewa suke hirar saboda ta turawa Bashir takaici se gashi kuwa Hira ta barke
tsakanin Yusuf da sauran Yaran Ma'u qarama na qara maimaita masa sunayen su se
dariya suke mata dan bata iya fada ba ya kalli Asma'u yace
"Gaskiya kin iya bida yara kiga yanda yarinyar nan ta sake lokaci daya anya bazan
bar miki ita ba kuwa"
"Ai na yara kadai ba har manyan in gaya maka ta iya tafi dasu ta kowacce hanya me
sauqi ko me daci, ka bar mana ita kawai mun samu qarin ya" Anty ta fada tana dariya
ta gefe kuma tana hararar Bashir da ya kumbura dan har kamar yafi Amirah kumbura
yanzu.
Shigowar yan Graduation ce ta dakatar dasu daga hirar, nan da nan aka shiga gabatar
da abinda aka je yi, an raba musu kyututtuka sosai Amna ta samu lambobin Yabo dan
ita ta lashe Best Student ta shekarar aka kira Iyayenta, Ma'u na miqewa Bashir
shima ya tashi daga kan stage ta hango Amna na tsalle tana nuna mata bayanta tana
waiwayawa se ganin Alhaji Qarami tayi tareda Matarsa ta biyu da daya daga cikin
Yaransa Abdullahi da suke cewa Baffa.
A tsakiyar Mu nida da Bashir Amnan ta tsaya akayi mana hoto se wani washe baki yake
shi ala dole ga Baban Amnah, ganin Alhaji Qarami da Yah Muslim da shima bamu san da
zuwan sa ba sun qaraso gurin se Bashir ya dan matsa yana shafa kai amma Alhajin ya
sake mayar dashi gefen Amnan su kuma suka tsaya daga gefe da gefen mu aka sake
daukar hoton.
Haka sauran yaran dukka suka shiga akayi ta hotuna harda su da Anty. Hoto daya muka
dauka tare da Yusuf ya mana sallama ya fita saboda kiransa da akayi.
Amirah tana daga can qarshen tana hangomu baqin ciki kamar tayi bunga dan
securities ne ma suka tare hanya kar su yan regular su shiga gurin VIP.
Har kwalla seda tayi saboda baqin ciki, tana gani muka gama hotunanmu cikin farin
ciki muka sauka kowa ya koma mazaunin sa kafin taro ya koma na ciye ciye da
maqulashe.
Abubuwa ne gasu nan birjik se wanda kake so a ka ringa ajiyewa, ita kanta Amirah ba
qaramar gara aka ajiye mata ba amma saboda qalata idonta nakan teburin su Bashir
har seda ta kasa daurewa ta zaro wayar tavta rubuta masa text tace
"Yaya naga abincinku ba irin namu bane, ka rage mun zanci nima"
"Ai se kici idan ke mayya ce ko kuma daga yunwa kika fito" Bashir da ransa yayi
bala'in baci ya mayar mata da Amsa. Tsabar haushi gaba daya ma ta saka abincin ya
fita daga ransa ya ringa zabga tsaki su dai yan gurin ba wanda ya kulashi abincinsu
suke loda kawai.
Qarfe sha biyu taro ya tashi, bayan abincin da aka ci a ciki harda wani Take away
aka sake binsu dashi, Su Ma'u na tsaye aka kai mata nasu ta bude boot aka zuba Anty
ta kama baki tana cewa
"Duk wannan abincin da muka ci a ciki qara raba wani suke yi lallai se a gaishe su"
"Yo ba dole ba wannan uban kudade da suka caji iyaye banda contribution da suka
samu daga sauran mutane ai dole kiga sunyi bushasha" shiru nayi lokacin dana hango
Amirah na cacar baki da daya daga cikin rabon Abincin da alama hanata yayi se na
nunawa Anty gurin yanda kasan da Bashir nake shima ya bita da kallo.
A tsawace ya kira sunanta, se gata ta taho gurin tana qunquni, "haka kawai a komai
se an nuna banbanci bayan duk abu daya muka zo kuma"
Mudai gabada ya ma dauke kawunan mu gefe mukayi dariya na cina a zuciya, Allah ya
sauwaqawa wasu dai da shegen kwadayi suke.
Qarasowar Alhaji Qarami, Yah Muslim tasa na qara fadada murmushi na,
"Gashi bamu zo da mota ba, taxi muka hawo daga Airport yanzu kuma ina so na leqa
gurin Olabode nayi masa ta'aziyyar Matarsa kafin dare mu wuce nasan kema baki je ba
ko Asma'u" Yaya Muslim ya fada yana kallona, sena kama baki nace
"Wallahi Yaya na manta, bama wannan ba gidan ne bazan iya kai kaina nikadai ba
shiyasa Amma yanzu seka kwatanta mun zan samu lokaci naje kar yace seda kazo mukaje
tare".
Motata ya karba shida Alhaji Qarami suka shiga suka tafi dan shima akwai inda zeje,
Bashir ma tuni ya kwashi yaransa da Amaryarsa da take ta faman zumbure zumburen
hanata karbar take away da yayi ya rage saura Ni da Anty se Anty Hadiza Amaryar
Yaya da zamu wuce gidana tare da ita kafin su dawo dasu Amnah.
Guri muka samu muka zauna muna ci gaba da hira dan Amnah har sannan tana can suna
hotuna da qawayenta. Yusuf ne ya taho gurin yana cewa
"Aa baku tafi ba Ma'u? Ina sauran Yaran dasu Alhaji Tukur?"
"Sun wuce gida, Alhaji Qarami kuma sun fita da Yah Muslim, muma Amnah muke jira mu
tafi, ka ganta nan ma zuwa" na fada ina miqewa tsaye. Wayata na zaro ina cewa
"Bari na kira mana Uber muma mu wuce toh"
"Aa bari na sauke ku mana, nima naje mun gaisa da Family colleague dina na dazun
nan da kika gani" Yusuf ya fada, se muka bishi gaba daya zuwa gurin wata Arniyar
mota High Lander.
Duk suka shige baya harda su Amnah akan dole ni na shiga gaba muka kama hanyar gida
muna tafe Yusuf dasu Anty suna ta hira amma na kasa aka musu baki saboda duk se
nake jina a takure ko dan yanda duk sanda zan daga ido se naga yana kallona har
tsoro na fara ji kar muje ya zubar damu a haka dai muka qarasa gida lafiya.
Tundaga Nesa na hango Bashir a zaune akan motar sa ya zubawa hanyar shigowa layin
namu ido kamar me jiran wani abu, kamar da gayya ma naga Yusuf ya taka motar tayi
wata qara da take nuna lafiyar injinta kafin ya fizgeta ya cake a qofar gidana,
muna tsayawa wayata ta sulale qasa dan haka na duqa ina nemanta kafin na ganota har
su Anty sun fice daga motarya rage daga ni se shi a ciki.
Murfin motar na kama da niyyar budewa ina cewa "mungode, zaka dawo anjima tareda su
Yaya ne ko se kazo daukar takwara?"
Shiru yayi mun, sema gyara zamansa da yayi ya juyo gaba daya yana jifana da wani
irin sanyayyan kallo daya saka naji tsikar jikina sun fara tashi bashiri na sauke
kaina qasa ina ci gaba da kiciniya da qofa amma taqi buduwa.
"Kinyi kyau sosai Asmy, amma kamata yayi ace kwalliyar nan ido na ne kawai ze ganta
kuma ni kafai zan shaqi wannan ni'imtaccen wamshin naki. Bazan gaji da kallonki da
yiwa ubagijij daya halicceki tasbihi ba Asmy dan yayi miki suffar da a kallo kadan
take iya sanyaya zuciyar wanda yayi tozali dake, ina ma zan iya ci gaba da kallon
ki har qarshen rayuwata nasan bazan taba gajiya ba".
Jikina ne ya dauki rawa saboda yanda kalaman Yusuf suka shigeni, qara damqe wayata
da jakar hannuna nayi yanda kasan wata mara gaskiya nace "Ka bude mun qofar na fita
kaga..kaga"
"Mijinki yana kallon mu ko?" Ya fada yana gyara zamansa kafin yayi wata siririyar
dariya yaci gaba da cewa
"Idan na samu dama anjiman zan dawo idan kuma banzo ba may be Monday nazo na dauki
Ma'u m. Zadai muyi waya kawai" yana gama fada ya sun kuyo ta barin da nake ba shiri
na dauke numfashi ya kuwa kwashe da wata dariya ya dannan wani abu a jikin qofar
yana cewa
"Ke kika kulle kanki bude mini zanyi amma ji yanda gaba daya kika dauke wuta kamar
mara jini" nidai ban kulashi ba na kwashi qafata nayi waje, ina direwa kuwa da
sauri nayi baya na jingina da motar ganin Bashir a gabana da yana numfarfashi kamar
me cutar Asthma.
Yana shirin bude baki na gewaye shi na wuce ina hada hanya dan fa har sannan jikina
rawa yakeyi, daga bakin qofa na tsaya ina daidaita nutsuwa ta, sena waiwaya na
kalli inda na bar Bashir a tsaye na hango Yusuf ya sauke glass din wundo da alama
magana sukeyi.
na seda naja iska na fesar kafin na tura qofar na shiga dan a bude suka barta.
BASHIR
Har suka isa gida Amirah na zuba masa mita da qorafin an mata wulaqanci amma tafi
ki mutu be ce mata ba gaba daya hankali da tunaninsa suna kan Ma'u daya baro acan.
Yana tsayar da motar a qofar gida ya waiwaya yace mata
"Ki dauki nawa a Boot gashi can kici shikenan dai ko?"
"Ai ba shikenan ba, bayan ma duk lefinka ne. Da ka nuna inada daraja da qima a
matsayina na matarka ai komai nima zuwa za'ayi ana girmamani ayi mun amma fa ji
irin wulaqancin da kayi mun ka kama ka kaini can qarshen bango kamar wata mara
galihu ko hoto baka ce nazo ayi dani ba seka..."
"Kinga fita, ki wuce gida sauri nakeyi ni akwai inda zanje" ya fada a hankali can
qasan zuciyarsa yana qoqarin danne fushi da bacin ran da suke taso masa. Yaga
alamar ita bata gajiya da tashin hankali shi kuma a yanayin da yake ciki yanzu
nutsuwa yake da buqata bawai qarin wata damuwa ba.
Fitar tayi tana masa qunquni, shidai yaja motar yayi gaba. Niyya yayi ya koma ya
dauko su Ma'u tunda yaga ta bayar da motarta amma se yayi tunanin tazarar gurin
kafin ya isa qila sun samu abun hawa sun taho gida.
Yusuf ne ya fado masa arai kar dai ya zama shi ze dawo dasu, nan da nan kuwa yaji
kansa na neman yayi ciwo se kuma ya tuna da ai tun suna cikin Hall din Yusuf ya
tafi be tsaya an tashi dashi ba wannan tunanin ya dan kwantar masa